×
Yayi Magana ne akan NAJASA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA. ,da nau aukata

    NAJASA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA

    [Hausa هوسا-]

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu

    2014 - 1435

    النجاسة وأحكامها

    [Hausa هوسا-]

    الشيخ : علي محمد السادس

    2014 - 1435

    NAJASA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA.

    Abubuwan Da Suke Najasa:

    Na farko: Fitsari. (Na mutum) Na babba ko na karami na mace ko na namiji, ya fara cin abinci ko bai faraba. Na biyu: Bayangida (Kashi na mutum). Na uku: Mushe, shine abinda ya mutu da karan kansa, ko aka yankashi ta hanyar da bata musulunci ba. Na hudu: Nonon dabbar da ta yi mushe. Na biyar: Nonon dabbar da aka haramta cin ta, kamar nonon karya, ko alade ko jaka...' Na shida: Fitsarin dabbar da aka haramta cin ta, kamar fitsarin jaki, ko kare…' Na bakwai: Kashin dukkanin dabbar da aka harantata, kamar kashin alade (alhanzir), kashin jaka/jaki..' Na takwas: Kashi da fitsari na dukkanin dabbar da take cin najasa. Na tara: Giya. Na goma: Jini, saboda haka bai halatta a tari jinin da aka yanka dabba ba wai ace za'a gasa shi ko a soya ko ayiwa dabbobi abinci da shi ba domin najasa ne (in banda jinin da ake samu a cikin dabba bayan anyankata wanda bai fitaba, ai dakyar a rasa jini a cikin dabba). Na sha-daya: Ruwan ciwo. Na sha-biyu: Maziyyi, shi kuma ruwane da yake fari yana da laushi yana fitane lokacin motsawar sha'awa ta mace ko namiji ta hanyar wasa ko kallo ko nitsewa cikin tunani, amma idan sha'awa ta kara karkafafa to maniyyine ke fita, shi kuma maniyyi ana jin fitarshi sabanin maziyyi, sannan shi kuma maniyyi yana da kauri sabanin maziyyi shi yana da laushine, bayanai za su zo akan shi nan gaba kada idan Allah Ya yarda. Na sha-uku: Wadiyyi, shi kuma ruwane fari yana kauri sau da yawa yana fine akarshen fitsari, ta sanadiyyar daukar kaya mai nauyi, ko matsanancin sanyi, ko kullewar ciki. Na sha-hudu: Ragowar ruwa ko aminci na dabbar da ba'a ci, kamar rowan da jaki ya sha ya raje, in banda mage. Na goma sha-biyar: Yawun kare da na alade, ko na dukkan babbar da ta samu ta hanyar su. Na goma sha-shida: Amai, alokacin da canza daga yanayin abinci, kenan idan aka ci abin ci yanzu sai kuma aka harar da shi wannan harawwar ba najasa bace. Wadannan sune abubuwan da suke najasa, amma akwai wadansu da malamai suka karawa juna sani akansu kan najasa ne ko ba najasa ne ba, kamar ragowar ruwa na wanda ba musulmi bane ya sha, hakanan akan maniyyi.

    Shidai Maniyyi na namiji: Ruwa ne da yake fari maikauri yana tunkudar junansa alokacin da zai fita, idan ka shinshina shi ya yi kama da hudar dabino, kuma ya yi kusa da kanshin kulli, amma idan ya bushe yana kasancewa kamar karnin fasasshan kwai. Wannan shine galibin yadda maniyyin namiji yake kasancewa, wani lokacin ya kanzo sabanin wadannan bayanai da suka gabata. Yana fitane lokacin matsananciyar sha'awa ta sanadiyyar kallo ko wasa ko matsanancin tunani ko lokacin saduwa. Shi kuma Maniyyin mace, shi ma: Ruwane fatsi-fatsi yana da laushi. Wannan ya tabbatar da cewa mace ma tana da maniyyi kuma da shi ne da na namiji Allah Yake halitta da su.

    Wasu malamai sunce maniyyi najasa ne domin yana fitane ta mafitar fitsari wanda yake shi kuma fitsari najasane, wasu malaman kuma sukace ba najasa bane domin da shi ne Allah Ya halicci dan'adam kuma a cikinsu akwai Annabawa da Manzanni, kenan ya za'a mutum da Allah ya karramashi da yaukaka shi har ya fitar da Annabawa da Manzanni ace kuma da najasa aka yi shi??. Wadannan sune abubuwan da suke najasa da kuma wadanda malamai suka yi wa juna Karin fahimta.

    Hukuncin Najasa:

    Wajibine gusar da najasa daga jiki da tufafi da wurin da za'a yi sallah, idan mutum yana da ikon gusar da ita kuma yana sane bai gusar da ita dinba ya yi sallah da ita to ba shi da sallah. Addinin musulunci addinin tsaftane abinda musulunci yake so shine akoda yaushe ka sance cikin tsarki, mafificin tsarki kuma shi ne tsarkin zuciya a kakkabeta daga barin shirka da zalinci da hassada da munafunci da dukkan wata mummunar dabi'a, idan aka samu tsarkin zuciya kuma ga tsarkin tufafi da ganganjiki da kuma mahalli to lalle wannan shi ke nuna kammaluwar mutum.

    Yadda Ake Gusar Da Najasa:

    Idan ka ga inda najasar take a jikinka ko a tufafinka to iya inda yake iya nan zaka kama ka wanke, sabanin yadda wasu matan suke yi wai dukkanin tufafin da tasa alokaci da take al'ada to sai ta wanke su, kama daga dankwali da zani da riga…' wannan musulunci bai zo da shi ba, inda kwai kika ga jini iya nan kawai za ki wanke. Idan kuma najasar ta rikice maka baka ganta ba, amma ka tabbata akwaita ajikin tufafin na ka shikenan sai ka wanke tufafin gabadaya. Amma idan najasa ta fantsamo sai kake kokwanton ta tabaka ko bata taba ka ba, kuma kai baka ganta ba kuma ka duba mai Ahlari yace sai ka yayyafa ruwa a wurin.

    Amma kuma idan wani abu ya fallatso maka sai kake kokwanto wannan abun najasane ko ba najasa ba ne, to awannan lokaci ba wani hukunci akanka, ba yayyafa ruwa ballantana wankewa, domin mafiyawan abubuwa masu tsarki ne, najasa kadanne shi yasa ake iya lissafe su.

    Idan inda najasar take kuma filine ko bango ko wani dutse sai aka yi ruwan sama ko kuma aka kwarara ruwa mai tsarki akai shikenen an gusar da wannan najasar. Amma idan ta kasace yawun karene wato karene ya baki a kwano ko a kwarya to za'a zubar da abinda yake ciki sannan a wanke sau bakwai sannan asa kasa a daya daga cikin bakwai din. Amma najasar da ba wannan ba sai a wanke ya wanku sabanin yadda ake yi, da yaro ya yi fitsari sai ace wai za'a yayyafa ruwa alhali wankewa akace a yi, wani ruwamma da aka yayyafa kamar karawa fitsarin yawa aka yi, Allah ya sawwake. Ya zama wajibi a tshi tsaye a gusar da najasa a tsaftace muhalli, musulmi ya kasance tsaftattace tsafta cikon addini ai ta fi ace ita ciko ce, ita sharadice sai mutum ya tsarkaka daga wadannan najasar ibadar shi zata karbu.

    Abubuwan Da Najasa Take Hanawa:

    Anan za'a anbaci wadansu abubuwa ne da basu halatta ga dukkan mara tsarki ya aikata su saboda darajarsu da matsayinsu, kuma hadasin babbane ko karami, wadannan abubuwa sune:

    (1) Taba Alkur'ani: Bai halatta ga mara tsarki ya taba Alkur'ani, har sai ya yi tsarki inda so samune ma ya yi alwala musamman idan ya kasance ba mai yawan daukan Alkur'ani bane.

    (2) Sllah: Hakanan bai halatta ga mara tsaki ya yi sallah ba farillace ko nafila, har sai ya tsarkaka ya kuma yi alwala, kamar yadda Ma'aikin Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace: '' Allah ba zai karbi sallar wanda ya yi hadasiba har sai ya yi alwala'' Bukhari:135, Muslim:225. Hakanan kuma ko da mutum yana da tsarki amma tufafinsa ko wurin sallar baida tsarki to delene ya tsarkake su kafin fara sallar, saidai idan bai saniba ko ya manta cewa a tufafinsa ko wurin da ya yi sallah akwai najasa sai kuma da lokacin sallar ya fita sannan ya gani ko ya tuna to anan ba komai sallar shi ta yi.

    (3) Tawafi: Kuma dukkan mutumin da bashi da tsarki to bai halatta ya yi Tawafin Ka'aba ba, daman kuma ananne kadai ake dawafi a sararin duniyar nan.

    Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata munsan abubuwan da suke najasa ta yadda ko yanzu akace ka kawo biyar zaka iya cikin gaggawa, da kuma hanyoyin da akebi wurin gusar da wannan najasa, wanda yake gusar da ita din wajibine domin munji abubuwan da bai halatta mara tsarki ya yi ba, akaro na gaba zamu kawo bayanai akan wadansu abubuwa da ake ganinsu kamar najasane alhali kuma ba najasa bane.

    Rbutawa :

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu