×
Yayi Magana ne akan HUKUN-HUKUNCEN RUWA ,da yakamaci Musulmi ya sansu

    HUKUN-HUKUNCEN RUWA أحكام المياه

    [Hausa هوسا-]

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu

    2014 - 1435

    HUKUN-HUKUNCEN RUWA (RUWA ABOKIN AIKI)

    Kada ka manta sallah itace shisshike na biyu daga cikin shikashikan musulunci guda biyar, itace kuma ginshikin addinin musulunci duk wanda ya tsaida ita to ya tsayar da addini, haka kuma duk wanda yabar sallah to yabar addini. Ita kuma sallah bata zama sallah sai idan an yi alwala, an tsarkaka daga dukkanin najasa an gusar da hadasi da kuma kabasi, wato dukkanin najasar da ta fito daga jiki ita ake kira Hadasi, kamar mutum ya yi: fitsari, bayangida, maziyyi…'' shikuma kabasi shine dukkanin najasar da ta shafi jikinka, ko tufafinka, ko kuma wurin sallah. Gusar da wadannan abubuwa na hadasi da kuma kabasi da aiwatar da alwala, basa tabbata sai da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa, wato kenan rowan sai ya cika sharudda biyu, na farko ya zama mai tsarki, na biyu kuma ya zama zai iya tsarkake wani.

    Allah madaukakin sarki yana cewa ''Kuma mun saukar da ruwa daga sama wanda za'a yi tsarki da shi'' Suratl Furkan, aya ta:48.

    Wannan ayar tana kunshe da hukunce hukunce da dama, daga ciki akwa: Allah ya sanya ruwa shine abinda za'ayi tsarki da shi, ba'ayi da yawu/miyau, abunmamaki sai mutum ya gama fitsa sai lakato yawunsa ya goga abansa, lalle wannan ya yi nesa da makaranta. Abu na biyu kuma shine ruwan sama ruwane da za'a yi tsarki da shi kai tsaye, abu na uku dukkan ruwan da yake a cikakkiyar siffarsa ta ruwa babu abinda ya canza shi to za'a yi tsarki da shi.

    Abubuwan Da Suke Canza Ruwa. Abubuwan da suke canza ruwa har ya zama wannan ba za'a yi ibada da shi ba (kamar alwala, tsarki..) abubuwane guda uku, da zarar ruwa ya canza da daya daga cikinsu to wannan rowan ba za'a yi ibada dashiba, wadannan abubuwa sune:

    (1) Launi: Kazarar kalar ruwa ta canza ba yadda aka san ruwaba, ko dai ya yi canza ya yi ja, ko baki, ko kore…' to wannan rowan ba za'a yi ibada dashiba.

    (2) Dandano: Idan dandanon ruwa ya canza to wannan ruwan ba za'a yi ibada dashi ba.

    (3) Shinshina: Hakana duk abinda ya jirta kanshin ruwa zuwa wani abu daban to wannan ruwan ba za'a yi ibada da shi ba.

    Idan ruwa ya canza da yada daga cikin wadancan abubuwa uku kenan wadannan abubuwa sun jirkita shi ta yadda ba zai iya amsa sunan ruwaba, domin ya zama Sobo (Zobo) ko kunu ko ruwannan datti, to wannan ruwan ba za'a yi ibada da shiba. Amma idan daya daga cikinsu ya fada cikin ruwa amma bai canza ruwanba ta dayan wadancan fuskoki uku to babu abinda ya sami ruwan za'a yi aiki da shi, kuma za'a ibada da shi. Wannan zai nuna kuskren da ake yi na idan ansa hannu a ruwa ko mutum ya tara fanfo sai kasa hannu ko kasa kwano ko buta sai ace za'a malalar da ruwan wai bashi da tsarki, ko wata dabba da ake ci (wacce ba ta cin najasa) ta sha, ko kuma dabba ta fada rijiya ko ma mutum sai ace wai za'a kwashe ruwan rijiyar azubar (ko guga kaza) wannan duk bai halattaba a musulunci, duk abinda ka ga ya cikin ruwa kuma ka cire shi ka ga babu abinda ya canza rowan kwatakwata cikin wadancan abubuwa uku ka yi shiru da bakinka aci gaba da aiki da ruwa.

    Nau'ukan Abinda Ruwa Yake Canzawa Da Su: Canzawar ruwa da muke Magana akanshi yana da kyau musan abinda ruwa yake da canzawa da shi lura da hukunce-hukuncen kowanne, kamar haka:

    - Da Makwancinsa: Idan ruwa ya canza kala ko dandano ko shinshina, saboda inda yake, kamar Jarkasa, Farar kasa, Kanwa, Kainuwa, Gansakuka… duk wadannan idan ruwa ya canza ya yi fari saboda wurin farar kasace ko ya yi Jaa saboda wurin jarkasace ko dandanonshi ya yi gafi saboda wurin kanwace ko tekuce ko wuraran da ake hakar mai, duk wannan canza wad a ruwa ya yi babu abinda ya shafeka zaka yi ibadarka da shi salin-alin alattacciyar ibada.

    Kenan waccar Magana da aka yi sai idan ruwan ya canza da wani abu na daban da ba makwancinsaba ta yadda zai iya yuwuwa a rabasu amma a inda yake makwancinsane babu yadda za'a yi ka rabasu.

    - Abu Mai Tsarki: Idan wani abu mai tsarki kamar gishiri ko yaji ko miya ko sabulu ya zuba cikin ruwa amma kwatakwata bai canza ruwanba to wannan ruwan za'a yi ibada dashi kamar yadda bayanai suka gabata, amma idan sun canza ruwane to wannan rowan ba za'a yi ibada da shi ba, amma za'a yi ayyukan gida da shi, kamar girki wanki kunun-zaki d.s.

    - Najasa: Idan najasa ta jirkita ruwa ta daya daga cikin abubuwannan uku, to bai halatta a yi anfani da wannan rowan kwatakwata ba za'a yi ibada da shi ba, kuma ba za'a yi wasu ayyuka nadaban da shiba kenan kwararar da shi kawai za'a yi.

    Lalle wannan ya nuna mana muhimmacin ruwa da kuma yadda addinin musulunci ruwa shine abinda ba yi za su ibada da shi bai sa musu feturba ko gas domin rahamar Allah ga bayinsa sai ya sanya musu ruwa kuma ya sanya shi ya zama sinadarin rayuwa. Saidai kawai idan mutum bai sami ruwaba a lokacinda zai yi tsarki sai ya yi Istijmari, ko zai yi alwala kuma gashi babu ruwa sai ya yi taimama, kamar yadda bayanansu zasu zo nan gaba.

    Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata zai nuna baka yadda addinin musulunci ya baima ruwa kulawa ya kuma sawwake shi, kuma wannan yana nuna mana yadda ya zama wajibi mu tashi musan hukunce-hukuncen ruwa domin idan mutum bai sani ba sai ya debi ruwan wanki ko kuma ruwan da ya gama wanka da shi bayan ya zama sabulu ya ce zai yi tsarki da shi, domin wasu sun dauka ruwan alwala shi ake bashi wannan hukunce-hukunce amma shi tsarki mutum zai iya yi da ko wanne, alhali abin ba haka bane, Allah ya sawwake amin. Allah Shi ne masani.

    Rbutawa :

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu