×
Littafine da mawallafinsa ya lissafo bayanai masu yawa na dabi’un maguzawa, wadanda tuni musulunci ya yi watsi da su kuma ya bayyana hatsarin da ke cikinsu a addinance da kuma duniyance, abinda yake da matukar muhimmanci kowanne musulmi ya sansu.

FASSARA LITTAFIN:

MASA'ILUL JAHILIYYAH.

(Munanan Dabi'un Maguzawa).

Wallafar:

Shaikhul Islam Muhammad bn Abdulwahhab.

Fassarar:

Aliyu Muhammad Sadisu.

(Hausa).

Gabatarwar Mai Fassara.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga ma'aikin Allah da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.

Bayan haka: Hakika wannan littafi yana da matukar falala da daraja da matsayi a zukatan al'ummar musulmi, wannan ko ya kasance ne lura da abinda littafin ya kunsa na wayar da kan al'umma da kuma fayyace hakkin Allah madaukakin sarki, musammamma a wannan lokaci na futuntunu da alfahari da dangi, da jiji-da-kai, da dogaro ga wanin Allah da yadda zukatan wasu suka karkata ga wanin Allah ta hanyar jahiltar Ubangiji ko kuma wadansu shubuhohi.

Mawallafin wannan littafi ya zayyano wadansu abubuwa kusan dari da ashirin da takwas (128), da suke halayene na maguzawa ko yahudawa ko kuma nasara. Abinda ya sa malam ya lissafosu dudda ba su Kenan ba, saboda kai musulmi ka nuisance su kuma ka gujesu ka nisantar da 'ya'yanka da iyalanka baki daya, domin ba ka da wata dabi'a ko al'ada sai wacce musulunci ya tabbatar maka da ita.

Idan akace 'Ahlul Jahiliyya' ana nufin dukkan al'ummar da take ba'akan ta farki na manzon Allah ba, komai ci gabansu kuma komai wayewarsu, kamar Yahudawa ko Nasara (Kiristoci) ko Maguzawa (duk wadanda ba yahudawaba ba kuma kiristociba) ko gargajiya, saboda haka da aka ce 'Masa'ilul Jahiliyyah' ana nufin wadansu halaye da dabi'u na 'Ahlul Jahiliyyah'.

Anan za ka ga wadansu dabi'un sun fi kama da na nasara ko kuma da na yahudu ko ma dana maguzawa, ko ma da na wa su ka yi kama baruwanka, kuma idan kana tare da wata to fa nan take ka bari domin gudun Kaman ceceniya da mai wannan dabi'a. Da fatan Allah ya tsare mu.

Tsarin gabatar da wannan aiki:

1. Za mu kawo takaitaccen tarihin mawallafin wannan littafi na 'Masa'ilul Jahilyyah'.

2. Za mu kawo gundarin bakin littafin da larabcinsa.

3. Sannan sai fassararshi.

Muna rokon Allah da sunayansa kyawawa da kuma siffofinsa madaukaka da ya yi mana jagora ya yi mana muwafaka, ya kuma sanya albarka a wannan aiki, ya anfanar da mu baki daya.

Mai fassara:

Aliyu Muhammad Sadisu.

Minna, Nigeria.

(aliyusadis@gmail.com)

Takaitaccan Tarihin Mawallafi.

Shi ne: Imam Muhammad dan Abdulwahhab dan Sulaiman dan Aliyu dan Muhammad dan Ahmad, daga kabilar Tamim. Ana mishi lakabi: Shehul Islam, Mujaddadi.

An haife shi a garin Uyaina dake arewa maso gabas da birni Riyadh, a shekara ta 1115, (bayan hijira), kuma anan ya tashi, a gidan na su da yake cike da ilimi da kuma kula.

Ya kammala haddace Alkur'ani mai girma alokacin shekarunsa na haihuwa ba su kai goma ba, a hannun mahaifinsa. Ya yi fice a fannoni da dama kamar Fikihu da Hadisi da Tauhidi da kumaTafsiri.

Ya yi tafiye-tafiye da dama domin neman ilimi, ya je birnin Makkah domin yin aikin hajji kuma ya yi anfani da wannan tafiya ya yi karatu awurin manyan malaman Makkah na wannan lokacin, kuma ya je birnin Madina ya kuma jima a wannan birni domin neman ilimi, haka nan kuma ya je kasar Iraki ya kuma jima a Basrah, ya kuma yi karatu a gaban malaman wannan gari, haka nan kuma ya je Ahsah, ya yi anfani da wadannan tafiye-tafiye domin neman ilimi da kuma isar da sakon Allah madaukakin sarki (wato Da'awah).

Ya yi karatu a gaban malamai da dama, ga kadan daga cikin su:

1. Mahaifinsa Shehun malami Abdulwahhab dan Sulaiman.

2. Shehun malami Shihabuddin Alkalin Basrah.

3. Shehun malami Abdullah dan Muhammad dan Abdulladif.

4. Shehun malami Muhammad dan Hayatu Sindi.

5. Shehun malami Abdullah dan Ibrahim dan Yusuf.

Haka kuma yana da dailibai masu tarin yawa, daga cikinsu akwai:

1. Shehun malami Ahmad dan Suwailim.

2. Shehun malami Aliyu dan Muhammad dan Abdulwahhab.

3. Shehun malami Abdurrahman dan Hasan dan Muhammad.

4. Shehun malami Imam Abdul'aziz dan Muhammad dan Sa'ud.

5. Shehun malami Husain dan Ganam.

Wannan shehun malami mawallafin wannan littafi ya karar da rayuwarsa ne wurin karantarwa da fadakarwa da kiran mutane akan su kasance a asalin karantarwar musulunci da Allah ya aiko manzan Shi da ita, akan haka ake kiran shi da mujaddadi, domin ya samu jama'a da yawa ana tafiya ne akan tatsunuyoyi da neman bukatu a kabarurruka da kiran matattu akan su kawo a gaji dadai sauran su.

Ya wallafa littafai da dama, daga cikin su akwai:

1. Takaitaccan Tarihin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), (Mukhtasaru Siratur Rasuli Sallallahu Alaihi wa sallam).

2. Munanan Dabi'un Maguzawa (Masa'ilul Jahiliyya).

3. Ladubban Tafiya Sallah (Aadabul Mashyi Ilas Salah).

4. Tushen Imani (Usulul Iman).

5. Ginshikai Uku. (Usulus Salasa).

6. Ka'idoji Hudu (Alkawa'idul Arba'ah).

7. Yaye Batutuwa Masu Rikitarwa (Kashfus Shubuhat).

8. Littafin Tauhidi (Kitabut Tauhid). Da wasu littafan masu tarin yawa.

Ya rasu a shekara ta: 1206. (bayan hijira), bayan ya shafe kusan shekaru (91), Allah ya ji kansa da gafara ya kuma rahamshe shi, in ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da Imani, amin.

[مُقَدِّمَةُ اَلْمُؤَلِّفِ]

بِسْمِ اَللهِ اَلرَّحْمَنِ اَلرَّحِيمِ

قَالَ اَلشَّيْخُ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اَلْوَهَّابِ رَحِمَهُ اَللهُ تَعَالَى:

هَذِهِ أُمُورٌ خَالَفَ فِيهَا رَسُولُ اَللهِ ﷺ‬ مَا عَلَيْهِ أَهْلُ اَلْجَاهِلِيَّةِ اَلْكِتَابِيِّينَ وَالأُمِّيِّينَ، مِمَّا لاَ غِنَى لِلْمُسْلِمِ عَنْ مَعْرِفَتِهَا.

فَالضِّدُ يُظْهِرُ حُسْنَهُ اَلضِّدُّ # وَبِضِدِّهَا تَتَبَيَّنُ اَلأَشْيَاءُ.

فَأَهَمُّ مَا فِيهَا وَأَشَدُّهَا خَطَرًا عَدَمُ إِيـمَانِ اَلْقَلْبِ بِمَا جَاءَ بِهِ اَلرَّسُولُ ﷺ‬ فَإِنِ اِنْضَافَ إِلَى ذَلِكَ اِسْتِحْسَانُ مَا عَلَيْهِ أَهْلُ اَلْجَاهِلِيَّةِ تَمَّتِ اَلْخَسَارَةُ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلبَطِلِ وَكَفَرُواْ بِٱللَّهِ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلخَسِرُونَ٥٢﴾ العنكبوت: ٥٢.

Gabatarwal Mawallafi.

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai.

Shaikh Muhammad dan Abdulwahhab Allah ya yi masa rahama ya ce:

Wadannan nan wadansu halayene da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya sabawa wadanda suke kan maguzanci yahudu da nasara dama 'yan gargajiya, abinda yake da matukar muhimmanci musulmi ya san su, wani abu kishiyarshi shi yake bayyanar da kyawunsa, abubuwa kishiyoyinsu ne suke bayyanar da kyawunsu.

Mafi girman abindake cikin wadan nan halaye kuma wacce ta fi kowacce hadari shine rashin Imani da zuciya bata yi ba da abin da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yazo da shi. Idan ko aka kara akan haka da ganin kyawun abinda su Ahlul Jahiyyah suke akai to kan an gama asara, kamar yadda Allah ya ce:

''Dukkanin wadanda suka yi Imani da karya kuma suka kafircewa Allah to wadan nan su ne asararru.'' (Suratul Ankabut, aya ta: 52).

اَلْمَسْأَلَةُ اَلأُولَى: أَنَّهُمْ يَتَعَبَّدُونَ بِإِشْرَاكِ اَلصَّالِحِينَ فِي دُعَاءِ اَللهِ وَعِبَادَتِهِ، يُرِيدُونَ شَفَاعَتَهُمْ عِنْدَ اَللهِ لِظَنِّهِمْ أَنَّ اَللهَ يُحِبُّ ذَلِكَ، وَأَنَّ اَلصَّالِحِينَ يُحِبُّونَهُ، كَمَا قَالَ تَعَالَى ﴿وَيَعبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَيَقُولُونَ هَؤُلَاءِ شُفَعَؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ ١٨﴾ يونس: ١٨، وَقَالَ تَعَالَى:﴿ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِ أَولِيَاءَ مَا نَعبُدُهُم إِلَّا لِيُقَرِّبُونَا إِلَى ٱللَّهِ زُلفَى ٣﴾ الزمر: ٣، وَهَذِهِ أَعْظَمُ مَسْأَلَةٍ خَالَفَهُمْ فِيهَا رَسُولُ اَللهِ ﷺ‬، فَأَتَى بِالإِخْلاَصِ، وَأَخْبَرَ أَنَّهُ دِينُ اَللهِ اَلَّذِي أَرْسَلَ بِهِ جَمِيعَ اَلرُّسُلِ، وَأَنَّهَ لاَ يَقْبَلُ مِنَ اَلأَعْمَالِ إِلاَّ اَلْخَالِصَ، وَأَخْبَرَ أَنَّ مَنْ فَعَلَ مَا اَسْتَحْسَنُواْ فَقَدْ حَرَّمَ اَللهُ عَلَيْهِ اَلْجَنَّةَ، وَمَأْوَاهُ اَلنَّارُ.

وَهَذِهِ هِيَ اَلْمَسْأَلَةُ اَلَّتِي تَفَرَّقَ اَلنَّاسُ لأَجْلِهَا بَيْنَ مُسْلِمٍ وَكَافِرٍ، وَعِنْدَهَا وَقَعَتِ اَلْعَدَاوَةُ، وَلأَجْلِهَا شُرِعَ اَلْجِهَادُ، كَمَا قَالَ تَعَالَى ﴿وَقَتِلُوهُم حَتَّى لَا تَكُونَ فِتنَة وَيَكُونَ ٱلدِّينُ كُلُّهُ لِلَّهِ ﴾ .[الأنفال: ٣٩.]

Dabi'a Ta: 1. Lalle sun kasance suna bauta ta hanyar hada salihan bayi wurin kiran Allah da kuma bauta masa, suna fatan samun ceton su a wurin Allah, saboda zaton da suke yin a Allah na son hakan, kuma lalle su salihan bayin suna son hakan, kamar yadda Allah ya ce: ''Kuma suna bautawa koma bayan Allah, abinda ba zai cutar da su ba (idan sun ki bauta masa) kuma ba zai anfanar da sub a (idan sun bauta masa) kuma suna cewa; Wadan nan su ne masu cetommu a wurin Allah''. Suratu Yunus, aya ta:18.

Kuma Allah madaukakin sarki ya ce: ''Duk wadanda suka riki koma bayansa (Shi Allah) amatsayin waliyyan, (cewa suke) ba komai ya sa muke bauta musuba sai domin su kara kusantar da mu zuwa ga Allah''. Suratu Zumar, aya ta:3.

Wannan itace mafi girman dabi'a da Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya saba musu, sai ya zo da Ihlasi, (wato kadaita Allah), kuma ya bada labarin cewa shine addinin Allah da ya turo dukkanin manzanni, kuma lalle (shi) Allah baya karbar duk wani aiki sai wanda aka yi domin shi kadai, kuma ya bada bayanin cewa duk wanda ya aikata abinda su (Ahalul Jahiliyyah) suka ga kyawunsa to lalle Allah ya haramta masa shiga aljanna, kuma makomarsa itace wuta.

Wannan fa shine abinda ya ke saboda shine mutane suka kasu gida biyu: Musulmi da kafiri, kuma akantane kiyayya ta auku, kuma saboda itane aka shar'anta jihadi, kamar yadda Allah yake cewa:

''Kuma ku dinga yakarsu har sai an kakkabe dukkan wata fitina (Shirka) kuma addini dukkansa na Allah ne (wato Allah kadai ake bautawa)''. Suratul Anfal, aya ta: 39.

اَلثَّانِيَةُ: أَنَّهُمْ مُتَفَرِّقُونَ فِي دِينِهِمْ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿مِنَ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُم وَكَانُواْ شِيَعا كُلُّ حِزبِ بِمَا لَدَيهِم فَرِحُونَ٣٢﴾ الروم: ٣٢، وَكَذَلِكَ فِي دُنْيَاهُمْ، وَيَرَوْنَ أَنَّ ذَلِكَ هُوَ اَلصَّوَابُ، فَأَتَى بِالاِجْتِمَاعِ فِي اَلدِّينِ بِقَوْلِهِ: ﴿شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّى بِهِ نُوحا وَٱلَّذِي أَوحَينَا إِلَيكَ وَمَا وَصَّينَا بِهِ إِبرَهِيمَ وَمُوسَى وَعِيسَى أَن أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِ كَبُرَ عَلَى ٱلمُشرِكِينَ مَا تَدعُوهُم إِلَيهِ ٱللَّهُ يَجتَبِي إِلَيهِ مَن يَشَاءُ وَيَهدِي إِلَيهِ مَن يُنِيبُ١٣﴾ الشورى: ١٣. وَقَالَ تَعَالَى ﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُم وَكَانُواْ شِيَعا لَّستَ مِنهُم فِي شَيءٍ ﴾ الأنعام: ١٥٩ وَنَهَاهُمْ عَنْ مُشَابَهَتِهِمْ بِقَوْلِهِ ﴿وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱختَلَفُواْ مِن بَعدِ مَا جَاءَهُمُ ٱلبَيِّنَتُ وَأُوْلَئِكَ لَهُم عَذَابٌ عَظِيم١٠٥﴾ آل عمران: ١٠٥ وَنَهَاهُمْ عَنِ اَلتَّفَرُّقِ فِي اَلدُّنْيَا بِقَوْلِهِ: ﴿وَٱعتَصِمُواْ بِحَبلِ ٱللَّهِ جَمِيعا وَلَا تَفَرَّقُواْ ١٠٣﴾ آل عمران: ١٠٣.

Dabi'a Ta: 2. Lalle kansu a rarrabe wurin bin addinsu, kamar yadda Allah ya ke cewa: ''Kowacce tawaga da abinda ke gabansu suke alfahari''. Suratu Rum, aya ta:32.

Haka kuma a harkarsu ta duniya, har ma suke ganin hakan shine daidai, sai (Ma'aikin Allah) ya zo da hadinkai akan abi addini guda, Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Anshar'anta muku abinda yake na addini dukkanin abinda aka yi wasiyyarsa ga (Annabi) Nuhu, da kuma wanda muka yi wahayinsa zuwa ga reka, da dukkan abinda muka yi wahayinsa ga (Annabi) Ibrahim da Musa da Isa, akan ku tsayar da addini kada ku rarraba a cikin sa''. Suratus Shura, aya ta:13.

Kuma Allah ya ce: ''Lalle dukkanin wadanda suka yi wa addinin su a yaga suka kasance kungiya-kungiya baka kasance a cikinsu a kowacce ba''. Suratul An'ama, aya ta: 159.

Kuma Allah ya hana su (Al'ummar musulmai) kamanceceniya da su (Ahlul jahiliyya) inda yake cewa: ''Kada ku kasance kamar wadannan da suka rarraba kuma suka sassaba bayan hujjojin sun zo musu''. Suratu Ali Imran, aya ta:105.

Kuma (Allah) ya hana rarraba akan al'amuran duniya inda yake cewa: ''Ku yi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba''. Suratu Ali Imran, aya ta: 103.

اَلثَّالِثَةُ: أَنَّ مُخَالَفَةَ وَلِيِّ اَلأَمْرِ وَعَدَمِ اَلاِنْقِيَادِ لَهُ فَضِيلَةٌ، وَالسَّمْعَ وَالطَّاعَةَ لَهُ ذُلٌّ وَمَهَانَةٌ، فَخَالَفَهُمْ رَسُولُ اَللهِ ﷺ‬، وَأَمَرَهُمْ بِالصَّبْرِ عَلَى جَوْرِ اَلْوُلاَةِ، وَأَمَرَ بِالسَّمْعِ وَالطَّاعَةِ لَهُمْ وَالنَّصِيحَةِ، وَغَلَّظَ فِي ذَلِكَ، وَأَبْدَأَ وَأَعَادَ.

وَهَذِهِ اَلثَّلاَثُ هِيَ اَلَّتِي جَمَعَ بَيْنَهَا فِيمَا صَحَّ عَنْهُ ﷺ‬ فِي ((اَلصَّحِيحَيْنِ)) أَنَّهُ قَالَ: (( إِنَّ اَللهَ يَرْضَى لَكُمْ ثَلاَثًا: أَنْ تَعْبُدُوهُ وَلاَ تُشْرِكُواْ بِهِ شَيْئًا، وَأَنْ تَعْتَصِمُواْ بِحَبْلِ اَللهِ جَمِيعًا وَلاَ تَفَرَّقُواْ، وَأَنْ تُنَاصِحُواْ مَنْ وَلاَّهُ اَللهُ أَمْرَكُمْ)). وَلَمْ يَقَعْ خَلَلٌ فِي دِينِ اَلنَّاسِ وَدُنْيَاهُمْ إِلاَّ بِسَبَبِ اَلإِخْلاَلِ بِهَذِهِ اَلثَّلاَثِ أَوْ بَعْضِهَا.

Dabi'a Ta: 3. Lalle sabawa shugaba da kin yi masa biyayya matsayi ne, kuma a ce an ji maganarsa an bita kaskancine da wulakanci, sai Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya saba musu akan haka, ya umarcesu da yin hakuri akan zalincin shugabanni, ya yi umarni da jin maganarsu da kuma bi da yi musu nasiha, kuma ya kausasa akan haka, ya fada ya kuma kara fada.

Wadannan abubuwa uku (daga na farko zuwa wannan) sune hadisi ingantacce daga Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a cikin Bukhari da Muslim ya kunsa, cewar Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya ce:

'' Lalle Allah yana yardarm muku da abubuwa uku: Ku bauta masa kada ku hada shi da komai, ku yi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba, kuma ku yi nasiha ga wadanda Allah ya sanya al'amuran ku a gare su''.

Ba'a taba samun tangarda a addinin mutane ba da kuma a duniyar su ba sai ta sanadiyyar tangarda a wadannan abubuwa uku ko wasu daga cikin su.

اَلرَّابِعَةُ: أَنَّ دِينَهُمْ مَبْنِيٌّ عَلَى أُصُولٍ أَعْظَمُهَا: اَلتَّقْلِيدُ، فَهُوَ اَلْقَاعِدَةُ اَلْكُبْرَى لِجَمِيعِ اَلْكُفَّارِ، أَوَّلِهِمْ وَآخِرِهِمْ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿وَكَذَلِكَ مَا أَرسَلنَا مِن قَبلِكَ فِي قَريَة مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُترَفُوهَا إِنَّا وَجَدنَا ءَابَاءَنَا عَلَى أُمَّة وَإِنَّا عَلَى ءَاثَرِهِم مُّقتَدُونَ٢٣﴾ الزخرف: ٢٣ وَقَالَ تَعَالَى: ﴿وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَا أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَل نَتَّبِعُ مَا وَجَدنَا عَلَيهِ ءَابَاءَنَا أَوَلَو كَانَ ٱلشَّيطَنُ يَدعُوهُم إِلَى عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ٢١﴾ لقمان: ٢١ . فَأَتَاهُمْ بِقَوْلِهِ: ﴿قُل إِنَّمَا أَعِظُكُم بِوَحِدَةٍ أَن تَقُومُواْ لِلَّهِ مَثنَى وَفُرَدَى ثُمَّ تَتَفَكَّرُواْ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍ إِن هُوَ إِلَّا نَذِير لَّكُم بَينَ يَدَي عَذَاب شَدِيد٤٦﴾ سبأ: ٤٦ وَقَوْلِهِ: ﴿ٱتَّبِعُواْ مَا أُنزِلَ إِلَيكُم مِّن رَّبِّكُم وَلَا تَتَّبِعُواْ مِن دُونِهِ أَولِيَاءَ قَلِيلا مَّا تَذَكَّرُونَ٣﴾ الأعراف: ٣ .

Dabi'a Ta: 4. Lalle addininsu (Su Ahlul Jahiliyyah) ya ginu ne akan wadansu turaku, babbab turken (shi ne): Al'ada. Ita ce babbar ka'ida ga dukkanin kafirai, tun na farkon su har na karshensu, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:

''Kuma haka nan ba mu taba aikowaba kafin kai a cikin birane (ba mu taba aiko) mai gargadi ba face sai manyan garin sun ce: Lalle mu mun sami iyayan mu ne akan wani addini kuma mu akan hanyarsu mu ke koyi''. Suratu Zukhruf, aya ta: 23.

Allah mai girma da daukak yana cewa:

'' Kuma idan aka ce; Ku bi abinda Allah ya saukar, sai su ce; A'a, za mu bi abinda muka sami iyayammu ne. To (haka za su bi iyayan) ko da shaidan yana kiran su ga azaba mai ruruwa''. Suratu Lukman, aya ta:21.

Sai Allah ya zo da fadinsa: '' Ka ce abin sani kawai ina muku wa'azine da (kalma) guda, akan ku mike (kan al'amarin) sabo da Allah bibiyu da kuma daidai sannan ku yi tunani, babu tabin hankali ga abokin ku''. Suratu Saba'i, aya ta: 46. Da kuma fadin sa (Shi Allah madaukakin sarki): '' Ku bi abinda aka saukar muku daga wurin Ubangijinku kada ku bi koma bayan amatsayin waliyyai, kadan ne matuka suke fada kuwa''. Suratul A'araf, aya ta: 3.

اَلْخَامِسَةُ: أَنَّ مِنْ أَكْبَرِ قَوَاعِدِهِمِ اَلاِغْتِرَارَ بِالأَكْثَرِ، وَيَحْتَجُّونَ بِهِ عَلَى صِحَّةِ اَلشَّيْءِ، وَيَسْتَدِلُّونَ عَلَى بُطْلاَنِ اَلشَّيْءِ بِغُرْبَتِهِ، وَقِلَّةِ أَهْلِهِ. فَأَتَاهُمْ بِضِدِّ ذَلِكَ، وَأَوْضَحَهُ فِي غَيْرِ مَوْضِعٍ مِنَ ((اَلْقُرْآنِ)).

Dabi'a Ta: 5. Tabbas yana daga cikin babbar ka'idar su, ruduwa da yawan mabiya, suna ma kafa hujja da yawan mabiya akan kyawun abu, suna kuma kafa hujja akan rashin kyawun wani abu da cewar; Ai ba'a san shi ba, kuma ai ba shi da yawan mabiya,to sai (Allah) ya zo musu da kishiyar haka, kuma ya yi bayaninsa a wurare da daman a Alkur'ani.

اَلسَّادِسَةُ: اَلاِحْتِجَاجُ بِالْمُتَقَدِّمِينَ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿قَالَ فَمَا بَالُ ٱلقُرُونِ ٱلأُولَى٥١﴾ طه: ٥١ ﴿ مَّا سَمِعنَا بِهَذَا فِي ءَابَائِنَا ٱلأَوَّلِينَ٢٤﴾ المؤمنون: ٢٤ .

Dabi'a Ta: 6. Kafa hujja da mutanan da. Kamar yadda Allah ya ke cewa:

'' Ya ce; To, menene labarin mutanan farko''. Suratu Taha, aya ta:51. (da kuma fadin sa): Ba mu taba jin wannan ba ga iyayammu na farko''. Suratul Muminun, aya ta:24.

اَلسَّابِعَةُ: اَلاِسْتِدْلاَلُ بِقَوْمٍ أُعْطُواْ قُوًى فِي اَلأَفْهَامِ وَالأَعْمَالِ وَفِي اَلْمُلْكِ وَالْمَالِ وَالْجَاهِ، فَرَدَّ اَللهُ ذَلِكَ بِقَوْلِهِ: ﴿وَلَقَد مَكَّنَّهُم فِيمَا إِن مَّكَّنَّكُم فِيهِ ٢٦﴾ الأحقاف: ٢٦ وَقَوْلِهِ: ﴿ وَكَانُواْ مِن قَبلُ يَستَفتِحُونَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَمَّا جَاءَهُم مَّا عَرَفُواْ كَفَرُواْ بِهِ فَلَعنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلكَفِرِينَ٨٩﴾ البقرة: ٨٩ وَقَوْلِهِ: ﴿ يَعرِفُونَهُ كَمَا يَعرِفُونَ أَبنَاءَهُم ١٤٦﴾ البقرة: ١٤٦ .

Dabi'a Ta: 7. Kafa hujja da mutanan da aka bas u karfi ta wajan fahimta da ayyuka da mulki da dukiya da matsayi, sai Allah ya mayar musu da wannan inda ya ce:

'' Kuma hakika mun tabbatar musu cikin abinda muka tabbatar muku a cikin sa''. Suratul Ahkaf, aya ta:26. Da kuma fadinsa (Shi Allah madaukakin sarki): ''Kuma sun kasance a tuntuuni suna razanar da wadanda suka kafirta, to alokacin da abinda suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa''. Suratul Bakara, aya ta: 89. Da kuma fadinsa: '' Sun san Shi kamar yadda suka san 'yayansu''. Suratul Bakarah, aya ta:146.

اَلثَّامِنَةُ: اَلاِسْتِدْلاَلُ عَلَى بُطْلاَنِ اَلشَّيْءِ بِأَنَّهُ لَمْ يَتْبَعْهُ إِلاَّ اَلضُّعَفَاءُ، كَقَوْلِهِ ﴿قَالُواْ أَنُؤمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلأَرذَلُونَ١١١﴾ الشعراء: ١١١ وَقَوْلِهِ: ﴿ أَهَؤُلَاءِ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيهِم مِّن بَينِنَا ٥٣﴾ الأنعام: ٥٣ فَرَدَّ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿ أَلَيسَ ٱللَّهُ بِأَعلَمَ بِٱلشَّكِرِينَ٥٣﴾ الأنعام: ٥٣

Dabi'a Ta: 8. Kafa hujja akan cewa abu bashi da kyau idan ya zama talakawane suka bi shi (shi wannan al'amarin). Kamar yadda Allah ya ce:

'' Yanzu za mu amince maka alhali talakawa su ka bi ka''?. Suratus Shu'ara'i, aya ta: 111, da fadinsa: “ Yanzu wadannan Allah ya yi wa ni'ima a gabammu''. Suratul An'am, aya ta:53. Sai Allah ya ce: ''Ashe Allah ba shi ne mafi sanin masu godiyaba''. Suratul An'am, aya ta:53.

اَلتَّاسِعَةُ: اَلاِقْتِدَاءُ بِفَسَقَةِ اَلْعُلَمَاءِ وَالْعُبَّادِ، فَأَتَى اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ إِنَّ كَثِيرا مِّنَ ٱلأَحبَارِ وَٱلرُّهبَانِ لَيَأكُلُونَ أَموَلَ ٱلنَّاسِ بِٱلبَطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ يَكنِزُونَ ٱلذَّهَبَ وَٱلفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَبَشِّرهُم بِعَذَابٍ أَلِيم٣٤﴾ التوبة: ٣٤ وَبِقَوْلِهِ: ﴿قُل يَأَهلَ ٱلكِتَبِ لَا تَغلُواْ فِي دِينِكُم غَيرَ ٱلحَقِّ وَلَا تَتَّبِعُواْ أَهوَاءَ قَوم قَد ضَلُّواْ مِن قَبلُ وَأَضَلُّواْ كَثِيرا وَضَلُّواْ عَن سَوَاءِ ٱلسَّبِيلِ٧٧﴾ المائدة: ٧٧ .

Dabi'a Ta: 9. Koyi da mugayan malamai da jahilan masu ibada, sai Allah yake cewa:

'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi Imani! Lalle da yawa daga cikin malaman yahudawa da masu ibadar nasara (wallahi) tabbas suna cin dukiyar mutane da barna, kuma suna kangewa daga barin hanyar Allah''. Suratut Taubah, aya ta:34.

Da kuma fadinsa: “ Kada ku ketare iyaka akan addininku ba ta hanyar gaskiya ba, kuma kada ku bi son zuciyar wasu mutane da sun bace tuntuni kuma sun batar da (mutane) masu yawa, kuma sun bace ma hanyar daidai''. Suratul Ma'idah, aya ta:77.

اَلْعَاشِرَةُ: اَلاِسْتِدَلاَلُ عَلَى بُطْلاَنِ اَلدِّينِ بِقِلَّةِ أَفْهَامِ أَهْلِهِ، وَعَدَمِ حِفْظِهِمْ،كَقَوْلِهِمْ: ﴿ بَادِيَ ٱلرَّأيِ ﴾ هود: ٢٧ .

Dabi'a Ta: 10. Kafa hujja akan bacin addini da cewar ai mabiyansa suna da karancin fahimta, kuma ba sa kiyaye al'amura, kamar yadda (mutanan Annabi Nuhu) suka ce: ''Masu gajeran tunani''. Suratu Hud, aya ta:27.

اَلْحَادِيَةَ عَشْرَةَ: اَلاِسْتِدْلاَلُ بِالْقِيَاسِ اَلْفَاسِدِ كَقَوْلِهِمْ: ﴿ َالُواْ إِن أَنتُم إِلَّا بَشَر مِّثلُنَا ١٠﴾ إبراهيم: ١٠ .

Dabi'a Ta: 11. Yadda suke kafa hujja da gurbatattacan kiyasi, kamar yadda suke cewa (Annabawa): '' Ku fa ba kowa bane face mutane kamar mu''. Suratu Ibrahim, aya ta: 10.

اَلثَّانِيَةَ عَشْرَةَ: إِنْكَارُ اَلْقِيَاسِ اَلصَّحِيحِ، وَالْجَامِعُ لِهَذَا وَمَا قَبْلَهُ عَدَمُ فَهْمِ اَلْجَامِعِ وَالْفَارِقِ.

Dabi'a Ta: 12. Yadda suke musun ingantaccan kiyasi, kuma abinda ya hada wannan da wanda ya zo kafin shi rashin fahimtar inda aka hadu da kuma inda aka rabu.

اَلثَّالِثَةَ عَشْرَةَ: اَلْغُلُوُّ فِي اَلْعُلَمَاءِ وَالصَّالِحِينَ، كَقَوْلِهِ ﴿يَأَهلَ ٱلكِتَبِ لَا تَغلُواْ فِي دِينِكُم وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلحَقَّ ﴾ النساء: ١٧١ .

Dabi'a Ta: 13. Ketare iyaka akan (abinda ya shafi) malamai da kuma salihan bayi, kamar yadda (Allah) yake cewa:

'' Ya ku ma'abota littafi! Kada ku wuce iyaka a al'amarin addininku, kuma kada ku fada dangane da Allah sai abinda yake gaskiya''. Suratun Nisa'i, aya ta: 171.

اَلرَّابِعَةَ عَشْرَةَ: أَنَّ كُلَّ مَا تَقَدَّمَ مَبْنِيٌّ عَلَى قَاعِدَةٍ، وَهِيَ: اَلنَّفْيُ وَالإِثْبَاتُ، فَيَتَّبِعُونَ اَلْهَوَى وَالظَّنَّ، وَيُعْرِضُونَ عَمَّا جَاءَتْ بِهِ اَلرُّسُلُ.

Dabi'a Ta: 14. Lalle dukkanin abinda ya gabata ya ginune akan wata ka'ida, ita ce kuwa: Kore (abinda bai yi musu ba), da kuma tabbatar (da abinda ya yi musu), sai suke bin son zuciya da zace-zace, sai kuma su kaudakai su bar abinda manzanni suka zo da shi.

اَلْخَامِسَةَ عَشْرَةَ: اِعْتِذَارُهُمْ عَنِ اتِّبَاعِ مَا آتَاهُمُ اَللهُ بِعَدَمِ اَلْفَهْمِ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ قُلُوبُنَا غُلفُ ﴾ البقرة: ٨٨ . ﴿قَالُواْ يَشُعَيبُ مَا نَفقَهُ كَثِيرا مِّمَّا تَقُولُ ﴾ هود: ٩١، فَأَكْذَبَهَمُ اَللهُ، وَبَيَّنَ أَنَّ ذَلِكَ بِسَبَبِ اَلطَّبْعِ عَلَى قُلُوبِهِمْ، وَأَنَّ اَلطَّبْعَ بِسَبَبِ كُفْرِهِمْ.

Dabi'a Ta: 15. Bada hanzari akan kin bin abinda Allah ya aiko musu da cewar ba sa fahimta, kamar yadda suka ce: '' Zukatammu a rufe su ke''. Suratul Bakara, aya ta:88. Da kuma (yadda suka ce):

'' Ya kai Shu'aibu ba ma fahimtar mafi yawan abinda kake fadi''. Suratu Hudu, aya ta: 91. Sai Allah ya karyata su, ya kuma yi bayanin hakan ya faru ne ta sanadiyyar toshewar zukatansu, sannan sanadiyyar toshewar kuwa shine kafircin su.

اَلسَّادِسَةَ عَشْرَةَ: اِعْتِيَاضُهُمْ عَمَّا أَتَاهُمْ مِنَ اَللهِ بِكُتُبِ اَلسِّحْرِ، كَمَا ذَكَرَ اَللهُ ذَلِكَ فِي قَوْلِهِ: ﴿وَلَمَّا جَاءَهُم رَسُول مِّن عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّق لِّمَا مَعَهُم نَبَذَ فَرِيق مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلكِتَبَ كِتَبَ ٱللَّهِ وَرَاءَ ظُهُورِهِم كَأَنَّهُم لَا يَعلَمُونَ١٠١ وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتلُواْ ٱلشَّيَطِينُ عَلَى مُلكِ سُلَيمَنَ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ وَلَكِنَّ ٱلشَّيَطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة فَلَا تَكفُر فَيَتَعَلَّمُونَ مِنهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَينَ ٱلمَرءِ وَزَوجِهِ وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِن أَحَدٍ إِلَّا بِإِذنِ ٱللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَلَقَد عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشتَرَىهُ مَا لَهُ فِي ٱلأخِرَةِ مِن خَلَق وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾ البقرة: ١٠١ – ١٠٢

Dabi'a Ta: 16. Kauda kai da suke yi da barin abinda ya zo musu daga wurin Allah ta hanyar riko da littafan sihiri (asiri), kamar yadda Allah madaukakin sarki ya anbaci haka a fadinsa:

'' …. (Sai) Wadansu tawaga daga cikin wadanda aka baiwa (ilimin) littafi suka yi watsi da littafi Allah can bayansu, kamar ka ce basu taba sanin (abinda ke ciki ba)* Kuma su ka bi abinda shaidanu suke karanta musu dangane da mulkin (Annabi) Sulaiman''. Suratul Bakarah, aya ta: 101-102.

اَلسَّابِعَةَ عَشْرَةَ: نِسْبَةُ بَاطِلِهِمْ إِلَى اَلأَنْبِيَاءِ، كَقَوْلِهِ: ﴿ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ ١٠٢﴾ البقرة: ١٠٢. وَقَوْلِهِ: ﴿مَا كَانَ إِبرَهِيمُ يَهُودِيّا وَلَا نَصرَانِيّا وَلَكِن كَانَ حَنِيفا مُّسلِما وَمَا كَانَ مِنَ ٱلمُشرِكِينَ٦٧﴾ آل عمران: ٦٧ .

Dabi'a Ta: 17. Jingina barna ga Annabawa, (kamar yadda suka jingina sihiri ga Annabi Sulaiman, suke cewa ai Annabi Sulaiman da asiri ya mallaki mutane da aljanu, har suke bada hatiminshi) kamar yadda Allah yake cewa:

'' (Annabi) Sulaiman bai yi kafirci ba''. Suratul Bakarah, aya ta: 102. Da kuma fadinsa: '' (Annabi) Ibrahim bait aba kasancewa bayahudeba haka nan bai taba kasancewa banasare ba''. Suratu Ali Imrana, aya ta: 67.

اَلثَّامِنَةَ عَشْرَةَ: تَنَاقُضُهُمْ فِي اَلاِنْتِسَابِ، يَنْتَسِبُونَ إِلَى إِبْرَاهِيمَ مَع إِظْهَارِهِمْ تَرْكَ اَتِّبَاعِهِ.

Dabi'a Ta: 18. Warwara a yadda suke danganta kawunan su, suna jingina kan su da cewa su tsatsan Annabi Ibrahim ne, kuma suna bayyanar da kin bin karantarwarsa a fili.

اَلتَّاسِعَةَ عَشْرَةَ: قَدْحُهُمْ فِي بَعْضِ اَلصَّالِحِينَ بِفِعْلِ بَعْضِ اَلْمُنْتَسِبِينَ إِلَيْهِمْ، كَقَدْحِ اَلْيَهُودِ فِي عِيسَى، وَقَدْحِ اَلْيَهُودِ وَالنَّصَارَى فِي مُحَمَّدٍ ﷺ‬.

Dabi'a Ta: 19. Yadda suke muzanta bayin Allah na kwarai, saboda aikin da wasu da suke jingina kan su ga wadannan bayin Allah suka aikata, kamar yadda yahudawa suke aibanta Annabi Isah (saboda aikin da nasara suke yi), da kuma yadda yahudu da nasara suke aibanta Ma'aikin Allah (Annabi) Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) saboda aikin da wasu mabiyansa suka aikata.

اَلْعِشْرُونَ: اِعْتِقَادُهُمْ فِي مَخَارِيقِ اَلسَّحَرَةِ وَأَمْثَالِهِمْ أَنَّهَا مِنْ كَرَامَاتِ اَلصَّالِحِينَ، وَنِسْبَتُهُ إِلَى اَلأَنْبِيَاءِ كَمَا نَسَبُوهُ لِسُلَيْمَانَ عَلَيْهِ اَلسَّلاَمُ.

Dabi'a Ta: 20. Yadda suka kudurce mugayan akidu dangane da masu rufa-ido da 'yan-dabo da ire-iren sun a cewa (wannan aikin na rufa-ido ko dabo) yana cikin karamomin waliyyai, har ma suke jingina shi ga Annabawa kamar yadda suka jin gina shi ga Annabi Sulaiman, tsiran Allah ya tabbata a gareshi.

اَلْحَادِيَةَ وَالْعِشْرُونَ: تَعَبُّدُهُمْ بِالْمُكَاءِ وَالتَّصْدِيَةِ.

Dabi'a Ta: 21. Yadda suke bauta ta hanyar kuka da kuma fito.

اَلثَّانِيَةُ وَالْعِشْرُونَ: أَنَّهُمُ اَتَّخَذُواْ دِينَهُمْ لَهْوًا وَلَعِباً.

Dabi'a Ta: 22. Su fa sun dauki addinin su wasa da cashewa.

اَلثَّالِثَةُ وَالْعِشْرُونَ: أَنَّ اَلْحَيَاةَ اَلدُّنْيَا غَرَّتْهُمْ، فَظَنُّواْ أَنَّ عَطَاءَ اَللهِ مِنْهَا يَدُلُّ عَلَى رِضَاهُ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ نَحنُ أَكثَرُ أَموَلا وَأَولَدا وَمَا نَحنُ بِمُعَذَّبِينَ٣٥﴾ سبأ: ٣٥

Dabi'a Ta: 22. Lalle fa rayuwar duniya ta rudesu, sai suka yi tsammanin duk wanda Allah ya ba arziki a duniya to ya yarda da shi, kamar yadda suke cewa:

'' Mu muka fi yawan dukiya da 'ya'ya, mu ba wadanda za'a yi wa azaba bane''. Suratu Saba'i, aya ta: 35.

اَلرَّابِعَةُ وَالْعِشْرُونَ: تَرْكُ اَلدُّخُولِ فِي اَلْحَقِّ إِذَا سَبَقَهُمْ إِلَيْهِ اَلضُّعَفَاءُ تَكَبُّرًا وَأَنَفَةً، فَأَنْزَلَ اَللهُ تَعَالَى: ﴿وَلَا تَطرُدِ ٱلَّذِينَ يَدعُونَ رَبَّهُم بِٱلغَدَوةِ وَٱلعَشِيِّ ............اَلآيَات. ﭼ الأنعام: ٥٢ وَمَا بَعْدَهَا.

Dabi'a Ta: 24. Yadda suke kin karbar gaskiya idan talakawa suka riga su kawai don girman kai da hura hanci, sai Allah ya saukar (da fadansa): '' Kada ka kori wadanda suke kiran Ubangijusu ….'' Ayoyin Suratul An'am, aya ta: 52, da wacce take bayanta (53).

اَلْخَامِسَةُ وَالْعِشْرُونَ: اَلاِسْتِدَلاَلُ عَلَى بُطْلاَنِهِ بِسَبْقِ اَلضُّعَفَاءُ، كَقَوْلِهِ: ﴿ لَو كَانَ خَيرا مَّا سَبَقُونَا إِلَيهِ ﴾ الأحقاف: ١١ .

Dabi'a Ta: 25. Yadda suka kafa hujja da cewa abu baida kyau idan talakawa suka riga su karba, kamar yadda (Allah) yake cewa:

'' Inda ya kasance alherine ai da basu riga mu ba''. Suratul Ahkaf, aya ta:11.

اَلسَّادِسَةُ وَالْعِشْرُونَ: تَحْرِيفُ ((كِتَابِ اَللهِ)) مِنْ بَعْدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمْ يَعْلَمُونَ.

Dabi'a Ta: 26. Yadda suke jirkita littafin Allah (kamar Attaura da Injila) bayan sun gane kuma fa suna sane.

اَلسَّابِعَةُ وَالْعِشْرُونَ: تَصْنِيفُ اَلْكُتُبِ اَلْبَاطِلَةِ وَنِسْبَتُهَا إِلَى اَللهِ، كَقَوْلِهِ: ﴿فَوَيل لِّلَّذِينَ يَكتُبُونَ ٱلكِتَبَ بِأَيدِيهِم ثُمَّ يَقُولُونَ هَذَا مِن عِندِ ٱللَّهِ لِيَشتَرُواْ بِهِ ثَمَنا قَلِيلا فَوَيل لَّهُم مِّمَّا كَتَبَت أَيدِيهِم وَوَيل لَّهُم مِّمَّا يَكسِبُونَ٧٩﴾ البقرة: ٧٩

Dabi'a Ta: 27. Yadda suke wallafa littafai na barna kuma suke jingina su ga Allah, kamar yadda (Allah) yake cewa:

'' To azaba ta tabbata ga dukkanin wadanda suke rubuta littafai da hannayansu sannan suce: wannan daga wurin Allah ne''. Suratul Bakarah, aya ta: 79.

الثَّامِنَةُ وَالعِشْرُونَ: أَنَّهُمْ لاَ يَقْبَلُونَ مِنَ اَلْحَقِّ إِلاَ اَلَّذِي مَعَ طَائِفَتِهِمْ، كَقَوْلِهِ: ﴿ قَالُواْ نُؤمِنُ بِمَا أُنزِلَ عَلَينَا ﴾ البقرة: ٩١ .

Dabi'a Ta: 28. Lalle su basa karbar gaskiya sai wacce ta yi daidai da bangaran su, kamar yadda (Allah) yake cewa:

“ Su ka ce: mun yarda da abinda aka saukar mana''. Suratul Bakarah, aya ta: 91.

اَلتَّاسِعَةُ وَالعِشْرُونَ: أَنَّهُمْ مَعَ ذَلِكَ لاَ يَعْلَمُونَ بِمَا تَقُولُهُ طَائِفَتُهُمْ، كَمَا نَبَّهَ اللهُ تَعَالَى عَلَيْهِ بِقَوْلِهِ: ﴿ قُل فَلِمَ تَقتُلُونَ أَنبِيَاءَ ٱللَّهِ مِن قَبلُ إِن كُنتُم مُّؤمِنِينَ٩١﴾ البقرة: ٩١ .

Dabi'a Ta: 29. Lalle su duk haka ba su samma me jama'ar ta su take cewa ba, kamar yadda Allah ya fadakar akan haka:

'' Ka ce; To damme kuke kashe Annabawan Allah tuntuni in kun kasance wadanda su ka yi imani''. Suratul Bakarah, aya ta: 91.

اَلثَّلاَثُونَ: وَهِيَ مِنْ عَجَائِبِ آيَاتِ اَللهِ، أَنَّهُمْ لَمَّا تَرَكُواْ وَصِيَّةَ اَللهِ بِالاجْتِمَاعِ، وَارْتَكَبُواْ مَا نَهَى اَللهُ عَنْهُ مِنَ الاِفْتِرَاقِ، صَارَ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحِينَ.

Dabi'a Ta: 30. Wannan ko tana cikin abubuwan ban-al'ajabi na ayoyin Allah, domin su lokacin da suka bar wasiyyar Allah akan ahadu, suka aikata abinda Allah ya hana na rarrabuwa, sai ya kasance kowacce kungiya da abinda ke gabansu suke alfahari.

اَلْحَادِيَةُ وَالثَّلاَثُونَ: وَهِيَ مِنْ أَعْجَبِ اَلآيَاتِ أَيْضًا: مُعَادَاتُهُمْ اَلدِّينِ اَلَّذِي اِنْتَسَبُوا إِلَيْهِ غَايَةَ اَلْعَدَاوَةِ، وَمَحَبَّتُهُمْ دِينَ الكُفَّارِ اَلَّذِينَ عَادَوْهُمْ وَعَادَواْ نَبِيَّهُمْ وَفِئَتَهُمْ غَايَةَ اَلْمَحَبَّةِ، كَمَا فَعَلُواْ مَعَ النَّبِيِّ ﷺ‬ لَمَّا أَتَاهُمْ بِدِينِ مُوسَى عَلَيهِ السَّلاَمُ، وَاتَّبَعُواْ كُتُبَ السِّحْرِ، وَهِيَ مِنْ دِينِ آلِ فِرْعَوْنَ.

Dabi'a Ta: 31. Ita din ma dai tana cikin manya-manyan ayoyin masu bammamaki, kiyayya da addinin da suka ce suna bi makurar kiyayya, da kuma yadda suke son addinin kafiran da su ka ki su suka kuma ki Annabinsu suka ki jama'ar su, ya zama na suna son (kafiran nan) makurar so.

Kamar yadda su ka yi da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a lokacin da ya zo musu da addinin Annabi Musa aminci Allah ya tabbata a gareshi, sai suka bi littafan sihiri, wanda yake wannan kuwa yana cikin gargajirar Fir'auna.

اَلثَّانِيَةُ وَالثَّلاَثوُنَ : كُفْرُهُمْ بِالْحَقِّ إِذَا كَانَ مَعَ مَنْ لاَ يَهْوَوْنَهُ كَمَا قَالَ تَعَالَ: ﴿وَقَالَتِ ٱليَهُودُ لَيسَتِ ٱلنَّصَرَى عَلَى شَيء وَقَالَتِ ٱلنَّصَرَى لَيسَتِ ٱليَهُودُ عَلَى شَيء ١١٣﴾ البقرة: ١١٣.

Dabi'a Ta: 32. Yadda suke kafircewa gaskiya idan ta kasance a tare da wanda su basa son shi, kamar yadda (Allah) madaukakin sarki yake cewa:

'' Yahudawa sun ce; Nasara ba akan komai suke ba, Nasara kuma sun ce; Yahudawa ba akan komai suke ba''. Suratul Bakarah, aya ta: 113.

اَلثَّالِثَةُ وَالثَّلاَثوُنَ: إِنْكَارُهُمْ مَا أَقَرُّوا أَنَّهُ مِنْ دِينِهِمْ، كَمَا فَعَلُوا فِي حَجِّ البَيْتِ، قَالَ تَعَالَى: ﴿وَمَن يَرغَبُ عَن مِّلَّةِ إِبرَهِمَ إِلَّا مَن سَفِهَ نَفسَهُ ﴾ البقرة: ١٣٠

Dabi'a Ta: 33. Yadda suke musun abinda suka tabbatar da shi a addinin su, kamar yadda suka yi hakan a aikin hajji, (Allah) mai girma da daukaka yana cewa:

'' Ba wanda zai kyamaci addinin (Annabi) Ibrahim sai wanda ya wawantar da kansa''. Suratul Bakarah, aya ta: 130.

اَلرَّابِعَةُ وَالثَّلاَثُونَ: أَنَّ كُلَّ فِرْقَةٍ تَدَّعِي أَنَّهَا النَّاجِيَةُ، فَأَكْذَبَهُمْ اَللهُ بِقَولِهِ: ﴿ قُل هَاتُواْ بُرهَنَكُم إِن كُنتُم صَدِقِينَ١١١﴾ البقرة: ١١١، ثُمَّ بَيَّنَ الصَّوَابَ بِقَوْلِهِ: ﴿بَلَى مَن أَسلَمَ وَجهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحسِن ﴾ البقرة: ١١٢ .

Dabi'a Ta: 34. Kowacce kungiya tana ganin itace kadai zata tsira, sai Allah ya karyata su da fadar Sa: '' Ka ce; Ku kawo dalilanku in kun kasance masu gaskiya''. Suratul Bakarah, aya ta: 111, sannan sai (Allah) ya bayyana abinda yake shine daidai inda ya ce:

'' Tabbas duk wanda ya mika fuskassa ( ya yi addini) domin Allah yana mai kyautatawa''. Suratul Bakarah, aya ta: 112.

اَلْخَامِسَةُ وَالثَّلاَثُونَ: اَلتَّعَبُّدُ بِكَشْفِ اَلْعَوْرَاتِ، كَقَوْلِهِ: ﴿وَإِذَا فَعَلُواْ فَحِشَة قَالُواْ وَجَدنَا عَلَيهَا ءَابَاءَنَا وَٱللَّهُ أَمَرَنَا بِهَا قُل إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَأمُرُ بِٱلفَحشَاءِ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعلَمُونَ٢٨﴾ الأعراف: ٢٨ .

Dabi'a Ta: 35. Yadda suke bauta ta hanyar bayyanar da tsiraici, kamar yadda (Allah) ya ce: '' Kuma idan suka aikata kazamin aiki sai su ce; Haka muka samu iyayammu akai kuma Allah ne ya umarce mu da hakan''. Suratul A'araf, aya ta: 28.

اَلسَّادِسَةُ وَالثَّلاَثوُنَ: اَلتَّعَبُّدُ بِتَحْرِيـمِ اَلْحَلاَلِ كَمَا تَعَبَّدُواْ بِالشِّرْكِ.

Dabi'a Ta: 36. Yadda suke bauta ta hanyar haramtar da halas, kamar yadda suka yi bautar da shirka.

اَلسَّابِعَةُ وَالثَّلاَثوُنَ: التَّعَبُّدُ بِاتِّخَاذِ اَلأَحْبَارِ وَالرُّهُبَانِ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللهِ.

Dabi'a Ta: 37. Yadda suke bauta ta hanyar daukar manyan malamai da masu ibada wasu abin bauta daban koma bayan Allah.

اَلثَّامِنَةُ وَالثَّلاَثُونَ: اَلإِلْحَادُ فِي اَلصِّفَاتِ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿ وَلَكِن ظَنَنتُم أَنَّ ٱللَّهَ لَا يَعلَمُ كَثِيرا مِّمَّا تَعمَلُونَ٢٢﴾ فصلت: ٢٢ .

Dabi'a Ta: 38. Kore siffofin (Ubangiji, kamar yadda basu yarda: Allah ya sani ba) kamar yadda (Allah) madaukakin sarki yake cewa: '' Sai dai kun yi zaton (cewar) Lalle Allah bai san mafi yawan abinda kuke aikatawa''. Suratu Fussilat, aya ta: 22.

اَلتَّاسِعَةُ وَالثَّلاَثُونَ: اَلإِلْحَادُ فِي اَلأَسْمَاءِ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿ وَهُم يَكفُرُونَ بِٱلرَّحمَنِ ٣٠﴾ الرعد: ٣٠ .

Dabi'a Ta: 39. Kore sunayan Allah, kamar yadda (Allah) mai girma da daukaka ya ce: '' Kuma su suna kafircewa; Mai yawan rahama''. Suratur Ra'ad, aya ta: 30.

اَلأَرْبِعُونَ: اَلتَّعْطِيلُ، كَقَوْلِ فِرْعَوْنَ

Dabi'a Ta: 40. Share (Sunaye da siffofin Allah) kamar yadda fir'auna ya ce: (''Bansan kuna da wani abin bauta ba in ba ni ba''. Suratul Kasas, aya ta: 38).

اَلْحَادِيَةُ وَالأَرْبَعُونَ: نِسْبَةُ اَلنَّقَائِصِ إِلَيْهِ سُبْحَانَهُ، كَالْوَلَدِ وَالْحَاجَةِ وَالتَّعَبِ، مَعَ تَنْزِيهِ رُهْبَانِهِمْ عَنْ بَعْضِ ذَلِكَ.

Dabi'a Ta: 41. Jingina (siffofi na) tawaya ga (Allah) mai tsarki da buwaya, kamar (da suka ce yana da) Da, Bukata, Gajiya, tare da tsarkake malaman su da wasu daga cikin su (wadannan siffofin).

اَلثَّانِيَةُ وَالأَرْبَعُونَ: اَلشِّرْكُ فِي اَلْمُلْكِ، كَقَوْلِ اَلْمَجُوسِ.

Dabi'a Ta: 42. Shirka a mulikin (Allah) kamar yadda majusawa suke cewa: (Akwai mahaliccin duhu akwai kuma mahaliccin haske).

اَلثَّالِثَةُ وَالأَرْبَعُونَ: جُحُودُ اَلْقَدَرِ.

Dabi'a Ta: 43. Kin yarda da kaddarar (Ubangiji).

اَلرَّابِعَةُ وَالأَرْبَعُونَ: اَلاِحْتِجَاجُ عَلَى اَللهِ بِهِ.

Dabi'a Ta: 44. Yi wa Allah hujja da ita (Kaddarar).

اَلْخَامِسَةُ وَاَلأَرْبَعُونَ: مُعَارَضَةُ شَرْعِ اَللهِ بِقَدَرِهِ.

Dabi'a Ta: 45. Yadda suke gwara shara'ar Allah da kaddarar sa.

اَلسَّادِسَةُ وَاَلأَرْبَعُونَ: مَسَبَّةُ اَلدَّهْرِ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿ وَمَا يُهلِكُنَا إِلَّا ٱلدَّهرُ ﴾ الجاثية: ٢٤ .

Dabi'a Ta: 46. Aibanta zamani, kamar yadda suke cewa: '' Ba abinda yake halakar da mu sai zamani''. Suratul Jasiya, aya ta: 24.

اَلسَّابِعَةُ وَالأَرْبَعُونَ:إِضَافَةُ نِعَمِ اللهِ إِلَى غَيْرِهِ، كَقَوْلِهِ: ﴿يَعرِفُونَ نِعمَتَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا ٨٣﴾النحل: ٨٣ .

Dabi'a Ta: 47. Jingina ni'imomin da Allah ya yi ga wanin Allah, kamar yadda fadarsa (Shi Allah); '' Sun san ni'imomin Allah sannan suke musun su''. Suratun Nahl, aya ta:83.

اَلثَّامِنَةُ وَالأَرْبَعُونَ: اَلْكُفْرُ بِآيَاتِ الله.

Dabi'a Ta: 48. Yadda suke kafurcewa ayoyin Allah.

اَلتَّاسِعَةُ وَالأَرْبَعُونَ: جَحْدُ بَعْضِهَا.

Dabi'a Ta: 49. Musun wasu daga cikin su (su ayoyin Allah din).

اَلْخَمْسُونَ: قَوْلُهُمْ: ﴿ مَا أَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَى بَشَر مِّن شَيء ﴾ الأنعام: ٩١

Dabi'a Ta: 50. Yadda suka ce “ Allah bai taba saukar da wani abu na ga wani mutum''. Suratul An'am, aya ta: 91.

اَلْحَادِيَةُ وَالْخَمْسُونَ: قَوْلُهُمْ فِي ((اَلْقُرْآنِ)) ﴿إِن هَذَا إِلَّا قَولُ ٱلبَشَرِ٢٥﴾ المدثر: ٢٥.

Dabi'a Ta: 51. Yadda suka ce dangane da Alkur'ani: '' Ai wannan ba komai bane sai zancan mutum''. Suratul Mudassir, aya ta: 25.

اَلثَّانِيَةُ وَالْخَمْسُونَ: اَلْقَدْحُ فِي حِكْمَةِ اَللهِ تَعَالَى.

Dabi'a Ta: 52. Yadda suke muzanta hikimomin Allah madaukakin sarki.

اَلثَّالِثَةُ وَالْخَمْسُونَ: إِعْمَالُ اَلْحِيَلِ اَلظَّاهِرَةِ وَالبَاطِنَةِ فِي دَفْعِ مَا جَاءِتْ بِهِ اَلرُّسُلُ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿وَمَكَرُواْ وَمَكَرَ ٱللَّهُ وَٱللَّهُ خَيرُ ٱلمَكِرِينَ٥٤﴾ آل عمران: ٥٤، وَقَوْلِهِ: ﴿وَقَالَت طَّائِفَة مِّن أَهلِ ٱلكِتَبِ ءَامِنُواْ بِٱلَّذِي أُنزِلَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَجهَ ٱلنَّهَارِ وَٱكفُرُواْ ءَاخِرَهُ لَعَلَّهُم يَرجِعُونَ٧٢﴾ آل عمران:٧٢.

Dabi'a Ta: 53. Yadda suke anfani da dabaru na zahiri da na boye domin kautar da abinda Manzanni suka zo da shi, kamar yadda (Allah) madaukakin sarki ya ce: ''Kuma sun kulla makirci, kuma Allah ya kulla musu makirci''. Suratu Ali Imran, aya ta:54. Da kuma fadinsa:

''Kuma wata kungiya daga cikin wadanda aka ba littafi ta ce: Ku yi Imani da abinda aka saukarwa wadanda suka yi Imani da farkon yini, sannan ku kafirce a karshansa (yinin)''. Suratu Ali Imran, aya ta: 72.

اَلرَّابِعَةُ وَالْخَمْسُونَ: اَلإِقْرَارُ بِالْحَقِّ لِيَتَوَصَّلُواْ بِهِ إِلَى دَفْعِهِ، كَمَا قَالَ فِي الآيَةِ.

Dabi'a Ta: 54. Furta gaskiya domin su yi anfani da hakan domin kautar da ita (gaskiyar), kamar yadda yadda ya gabata a ayar da ta wuce.

اَلْخَامِسَةُ وَالْخَمْسُونَ: اَلتَّعَصُّبُ لِلْمَذْهَبِ، كَقَوْلِهِ فِيهَا: ﴿وَلَا تُؤمِنُواْ إِلَّا لِمَن تَبِعَ دِينَكُم ٧٣﴾ آل عمران: ٧٣.

Dabi'a Ta: 55. Kafewa akan ra'ayi, Kamar yadda (Allah) yake cewa: ''Kada ku yi Imani da kowa sai wanda ya bi addinin ku''. Suratu Ali Imrana, aya ta: 73.

اَلسَّادِسَةُ وَالْخَمْسُونَ: تَسْمِيَةُ اتِّبَاعِ الإِسْلاَمِ شِرْكًا، كَمَا ذَكَرَهُ فِي قَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُؤتِيَهُ ٱللَّهُ ٱلكِتَبَ وَٱلحُكمَ وَٱلنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُواْ عِبَادا لِّي مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَكِن كُونُواْ رَبَّنِيِّنَ بِمَا كُنتُم تُعَلِّمُونَ ٱلكِتَبَ وَبِمَا كُنتُم تَدرُسُونَ٧٩ وَلَا يَأمُرَكُم أَن تَتَّخِذُواْ ٱلمَلَئِكَةَ وَٱلنَّبِيِّنَ أَربَابًا أَيَأمُرُكُم بِٱلكُفرِ بَعدَ إِذ أَنتُم مُّسلِمُونَ٨٠﴾ آل عمران: ٧٩ – ٨٠.

Dabi'a Ta: 56. Anbaton wadanda suke bin tsarin musulunci da shirka, kamar fadin (Allah) madaukakin sarki:

'' Bai taba kasancewa ga wani mutum dan Allah ya bas hi littafi da hukunci da kuma annabta sannan ya cewa mutane; ku kasance bayi na koma bayan Allah, saidai ku kasance masu reno (n al'umma) ta hanyar karantar da littafi (Alkur'ani) da kuma abinda ku ka kasance kuke karantowa. () kuma ba zai taba umanartarku ba da ku riki mala'iku da Annabawa abeban bauta, yanzu za su umarceku da kafirci bayan kuna musulmai''. Suratu Ali Imran.

اَلسَّاِبعَةُ وَالْخَمْسُونَ: تَحْرِيفُ اَلْكَلِمِ عَنْ مَوَاضِعِهِ.

Dabi'a Ta: 57. Canza zancan (Allah) daga yadda yake.

الثَّامِنَةُ وَالْخَمْسُونَ: لَيُّ اَلأَلْسِنَةِ بِالْكِتَابِ.

Dabi'a Ta: 58. Karkatar da harsuna wurin fassara littafin (Allah).

اَلتاَّسِعَةُ وَالْخَمْسُونَ: تَلْقِيبُ أَهْلِ اَلْهُدَى بِالصُّبَاةِ وَالْحَشْوِيَّةِ.

Dabi'a Ta: 59. Lakkabawa wadanda ke kan hanyar daidai (sunan) yarane ko marasa aikin yi.

اَلسِّتُّونَ: اِفْتِرَاءُ اَلْكَذِبِ عَلَى اَللهِ.

Dabi'a Ta: 60. Kagar karya a jinginawa Allah.

اَلْحَادِيَةُ وَالسِّتُّونَ: اَلتَّكْذِيبُ.

Dabi'a Ta: 61. Karyata (sakon Allah da manzan Sa).

اَلثَّانِيَةُ وَالسِّتُّونَ: كَوْنُهُمْ إِذَا غُلِبُواْ بِالْحُجَّةِ فَزِعُوا إِلَى اَلشَّكْوَى لِلْمُلُوكِ، كَمَا قَالوُا: ﴿ أَتَذَرُ مُوسَى وَقَومَهُ لِيُفسِدُواْ فِي ٱلأَرضِ ﴾الأعراف: ١٢٧.

Dabi'a Ta: 62. Yadda suka kasance idan an yi nasara akan su da hujjoji sais u dunguma su kai kuka ga sarakuna, kamar yadda (mutanan Fir'auna) suka ce:

'' Yanzu zaka bar Musa da jama'arsa su na barna a bayan kasa''.? Suratul A'araf, aya ta: 127.

اَلثَّالِثَةُ وَالسِّتُّونَ: رَمْيُهُم إِيّاهُمْ بِالْفَسَادِ فِي الأَرْضِ كَمَا فِي الآيَةِ.

Dabi'a Ta: 63. Yadda suke jifansu (wadanda ke kan shiriya) da barna adoron kasa, kamar yadda ya gabata a ayar.

اَلرَّابِعَةُ وَالسِّتُّونَ: رَمْيُهُم إِيَّاهُمْ بِانْتِقَاصِ دِينِ اَلْمَلِكِ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَ ﴾ الأعراف: ١٢٧، وَكَمَا قَالَ: ﴿ إِنِّي أَخَافُ أَن يُبَدِّلَ دِينَكُم ﴾ غافر: ٢٦.

Dabi'a Ta: 64. Yadda suke jifansu da rage darajar tsarin sarauta, kamar ya (Allah) maigirma da daukaka ya fada:

'' Su kyaleka da ababan bautarka''?. Suratul A'araf, aya ta: 127. Kuma kamar yadda (Allah) ya ce: '' Lalle ni (inji Fir'auna) ina jin tsoron kada ya canza muku addininku''. Suratu Zukhruf, aya ta: 26.

اَلْخَامِسَةُ وَالسِّتُّونِ: رَمْيُهُمْ إِيَّاهُمْ بِانْتِقَاصِ آلِهَةِ الْمَلِكِ، كَمَا فِي الآيَةِ.

Dabi'a Ta: 65. Yadda suke jifansu rage darajar abin bautar sarki, kamar yadda ya ke a ayar.

اَلسَّادِسَةُ وَالسِّتُّونَ: رَمْيُهُمْ إِيَّاهُمْ بِتَبْدِيلِ اَلدِّينِ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ إِنِّي أَخَافُ أَن يُبَدِّلَ دِينَكُم أَو أَن يُظهِرَ فِي ٱلأَرضِ ٱلفَسَادَ٢٦﴾ غافر: ٢٦.

Dabi'a Ta: 66. Yadda suke jifansu (wadanda suke kan hanyar daidai) da cewar suna canza addini (sun zo da sabon addini), kamar yadda (Allah) mai girma da daukaka ya ce:

''… (in ji Fir'auna) Laale ni ina tsoron kada ya canza muku addini ko kuma ya bayyanar da barna abayan kasa''. Suratul Ghafir, aya ta: 26.

اَلسَّابِعَةُ وَالسَّتُّونَ: رَمْيُهُمْ إِيَاهُمْ بِانْتِقَاصِ اَلْمَلِكِ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَ ﴾ الأعراف: ١٢٧.

Dabi'a Ta: 67. Yadda suke jifansu da rage darajar sarauta, kamar yadda suka ce: '' Ya kyaleka da ababan bautarka''. Suratul A'araf, aya ta: 127.

اَلثَّامِنَةُ وَالسَّتُّونَ: دَعْوَاهُمُ اَلْعَمَلَ بِمَا عِنْدَهُمْ مِنَ اَلْحَقَّ، كَقَوْلِهِم: ﴿ قَالُواْ نُؤمِنُ بِمَا أُنزِلَ عَلَينَا ﴾ البقرة: ٩١ مَعَ تَرْكِهِمْ إِيَّاهُ.

Dabi'a Ta: 68. Yadda wai suke cewa suna aiki da abinda yake wurin su na gaskiya, kamar yadda suka ce: '' Muna yin Imani ne da abinda aka saukar mana''. Bakara, aya ta: 91. Tare kuma basa aikin.

اَلتَّاسِعَةُ وَالسِّتُّونَ :الزِّيَادَةُ فِي اَلْعِبَادَةِ، كَفِعْلِهِمْ يَوْمَ عَاشُورَاءَ.

Dabi'a Ta: 69. Kari a ibada, kamar yadda suke yi ranan Ashurah.

اَلسَّبْعُونَ: نَقْصُهُم مِنْهَا، كَتَرْكِهِمُ اَلْوُقُوُفَ بِعَرَفَاتٍ.

Dabi'a Ta: 70. Yadda suke yage wani abu daga cikinta (ibadar) kamar yadda suke (tsayawa a muzdalifa) su ki tsaya a Arafat.

اَلْحَادِيَةُ وَالسَّبْعُونَ: تَرْكُهُمُ اَلْوَاجِبَ وَرَعًا.

Dabi'a Ta: 71. Yadda suke barin wajibi wai saboda tsantseni.

اَلثَّانِيَةُ وَالسَّبْعُونَ: تَعَبُّدُهُمْ بِتَرْكِ اَلطَّيِّبَاتِ مِنَ اَلرِّزْقِ.

Dabi'a Ta: 72. Yadda suke ibada ta hanyar kin cin abubuwa na halas da (Allah ya) bada su na arziki.

اَلثَّالِثَةُ وَالسَّبْعُونَ: تَعَبُّدُهُمْ بِتَرْكِ زِينَةِ اللهِ.

Dabi'a Ta:73. Yadda suke su ka dauka ibada ne barin sa kaya na ado da Allah ya azurta su da shi.

اَلرَّابِعَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَتُهُمُ اَلناَّسَ إِلَى اَلضَّلاَلِ بِغَيْرِ عِلْمٍ.

Dabi'a Ta: 74. Yadda suke kiran mutane zuwa bata ba tare da wani ilimi ba.

اَلْخَامِسَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَتُهُمْ إِيَّاهُمْ إِلَى اَلْكُفْرِ مَعَ اَلْعِلْمِ.

Dabi'a Ta: 75. Yadda suke kiran mutane zuwa ga kafirci alhalin suna sane.

اَلسَّادِسَةُ وَالسَّبْعُونَ: اَلْمَكْرُ اَلْكُبَّارُ، كَفِعْلِ قَوْمِ نُوحٍ.

Dabi'a Ta: 76. Kulla manyan-manyan makirci, kamar dai yadda mutanan Annabi Nuh su ka yi.

اَلسَّابِعَةُ وَالسَّبْعُونَ: أَنَّ أَئِمَّتَهُمْ إِمَّا عَالِمٌ فَاجِرٌ، وَإِمَّا عَابِدٌ جَاهِلٌ، كَمَا فِي قَوْلِهِ: ﴿ وَقَد كَانَ فَرِيق مِّنهُم يَسمَعُونَ كَلَمَ ٱللَّهِ ﴾ إِلَى قَوْلِهِ: ﴿وَمِنهُم أُمِّيُّونَ لَا يَعلَمُونَ ٱلكِتَبَ إِلَّا أَمَانِيَّ وَإِن هُم إِلَّا يَظُنُّونَ٧٨﴾ البقرة:75 – ٧٨.

Dabi'a Ta: 77. Lalle jagororin su kodai fandararran malami, ko kuma wani mai ibada da yake tintirin jahili, kamar yadda (Allah madaukakin sarki) yace:

'' Kuma hakika wasu jama'a daga cikinsu sun kasance suna sauraron zancan Allah)) hardai zuwa inda Allah ya ce ((Kuma akwai daga cikin su wadanda suke basu iya rubutu ba kuma basu iya karatuba saidai karyace-karyace (shi suka iya). Suratul Bakara, aya ta: 75-78.

اَلثَّامِنَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَاهُمْ أَنَّهُمْ أَوْلِيَاءُ اَللهِ مِنْ دُونِ الناَّسِ.

Dabi'a Ta: 78. Yadda suke cewa su waliyyan Allah ne banda sauran mutane.

اَلتَّاسِعَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَاهُمْ مَحَبَّةَ اَللهِ مَعَ تَرْكِهِمْ شَرْعَهُ، فَطَالَبَهُمُ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿قُل إِن كُنتُم تُحِبُّونَ ٱللَّهَ ﴾ آل عمران: ٣١.

Dabi'a Ta: 79. Yadda suke cewa wai suna son Allah, amma kuma basa bin shari'ar Sa, sai Allah ya kalubalance su da fadin Sa: '' Ka ce: (Har) in kun kasance kuna son Allah (To ku bini, sai Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku). Suratu Ali Imran, aya ta: 31.

اَلثَّمَانُونَ: تَمَنِّيهِمُ اَلأَمَانِيَّ اَلْكَاذِبَةَ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ لَن تَمَسَّنَا ٱلنَّارُ إِلَّا أَيَّاما مَّعدُودَة﴾ البقرة: ٨٠. وَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ لَن يَدخُلَ ٱلجَنَّةَ إِلَّا مَن كَانَ هُودًا أَو نَصَرَى ﴾ البقرة: ١١١.

Dabi'a Ta: 80. Yadda su ke burace-burace na karya, kamar yadda suka ce:

'' Ai wuta ba zata taba shafarmu ba sai wasu kwanaki kididdigaggu''. Suratul Bakara, aya ta: 80. Da kuma fadin su: '' Ba mai taba shiga aljanna sai wanda ya kasance bayahude (inji yahudawa) ko nasara (inji kiristoci)''. Suratul Bakara, aya ta: 111.

اَلْحَادِيَةُ وَالثَّمَانُونَ: اتِّخَاذُ قُبُورِ أَنْبِيَائِهِمْ وَصَالِحِيهِمْ مَسَاجِدَ.

Dabi'a Ta: 81. Yadda suke daukar kabarurrukan Annabawan su da kuma na salihan bayin cikinsu masallatai. (kawai sai su gina masallaci a kabarin wani Annabi ko wani salihin bawa).

اَلثَّانِيَةُ وَالثَّمَانُونَ: اِتِّخَاذُ آثَارِ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ كَمَا ذَكَرَ عَنْ عُمَرَ.

Dabi'a Ta: 82. Yadda suke daukar wuraran tarihi na Annabawa (sai su gida) masallatai, kamar yadda aka ruwaito da Umar (dan Khaddab, ya sare bishiyar da aka yi mubaya'a a karkashinta, domin mutane su na shafarta da neman albarka…''.

اَلثَّالِثَةُ وَالثَّمَانُونَ: اِتِّخَاذُ السُّرُجِ عَلَى اَلْقُبُورِ.

Dabi'a Ta: 83. Yadda suke sanya futulu a makabartu.

اَلرَّابِعَةُ وَالثَّمَانُونَ: اِتِّخَاذُهَا أَعْياَدًا.

Dabi'a Ta: 84. Yadda suke daukar su (makabartun) wuraran idi (shekara-shekara).

اَلْخَامِسَةُ وَالثَّمَانُون: اَلذَّبْحُ عِنْدَ اَلْقُبُورِ.

Dabi'a Ta: 85. Yadda suke yanke-yanke a wuraran kabarurrukan.

اَلسَّادِسَةُ وَالثَّمَانُونَ: اَلتَّبَرُّكُ بِآثَارِ اَلْمُعَظَّمِينَ كَدَارِ النَّدْوَةَ، وَافْتِخَارِ مَنْ كَانَتْ تَحْتَ يَدِهِ، كَمَا قِيلَ لِحَكِيمِ بنِ حِزَامٍ: بِعْتَ مَكْرُمَةَ قُرَيْشٍ. فَقَالَ: ذَهَبَتِ اَلْمَكَارِمُ إِلاَّ اَلتَّقْوَى.

Dabi'a Ta: 86. Neman albarka daga wuraran da suke girmamawa, kamar gidan taron su (Darun Nadawa), da kuma alfahari na wanda yake kula da gidan, kamar yadda aka cewa Hakim dan Hizam; Kasayar da darajar kuraishawa'. Sai ya ce: Dukkanin daraja ta tafi saidai tsoron Allah.

اَلسَّابِعَةُ وَالثَّمَانوُن: اَلْفَخْرُ باِلأَحْسَابِ.

Dabi'a Ta: 87. Alfahari da dangantaka.

اَلثَّامِنَةُ وَالثَّمَانُونَ: اَلطَّعْنُ فِي اَلأَنْسَابِ.

Dabi'a Ta: 88. Sukar dangantakar (wasu).

اَلتَّاسِعَةُ وَالثَّمَانُونَ: اَلاِسْتِسْقَاءُ بِالأَنْوَاءِ.

Dabi'a Ta: 89. Rokon ruwa ta hanyar taurarai

اَلتِّسْعُونَ: اَلنِّيَاحَةُ.

Dabi'a Ta: 90. Kukan mutuwa.

اَلْحَادِيَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ أَجَلَّ فَضَائِلِهِمُ اَلْبَغْيُ، فَذَكَرَ اَللهُ فِيهِ مَا ذَكَرَ.

Dabi'a Ta: 91. Lalle mafi girman matsayi a wurin su shine; Zalinci. Sai Allah madaukakin sarki ya anbaci bayanai akan zalinci da azzalumai irin abinda ya anbata (akan su).

اَلثَّانِيَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ أَجَلَّ فَضَائِلِهِمُ اَلْفَخْرُ، وَلَوْ بِحَقٍّ، فَنُهِيَ عَنْهُ.

Dabi'a Ta: 92. Lalle mafi girman matsayi a wurin su shi ne; Alfari, ko da ko da hakki ne, sai akan hana.

اَلثَّالِثَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ تَعَصُّبَ اَلإِنْسَانِ لِطَائِفَتِهِ عَلَى اَلْحَقِّ وَالْبَاطِلِ أَمْرٌ لاَ بُدَّ مِنْهُ عِنْدَهُمْ، فَذَكَرَ اَللهُ فِيهِ مَا ذَكَرَ.

Dabi'a Ta: 93. Lalle mutum ya makalkalewa (ra'ayin) jama'arsa akan gaskiya ko akan karya, wannan abune da ya zama ba makawa a wurin su, sai Allah ya anbaci bayani akan hakan irin bayanan da ya anbata.

اَلرَّابِعَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ مِنْ دِينِهِمْ أَخْذَ اَلرَّجُلِ بِجَرِيـمَةِ غَيْرِهِ، فَأَنْزَلَ اَللهُ: ﴿ وَلَا تَزِرُ وَازِرَة وِزرَ أُخرَى﴾لإسراء: ١٥.

Dabi'a Ta: 94. Yana daga cikin tsarin addinin su akama mutum da laifin da wani ya aikata, sai Allah ya saukar da:

'' Rai ba ta daukar laifin wata rai'' Suratu Isra'i, aya ta:15.

اَلْخَامِسَةُ وَالتِّسْعُونَ: تَعْيِيرُ اَلرَّجُلِ بـمَا فِي غَيْرِهِ، فَقَالَ: ((أَعَيَّرْتَهُ بِأُمِّهِ؟ إِنَّكَ اَمْرُؤٌ فِيكَ جَاهِلِيَّةٌ)).

Dabi'a Ta: 95. Muzanta mutum da abinda bai da shi. (da wani ya yi haka, sai ma'aikin Allah ya ce; Yanzu zaka muzanta shi gyatumarsa (mahaifiyarsa), lalle kai mutumne da akwai jahiyya a tare da kai''.

اَلسَّادِسَةُ وَالتِّسْعُونَ: اَلاِفْتِخَارُ بِوَلاَيَةِ اَلْبَيْتِ، فَذَمَّهُمُ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿مُستَكبِرِينَ بِهِ سَمِرا تَهجُرُونَ٦٧﴾ المؤمنون: ٦٧.

Dabi'a Ta: 96. Alfahari da cewar (mu) muke kula da dakin (Ka'abah), sai Allah ya zarge su da fadar Sa: '' Su na ta girman kai (alfahari) da shi, sun a fira, su na kuma kaurace masa''. Suratul Mu'aminun, aya ta: 67.

اَلسَّابِعَةُ وَالتِّسْعُونَ: اَلاِفْتِخَارُ بِكَوْنِهِمْ ذُرِيَّةَ اَلأَنْبِيَاءِ، فَأَتَى اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿تِلكَ أُمَّة قَد خَلَت لَهَا مَا كَسَبَت﴾ البقرة: ١٣٤.

Dabi'a Ta: 97. Alfari da cewa ai su zuriyar Annabawa ne, sai Allah ya zo da fadar Sa: ''Waccan al'umma ce da ta riga ta wuce, ta na da abinda ta aikata, (Kuma kuna da abinda kuma aikata)''. Suratul Bakarah, aya ta: 134.

اَلثَّامِنَةُ وَالتِّسْعُونَ: اَلاِفْتِخَارُ بِالصَّنَائِعِ، كَفِعْلِ أَهْلِ اَلرِّحْلَتَيْنِ عَلَى أَهْلِ اَلْحَرْثِ.

Dabi'a Ta: 98. Alfahari da kere-kere, kamar yadda ma su tafiyoyi biyun nan (lokacin bazara da lokaci sanyi) suke alfahari akan manoma.

اَلتَّاسِعَةُ وَالتِّسْعُونَ: عَظَمَةُ اَلدُّنْيَا فِي قُلُوبِهِمْ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ لَولَا نُزِّلَ هَذَا ٱلقُرءَانُ عَلَى رَجُل مِّنَ ٱلقَريَتَينِ عَظِيمٍ٣١﴾ الزخرف: ٣١.

Dabi'a Ta: 99. Yadda duniya take da girma a zukatan su, kamar yadda suka ce:

'' Damme ba'a saukar da wannan Alkur'ani ba ga wani mutum daga garuruwan nan biyu ba mai girma''. Suratuz Zukhruf, aya ta: 31.

اَلْمِائَةُ: اَلتَّحَكُّمُ عَلَى اَللهِ، كَمَا فِي اَلآيَةِ.

Dabi'a Ta: 100. Cewa Allah damme?, kamar yadda ya zo a ayar data gabata.

اَلْحَادِيَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اِزْدِرَاءُ اَلْفُقَرَاءِ، فَأَتَاهُمْ بِقَوْلِهِ: ﴿وَلَا تَطرُدِ ٱلَّذِينَ يَدعُونَ رَبَّهُم بِٱلغَدَوةِ وَٱلعَشِيِّ ﴾ الأنعام: ٥٢ .

Dabi'a Ta: 101. Wulakantar da talakawa, sai (Allah) ya zo musu da fadarsa:

''Kada ka kori wadanda su ke kiran Ubangijinsu da safiya da kuma yammaci''. Suratul An'am, aya ta: 52.

اَلثَّانِيَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: رَمْيُهُمْ أَتْبَاعَ اَلرُّسُلِ بِعَدَمِ اَلإِخْلاَصِ وَطَلَبِ اَلدُّنْيَا، فَأَجَابَهُمُ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿ مَا عَلَيكَ مِن حِسَابِهِم مِّن شَيء ﴾ الأنعام: ٥٢ وَأَمْثَالِهَا.

Dabi'a Ta: 102. Yadda su ke aibanta mabiya manzanni da cewar; Ai badon Allah su ke yi ba, kuma diniya su k enema, sai Allah ya amsa musu (da wannan ayar) da ire-iren ta, da fadin Sa : '' Ba'a dora maka wani na hisabin su komai kankantar shi''. Suratul An'am, aya: 52.

اَلثَّالِثَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرُ بِالْمَلاَئِكَةِ.

Dabi'a Ta: 103. Kafircewa mala'ikun Allah.

اَلرَّابِعَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرُ بِالرُّسُلِ.

Dabi'a Ta: 104. Kafircewa manzannin Allah.

اَلْخَامِسَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرُ بِالْكُتُبِ.

Dabi'a Ta: 105. Kafircewa littafan Allah.

اَلسَّادِسَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلإِعْرَاضُ عَمَّا جَاءَ عَنِ اَللهِ.

Dabi'a Ta: 106. Kaudakai daga abinda ya zo daga wurin Allah.

اَلسَّابِعَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرِ بِالْيَوْمِ اَلآخِرِ.

Dabi'a Ta: 107. Kinyarda da cewa akwai ranar lahira.

اَلثَّامِنَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلتَّكْذِيبُ بِلِقَاءِ اَللهِ.

Dabi'a Ta: 108. Karyata cewa ba za su taba haduwa da Allah.

اَلتَّاسِعَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلتَّكْذِيبُ بِبَعْضِ مَا أَخْبَرَتْ بِهِ اَلرُّسُلُ عَنِ اَلْيَوْمِ اَلآخِرِ،كَمَا فِي قَوْلِهِ: ﴿أُوْلَئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَِايَتِ رَبِّهِم وَلِقَائِهِ فَحَبِطَت أَعمَلُهُم فَلَا نُقِيمُ لَهُم يَومَ ٱلقِيَمَةِ وَزنا١٠٥﴾ الكهف: ١٠٥. وَمِنْهَا اَلتَّكْذِيبُ بِقَوْلِهِ: ﴿مَلِكِ يَومِ ٱلدِّينِ٤﴾ الفاتحة: ٤. وَقَوْلِهِ: ﴿ لَّا بَيع فِيهِ وَلَا خُلَّة وَلَا شَفَعَة ﴾ البقرة: ٢٥٤. وَقَوْلِهِ:﴿ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلحَقِّ وَهُم يَعلَمُونَ٨٦﴾ الزخرف: ٨٦.

Dabi'a Ta: 109. Karyata wani sashi na abinda manzanni suka bada labarinsa dangane da ranar tashin alkiyama, kamar yadda (Allah) ya ce:

''Wadan nan su ne fa wadanda suka kafircewa Ubangijinsu da kuma haduwa da Shi''. Suratul Kahf, aya ta:105, kuma yana daga ciki; Karyata zancan Sa (Shi Allah madaukakin sarki): ''Mamallakin ranar sakamako''. Suratul Fatiha, aya ta:4. Da kuma fadansa (Shi Allah): '' Babu wani saye da sayarwa babu kuma kauna kuma babu ceto''. Suratul Bakarah, aya ta:254. Da kuma fadan Sa: '' Sai kawai wanda ya shaida da gaskiya kuma su na sane''. Suratuz Zukhruf, aya ta: 86.

اَلْعَاشِرَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: قَتْلُ اَلَّذِينَ يَأْمُرُونَ بِالْقِسْطِ مِنَ اَلنَّاسِ.

Dabi'a Ta: 110. Kashe wadanda suke umarnin a tsayar da adalci a cikin al'umma.

اَلْحَادِيَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلإِيـمَانُ بِالْجِبْتِ وَالطَّاغُوتِ.

Dabi'a Ta: 111. Yarda da bokaye ('yanbori) da duk wani abu da ya sabawa tsarin Allah.

اَلثَّانِيَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: تَفْضِيلُ دِينِ اَلْمُشْرِكِينَ عَلَى دِينِ اَلْمُسْلِمِينَ.

Dabi'a Ta: 112. Fifita tsarin mushirikai akan addinin musulunci.

اَلثَّالِثَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: لَبْسُ اَلْحَقِّ بِالْبَاطِلِ.

Dabi'a Ta: 113. Rufe gaskiya da karya.

اَلرَّابِعَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: كِتْمَانُ اَلْحَقِّ مَعَ اَلْعِلْمِ بِهِ.

Dabi'a Ta: 114. Boye gaskiya tare da sun santa.

اَلْخَامِسَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: قَاعِدَةُ اَلضَّلاَلِ، وَهِيَ اَلْقَوْلُ عَلَى اَللهِ بِلاَ عِلْمٍ.

Dabi'a Ta: 115. Babbar ka'ika akan bata ita ce kuwa: A fadi Magana dan gane da Allah ba tare da sani ba.

اَلسَّادِسَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلتَّنَاقُضُ اَلْوَاضِحُ لِمَا كَذَّبُواْ بِالْحَقِّ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿بَل كَذَّبُواْ بِٱلحَقِّ لَمَّا جَاءَهُم فَهُم فِي أَمر مَّرِيجٍ٥﴾ ق: ٥.

Dabi'a Ta: 116. Tufka da warware a bayyane na abinda suka karyata na gaskiya, kamar yadda (Allah) madaukakin sarki ya ce:

'' A'a, sun karyata da gaskiya a lokacin da (gaskiyar) ta zo mu su, to su fa suna cikin wani al'amari mai rikitarwa.''. Suratu Kaaf, aya ta: 5.

اَلسَّابِعَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلإِيـمَانُ بِبَعْضِ اَلْمُنَزَّلِ دُونَ بَعْضٍ.

Dabi'a Ta: 117. Imani da wani sashi na abinda aka saukar da (kuma kafircewa) wani sashi.

اَلثَّامِنَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلتَّفْرِيقُ بَيْنَ اَلرُّسُلِ.

Dabi'a Ta: 118. Rarrabe tsakanin manzanni (sai su yarda da wasu su ki yarda da wasu).

اَلتَّاسِعَةَ عَشْرَةَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: مُخَاصَمَتُهُمْ فِيمَا لَيْسَ لَهُمْ بِهِ عِلْمٌ.

Dabi'a Ta: 119. Jayayya akan abinda ba su da ilimi akan shi.

اَلْعِشْرُونَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: دَعْوَاهُمُ اَتِّبَاعَ اَلسَّلَفِ مَعَ اَلتَّصْرِيحِ بِمُخَالَفَتِهِمْ.

Dabi'a Ta: 120. Yadda suke cewa wai su na bin (karantarwar) magabata amma kuma ga shi afili su na sabawa karantarwar ta su.

اَلْحَادِيَةُ وَالْعِشْرُونَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: صَدُّهُمْ عَنْ سَبِيلِ اَللهِ مَنْ آمَنَ بِهِ.

Dabi'a Ta: 121. Yadda su ke hana duk wanda ya yi Imani (su hana shi) bin karantarwar Allah (Mai girma da daukaka).

اَلثَّانِيَةُ وَالْعِشْرُونَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: مَوَدَّتُهُمُ اَلْكُفْرَ وَالْكَافِرِينَ.

Dabi'a Ta: 122. Yadda su ke kaunar kafirci da kuma kafirai.

اَلثَّالِثَةُ وَالْعِشْرُونَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ وَالرَّابِعَةُ وَالْخَامِسَةُ وَالسَّادِسَةُ وَالسَّابِعَةُ وَالثَّامِنَةُ وَالْعِشْرُونَ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْعِيَافَةُ، وَالطَّرْقُ، وَالطِّيَرَةُ، وَالْكِهَانَةُ، وَالتَّحَاكُمُ إِلَى اَلطَّاغُوتِ، وَكَرَاهَةُ اَلتَّزْوِيجِ بَيْنَ اَلْعَبْدَيْنِ. وَاَللهُ أَعْلَمُ.

Dabi'a Ta: 123. Zaburar da tsuntsaye (idan su ka waste to inda suka nufa nana sa'a ta ke, wannan wani nau'ine na canfi da tsunye da su ke yi).

Dabi'a Ta: 124. Zane a kasa (duba).

Dabi'a Ta: 125. Canfi.

Dabi'a Ta: 126. Bokanci.

Dabi'a Ta: 127. Kai kara ga dagutai (tsarin da ba na Allah ba).

Dabi'a Ta: 128. Kyamatar kulla aure tsakanin bawa da baiwa, (to idan ya kasance an kyamaci kulla aure tsakanin kabilu biyu ne fa!). Allah Shi ne masani.

وَصَلَّى اَللهُ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِهِ وَصَحْبِهِ وَسَلَّمَ.

Allah Ya yi dadin tsira ga (Annabi) Muhammad da iyalan Shi da kuma sahabban Shi da kuma aminci.

Takaitaccan Tarihin Mawallafi.

Shi ne: Imam Muhammad dan Abdulwahhab dan Sulaiman dan Aliyu dan Muhammad dan Ahmad, daga kabilar Tamim. Ana mishi lakabi: Shehul Islam, Mujaddadi.

An haife shi a garin Uyaina dake arewa maso gabas da birni Riyadh, a shekara ta 1115, (bayan hijira), kuma anan ya tashi, a gidan na su da yake cike da ilimi da kuma kula.

Ya kamala haddace Alkur'ani mai girma alokacin shekarunsa na haihuwa ba su kai goma ba, a hannun mahaifinsa. Ya yi fice a fannoni da dama kamar Fikihu da Hadisi da Tauhidi da kumaTafsiri.

Ya yi tafiye-tafiya da dama domin neman ilimi, ya je birnin Makkah domin yin aikin hajji kuma ya yi anfani da wannan tafiya ya yi karatu awurin manyan malaman Makkah na wannan lokacin, kuma ya je birnin Madina ya kuma jima a wannan birni domin neman ilimi, haka nan kuma ya je kasar Iraki ya kuma jima a Basrah, ya kuma yi karatu a gaban malaman wannan gari, haka nan kuma ya je Ahsah, ya yi anfani da wadannan tafiye-tafye domin neman ilimi da kuma isar da sakon Allah madaukakin sarki (wato Da'awah).

Ya yi karatu a gaban malamai da dama, ga kadan daga cikin su:

6. Mahaifinsa Shehun malami Abdulwahhab dan Sulaiman.

7. Shehun malami Shihabuddin Alkalin Basrah.

8. Shehun malami Abdullah dan Muhammad dan Abdulladif.

9. Shehun malami Muhammad dan Hayatu Sindi.

10. Shehun malami Abdullah dan Ibrahim dan Yusuf.

Haka kuma yana da dailibai masu tarin yawa, daga cikinsu akwai:

6. Shehun malami Ahmad dan Suwailim.

7. Shehun malami Aliyu dan Muhammad dan Abdulwahhab.

8. Shehun malami Abdurrahman dan Hasan dan Muhammad.

9. Shehun malami Imam Abdul'aziz dan Muhammad dan Sa'ud.

10. Shehun malami Husain dan Ganam.

Wannan shehun malami mawallafin wannan littafi ya karar da rayuwarsa ne wurin karantarwa da fadakarda da kiran mutane akan su kasance a asalin karantarwar musulunci da Allah ya aiko manzan Shi da ita, akan haka ake kiran shi da mujaddadi, domin ya samu jama'a da yawa ana tafiya ne akan tatsunuyoyi da neman bukatu a kabarurruka da kiran matattu akan su kawo a gaji dadai sauran su.

Ya wallafa littafai da dama, daga cikin su akwai:

9. Takaitaccan Tarihin Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), (Mukhtasaru Siratur Rasuli Sallallahu Alaihi wa sallam).

10. Munanan Dabi'un Maguzawa (Masa'ilul Jahiliyya).

11. Ladubban Tafiya Sallah (Aadabul Mashyi Ilas Salah).

12. Tushen Imani (Usulul Iman).

13. Ginshikai Uku. (Usulus Salasa).

14. Ka'idoji Hudu (Alkawa'idul Arba'ah).

15. Yaye Batutuwa Masu Rikitarwa (Kashfus Shubuhat).

16. Littafin Tauhidi (Kitabut Tauhid). Da wasu littafan masu tarin yawa.

Ya rasu a shekara ta: 1206. (bayan hjira), bayan ya shafe kusan shekaru (91), Allah ya ji kansa da gafara ya kuma rahamshe shi, in ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da Imani, amin.

[مُقَدِّمَةُ اَلْمُؤَلِّفِ]

بِسْمِ اَللهِ اَلرَّحْمَنِ اَلرَّحِيمِ

قَالَ اَلشَّيْخُ مُحَمَّدُ بْنُ عَبْدِ اَلْوَهَّابِ رَحِمَهُ اَللهُ تَعَالَى:

هَذِهِ أُمُورٌ خَالَفَ فِيهَا رَسُولُ اَللهِ ﷺ‬ مَا عَلَيْهِ أَهْلُ اَلْجَاهِلِيَّةِ اَلْكِتَابِيِّينَ وَالأُمِّيِّينَ، مِمَّا لاَ غِنَى لِلْمُسْلِمِ عَنْ مَعْرِفَتِهَا.

فَالضِّدُ يُظْهِرُ حُسْنَهُ اَلضِّدُّ # وَبِضِدِّهَا تَتَبَيَّنُ اَلأَشْيَاءُ.

فَأَهَمُّ مَا فِيهَا وَأَشَدُّهَا خَطَرًا عَدَمُ إِيـمَانِ اَلْقَلْبِ بِمَا جَاءَ بِهِ اَلرَّسُولُ ﷺ‬ فَإِنِ اِنْضَافَ إِلَى ذَلِكَ اِسْتِحْسَانُ مَا عَلَيْهِ أَهْلُ اَلْجَاهِلِيَّةِ تَمَّتِ اَلْخَسَارَةُ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلبَطِلِ وَكَفَرُواْ بِٱللَّهِ أُوْلَئِكَ هُمُ ٱلخَسِرُونَ٥٢﴾ العنكبوت: ٥٢.

Gabatarwal Mawallafi.

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai.

Shaikh Muhammad dan Abdulwahhab Allah ya yi masa rahama ya ce:

Wadannan nan wadansu halayene da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya sabawa wadanda suke kan maguzanci yahudu da nasara dama 'yan gargajiya, abinda yake da matukar muhimmanci musulmi ya san su, wani abu kishiyarshi shi yake bayyanar da kyawunsa, abubuwa kishiyoyinsu ne suke bayyanar da kyawunsu.

Mafi girman abindake cikin wadan nan halaye kuma wacce ta fi kowacce hadari shine rashin Imani da zuciya bata yi ba da abin da ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) yazo da shi. Idan ko aka kara akan haka da ganin kyawun abinda su Ahlul Jahiyyah suke akai to kan an gama asara, kamar yadda Allah ya ce:

''Dukkanin wadanda suka yi Imani da karya kuma suka kafircewa Allah to wadan nan su ne asararru.'' (Suratul Ankabut, aya ta: 52).

اَلْمَسْأَلَةُ اَلأُولَى: أَنَّهُمْ يَتَعَبَّدُونَ بِإِشْرَاكِ اَلصَّالِحِينَ فِي دُعَاءِ اَللهِ وَعِبَادَتِهِ، يُرِيدُونَ شَفَاعَتَهُمْ عِنْدَ اَللهِ لِظَنِّهِمْ أَنَّ اَللهَ يُحِبُّ ذَلِكَ، وَأَنَّ اَلصَّالِحِينَ يُحِبُّونَهُ، كَمَا قَالَ تَعَالَى ﴿وَيَعبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَيَقُولُونَ هَؤُلَاءِ شُفَعَؤُنَا عِندَ ٱللَّهِ ١٨﴾ يونس: ١٨، وَقَالَ تَعَالَى:﴿أَلَا لِلَّهِ ٱلدِّينُ ٱلخَالِصُ وَٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِ أَولِيَاءَ مَا نَعبُدُهُم إِلَّا لِيُقَرِّبُونَا إِلَى ٱللَّهِ زُلفَى ﴾ الزمر: ٣، وَهَذِهِ أَعْظَمُ مَسْأَلَةٍ خَالَفَهُمْ فِيهَا رَسُولُ اَللهِ ﷺ‬، فَأَتَى بِالإِخْلاَصِ، وَأَخْبَرَ أَنَّهُ دِينُ اَللهِ اَلَّذِي أَرْسَلَ بِهِ جَمِيعَ اَلرُّسُلِ، وَأَنَّهَ لاَ يَقْبَلُ مِنَ اَلأَعْمَالِ إِلاَّ اَلْخَالِصَ، وَأَخْبَرَ أَنَّ مَنْ فَعَلَ مَا اَسْتَحْسَنُواْ فَقَدْ حَرَّمَ اَللهُ عَلَيْهِ اَلْجَنَّةَ، وَمَأْوَاهُ اَلنَّارُ.

وَهَذِهِ هِيَ اَلْمَسْأَلَةُ اَلَّتِي تَفَرَّقَ اَلنَّاسُ لأَجْلِهَا بَيْنَ مُسْلِمٍ وَكَافِرٍ، وَعِنْدَهَا وَقَعَتِ اَلْعَدَاوَةُ، وَلأَجْلِهَا شُرِعَ اَلْجِهَادُ، كَمَا قَالَ تَعَالَى ﴿وَقَتِلُوهُم حَتَّى لَا تَكُونَ فِتنَة وَيَكُونَ ٱلدِّينُ كُلُّهُ لِلَّهِ فَإِنِ ٱنتَهَواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِمَا يَعمَلُونَ بَصِير٣٩﴾[الأنفال: ٣٩.]

Dabi'a Ta: 1. Lalle sun kasance suna bauta ta hanyar hada salihan bayi wurin kiran Allah da kuma bauta masa, suna fatan samun ceton su a wurin Allah, saboda zaton da suke yin a Allah na son hakan, kuma alle su salihan bayin suna son kana, kamar yadda Allah ya ce: ''Kuma suna bautawa koma bayan Allah, abinda ba zai cutar da su ba (idan sun ki bauta masa) kuma ba zai anfanar da sub a (idan sun bauta masa) kuma suna cewa; Wadan nan su ne masu cetommu a wurin Allah''. Suratu Yunus, aya ta:18.

Kuma Allah madaukakin sarki ya ce: ''Duk wadanda suka riki koma bayansa (Shi Allah) amatsayin waliyyan, (cewa suke) ba komai ya sa muke bauta musuba sai domin su kara kusantar da mu zuwa ga Allah''. Suratu Zumar, aya ta:3.

Wannan itace mafi girman dabi'a da Ma'aikin Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya saba musu, sai ya zo da Ihlasi, (wato kadaita Allah), kuma ya bada labarin cewa shine addinin Allah da ya turo dukkanin manzanni, kuma lalle (shi) Allah baya karbar duk wani aiki sai wanda aka yi domin shi kadai, kuma ya bada bayanin cewa duk wanda ya aikata abinda su (Ahalul Jahiliyyah) suka ga kyawunsa to lalle Allah ya haramta masa shiga aljanna, kuma makomarsa itace wuta.

Wannan fa shine abinda ya ke sabo da shine mutane suka kasu gida biyu: Musulmi da kafiri, kuma akantane kiyayya ta auku, kuma saboda itane aka shar'anta jihadi, kamar yadda Allah yake cewa:

''Kuma ku dinga yakarsu har sai an kakkabe dukkan wata fitina (Shirka) kuma addini dukkansa ya na Allah ne (wato Allah kadai ake bautawa)''. Suratul Anfal, aya ta: 39.

اَلثَّانِيَةُ: أَنَّهُمْ مُتَفَرِّقُونَ فِي دِينِهِمْ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ كُلُّ حِزبِ بِمَا لَدَيهِم فَرِحُونَ٣٢﴾ الروم: ٣٢، وَكَذَلِكَ فِي دُنْيَاهُمْ، وَيَرَوْنَ أَنَّ ذَلِكَ هُوَ اَلصَّوَابُ، فَأَتَى بِالاِجْتِمَاعِ فِي اَلدِّينِ بِقَوْلِهِ: ﴿شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّى بِهِ نُوحا وَٱلَّذِي أَوحَينَا إِلَيكَ وَمَا وَصَّينَا بِهِ إِبرَهِيمَ وَمُوسَى وَعِيسَى أَن أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِ كَبُرَ عَلَى ٱلمُشرِكِينَ مَا تَدعُوهُم إِلَيهِ ٱللَّهُ يَجتَبِي إِلَيهِ مَن يَشَاءُ وَيَهدِي إِلَيهِ مَن يُنِيبُ١٣﴾ الشورى: ١٣. وَقَالَ تَعَالَى ﴿إِنَّ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُم وَكَانُواْ شِيَعا لَّستَ مِنهُم فِي شَيءٍ إِنَّمَا أَمرُهُم إِلَى ٱللَّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُواْ يَفعَلُونَ١٥٩﴾ الأنعام: ١٥٩ وَنَهَاهُمْ عَنْ مُشَابَهَتِهِمْ بِقَوْلِهِ ﴿وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ تَفَرَّقُواْ وَٱختَلَفُواْ مِن بَعدِ مَا جَاءَهُمُ ٱلبَيِّنَتُ وَأُوْلَئِكَ لَهُم عَذَابٌ عَظِيم١٠٥﴾ آل عمران: ١٠٥ وَنَهَاهُمْ عَنِ اَلتَّفَرُّقِ فِي اَلدُّنْيَا بِقَوْلِهِ: ﴿وَٱعتَصِمُواْ بِحَبلِ ٱللَّهِ جَمِيعا وَلَا تَفَرَّقُواْ ١٠٣﴾ آل عمران: ١٠٣.

Dabi'a Ta: 2. Lalle kansu a rarrabe wurin bin addinsu, kamar yadda Allah ya ke cewa: ''Kowacce tawaga da abinda ke gabansu suke alfahari''. Suratu Rum, aya ta:32.

Haka kuma a harkarsu ta duniya, har ma suke ganin hakan shine daidai, sai (Ma'aikin Allah) ya zo da hadinkai akan abi addini guda, Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Anshar'anta muku abinda yake na addini dukkanin abinda aka yi wasiyyarsa ga (Annabi) Nuhu, da kuma wanda muka yi wahayinsa zuwa ga reka, da dukkan abinda muka yi wahayinsa ga (Annabi) Ibrahim da Musa da Isa, akan ku tsayar da addini kada ku rarraba a cikin sa''. Suratus Shura, aya ta:13.

Kuma Allah ya ce: ''Lalle dukkanin wadanda suka yi wa addinin su a yaga suka kasance kungiya-kungiya baka kasance a cikinsu a kowacce ba''. Suratul An'ama, aya ta: 159.

Kuma Allah ya hana su (Al'ummar musulmai) kamanceceniya da su (Ahlul jahiliyya) inda yake cewa: ''Kada ku kasance kamar wadannan da suka rarraba kuma suka sassaba bayan hujjojin sun zo musu''. Suratu Ali Imran, aya ta:105.

Kuam (Allah) ya hana rarraba akan al'amuran duniya inda yake cewa: ''Ku yi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba''. Suratu Ali Imran, aya ta: 103.

اَلثَّالِثَةُ: أَنَّ مُخَالَفَةَ وَلِيِّ اَلأَمْرِ وَعَدَمِ اَلاِنْقِيَادِ لَهُ فَضِيلَةٌ، وَالسَّمْعَ وَالطَّاعَةَ لَهُ ذُلٌّ وَمَهَانَةٌ، فَخَالَفَهُمْ رَسُولُ اَللهِ ﷺ‬، وَأَمَرَهُمْ بِالصَّبْرِ عَلَى جَوْرِ اَلْوُلاَةِ، وَأَمَرَ بِالسَّمْعِ وَالطَّاعَةِ لَهُمْ وَالنَّصِيحَةِ، وَغَلَّظَ فِي ذَلِكَ، وَأَبْدَأَ وَأَعَادَ.

وَهَذِهِ اَلثَّلاَثُ هِيَ اَلَّتِي جَمَعَ بَيْنَهَا فِيمَا صَحَّ عَنْهُ ﷺ‬ فِي ((اَلصَّحِيحَيْنِ)) أَنَّهُ قَالَ: (( إِنَّ اَللهَ يَرْضَى لَكُمْ ثَلاَثًا: أَنْ تَعْبُدُوهُ وَلاَ تُشْرِكُواْ بِهِ شَيْئًا، وَأَنْ تَعْتَصِمُواْ بِحَبْلِ اَللهِ جَمِيعًا وَلاَ تَفَرَّقُواْ، وَأَنْ تُنَاصِحُواْ مَنْ وَلاَّهُ اَللهُ أَمْرَكُمْ)). وَلَمْ يَقَعْ خَلَلٌ فِي دِينِ اَلنَّاسِ وَدُنْيَاهُمْ إِلاَّ بِسَبَبِ اَلإِخْلاَلِ بِهَذِهِ اَلثَّلاَثِ أَوْ بَعْضِهَا.

Dabi'a Ta: 3. Lalle sabawa shugaba da kin yi masa biyayya matsayi ne, kuma a ce an ji maganarsa an bita kaskancine da wulakanci, sai Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya saba musu akan haka, ya umarcesu da yin hakuri akan zalincin shugabanni, ya yi umarni da jin maganarsu da kuma bi da yi musu nasiha, kuma ya kausasa akan haka, ya fada ya kuma kara fada.

Wadannan abubuwa uku (daga na farko zuwa wannan) sune hadisi ingantacce daga Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) a cikin Bukhari da Muslim ya kunsa, cewar Ma'aikin Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) ya ce:

'' Lalle Allah yana yardarm muku da abubuwa uku: Ku bauta masa kada ku hada shi da komai, ku yi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba, kuma ku yi nasiha ga wadanda Allah ya sanya al'amuran ku a gare su''.

Ba'a taba samun tangarda a addinin mutane ba da kuma a duniyar su ba sai ta sanadiyyar tangarda a wadannan abubuwa uku ko wasu daga cikin su.

اَلرَّابِعَةُ: أَنَّ دِينَهُمْ مَبْنِيٌّ عَلَى أُصُولٍ أَعْظَمُهَا: اَلتَّقْلِيدُ، فَهُوَ اَلْقَاعِدَةُ اَلْكُبْرَى لِجَمِيعِ اَلْكُفَّارِ، أَوَّلِهِمْ وَآخِرِهِمْ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿وَكَذَلِكَ مَا أَرسَلنَا مِن قَبلِكَ فِي قَريَة مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُترَفُوهَا إِنَّا وَجَدنَا ءَابَاءَنَا عَلَى أُمَّة وَإِنَّا عَلَى ءَاثَرِهِم مُّقتَدُونَ٢٣﴾ الزخرف: ٢٣ وَقَالَ تَعَالَى: ﴿وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَا أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَل نَتَّبِعُ مَا وَجَدنَا عَلَيهِ ءَابَاءَنَا أَوَلَو كَانَ ٱلشَّيطَنُ يَدعُوهُم إِلَى عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ٢١﴾ لقمان: ٢١ . فَأَتَاهُمْ بِقَوْلِهِ: ﴿قُل إِنَّمَا أَعِظُكُم بِوَحِدَةٍ أَن تَقُومُواْ لِلَّهِ مَثنَى وَفُرَدَى ثُمَّ تَتَفَكَّرُواْ مَا بِصَاحِبِكُم مِّن جِنَّةٍ إِن هُوَ إِلَّا نَذِير لَّكُم بَينَ يَدَي عَذَاب شَدِيد٤٦﴾ سبأ: ٤٦ وَقَوْلِهِ: ﴿ٱتَّبِعُواْ مَا أُنزِلَ إِلَيكُم مِّن رَّبِّكُم وَلَا تَتَّبِعُواْ مِن دُونِهِ أَولِيَاءَ قَلِيلا مَّا تَذَكَّرُونَ٣﴾ الأعراف: ٣ .

Dabi'a Ta: 4. Lalle addininsu (Su Ahlul Jahiliyyah) ya ginu ne akan wadansu turaku, babbab turken (shi ne): Al'ada. Ita ce babbar ka'ida ga dukkanin kafirai, tun na farkon su har na karshensu, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:

''Kuma haka nan ba mu taba aikowaba kafin kai a cikin birane (ba mu taba aiko) mai gargadi ba face sai manyan garin sun ce: Lalle mu mun sami iyayan mu ne akan wani addini kuma mu akan hanyarsu mu ke koyi''. Suratu Zukhruf, aya ta: 23.

Allah mai girma da daukak yana cewa:

'' Kuma idan aka ce; Ku bi abinda Allah ya saukar, sai su ce; A'a, za mu bi abinda muka sami iyayammu ne. To (haka za su bi iyayan) ko da shaidan yana kiran su ga azaba mai ruruwa''. Suratu Lukman, aya ta:21.

Sai Allah ya zo da fadinsa: '' Ka ce abin sani kawai ina muku wa'azine da (kalama) guda, akan ku mike (kan al'amarin) sabo da Allah bibiyu da kuma daidai sannan ku yi tunani, babu tabin hankali ga abokin ku''. Suratu Saba'i, aya ta: 46. Da kuma fadin sa (Shi Allah madaukakin sarki): '' Ku bi abinda aka saukar muku daga wurin Ubangijinku kada ku bi koma bayan amatsayin waliyyai, kadan ne matuka suke fada kuwa''. Suratul A'araf, aya ta: 3.

اَلْخَامِسَةُ: أَنَّ مِنْ أَكْبَرِ قَوَاعِدِهِمِ اَلاِغْتِرَارَ بِالأَكْثَرِ، وَيَحْتَجُّونَ بِهِ عَلَى صِحَّةِ اَلشَّيْءِ، وَيَسْتَدِلُّونَ عَلَى بُطْلاَنِ اَلشَّيْءِ بِغُرْبَتِهِ، وَقِلَّةِ أَهْلِهِ. فَأَتَاهُمْ بِضِدِّ ذَلِكَ، وَأَوْضَحَهُ فِي غَيْرِ مَوْضِعٍ مِنَ ((اَلْقُرْآنِ)).

Dabi'a Ta: 5. Tabbas yana daga cikin babbar ka'idar su, ruduwa da yawan mabiya, suna ma kafa hujja da yawan mabiya akan kyawun abu, suna kuma kafa hujja akan rashin kyawun wani abu da cewar; Ai ba'a san shi ba, kuma ai ba shi da yawan mabiya,to sai (Allah) ya zo musu da kishiyar haka, kuma ya yi bayaninsa a wurare da daman a Alkur'ani.

اَلسَّادِسَةُ: اَلاِحْتِجَاجُ بِالْمُتَقَدِّمِينَ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿قَالَ فَمَا بَالُ ٱلقُرُونِ ٱلأُولَى٥١﴾ طه: ٥١ ﴿ مَّا سَمِعنَا بِهَذَا فِي ءَابَائِنَا ٱلأَوَّلِينَ٢٤﴾ المؤمنون: ٢٤ .

Dabi'a Ta: 6. Kafa hujja da mutanan da. Kamar yadda Allah ya ke cewa:

'' Ya ce; To, menene labarin mutanan farko''. Suratu Taha, aya ta:51. (da kuma fadin sa): Ba mu taba jin wannan ba ga iyayammu na farko''. Suratul Muminun, aya ta:24.

اَلسَّابِعَةُ: اَلاِسْتِدْلاَلُ بِقَوْمٍ أُعْطُواْ قُوًى فِي اَلأَفْهَامِ وَالأَعْمَالِ وَفِي اَلْمُلْكِ وَالْمَالِ وَالْجَاهِ، فَرَدَّ اَللهُ ذَلِكَ بِقَوْلِهِ: ﴿وَلَقَد مَكَّنَّهُم فِيمَا إِن مَّكَّنَّكُم فِيهِ ٢٦﴾ الأحقاف: ٢٦ وَقَوْلِهِ: ﴿ وَكَانُواْ مِن قَبلُ يَستَفتِحُونَ عَلَى ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَلَمَّا جَاءَهُم مَّا عَرَفُواْ كَفَرُواْ بِهِ فَلَعنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلكَفِرِينَ٨٩﴾ البقرة: ٨٩ وَقَوْلِهِ: ﴿ يَعرِفُونَهُ كَمَا يَعرِفُونَ أَبنَاءَهُم ١٤٦﴾ البقرة: ١٤٦ .

Dabi'a Ta: 7. Kafa hujja da mutanan da aka bas u karfi ta wajan fahimta da ayyuka da mulki da dukiya da matsayi, sai Allah ya mayar musu da wannan inda ya ce:

'' Kuma hakika mun tabbatar musu cikin abinda muka tabbatar muku a cikin sa''. Suratul Ahkaf, aya ta:26. Da kuma fadinsa (Shi Allah madaukakin sarki): ''Kuma sun kasance a tuntuuni suna razanar da wadanda suka kafirta, to alokacin da abinda suka sani ya zo musu sai suka kafirce masa''. Suratul Bakara, aya ta: 89. Da kuma fadinsa: '' Sun san Shi kamar yadda suka san 'yayansu''. Suratul Bakarah, aya ta:146.

اَلثَّامِنَةُ: اَلاِسْتِدْلاَلُ عَلَى بُطْلاَنِ اَلشَّيْءِ بِأَنَّهُ لَمْ يَتْبَعْهُ إِلاَّ اَلضُّعَفَاءُ، كَقَوْلِهِ ﴿قَالُواْ أَنُؤمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلأَرذَلُونَ١١١﴾ الشعراء: ١١١ وَقَوْلِهِ: ﴿ أَهَؤُلَاءِ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيهِم مِّن بَينِنَا ﴾ الأنعام: ٥٣ فَرَدَّ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿ أَلَيسَ ٱللَّهُ بِأَعلَمَ بِٱلشَّكِرِينَ٥٣﴾ الأنعام: ٥٣

Dabi'a Ta: 8. Kafa hujja akan cewa abu bashi da kyau idan ya zama talakawane suka bi shi (shi wannan al'amarin). Kamar yadda Allah ya ce:

'' Yanzu za mu amince maka alhali talakawa su ka bi ka''?. Suratus Shu'ara'i, aya ta: 111, da fadinsa: “ Yanzu wadannan Allah ya yi wa ni'ima a gabammu''. Suratul An'am, aya ta:53. Sai Allah ya ce: ''Ashe Allah ba shi ne mafi sanin masu godiyaba''. Suratul An'am, aya ta:53.

اَلتَّاسِعَةُ: اَلاِقْتِدَاءُ بِفَسَقَةِ اَلْعُلَمَاءِ وَالْعُبَّادِ، فَأَتَى اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ إِنَّ كَثِيرا مِّنَ ٱلأَحبَارِ وَٱلرُّهبَانِ لَيَأكُلُونَ أَموَلَ ٱلنَّاسِ بِٱلبَطِلِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ يَكنِزُونَ ٱلذَّهَبَ وَٱلفِضَّةَ وَلَا يُنفِقُونَهَا فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَبَشِّرهُم بِعَذَابٍ أَلِيم٣٤﴾ التوبة: ٣٤ وَبِقَوْلِهِ: ﴿قُل يَأَهلَ ٱلكِتَبِ لَا تَغلُواْ فِي دِينِكُم غَيرَ ٱلحَقِّ وَلَا تَتَّبِعُواْ أَهوَاءَ قَوم قَد ضَلُّواْ مِن قَبلُ وَأَضَلُّواْ كَثِيرا وَضَلُّواْ عَن سَوَاءِ ٱلسَّبِيلِ٧٧﴾ المائدة: ٧٧ .

Dabi'a Ta: 9. Koyi da mugayan malamai da jahilan masu ibada, sai Allah yake cewa:

'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi Imani! Lalle da yawa daga cikin malaman yahudawa da masu ibadar nasara (wallahi) tabbas suna cin dukiyar mutane da barna, kuma suna kangewa daga barin hanyar Allah''. Suratut Taubah, aya ta:34.

Da kuma fadinsa: “ Kada ku ketare iyaka akan addininku ba ta hanyar gaskiya ba, kuma kada ku bi son zuciyar wasu mutane da sun bace tuntuni kuma sun batar da (mutane) masu yawa, kuma sun bace ma hanyar daidai''. Suratul Ma'idah, aya ta:77.

اَلْعَاشِرَةُ: اَلاِسْتِدَلاَلُ عَلَى بُطْلاَنِ اَلدِّينِ بِقِلَّةِ أَفْهَامِ أَهْلِهِ، وَعَدَمِ حِفْظِهِمْ،كَقَوْلِهِمْ: ﴿ بَادِيَ ٱلرَّأيِ ﴾ هود: ٢٧ .

Dabi'a Ta: 10. Kafa hujja akan bacin addini da cewar ai mabiyansa suna da karancin fahimta, kuma ba sa kiyaye al'amura, kamar yadda (mutanan Annabi Nuhu) suka ce: ''Masu gajeran tunani''. Suratu Hud, aya ta:27.

اَلْحَادِيَةَ عَشْرَةَ: اَلاِسْتِدْلاَلُ بِالْقِيَاسِ اَلْفَاسِدِ كَقَوْلِهِمْ: ﴿ قَالُواْ إِن أَنتُم إِلَّا بَشَر مِّثلُنَا ﴾ إبراهيم: ١٠ .

Dabi'a Ta: 11. Yadda suke kafa hujja da gurbatattacan kiyasi, kamar yadda suke cewa (Annabawa): '' Ku fa ba kowa bane face mutane kamar mu''. Suratu Ibrahim, aya ta: 10.

اَلثَّانِيَةَ عَشْرَةَ: إِنْكَارُ اَلْقِيَاسِ اَلصَّحِيحِ، وَالْجَامِعُ لِهَذَا وَمَا قَبْلَهُ عَدَمُ فَهْمِ اَلْجَامِعِ وَالْفَارِقِ.

Dabi'a Ta: 12. Yadda suke musun ingantaccan kiyasi, kuma abinda ya hada wannan da wanda ya zo kafin shi rashin fahimtar inda aka hadu da kuma inda aka rabu.

اَلثَّالِثَةَ عَشْرَةَ: اَلْغُلُوُّ فِي اَلْعُلَمَاءِ وَالصَّالِحِينَ، كَقَوْلِهِ ﴿يَأَهلَ ٱلكِتَبِ لَا تَغلُواْ فِي دِينِكُم وَلَا تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلحَقَّ ﴾ النساء: ١٧١ .

Dabi'a Ta: 13. Ketare iyaka akan (abinda ya shafi) malamai da kuma salihan bayi, kamar yadda (Allah) yake cewa:

'' Ya ku mabota littafi! Kada ku wuce iyaka a al'amarin addininku, kuma kada ku fada dangane da Allah sai abinda yake gaskiya''. Suratun Nisa'i, aya ta: 171.

اَلرَّابِعَةَ عَشْرَةَ: أَنَّ كُلَّ مَا تَقَدَّمَ مَبْنِيٌّ عَلَى قَاعِدَةٍ، وَهِيَ: اَلنَّفْيُ وَالإِثْبَاتُ، فَيَتَّبِعُونَ اَلْهَوَى وَالظَّنَّ، وَيُعْرِضُونَ عَمَّا جَاءَتْ بِهِ اَلرُّسُلُ.

Dabi'a Ta: 14. Lalle dukkanin abinda ya gabata ya ginune akan wata ka'ida, ita ce kuwa: Kore (abinda bai yi musu ba), da kuma tabbatar (da abinda ya yi musu), sai suke bin son zuciya da zace-zace, sai kuma su kaudakai su bar abinda manzanni suka zo da shi.

اَلْخَامِسَةَ عَشْرَةَ: اِعْتِذَارُهُمْ عَنِ اتِّبَاعِ مَا آتَاهُمُ اَللهُ بِعَدَمِ اَلْفَهْمِ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ قُلُوبُنَا غُلفُ ﴾ البقرة: ٨٨ . ﴿قَالُواْ يَشُعَيبُ مَا نَفقَهُ كَثِيرا مِّمَّا تَقُولُ ﴾ هود: ٩١، فَأَكْذَبَهَمُ اَللهُ، وَبَيَّنَ أَنَّ ذَلِكَ بِسَبَبِ اَلطَّبْعِ عَلَى قُلُوبِهِمْ، وَأَنَّ اَلطَّبْعَ بِسَبَبِ كُفْرِهِمْ.

Dabi'a Ta: 15. Bada hanzari akan kin bin abinda Allah ya aiko musu da cewar ba sa fahimta, kamar yadda suka ce: '' Zukatammu a rufe su ke''. Suratul Bakara, aya ta:88. Da kuma (yadda suka ce):

'' Ya kai Shu'aibu ba ma fahimtar mafi yawan abinda kake fadi''. Suratu Hudu, aya ta: 91. Sai Allah ya karyata su, ya kuma yi bayanin hakan ya faru ne ta sanadiyyar toshewar zukatansu, sannan sanadiyyar toshewar kuwa shine kafircin su.

اَلسَّادِسَةَ عَشْرَةَ: اِعْتِيَاضُهُمْ عَمَّا أَتَاهُمْ مِنَ اَللهِ بِكُتُبِ اَلسِّحْرِ، كَمَا ذَكَرَ اَللهُ ذَلِكَ فِي قَوْلِهِ: ﴿وَلَمَّا جَاءَهُم رَسُول مِّن عِندِ ٱللَّهِ مُصَدِّق لِّمَا مَعَهُم نَبَذَ فَرِيق مِّنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلكِتَبَ كِتَبَ ٱللَّهِ وَرَاءَ ظُهُورِهِم كَأَنَّهُم لَا يَعلَمُونَ١٠١ وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتلُواْ ٱلشَّيَطِينُ عَلَى مُلكِ سُلَيمَنَ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ وَلَكِنَّ ٱلشَّيَطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحرَ وَمَا أُنزِلَ عَلَى ٱلمَلَكَينِ بِبَابِلَ هَرُوتَ وَمَرُوتَ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة فَلَا تَكفُر فَيَتَعَلَّمُونَ مِنهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِ بَينَ ٱلمَرءِ وَزَوجِهِ وَمَا هُم بِضَارِّينَ بِهِ مِن أَحَدٍ إِلَّا بِإِذنِ ٱللَّهِ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُم وَلَا يَنفَعُهُم وَلَقَد عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشتَرَىهُ مَا لَهُ فِي ٱلأخِرَةِ مِن خَلَق وَلَبِئسَ مَا شَرَواْ بِهِ أَنفُسَهُم لَو كَانُواْ يَعلَمُونَ١٠٢﴾ البقرة: ١٠١ – ١٠٢

Dabi'a Ta: 16. Kauda kai da suke yi da barin abinda ya zo musu daga wurin Allah ta hanyar riko da littafan sihiri (asiri), kamar yadda Allah madaukakin sarki ya anbaci haka a fadinsa:

'' …. (Sai) Wadansu tawaga daga cikin wadanda aka baiwa (ilimin) littafi suka yi watsi da littafi Allah can bayansu, kamar ka ce basu taba sanin (abinda ke ciki ba)* Kuma su ka bi abinda shaidanu suke karanta musu dangane da mulkin (Annabi) Sulaiman''. Suratul Bakarah, aya ta: 101-102.

اَلسَّابِعَةَ عَشْرَةَ: نِسْبَةُ بَاطِلِهِمْ إِلَى اَلأَنْبِيَاءِ، كَقَوْلِهِ: ﴿ وَمَا كَفَرَ سُلَيمَنُ ﴾ البقرة: ١٠٢. وَقَوْلِهِ: ﴿مَا كَانَ إِبرَهِيمُ يَهُودِيّا وَلَا نَصرَانِيّا ﴾ آل عمران: ٦٧ .

Dabi'a Ta: 17. Jingina barna ga Annabawa, (kamar yadda suka jingina sihiri ga Annabi Sulaiman, suke cewa ai Annabi Sulaiman da asiri ya mallaki mutane da aljanu, har suke bada hatiminshi) kamar yadda Allah yake cewa:

'' (Annabi) Sulaiman bai yi kafirci ba''. Suratul Bakarah, aya ta: 102. Da kuma fadinsa: '' (Annabi) Ibrahim bait aba kasancewa bayahudeba haka nan bai taba kasancewa banasare ba''. Suratu Ali Imrana, aya ta: 67.

اَلثَّامِنَةَ عَشْرَةَ: تَنَاقُضُهُمْ فِي اَلاِنْتِسَابِ، يَنْتَسِبُونَ إِلَى إِبْرَاهِيمَ مَع إِظْهَارِهِمْ تَرْكَ اَتِّبَاعِهِ.

Dabi'a Ta: 18. Warwara a yadda suke danganta kawunan su, suna jingina kan su da cewa su tsatsan Annabi Ibrahim ne, kuma suna bayyanar da kin bin karantarwarsa a fili.

اَلتَّاسِعَةَ عَشْرَةَ: قَدْحُهُمْ فِي بَعْضِ اَلصَّالِحِينَ بِفِعْلِ بَعْضِ اَلْمُنْتَسِبِينَ إِلَيْهِمْ، كَقَدْحِ اَلْيَهُودِ فِي عِيسَى، وَقَدْحِ اَلْيَهُودِ وَالنَّصَارَى فِي مُحَمَّدٍ ﷺ‬.

Dabi'a Ta: 19. Yadda suke muzanta bayin Allah na kwarai, saboda aikin da wasu da suke jingina kan su ga wadannan bayin Allah suka aikata, kamar yadda yahudawa suke aibanta Annabi Isah (saboda aikin da nasara suke yi), da kuma yadda yahudu da nasara suke aibanta Ma'aikin Allah (Annabi) Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi) saboda aikin da wasu mabiyansa suka aikata.

اَلْعِشْرُونَ: اِعْتِقَادُهُمْ فِي مَخَارِيقِ اَلسَّحَرَةِ وَأَمْثَالِهِمْ أَنَّهَا مِنْ كَرَامَاتِ اَلصَّالِحِينَ، وَنِسْبَتُهُ إِلَى اَلأَنْبِيَاءِ كَمَا نَسَبُوهُ لِسُلَيْمَانَ عَلَيْهِ اَلسَّلاَمُ.

Dabi'a Ta: 20. Yadda suka kudurce mugayan akidu dangane da masu rufa-ido da 'yan-dabo da ire-iren sun a cewa (wannan aikin na rufa-ido ko dabo) yana cikin karamomin waliyyai, har ma suke jingina shi ga Annabawa kamar yadda suka jin gina shi ga Annabi Sulaiman, tsiran Allah ya tabbata a gareshi.

اَلْحَادِيَةَ وَالْعِشْرُونَ: تَعَبُّدُهُمْ بِالْمُكَاءِ وَالتَّصْدِيَةِ.

Dabi'a Ta: 21. Yadda suke bauta ta hanyar kuka da kuma fito.

اَلثَّانِيَةُ وَالْعِشْرُونَ: أَنَّهُمُ اَتَّخَذُواْ دِينَهُمْ لَهْوًا وَلَعِباً.

Dabi'a Ta: 22. Su fa sun dauki addinin su wasa da cashew.

اَلثَّالِثَةُ وَالْعِشْرُونَ: أَنَّ اَلْحَيَاةَ اَلدُّنْيَا غَرَّتْهُمْ، فَظَنُّواْ أَنَّ عَطَاءَ اَللهِ مِنْهَا يَدُلُّ عَلَى رِضَاهُ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ نَحنُ أَكثَرُ أَموَلا وَأَولَدا وَمَا نَحنُ بِمُعَذَّبِينَ٣٥﴾ سبأ: ٣٥

Dabi'a Ta: 22. Lalle fa rayuwar duniya ta rudesu, sai suka yi tsammanin duk wanda Allah ya arziki a duniya to ya yarda da shi, kamar yadda suke cewa:

'' Mu muka fi yawan dukiya da 'ya'ya, mu ba wadanda za'a yi wa azaba bane''. Suratu Saba'i, aya ta: 35.

اَلرَّابِعَةُ وَالْعِشْرُونَ: تَرْكُ اَلدُّخُولِ فِي اَلْحَقِّ إِذَا سَبَقَهُمْ إِلَيْهِ اَلضُّعَفَاءُ تَكَبُّرًا وَأَنَفَةً، فَأَنْزَلَ اَللهُ تَعَالَى: ﴿وَلَا تَطرُدِ ٱلَّذِينَ يَدعُونَ رَبَّهُم.... اَلآيَات) الأنعام: ٥٢ وَمَا بَعْدَهَا.

Dabi'a Ta: 24. Yadda suke kin karbar gaskiya idan talakawa suka ruga su kawai don girman kai da hura hanci, sai Allah ya saukar (da fadansa): '' Kada ka kori wadanda suke kiran Ubangijusu ….'' Ayoyin Suratul An'am, aya ta: 52, da wacce take bayanta (53).

اَلْخَامِسَةُ وَالْعِشْرُونَ: اَلاِسْتِدَلاَلُ عَلَى بُطْلاَنِهِ بِسَبْقِ اَلضُّعَفَاءُ، كَقَوْلِهِ: ﴿ لَو كَانَ خَيرا مَّا سَبَقُونَا إِلَيهِ وَإِذ لَم يَهتَدُواْ بِهِ فَسَيَقُولُونَ هَذَا إِفك قَدِيم١١﴾الأحقاف: ١١ .

Dabi'a Ta: 25. Yadda suka kafa hujja da cewa abu baida kyau idan talakawa suka riga su karba, kamar yadda (Allah) yake cewa:

'' Inda ya kasance alherine ai da basu riga mu ba''. Suratul Ahkaf, aya ta:11.

اَلسَّادِسَةُ وَالْعِشْرُونَ: تَحْرِيفُ ((كِتَابِ اَللهِ)) مِنْ بَعْدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمْ يَعْلَمُونَ.

Dabi'a Ta: 26. Yadda suke jirkita littafin Allah (kamar Attaura da Injila) bayan sun gane kuma fa suna sane.

اَلسَّابِعَةُ وَالْعِشْرُونَ: تَصْنِيفُ اَلْكُتُبِ اَلْبَاطِلَةِ وَنِسْبَتُهَا إِلَى اَللهِ، كَقَوْلِهِ: ﴿فَوَيل لِّلَّذِينَ يَكتُبُونَ ٱلكِتَبَ بِأَيدِيهِم ثُمَّ يَقُولُونَ هَذَا مِن عِندِ ٱللَّهِ ﴾ البقرة: ٧٩

Dabi'a Ta: 27. Yadda suke wallafa littafai na barna kuma suke jingina su ga Allah, kamar yadda (Allah) yake cewa:

'' To azaba ta tabbata ga dukkanin wadanda suke rubuta littafai da hannayansu sannan suce: wannan daga wurin Allah ne''. Suratul Bakarah, aya ta: 79.

الثَّامِنَةُ وَالعِشْرُونَ: أَنَّهُمْ لاَ يَقْبَلُونَ مِنَ اَلْحَقِّ إِلاَ اَلَّذِي مَعَ طَائِفَتِهِمْ، كَقَوْلِهِ: ﴿وَإ قَالُواْ نُؤمِنُ بِمَا أُنزِلَ عَلَينَا ﴾ البقرة: ٩١ .

Dabi'a Ta: 28. Lalle su basa karbar gaskiya sai wacce ta yi daidai da bangaran su, kamar yadda (Allah) yake cewa:

“ Su ka ce: mun yarda da abinda aka saukar mana''. Suratul Bakarah, aya ta: 91.

اَلتَّاسِعَةُ وَالعِشْرُونَ: أَنَّهُمْ مَعَ ذَلِكَ لاَ يَعْلَمُونَ بِمَا تَقُولُهُ طَائِفَتُهُمْ، كَمَا نَبَّهَ اللهُ تَعَالَى عَلَيْهِ بِقَوْلِهِ: ﴿ قُل فَلِمَ تَقتُلُونَ أَنبِيَاءَ ٱللَّهِ مِن قَبلُ إِن كُنتُم مُّؤمِنِينَ٩١﴾ البقرة: ٩١ .

Dabi'a Ta: 29. Lalle su duk haka ba su samma me jama'ar ta su take cewa ba, kamar yadda Allah ya fadakar akan haka:

'' Ka ce; To damme kuke kasha Annabawan Allah tuntuni in kun kasance wadanda su ka yi imani''. Suratul Bakarah, aya ta: 91.

اَلثَّلاَثُونَ: وَهِيَ مِنْ عَجَائِبِ آيَاتِ اَللهِ، أَنَّهُمْ لَمَّا تَرَكُواْ وَصِيَّةَ اَللهِ بِالاجْتِمَاعِ، وَارْتَكَبُواْ مَا نَهَى اَللهُ عَنْهُ مِنَ الاِفْتِرَاقِ، صَارَ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحِينَ.

Dabi'a Ta: 30. Wannan ko tana cikin abubuwan ban-al'ajabi na ayoyin Allah, domin su lokacin da suka bar wasiyyar Allah akan ahadu, suka aikata abinda Allah ya hana na rarrabuwa, sai ya kasance kowacce kungiya da abinda ke gabansu suke alfahari.

اَلْحَادِيَةُ وَالثَّلاَثُونَ: وَهِيَ مِنْ أَعْجَبِ اَلآيَاتِ أَيْضًا: مُعَادَاتُهُمْ اَلدِّينِ اَلَّذِي اِنْتَسَبُوا إِلَيْهِ غَايَةَ اَلْعَدَاوَةِ، وَمَحَبَّتُهُمْ دِينَ الكُفَّارِ اَلَّذِينَ عَادَوْهُمْ وَعَادَواْ نَبِيَّهُمْ وَفِئَتَهُمْ غَايَةَ اَلْمَحَبَّةِ، كَمَا فَعَلُواْ مَعَ النَّبِيِّ ﷺ‬ لَمَّا أَتَاهُمْ بِدِينِ مُوسَى عَلَيهِ السَّلاَمُ، وَاتَّبَعُواْ كُتُبَ السِّحْرِ، وَهِيَ مِنْ دِينِ آلِ فِرْعَوْنَ.

Dabi'a Ta: 31. Ita din ma dai tana cikin manya-manyan ayoyin masu bammamaki, kiyayya da addinin da suka ce suna bi makurar kiyayya, da kuma yadda suke son addinin kafiran da su ka ki su suka kuma ki Annabinsu suka ki jama'ar su, ya zama na suna son (kafiran nan) makurar so.

Kamar yadda su ka yi da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a lokacin da ya zo musu da addinin Annabi Musa aminci Allah ya tabbata a gareshi, sai suka bi littafan sihiri, wanda yake wannan kuwa yana cikin gargajirar Fir'auna.

اَلثَّانِيَةُ وَالثَّلاَثوُنَ : كُفْرُهُمْ بِالْحَقِّ إِذَا كَانَ مَعَ مَنْ لاَ يَهْوَوْنَهُ كَمَا قَالَ تَعَالَ: ﴿وَقَالَتِ ٱليَهُودُ لَيسَتِ ٱلنَّصَرَى عَلَى شَيء وَقَالَتِ ٱلنَّصَرَى لَيسَتِ ٱليَهُودُ عَلَى شَيء ﴾ البقرة: ١١٣.

Dabi'a Ta: 32. Yadda suke kafircewa gaskiya idan ta kasance a tare da wanda su basa son shi, kamar yadda (Allah) madaukakin sarki yake cewa:

'' Yahudawa sun ce; Nasara ba akan komai suke ba, Nasara kuma sun ce; Yahudawa ba akan komai suke ba''. Suratul Bakarah, aya ta: 113.

اَلثَّالِثَةُ وَالثَّلاَثوُنَ: إِنْكَارُهُمْ مَا أَقَرُّوا أَنَّهُ مِنْ دِينِهِمْ، كَمَا فَعَلُوا فِي حَجِّ البَيْتِ، قَالَ تَعَالَى: ﴿وَمَن يَرغَبُ عَن مِّلَّةِ إِبرَهِمَ إِلَّا مَن سَفِهَ نَفسَهُ ﴾ البقرة: ١٣٠

Dabi'a Ta: 33. Yadda suke musun abinda suka tabbatar da shi a addinin su, kamar yadda suka yi hakan a aikin hajji, (Allah) mai girma da daukaka yana cewa:

'' Ba wanda zai kyamaci addinin (Annabi) Ibrahim sai wanda ya wawantar da kansa''. Suratul Bakarah, aya ta: 130.

اَلرَّابِعَةُ وَالثَّلاَثُونَ: أَنَّ كُلَّ فِرْقَةٍ تَدَّعِي أَنَّهَا النَّاجِيَةُ، فَأَكْذَبَهُمْ اَللهُ بِقَولِهِ: ﴿ قُل هَاتُواْ بُرهَنَكُم إِن كُنتُم صَدِقِينَ١١١﴾ البقرة: ١١١، ثُمَّ بَيَّنَ الصَّوَابَ بِقَوْلِهِ: ﴿بَلَى مَن أَسلَمَ وَجهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحسِن ﴾ البقرة: ١١٢ .

Dabi'a Ta: 34. Kowacce kungiya tana ganin itace kadai zata tsira, sai Allah ya karyata su da fadar Sa: '' Ka ce; Ku kawo dalilanku in kun kasance masu gaskiya''. Suratul Bakarah, aya ta: 111, sannan sai (Allah) ya bayyana abinda yake shine daidai inda ya ce:

'' Tabbas duk wanda ya fuskassa ( ya yi addini) domin Allah yana mai kyautatawa''. Suratul Bakarah, aya ta: 112.

اَلْخَامِسَةُ وَالثَّلاَثُونَ: اَلتَّعَبُّدُ بِكَشْفِ اَلْعَوْرَاتِ، كَقَوْلِهِ: ﴿وَإِذَا فَعَلُواْ فَحِشَة قَالُواْ وَجَدنَا عَلَيهَا ءَابَاءَنَا وَٱللَّهُ أَمَرَنَا بِهَا قُل إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَأمُرُ بِٱلفَحشَاءِ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعلَمُونَ٢٨﴾ الأعراف: ٢٨ .

Dabi'a Ta: 35. Yadda suke bauta ta hanyar bayyanar da tsiraici, kamar yadda (Allah) ya ce: '' Kuma idan suka aikata kazamin aiki sai su ce; Haka muka samu iyayammu akai kuma Allah ne ya umarce mu da hakan''. Suratul A'araf, aya ta: 28.

اَلسَّادِسَةُ وَالثَّلاَثوُنَ: اَلتَّعَبُّدُ بِتَحْرِيـمِ اَلْحَلاَلِ كَمَا تَعَبَّدُواْ بِالشِّرْكِ.

Dabi'a Ta: 36. Yadda suke bauta ta hanyar haramtar da halas, kamar yadda suka yi bautar da shirka.

اَلسَّابِعَةُ وَالثَّلاَثوُنَ: التَّعَبُّدُ بِاتِّخَاذِ اَلأَحْبَارِ وَالرُّهُبَانِ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللهِ.

Dabi'a Ta: 37. Yadda suke bauta ta hanyar daukar manyan malamai da masu ibada wasu abin bauta daban koma bayan Allah.

اَلثَّامِنَةُ وَالثَّلاَثُونَ: اَلإِلْحَادُ فِي اَلصِّفَاتِ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿ وَلَكِن ظَنَنتُم أَنَّ ٱللَّهَ لَا يَعلَمُ كَثِيرا مِّمَّا تَعمَلُونَ٢٢﴾ فصلت: ٢٢ .

Dabi'a Ta: 38. Kore siffofin (Ubangiji, kamar yadda basu yarda: Allah ya sani ba) kamar yadda (Allah) madaukakin sarki yake cewa: '' Sai dai kun yi zaton (cewar) Lalle Allah bai sai mafi yawan abinda kuke aikatawa''. Suratu Fussilat, aya ta: 22.

اَلتَّاسِعَةُ وَالثَّلاَثُونَ: اَلإِلْحَادُ فِي اَلأَسْمَاءِ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿وَهُم يَكفُرُونَ بِٱلرَّحمَنِ ﴾ الرعد: ٣٠ .

Dabi'a Ta: 39. Kore sunayan Allah, kamar yadda (Allah) mai girma da daukaka ya ce: '' Kuma su suna kafircewa; Mai yawan rahama''. Suratur Ra'ad, aya ta: 30.

اَلأَرْبِعُونَ: اَلتَّعْطِيلُ، كَقَوْلِ فِرْعَوْنَ

Dabi'a Ta: 40. Share (Sunaye da siffofin Allah) kamar yadda fir'auna ya ce: (''Bansan kuna da wani abin bauta ba in ba ni ba''. Suratul Kasas, aya ta: 38).

اَلْحَادِيَةُ وَالأَرْبَعُونَ: نِسْبَةُ اَلنَّقَائِصِ إِلَيْهِ سُبْحَانَهُ، كَالْوَلَدِ وَالْحَاجَةِ وَالتَّعَبِ، مَعَ تَنْزِيهِ رُهْبَانِهِمْ عَنْ بَعْضِ ذَلِكَ.

Dabi'a Ta: 41. Jingina (siffofi na) tawaya ga (Allah) mai tsarki da buwaya, kamar (da suka ce yana da) Da, Bukata, Gajiya, tare da tsarkake malaman su da wasu daga cikin su (wadannan siffofin).

اَلثَّانِيَةُ وَالأَرْبَعُونَ: اَلشِّرْكُ فِي اَلْمُلْكِ، كَقَوْلِ اَلْمَجُوسِ.

Dabi'a Ta: 42. Shirka a mulikin (Allah) kamar yadda majusawa suke cewa: (Akwai mahaliccin duhu akwai kuma mahaliccin haske).

اَلثَّالِثَةُ وَالأَرْبَعُونَ: جُحُودُ اَلْقَدَرِ.

Dabi'a Ta: 43. Kin yarda da kaddarar (Ubangiji).

اَلرَّابِعَةُ وَالأَرْبَعُونَ: اَلاِحْتِجَاجُ عَلَى اَللهِ بِهِ.

Dabi'a Ta: 44. Yi wa Allah hujja da ita (Kaddarar).

اَلْخَامِسَةُ وَاَلأَرْبَعُونَ: مُعَارَضَةُ شَرْعِ اَللهِ بِقَدَرِهِ.

Dabi'a Ta: 45. Yadda suke gwara shara'ar Allah da kaddarar sa.

اَلسَّادِسَةُ وَاَلأَرْبَعُونَ: مَسَبَّةُ اَلدَّهْرِ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿ وَمَا يُهلِكُنَا إِلَّا ٱلدَّهرُ ﴾ الجاثية: ٢٤ .

Dabi'a Ta: 46. Aibanta zamani, kamar yadda suke cewa: '' Ba abinda yake ya ke halakar da mu sai zamani''. Suratul Jasiya, aya ta: 24.

اَلسَّابِعَةُ وَالأَرْبَعُونَ:إِضَافَةُ نِعَمِ اللهِ إِلَى غَيْرِهِ، كَقَوْلِهِ: ﴿يَعرِفُونَ نِعمَتَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكثَرُهُمُ ٱلكَفِرُونَ٨٣﴾ النحل: ٨٣ .

Dabi'a Ta: 47. Jingina ni'imomin da Allah ya yi ga wanin Allah, kamar yadda fadarsa (Shi Allah); '' Sun san ni'imomin Allah sannan suke musun su''. Suratun Nahl, aya ta:83.

اَلثَّامِنَةُ وَالأَرْبَعُونَ: اَلْكُفْرُ بِآيَاتِ الله.

Dabi'a Ta: 48. Yadda suke kafurcewa ayoyin Allah.

اَلتَّاسِعَةُ وَالأَرْبَعُونَ: جَحْدُ بَعْضِهَا.

Dabi'a Ta: 49. Musun wasu daga cikin su (su ayoyin Allah din).

اَلْخَمْسُونَ: قَوْلُهُمْ: ﴿ مَا أَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَى بَشَر مِّن شَيء ﴾ الأنعام: ٩١

Dabi'a Ta: 50. Yadda suka ce “ Allah bai taba saukar da wani abu na ga wani mutum''. Suratul An'am, aya ta: 91.

اَلْحَادِيَةُ وَالْخَمْسُونَ: قَوْلُهُمْ فِي ((اَلْقُرْآنِ)) ﴿إِن هَذَا إِلَّا قَولُ ٱلبَشَرِ٢٥﴾ المدثر: ٢٥.

Dabi'a Ta: 51. Yadda suka ce dangane da Alkur'ani: '' Ai wannan ba komai bane sai zancan mutum''. Suratul Mudassir, aya ta: 25.

اَلثَّانِيَةُ وَالْخَمْسُونَ: اَلْقَدْحُ فِي حِكْمَةِ اَللهِ تَعَالَى.

Dabi'a Ta: 52. Yadda suke muzanta hikimomin Allah madaukakin sarki.

اَلثَّالِثَةُ وَالْخَمْسُونَ: إِعْمَالُ اَلْحِيَلِ اَلظَّاهِرَةِ وَالبَاطِنَةِ فِي دَفْعِ مَا جَاءِتْ بِهِ اَلرُّسُلُ، كَقَوْلِهِ تَعَالَى: ﭽ ﭛ ﭜ ﭝ ﭼ آل عمران: ٥٤، وَقَوْلِهِ: ﴿وَقَالَت طَّائِفَة مِّن أَهلِ ٱلكِتَبِ ءَامِنُواْ بِٱلَّذِي أُنزِلَ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَجهَ ٱلنَّهَارِ وَٱكفُرُواْ ءَاخِرَهُ لَعَلَّهُم يَرجِعُونَ٧٢﴾ آل عمران:٧٢.

Dabi'a Ta: 53. Yadda suke anfani da dabaru na zahiri da na boye domin kautar da abinda Manzanni suka zo da shi, kamar yadda (Allah) madaukakin sarki ya ce: ''Kuma sun kulla makirci, kuma Allah ya kulla musu makirci''. Suratu Ali Imran, aya ta:54. Da kuma fadinsa:

''Kuma wata kungiya daga cikin wadanda aka ba littafi ta ce: Ku yi Imani da abinda aka saukarwa wadanda suka yi Imani da farkon yini, sannan ku kafirce a karshansa (yinin)''. Suratu Ali Imran, aya ta: 72.

اَلرَّابِعَةُ وَالْخَمْسُونَ: اَلإِقْرَارُ بِالْحَقِّ لِيَتَوَصَّلُواْ بِهِ إِلَى دَفْعِهِ، كَمَا قَالَ فِي الآيَةِ.

Dabi'a Ta: 54. Furta gaskiya domin su yi anfani da hakan domin kautar da ita (gaskiyar), kamar yadda yadda ya gabata a ayar da ta wuce.

اَلْخَامِسَةُ وَالْخَمْسُونَ: اَلتَّعَصُّبُ لِلْمَذْهَبِ، كَقَوْلِهِ فِيهَا: ﴿وَلَا تُؤمِنُواْ إِلَّا لِمَن تَبِعَ دِينَكُم ٧٣﴾ آل عمران: ٧٣.

Dabi'a Ta: 55. (Allah) ya ce: ''Kafewa akan ra'ayi".

اَلسَّادِسَةُ وَالْخَمْسُونَ: تَسْمِيَةُ اتِّبَاعِ الإِسْلاَمِ شِرْكًا، كَمَا ذَكَرَهُ فِي قَوْلِهِ تَعَالَى: ﴿مَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُؤتِيَهُ ٱللَّهُ ٱلكِتَبَ وَٱلحُكمَ وَٱلنُّبُوَّةَ ثُمَّ يَقُولَ لِلنَّاسِ كُونُواْ عِبَادا لِّي مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَكِن كُونُواْ رَبَّنِيِّنَ بِمَا كُنتُم تُعَلِّمُونَ ٱلكِتَبَ وَبِمَا كُنتُم تَدرُسُونَ٧٩ وَلَا يَأمُرَكُم أَن تَتَّخِذُواْ ٱلمَلَئِكَةَ وَٱلنَّبِيِّنَ أَربَابًا أَيَأمُرُكُم بِٱلكُفرِ بَعدَ إِذ أَنتُم مُّسلِمُونَ٨٠﴾ آل عمران: ٧٩ – ٨٠.

Dabi'a Ta: 56. Anbaton wadanda suke bin tsarin musulunci da shirka, kamar fadin (Allah) madaukakin sarki:

'' Bai taba kasancewa ga wani mutum dan Allah ya bas hi littafi da hukunci da kuma annabta sannan ya cewa mutane; ku kasance bayi na koma bayan Allah, saidai ku kasance masu reno (n al'umma) ta hanyar karantar da littafi (Alkur'ani) da kuma abinda ku ka kasance kuke karantowa. () kuma ba zai taba umanartarku ba da ku riki mala'iku da Annabawa abeban bauta, yanzu za su umarceku da kafirci bayan kuna musulmai''. Suratu Ali Imran.

اَلسَّاِبعَةُ وَالْخَمْسُونَ: تَحْرِيفُ اَلْكَلِمِ عَنْ مَوَاضِعِهِ.

Dabi'a Ta: 57. Canza zancan (Allah) daga yadda yake.

الثَّامِنَةُ وَالْخَمْسُونَ: لَيُّ اَلأَلْسِنَةِ بِالْكِتَابِ.

Dabi'a Ta: 58. Karkatar da harsuna wurin fassara littafin (Allah).

اَلتاَّسِعَةُ وَالْخَمْسُونَ: تَلْقِيبُ أَهْلِ اَلْهُدَى بِالصُّبَاةِ وَالْحَشْوِيَّةِ.

Dabi'a Ta: 59. Lakkabawa wadanda ke kan hanyar daidai (sunan) yarane ko marasa aikin yi.

اَلسِّتُّونَ: اِفْتِرَاءُ اَلْكَذِبِ عَلَى اَللهِ.

Dabi'a Ta: 60. Kagar karya a jinginawa Allah.

اَلْحَادِيَةُ وَالسِّتُّونَ: اَلتَّكْذِيبُ.

Dabi'a Ta: 61. Karyata (sakon Allah da manzan Sa).

اَلثَّانِيَةُ وَالسِّتُّونَ: كَوْنُهُمْ إِذَا غُلِبُواْ بِالْحُجَّةِ فَزِعُوا إِلَى اَلشَّكْوَى لِلْمُلُوكِ، كَمَا قَالوُا: ﴿ أَتَذَرُ مُوسَى وَقَومَهُ لِيُفسِدُواْ فِي ٱلأَرضِ ﴾ الأعراف: ١٢٧.

Dabi'a Ta: 62. Yadda suka kasance idan an yi nasara akan su da hujjoji sais u dunguma su kai kuka ga sarakuna, kamar yadda (mutanan Fir'auna) suka ce:

'' Yanzu zaka bar Musa da jama'arsa su na barna a bayan kasa''.? Suratul A'araf, aya ta: 127.

اَلثَّالِثَةُ وَالسِّتُّونَ: رَمْيُهُم إِيّاهُمْ بِالْفَسَادِ فِي الأَرْضِ كَمَا فِي الآيَةِ.

Dabi'a Ta: 63. Yadda suke jifansu (wadanda ke kan shiriya) da barna adoron kasa, kamar yadda ya gabata a ayar.

اَلرَّابِعَةُ وَالسِّتُّونَ: رَمْيُهُم إِيَّاهُمْ بِانْتِقَاصِ دِينِ اَلْمَلِكِ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَ ﴾ الأعراف: ١٢٧، وَكَمَا قَالَ: ﴿ إِنِّي أَخَافُ أَن يُبَدِّلَ دِينَكُم أَو أَن يُظهِرَ فِي ٱلأَرضِ ٱلفَسَادَ٢٦﴾ غافر: ٢٦.

Dabi'a Ta: 64. Yadda suke jifansu da rage darajar tsarin sarauta, kamar ya (Allah) maigirma da daukaka ya fada:

'' Su kyaleka da ababan bautarka''?. Suratul A'araf, aya ta: 127. Kuma kamar yadda (Allah) ya ce: '' Lalle ni (inji Fir'auna) ina jin tsoron kada ya canza muku addininku''. Suratu Zukhruf, aya ta: 26.

اَلْخَامِسَةُ وَالسِّتُّونِ: رَمْيُهُمْ إِيَّاهُمْ بِانْتِقَاصِ آلِهَةِ الْمَلِكِ، كَمَا فِي الآيَةِ.

Dabi'a Ta: 65. Yadda suke jifansu rage darajar abin bautar sarki, kamar yadda ya ke a ayar.

اَلسَّادِسَةُ وَالسِّتُّونَ: رَمْيُهُمْ إِيَّاهُمْ بِتَبْدِيلِ اَلدِّينِ، كَمَا قَالَ تَعَالَى: ﴿ إِنِّي أَخَافُ أَن يُبَدِّلَ دِينَكُم أَو أَن يُظهِرَ فِي ٱلأَرضِ ٱلفَسَادَ٢٦﴾ غافر: ٢٦.

Dabi'a Ta: 66. Yadda suke jifansu (wadanda suke kan hanyar daidai) da cewar suna canza addini (sun zo da sabon addini), kamar yadda (Allah) mai girma da daukaka ya ce:

''… (in ji Fir'auna) Laale ni ina tsoron kada ya canza muku addini ko kuma ya bayyanar da barna abayan kasa''. Suratul Ghafir, aya ta: 26.

اَلسَّابِعَةُ وَالسَّتُّونَ: رَمْيُهُمْ إِيَاهُمْ بِانْتِقَاصِ اَلْمَلِكِ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿ وَيَذَرَكَ وَءَالِهَتَكَ ﴾ الأعراف: ١٢٧.

Dabi'a Ta: 67. Yadda suke jifansu da rage darajar sarauta, kamar yadda suka ce: '' Ya kyaleka da ababan bautarka''. Suratul A'araf, aya ta: 127.

اَلثَّامِنَةُ وَالسَّتُّونَ: دَعْوَاهُمُ اَلْعَمَلَ بِمَا عِنْدَهُمْ مِنَ اَلْحَقَّ، كَقَوْلِهِم: ﴿ قَالُواْ نُؤمِنُ بِمَا أُنزِلَ عَلَينَا ﴾ البقرة: ٩١ مَعَ تَرْكِهِمْ إِيَّاهُ.

Dabi'a Ta: 68. Yadda wai suke cewa suna aiki da abinda yake wurin su na gaskiya, kamar yadda suka ce: '' Muna yin Imani ne da abinda aka saukar mana''. Bakara, aya ta: 91. Tare kuma basa aikin.

اَلتَّاسِعَةُ وَالسِّتُّونَ :الزِّيَادَةُ فِي اَلْعِبَادَةِ، كَفِعْلِهِمْ يَوْمَ عَاشُورَاءَ.

Dabi'a Ta: 69. Kari a ibada, kamar yadda suke yi ranan Ashurah.

اَلسَّبْعُونَ: نَقْصُهُم مِنْهَا، كَتَرْكِهِمُ اَلْوُقُوُفَ بِعَرَفَاتٍ.

Dabi'a Ta: 70. Yadda suke yage wani abu daga cikinta (ibadar) kamar yadda suke (tsayawa a muzdalifa) su ki tsaya a Arafat.

اَلْحَادِيَةُ وَالسَّبْعُونَ: تَرْكُهُمُ اَلْوَاجِبَ وَرَعًا.

Dabi'a Ta: 71. Yadda suke barin wajibi wai saboda tsantseni.

اَلثَّانِيَةُ وَالسَّبْعُونَ: تَعَبُّدُهُمْ بِتَرْكِ اَلطَّيِّبَاتِ مِنَ اَلرِّزْقِ.

Dabi'a Ta: 72. Yadda suke ibada ta hanyar kin cin abubuwa nah alas da (Allah ya) bada su na arziki.

اَلثَّالِثَةُ وَالسَّبْعُونَ: تَعَبُّدُهُمْ بِتَرْكِ زِينَةِ اللهِ.

Dabi'a Ta:73. Yadda suke su ka dauka ibada ne barin sa kaya na ado da Allah ya azurta su da shi.

اَلرَّابِعَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَتُهُمُ اَلناَّسَ إِلَى اَلضَّلاَلِ بِغَيْرِ عِلْمٍ.

Dabi'a Ta: 74. Yadda suke kiran mutane zuwa bata ba tare da wani ilimi ba.

اَلْخَامِسَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَتُهُمْ إِيَّاهُمْ إِلَى اَلْكُفْرِ مَعَ اَلْعِلْمِ.

Dabi'a Ta: 75. Yadda suke kiran mutane zuwa ga kafirci alhalin suna sane.

اَلسَّادِسَةُ وَالسَّبْعُونَ: اَلْمَكْرُ اَلْكُبَّارُ، كَفِعْلِ قَوْمِ نُوحٍ.

Dabi'a Ta: 76. Kulla manyan-manyan makirci, kamar dai yadda mutanan Annabi Nuh su ka yi.

اَلسَّابِعَةُ وَالسَّبْعُونَ: أَنَّ أَئِمَّتَهُمْ إِمَّا عَالِمٌ فَاجِرٌ، وَإِمَّا عَابِدٌ جَاهِلٌ، كَمَا فِي قَوْلِهِ: ﴿ وَقَد كَانَ فَرِيق مِّنهُم يَسمَعُونَ كَلَمَ ٱللَّهِ ﴾ إِلَى قَوْلِهِ: ﴿وَمِنهُم أُمِّيُّونَ لَا يَعلَمُونَ ٱلكِتَبَ إِلَّا أَمَانِيَّ وَإِن هُم إِلَّا يَظُنُّونَ٧٨﴾ البقرة:75 – ٧٨.

Dabi'a Ta: 77. Kodai fandararran malami, ko kuma wani mai ibada da yake tintirin jahili, kamar yadda (Allah madaukakin sarki) yace:

'' Kuma hakika wasu jama'a daga cikinsu sun kasance suna sauraron zancan Allah)) hardai zuwa inda Allah ya ce ((Kuma akwai daga cikin su wadanda suke basu iya rubutu ba kuma basu iya karatuba saidai karyace-karyace (shi suka iya). Suratul Bakara, aya ta: 75-78.

اَلثَّامِنَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَاهُمْ أَنَّهُمْ أَوْلِيَاءُ اَللهِ مِنْ دُونِ الناَّسِ.

Dabi'a Ta: 78. Yadda suke cewa su waliyyan Allah ne banda sauran mutane.

اَلتَّاسِعَةُ وَالسَّبْعُونَ: دَعْوَاهُمْ مَحَبَّةَ اَللهِ مَعَ تَرْكِهِمْ شَرْعَهُ، فَطَالَبَهُمُ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿قُل إِن كُنتُم تُحِبُّونَ ٱللَّهَ﴾ آل عمران: ٣١.

Dabi'a Ta: 79. Yadda suke cewa wai suna son Allah, amma kuma basa bin shari'ar Sa, sai Allah ya kalubalance su da fadin Sa: '' Ka ce: (Har) in kun kasance kuna son Allah (To ku bini, sai Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku zunubanku). Suratu Ali Imran, aya ta: 31.

اَلثَّمَانُونَ: تَمَنِّيهِمُ اَلأَمَانِيَّ اَلْكَاذِبَةَ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ لَن تَمَسَّنَا ٱلنَّارُ إِلَّا أَيَّاما مَّعدُودَة ﴾ البقرة: ٨٠. وَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ لَن يَدخُلَ ٱلجَنَّةَ إِلَّا مَن كَانَ هُودًا أَو نَصَرَى ﴾ البقرة: ١١١.

Dabi'a Ta: 80. Yadda su ke burace-burace na karya, kamar yadda suka ce:

'' Ai wuta ba zata taba shafarmu ba sai wasu kwanaki kididdigaggu''. Suratul Bakara, aya ta: 80. Da kuma fadin su: '' Ba mai taba shiga aljanna sai wanda ya kasance bayahude (inji yahudawa) ko nasara (inji kiristoci)''. Suratul Bakara, aya ta: 111.

اَلْحَادِيَةُ وَالثَّمَانُونَ: اتِّخَاذُ قُبُورِ أَنْبِيَائِهِمْ وَصَالِحِيهِمْ مَسَاجِدَ.

Dabi'a Ta: 81. Yadda suke daukar kabarurrukan Annabawan su da kuma na salihan bayin cikinsu masallatai. (kawai sai su gina masallaci a kabarin wani Annabi ko wani salihin bawa).

اَلثَّانِيَةُ وَالثَّمَانُونَ: اِتِّخَاذُ آثَارِ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ كَمَا ذَكَرَ عَنْ عُمَرَ.

Dabi'a Ta: 82. Yadda suke daukar wuraran tarihi na Annabawa (sai su gida) masallatai, kamar yadda aka ruwaito da Umar (dan Khaddab, ya sare bishiyar da aka yi mubaya'a a karkashinta, domin mutane su na shafarta da neman albarka…''.

اَلثَّالِثَةُ وَالثَّمَانُونَ: اِتِّخَاذُ السُّرُجِ عَلَى اَلْقُبُورِ.

Dabi'a Ta: 83. Yadda suke sanya futulu a makabartu.

اَلرَّابِعَةُ وَالثَّمَانُونَ: اِتِّخَاذُهَا أَعْياَدًا.

Dabi'a Ta: 84. Yadda suke daukar su (makabartun) wuraran idi (shekara-shekara).

اَلْخَامِسَةُ وَالثَّمَانُون: اَلذَّبْحُ عِنْدَ اَلْقُبُورِ.

Dabi'a Ta: 85. Yadda suke yanke-yanke a wuraran kabarurrukan.

اَلسَّادِسَةُ وَالثَّمَانُونَ: اَلتَّبَرُّكُ بِآثَارِ اَلْمُعَظَّمِينَ كَدَارِ النَّدْوَةَ، وَافْتِخَارِ مَنْ كَانَتْ تَحْتَ يَدِهِ، كَمَا قِيلَ لِحَكِيمِ بنِ حِزَامٍ: بِعْتَ مَكْرُمَةَ قُرَيْشٍ. فَقَالَ: ذَهَبَتِ اَلْمَكَارِمُ إِلاَّ اَلتَّقْوَى.

Dabi'a Ta: 86. Neman albarka daga wuraran da suke girmamawa, kamar gidan taron su (Darun Nadawa), da kuma alfahari na wanda yake kula da gidan, kamar yadda aka cewa Hakim dan Hizam; Kasayar da darajar kuraishawa'. Sai ya ce: Dukkanin daraja ta tafi saidai tsoron Allah.

اَلسَّابِعَةُ وَالثَّمَانوُن: اَلْفَخْرُ باِلأَحْسَابِ.

Dabi'a Ta: 87. Alfahari da dangantaka.

اَلثَّامِنَةُ وَالثَّمَانُونَ: اَلطَّعْنُ فِي اَلأَنْسَابِ.

Dabi'a Ta: 88. Sukar dangantakar (wasu).

اَلتَّاسِعَةُ وَالثَّمَانُونَ: اَلاِسْتِسْقَاءُ بِالأَنْوَاءِ.

Dabi'a Ta: 89. Rokon ruwa ta hanyar taurarai

اَلتِّسْعُونَ: اَلنِّيَاحَةُ.

Dabi'a Ta: 90. Kukan mutuwa.

اَلْحَادِيَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ أَجَلَّ فَضَائِلِهِمُ اَلْبَغْيُ، فَذَكَرَ اَللهُ فِيهِ مَا ذَكَرَ.

Dabi'a Ta: 91. Lalle mafi girman matsayi a wurin su shine; Zalinci. Sai Allah madaukakin sarkai ya anbaci bayanai akan zalinci da azzali irin abinda ya anbata (akan su).

اَلثَّانِيَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ أَجَلَّ فَضَائِلِهِمُ اَلْفَخْرُ، وَلَوْ بِحَقٍّ، فَنُهِيَ عَنْهُ.

Dabi'a Ta: 92. Lalle mafi girman matsayi a wurin su shi ne; Alfari, ko da ko da hakki ne, sai akan hana.

اَلثَّالِثَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ تَعَصُّبَ اَلإِنْسَانِ لِطَائِفَتِهِ عَلَى اَلْحَقِّ وَالْبَاطِلِ أَمْرٌ لاَ بُدَّ مِنْهُ عِنْدَهُمْ، فَذَكَرَ اَللهُ فِيهِ مَا ذَكَرَ.

Dabi'a Ta: 93. Lalle mutum ya makalkalewa (ra'ayin) jama'arsa akan gaskiya ko akan karya, wannan abune da ya zama ba makawa a wurin su, sai Allah ya anbaci bayani akan hakan irin bayanan da ya anbata.

اَلرَّابِعَةُ وَالتِّسْعُونَ: أَنَّ مِنْ دِينِهِمْ أَخْذَ اَلرَّجُلِ بِجَرِيـمَةِ غَيْرِهِ، فَأَنْزَلَ اَللهُ: ﴿ وَلَا تَزِرُ وَازِرَة وِزرَ أُخرَى ﴾ الإسراء: ١٥.

Dabi'a Ta: 94. Yana gada cikin tsarin addinin su akama mutum da laifin da wani ya aikata, sai Allah ya saukar da:

'' Rai ba ta daukar laifin wata rai'' Suratu Isra'i, aya ta:15.

اَلْخَامِسَةُ وَالتِّسْعُونَ: تَعْيِيرُ اَلرَّجُلِ بـمَا فِي غَيْرِهِ، فَقَالَ: ((أَعَيَّرْتَهُ بِأُمِّهِ؟ إِنَّكَ اَمْرُؤٌ فِيكَ جَاهِلِيَّةٌ)).

Dabi'a Ta: 95. Muzanta mutum da abinda bai da shi. (da wani ya yi haka, sai ma'aikin Allah ya ce; Yanzu zaka muzanta shi gyatumarsa (mahaifiyarsa), lalle kai mutumne da akwai jahiyya a tare da kai''.

اَلسَّادِسَةُ وَالتِّسْعُونَ: اَلاِفْتِخَارُ بِوَلاَيَةِ اَلْبَيْتِ، فَذَمَّهُمُ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿مُستَكبِرِينَ بِهِ سَمِرا تَهجُرُونَ٦٧﴾المؤمنون: ٦٧.

Dabi'a Ta: 96. Alfahari da cewar (mu) muke kula da dakin (Ka'abah), sai Allah ya zarge su da fadar Sa: '' Su na ta girman kai (alfahari) da shi, sun a fira, su na kuma kaurace masa''. Suratul Mu'aminun, aya ta: 67.

اَلسَّابِعَةُ وَالتِّسْعُونَ: اَلاِفْتِخَارُ بِكَوْنِهِمْ ذُرِيَّةَ اَلأَنْبِيَاءِ، فَأَتَى اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿تِلكَ أُمَّة قَد خَلَت لَهَا مَا كَسَبَت ﴾ البقرة: ١٣٤.

Dabi'a Ta: 97. Alfari da cewa ai su zuriyar Annabawa ne, sai Allah ya zo da fadar Sa: ''Waccan al'umma ce da ta riga ta wuce, ta na da abinda ta aikata, (Kuma kuna da abinda kuma aikata)''. Suratul Bakarah, aya ta: 134.

اَلثَّامِنَةُ وَالتِّسْعُونَ: اَلاِفْتِخَارُ بِالصَّنَائِعِ، كَفِعْلِ أَهْلِ اَلرِّحْلَتَيْنِ عَلَى أَهْلِ اَلْحَرْثِ.

Dabi'a Ta: 98. Alfahari da kere-kere, kamar yadda ma su tafiyoyi biyun nan (lokacin bazara da lokaci sanyi) suke alfahari akan manoma.

اَلتَّاسِعَةُ وَالتِّسْعُونَ: عَظَمَةُ اَلدُّنْيَا فِي قُلُوبِهِمْ، كَقَوْلِهِمْ: ﴿وَقَالُواْ لَولَا نُزِّلَ هَذَا ٱلقُرءَانُ عَلَى رَجُل مِّنَ ٱلقَريَتَينِ عَظِيمٍ٣١﴾ الزخرف: ٣١.

Dabi'a Ta: 99. Yadda duniya take da girma a zukatan su, kamar yadda suka ce:

'' Damme ba'a saukar da wannan Alkur'ani ba ga wani mutum daga garuruwan nan biyu ba mai girma''. Suratuz Zukhruf, aya ta: 31.

اَلْمِائَةُ: اَلتَّحَكُّمُ عَلَى اَللهِ، كَمَا فِي اَلآيَةِ.

Dabi'a Ta: 100. Cewa Allah damme?, kamar yadda ya zo a ayar data gabata.

اَلْحَادِيَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اِزْدِرَاءُ اَلْفُقَرَاءِ، فَأَتَاهُمْ بِقَوْلِهِ: ﴿وَلَا تَطرُدِ ٱلَّذِينَ يَدعُونَ رَبَّهُم بِٱلغَدَوةِ وَٱلعَشِيِّ ﴾ الأنعام: ٥٢ .

Dabi'a Ta: 101. Wulakantar da talakawa, sai (Allah) ya zo musu da fadarsa:

''Kada ka kori wadanda su ke kiran Ubangijinsu da safiya da kuma yammaci''. Suratul An'am, aya ta: 52.

اَلثَّانِيَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: رَمْيُهُمْ أَتْبَاعَ اَلرُّسُلِ بِعَدَمِ اَلإِخْلاَصِ وَطَلَبِ اَلدُّنْيَا، فَأَجَابَهُمُ اَللهُ بِقَوْلِهِ: ﴿ مَا عَلَيكَ مِن حِسَابِهِم مِّن شَيء وَمَا مِن حِسَابِكَ عَلَيهِم مِّن شَيء فَتَطرُدَهُم فَتَكُونَ مِنَ ٱلظَّلِمِينَ٥٢﴾ الأنعام: ٥٢ وَأَمْثَالِهَا.

Dabi'a Ta: 102. Yadda su ke aibanta mabiya manzanni da cewar; Ai badon Allah su ke yi ba, kuma diniya su k enema, sai Allah ya amsa musu (da wannan ayar) da ire-iren ta, da fadin Sa : '' Ba'a dora maka wani na hisabin su komai kankantar shi''. Suratul An'am, aya: 52.

اَلثَّالِثَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرُ بِالْمَلاَئِكَةِ.

Dabi'a Ta: 103. Kafircewa mala'ikun Allah.

اَلرَّابِعَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرُ بِالرُّسُلِ.

Dabi'a Ta: 104. Kafircewa manzannin Allah.

اَلْخَامِسَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرُ بِالْكُتُبِ.

Dabi'a Ta: 105. Kafircewa littafan Allah.

اَلسَّادِسَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلإِعْرَاضُ عَمَّا جَاءَ عَنِ اَللهِ.

Dabi'a Ta: 106. Kaudakai daga abinda ya zo daga wurin Allah.

اَلسَّابِعَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلْكُفْرِ بِالْيَوْمِ اَلآخِرِ.

Dabi'a Ta: 107. Kinyarda da cewa akwai ranar lahira.

اَلثَّامِنَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلتَّكْذِيبُ بِلِقَاءِ اَللهِ.

Dabi'a Ta: 108. Karyata cewa ba za su taba haduwa da Allah.

اَلتَّاسِعَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: اَلتَّكْذِيبُ بِبَعْضِ مَا أَخْبَرَتْ بِهِ اَلرُّسُلُ عَنِ اَلْيَوْمِ اَلآخِرِ،كَمَا فِي قَوْلِهِ: ﴿أُوْلَئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بَِايَتِ رَبِّهِم وَلِقَائِهِ ﴾ الكهف: ١٠٥. وَمِنْهَا اَلتَّكْذِيبُ بِقَوْلِهِ: ﴿مَلِكِ يَومِ ٱلدِّينِ٤﴾ الفاتحة: ٤. وَقَوْلِهِ: ﴿ لَّا بَيع فِيهِ وَلَا خُلَّة وَلَا شَفَعَة ﴾ البقرة: ٢٥٤. وَقَوْلِهِ:﴿ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلحَقِّ وَهُم يَعلَمُونَ٨٦﴾ الزخرف: ٨٦.

Dabi'a Ta: 109. Karyata wani sashi na abinda manzanni suka bada labarinsa dangane da ranar tashin alkiyama, kamar yadda (Allah) ya ce:

''Wadan nan su ne fa wadanda suka kafircewa Ubangijinsu da kuma haduwa da Shi''. Suratul Kahf, aya ta:105, kuma yana daga ciki; Karyata zancan Sa (Shi Allah madaukakin sarki): ''Mamallakin ranar sakamako''. Suratul Fatiha, aya ta:4. Da kuma fadansa (Shi Allah): '' Babu wani saye da sayarwa babu kuma kauna kuma babu ceto''. Suratul Bakarah, aya ta:254. Da kuma fadan Sa: '' Sai kawai wanda ya shaida da gaskiya kuma su na sane''. Suratuz Zukhruf, aya ta: 86.

اَلْعَاشِرَةُ بَعْدَ اَلْمِائَةِ: قَتْلُ اَلَّذِينَ يَأْمُرُونَ بِالْقِسْطِ مِنَ اَلنَّاسِ.

Dabi'a Ta: 110. Kasha wadanda suke umarnin a tsayar da adalci a cikin al'umma.