×
Yayi Magana akan HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI ,da yakamaci Musulmi yasansu

    HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI

    أحكام صلاة العيد

    [Hausa هوسا-]

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu

    2014 - 1435

    HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI

    Gabatarwa: Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare da ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi ne na SALLAR IDI! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana komai abinda ya rage kawai a garemu shi ne bi, komai angama, Allah tabbatar da duga-dugammu akan tafarkin Ma'aikin Allah.

    Mecece Sallar Idi:''Ita sallar idi sallace da ake gabatar da ita a wani lokaci kebantacce, awata siffa kebantacciya, sau biyu a shekara''. Kafin mu kai ga fashin bakin wannan ta'arifi na sallar idi, bari mu gabatar da tabbatuwarta tukunna.

    Tabbatuwar Sallar Idi: Sallolin idi guda biyu da musulunci yake da su (Karamar Sallah da Babbar Sallah) kowacce ta tabbata a shara'a, ba wai bikine haka kwai na gargajiyaba.

    Tabbatuwar Karamar Sallah: itace sallar da ake gabatarwa a ranar 1 ga Shawwal, don godiya ga Allah akan baiwar da ya yi mana na kammala azumin watan Ramadan, wannan sallar ta tabbata a Suratul-A'alah aya ta:14-15, Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Tabbas duk wanda ya bayar da zakka (Fidda-kai) ya rabauta. Kuma ya anbaci sunan UbangijinSa sannan kuma ya yi sallah''. Sai malamai sukace 'Zakka da aka anbata a ayar farko itace zakkar fidda-kai, Sallah kuma da aka anbata a aya ta biyu itace, karamar sallah domin itace ake fitar da zakkar Fidda-kai kafin a ta fi, sannan kuma ga zikirin da aka an'anbata shine wanda ake yi lokacin tafiya sallar idin'.

    Tabbatuwar Babbar Sallah: Ita kuma sallah ce da ake gabatar da ita a ranar 10 ga watan Zul-Hajji. Ita ma babbar Sallah ta tabbata a Suratul-Kauthar a aya ta: 2. a inda Allah madaukakin sarki yake cewa ''Ka yi Sallah domin Ubangijinka, kuma ka soke (abin hadayarka)'', malamai sukace 'Babbar Sallah ce domin an hada Sallah da Yanka' a ayar kamar wacce ta gabata an'hada Zakka da Sallah. Wannan tabbatuwar wadannan sallolike nan ta ayoyin alkur'ani, hakanamma sun tabbata ta ayyukan Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, Bukhari da Muslim da Abu-Daud da Nasa'i duk sun ruwaito daga Jabir-Allah Ya kara masa yarda yace ''Na harci Sallar idi tare da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- sai ya fara gabatar da sallah kafin Huduba ba tare da an yi kiran sallaba ko an tada Ikama''. Haka shima Bara'u dan Azib –Allah Ya kara masa yarda yace ''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya yi mana huduba a ranar babbar sallah, bayan ya idar da sallah sai yace ''Duk wanda ya yi wannan sallar tamu, kuma ya yi yanka irin namu to yankanshi ya yi daidai, wandako ya yanka kafin ayi sallah to wannan bashi (da ladan) yanka''. Wannan hadisin malaman Hadisi bakwaine suka ruwaito shi.

    Hukuncin Sallar Idi: Hukuncin sallar idi shine, Sunnace mai karfin gaske, domin Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya aikata ta kuma ya lizimceta, hakanan kuma ya fitar da mata da kanan yara zuwa halartar wannan sallah. Saboda haka bai kamata mutum ya yi sakaci da itaba har ya rasa samun wannan sallah wanda saboda ita nema aka bada hutu a kasa baki daya, ka rufe shagonka na kasuwanci ka dakatar da ayyukanka.

    Lokacin Sallar Idi: Kamar yadda bayani ya gabata a ta'arifi cewa sallace da ake gabatarwa a lokaci kebantacce to wannan lokacin kuwa shine ''Daga lokacin da rana ta fito ta daga kamar tsawon sandar mashi harzuwa lokacin da rana zata karkata daga tsakiyar sama''. Amma malamai sukace 'An fi so a babbar sallah a yi ta da wurwuri domin mutane su samu su koma gida domin su yanka layyarsu a daidai lokacin walaha, sannan kuma su ci abinci domin basu ci ba suka fito sallah. Amma akaramar sallah an fi so a dan jinkirta sallar domin mutane su samu su gama fitar da Zakkar su ta fidda-kai, su kuma ci abinci domin iti an fi so a ci kafin a fito sallah'.

    Ladubban Sallar Idi: Akwai wadansu ladubba da yakamata a ladabtu da su, wadannan ladubba suna da yawa daga ciki akwai:

    1. Yin wanka da sanya turare da kuma sanya tufafi masu kyau sababbine ko nada.

    2. Hakanan yana daga cikin labudda a ci abinci kafin a fita sallar idi a karamar sallah, da kuma jinkirta cin abinci a babbar sallah har sai an yi sallah, da kuma cin wani abu na hantar dabbar layyah ga wanda ya yi. Ankarbo daga Buraidah –Allah Ya yarda da shi- yace; ''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya kasance baya fita zuwa masallcin idi a karamar sallah har sai ya ci abinci, kuma ya kasance baya cin abinci a babbar sallah har sai ya dawo daga masallacin idi, sai ya ci wani abu na dabbar layyarsa''.wannan Hadisi Tirmizine ya ruwaito.

    3. Kana yana daga cikin ladubba yin kabarbari, kuma lafazinta shine: Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamd.

    4. Yin gaisuwar sallah wato kacewa dan'uwanka musulmi ''Allah Ya karba mana ya karba muku''.

    Siffar Sallar Idi: Kamar yadda ya gabata a farkon bayani cewa sallace da ake gabatar da ita a wata siffa kebantatta, wannan siffa kuwa itace; wannan sallah ana yin ta ne Raka'a biyu, kuma ana bayyana karatun, ba tare da angabatar da kiran sallah ba, ko tada ikama, sannan kuma ba'a gabatar da nafila kafin sallar ko bayan sallar. A raka'ar farko bayan kabbarar harama anayin kabarbari shida kafin fara karatu (wato kabarbari bakwai kenana). A Raka'a ta biyu bayan kabbarar tasowa sai a yi kabarbari biyar, kafin fara karatu (wato kabarbari shida kenan), wadannan kabarbari liman da mamu duk suna yinsu sai dai mamu baya karatun sallah saboda karatun liman, sannan sai ayi sallar kamar sauran salloli, bayan liman ya yi Tahiya ya yi sallama sai ya gabatar da Huduba, sannan yana da matukar muhimmanci a tsaya a saurari hudubar, wadannanfa sune ayyukan ranar, amma wacce gaggawa mutane suke yi suke barin sauraron Hudubar?.

    Wanda bai samu sallar idi ba ya samu ya yi sallah Raka'a hudu kamar nafilfili, idan kuma ya ga dama ya yi ta a siffar sallar idi.

    Idan kazo ka sami liman yana Tahiya sai ka zauna tare da shi, idan ya yi sallama sai ka mike ka kawo raka'oinka biyu a siffar su da ta gabata.

    Wadansu Mas'aloli: A yanzu za'a kawo wadansu halaye da mutum yakan samu kanshi a ciki idan ya zo ya samu tuni anfara sallah.

    1. Idan mutum ya zo ya sami liman ya kammala kabarbari ya fara karatu ya zai yi?. Amsa: Anan zaka yi wadannan kabarbarin, kasancewar ba abune mejan lokaci ba, sannan sai ka raurari karatun liman.

    2. Idan ka zo ka sami liman ya fara kabarbari amma bai gamaba, to anan zaka yi sauran kabarbarin da suka ragewa liman tare da shi, sannan sai ka kawo wadanda suka wuceka, koda liman ya fara karatu, kenan anan ba zaka yi wadanda suka wucekaba a lokacin kabarbarin liman.

    3. Idan kazo ka sami liman yana Ruku'u sai ka yi kabbarar harama kadai ka bishi, ba sai ka kawo sauran kabarbarinba.

    Tambihi: Ya kamata mu san girman wadannan salloli da matsayinsu a addini, tunda har yakai Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa a fita sallar har da mata da kananan yara, har mata marasa tsarki idan sun je sai su yi nesa da wurin sallah idan anzo huduba suma sai su anfana. Kada mu sha'afa akan wannan sallarne aka bada hutu duka kasa, aka rufe shaguna kada mutum ya shagala a wannan lokaci da abinda zai hana mishi samun wannan sallah. Sannan kuma a kula da yara da irin suturar da za su sa, domin idan ka ga wadansu yaran ba kace 'ya'yan musulmi bane, wannan baidace ba kuma baikamata, wasu kuma rawa kamar mazari, Allah Ya sawwaka, amin.

    Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata ya bayyana a garemu cewar sallar idi ba wata gargajiya bace ibadace da Allah ya shar'anta ta ta harshen fiyayyan halitta Annabi Muhammad –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, itako ibada anayinta akan yadda aka tsarata ne, Allah ya karbi ibadarmu ya sa ayi sallah lamilafiya ya tsaremu ya tsare mana imaninnu, amin.

    Rbutawa :

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu