×
Malan yayi bayani akan lokutan da addini ya halasta hada salloli biyi da kuma yadda ake hadawa da sallolinda ake hadi tsakaninsu da dalilan dakesa ahada tsakanin salloli biyu.

    HUKUNCIN HADA SALLOLI BIYU

    [Hausa هوسا-]

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu

    2014 - 1435

    أحكام الجمع بين الصلاتين

    [Hausa هوسا-]

    الشيخ: علي محمد السادس

    2014 - 1435

    HUKUNCIN HADA SALLOLI BIYU

    Gabatarwa: Bayan da bayanai suka gabata akan abinda ya shafi lokutan sallah, da kuma cewar kowacce sallah da lokacin da mahalicci ya sanya ayi ta, to a wannan lokaci zamu kawo bayanai na wadansu lokuta da shara'a ta sawwaka akan hada salloli biyu alokacin daya a gabatar da su, har ma shari'a ta tabbatar da wajibcin hakan a wasu wuraren.

    Sallolin Da Ake Hadawa:

    Mu sani dan ance hada salloli biyu bashi ke nuna mutum ya hada kowacce da wacce ya ga damaba, a'a muslunci ya haskaka mana yadda ake hadawa da kuma wadanda ake hadawa.

    1. Azahar da La'asar.

    2. Magariba da Lisha.

    Kenan ba'a hada isha da asuba, ko asuba da azahar ko la'asar da magariba, hakanan ba'a hada juma'a da la'asar.

    Nau'ukan Hadawar:

    Malamai sun kasa hadawar zuwa gida uku, wato:

    1. Hada azahar da la'asar a lokacin azahar, ko hada magariba da isha a lokacin magariba, shi malamai suke kira ' Jam'u Taqdeem' domin an janyo ta biyu an yi ta a lokacin ta farko.

    2. Hada azahar da la'asar a lokacin la'asar, ko magariba da isha a lokcin isha, shi wannan malamai suke kira da 'Jam'u Ta'akheer' domin an jinkirtar da ta farko har zuwa lokacin ta biyu.

    3. Yin sallar farko akarshen muhtarinta wanda yake ana gamawa farkon muhtarin sallah ta biyu ya shiga sai a yita ita sallah tabiyun, wanda bai luraba sai yace an hada salloli biyune alokacin daya alhali kuma kowacce an yi ta a lokacinta, amma a surar an hadane shi yasa malamai suke kiran wanna'Jam'us Suuree'.

    Wuraran Da ake Hada Salloli:

    Mu sani asali shine kowacce sallah ayi ta akan lokacinta, bai halatta ka tashi daga wannan asali sai kana da dalilai da malamai suka karanta maka masu kwarin gaske, ba wai dalilan da kai ka karanta da kankaba, wadannan wurare sune kamar haka:

    1.Arafat: Idan maniyyaci yana a filin Arafat ranar tara ga watan Zul Hajj, to zai hada azahar da la'asarne a farkon lokacin azahar, kenan da lokacin azahar sai a kira sallah ayi ikamah a sallaci azahar raka'a biyu, sannan sai a mike a kira sallah kiran la'asar kenan sai kuma ayi ikama sai a sallaci la'asar a wannan lokacin, wannan shi ake kira 'Jam'u Taqdeem', yin haka kuma sunnace wajibah in ji mai risalah.

    2. Muzdalifah: Sannan bayan ya kammala tsaiwar Arafat rana ta fadi ba zai sallaci magariba sai ya jinkirta sai ya kai muzdalifa sai ya hada magariba da isha ya sallace su a lokacin isha, ko wacce da kiran sallah da kuma ikama, sai dai idan an yi sallah amma su basu yi ba to anan ba za su kira sallah ba sai su yi ikama su sallaci magariba raka'a uku isha kuma raka'a biyu. Wannan jinkirta magariba da aka yi a ka sallaceta a lokacin isha shi ake kira'Jam'u Ta'akheer' kamar yadda bayani ya gabata.

    3. Ruwan Sama: Haka nan kuma ida ya zama ruwan samane ko kuma duhune da tabo to anan wadanda ke masallaci sai su hada magariba da lisha sai kowa ya wuce gida, ga yadda ake hadawar:

    'Za'a kira sallar magariba a farkon lokacinta a wajan masallaci (wato da lasifika) sannan sai a dan jinkirta sallar kadan, sannan sai a tada ikama sai a sallaceta. Sannan sai a kira sallar isha a cikin masallaci (kenan ba tare da lasifikaba) sai a tada ikama a sallace raka'a hudu, a lokacin akwai haske shafaki bai baceba kowa sai ya koma gida'.

    Anan sai a kiyaye wasu kwata-kwata ba ruwansu da wani abu waishi hada sallolin magariba da lisha saboda ruwan sama.

    Wasu kuma da zarar hadari ya daga ko ya kai yadda ya kamata ayi tunanin hadawa ko bai kaiba sai ace an hada salloli a su, wannan kuskurene, hadawar saukine musulunci ya zo da shi, yin kowacce sallah a lokacinta wajibine, to kada ka tashi daga wannan wajibin zuwa ga wannan saukin sai kana da dalilai masu kwari.

    4. Halin Tafiya: Idan mutum ya fara tafiya kafin lokacin sallah ta farko a sallolin da ake hadawa ya shiga kuma ga shi sun kan tafiya sun samu su jinkirta ta farkon su yita a lokacin ta biyu, idan kuma sun sami dama sai su yi ta biyun alokacin ta farko, ma'a ko su yi 'Jam'u Taqdeem' ko kuma su yi'Jam'u Ta'akheer', misali; mutum ya bar gida karfe: 10:30am na safe ai lokaci azahar bai yiba sai suke ta tafiya ba'a tsaba sai 2:30 na rana to anan sai su hada azahar da la'asar ko ba'a tsaya ba sai kafe 4:30pm na yamma duk anan ba komai sai su hada azahar da la'asar kowacce raka'a biyu biyu, ba sai an sami matsala da direbaba, domin su mutane sun dauka kowacce sallah sai an tsaya an yi ta a lokacinta, ai ida kana halin tafiya zaka iya hada azahar da la'asar, ko kuma magariba da lisha a lokacin kowacce daya daga cikinsu, amma ba'a hada azahar da la'asar da magariba a lokacin isha, bayanai sun gabata.

    Al'amarin addinin musulunci al'amarine mai saukin gaske, kuma kullum gwargwadon yadda ka fahimceshi gwargwadon yadda yake da sauki a gareka, Allah mun gode maka.

    Saboda haka koda tsayawa aka yi domin aci abinci sai kake ganin lokacin ba zai ishekaba sai ka yi sallah a lokacin abincin ka saya ka ci a cikin mota.

    Idan kuma yanzu zaku fara tafiya kuma gashi lokacin azahar ya yi shikenen sai ku sallaci azahar raka'a hudu bayan kun yi sallama sai ku mike ku kawo la'asar itama raka'a hudu. Haka kuma ida lokacin magaribane sai ku yita raka'a uku sai kuma ku mike ku kawo isha raka'a hudu sai akama hanya, Allah ya sakeku lafiya.

    5. Rashin Lafiya: idan mutum bashi da lafiya ya samu ya jinkirta sallar farko zuwa karshen muhtarinta wanda yake shine farkon muhtarin sallah ta biyu, sai ya sallace su, ma'ana ya yi sallar farko a lokacinta sallah ta biyu ma a lokacinta wannan malamai suke kira ' Jam'us Suuree', hakanan ma idan za'a yi mishi fida ya zama idan an jira lokcin sallah ya yi babu wata damuwa sai ajira domin ya sallace su duka, misali idan aka jira azahar ta yi sai ya yi azahar ya kuma kawo la'asar idan ya fi kusa da su, ko a jira magariba sai ya yi ta ya kuma kawo lisha idan dasu ya fi kusa, sannan sai ayi masa aiki, amma idan jinkirin zai kawo masala alafiyarsa sai ayi mishi aikin ba tare da an jira lokacinba.

    Hadisi ya tabbata a ruwayar Muslim da Imam Ahmad da Tirmizi da Nasa'i da Abu Daud cewar ''Ma'aikin Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya hada azahar da la'asar, ya kuma hada magariba da lisha a birnin madina ba tare da tsoroba ba kuma ruwan sama ba'' sai aka tambayi Abdullah ibu Abbas akace; ''Me yake nufi da hakan kenan? Sai ibnu Abbas yace: ''Yana son kada ya kuntatawa al'ummarsa''.

    Sai malamai sukace wannan ya nuna halaccin jinkirta sallah zuwa karshen muhtarinta sannan a sallaceta wanda yake nuna shine kuma farkon muhtarin sallah ta biyu sai wanda bai luraba yace an hada su, Eh, an hada kuma an raba, an yi kowacce a lokacinta wannan ya nuna an raba, an yi ta farko sai aka mike aka kawo ta biyu wannan yake nuna an hada shi yasa malamai suke kiran wannan da 'Jam'us Suuree'.

    Saboda haka wannan baya nuna haka kawai mutum ya tashi da zarar an kammala azahar ya kawo la'asar ko da zarar an kammala magariba ya kawo lishi dogaro da wannan hadisin domin yin haka ya sabawa fahimtar magabata a kan hadisin.

    Kammalawa: Lalle wannan ya nuna mana irin gatan da musulunci ya yi ma da irin yadda Allah yake nufatar wannan al'umma da sauki bad a tsanani ba, ta yadda dudda cewar shigar lokaci sharidine na sallah amma aka sami wasu wurare da musulunci ya yarda da a hada wadannan salloli, wannan kuma saukine a garemu, Ya Allah mun gode.

    Rubutawa :

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu