×
Wannan wani littafi ne takaitacce kuma cikinsa akwai abinda ya wajaba Mutum ya sanshi kuma ya kudurce shi na abubuwan da suka shafi kadaita Allah, da kuma Tushen Addini da wasu abubuwan da suke da alaka da shi wadanda aka samo su daga litattafan Tauhidi na Manyan Malaman Mazhabobin nan guda Hudu. Iman Abu hanifa, Imam Malik, Imam Shafi'i, Imam Ahmad bn Hanbal, da kuma mabiyansu - Allah ya yi musu Rahama, kuma su ne wadanda Mutane suka hadu kan cewa Akidar su tana kan Akidar Ahlusunnah da Jama'a babu wanda kuma ya saba kan hakan.

Akidar Limaman Mazhabobi Hudu

– Allah ya yarda da su –

(Abu Hanifa Malik Shafi'i da kuma Ibn Hanbal)

Wallafar: Wasu Zababbun Malamai

Gabatarwar Babban Malami: Salah Bn Muhammad Al'budair

Fassara da Bitar:

Cibiyar Jagororin Fassara

Gabatarwar Shiekh Salah Al'budair

Gidiya ta tabbata ga Allah wanda yayi Hukunci kuma ya kafu daram, kuma ya halatta kuma ya haramta, kuma ya sanar kuma ya Ilmantar, ya Sanar a cikin Addininsa kuma ya fahimtar, kuma na shaida cewa babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, ya shimfida durakun Addini da littafinsa tabbatacce wanda ya shi ne shiriya ga baki dayan Al'ummai, kuma na shaida cewa lallai cewa Annabi Muhammadu Bawansa ne kuma Manzonsa ne, wanda aka aiko shi ga baki dayan Duniya, na larabawa da kuma Baibayi da tafarki wanda ya kaucewa dukkan bata da sharia ga Mukallafai, bai gushe ba yana kira da ita kuma zuwa gareta, kuma yana ta fafatawa da Dalilai akanta, kuma yana karewa da Takobbinsa Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi da Sauraran Sahabbansa kan tafarki madaidaici, da kuma sauran masu dangantuwa zuwa ga wannan, Bayan haka:

Kuma hakika na duba wannan littafin mi suna (Akidar Malaman Mazhabobi Hudu) kuma wanda wasu gungu na Daliban Ilimi, sai na sameshi yayi daidai da Ingantacciyar Akida kuma yana tabbatar da Mas'alolinta, daidai da Akidar Magabata na kwarai wanda aka gina akan littafin Allah da Sunnah. kuma sabida muhimmancin wanan Maudhu'i ne da abinda ya kunsa na Mas'aloli ne nake wasiyya da a buga shi da kuma yada shi ina mai rokon Sarki majibinci kuma mai Iko da ya Amfanar da shi ga duk wanda ya karanta shi kuma ya sakawa wanda yayi shi da Mafificin Alkairi kuma mafi cikarsa Allah kayi tsira da Aminci ga Annabi Muhammad da Alayansa da Sahabbansa baki daya.

Limamin Massallacin Annabi

kuma Alkali a gamammiyar Kotu a Birnin Madina

Salah Bn Muhammad Al'budair

Gabatarwar Mawallafa

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai kuma tsira da Aminci su tabbata ga Anabinmu Muhammad shugaban Manzanni, da Alayansa da Sahabbansa baki daya. Bayan haka:

Wannan wani littafi ne takaitacce kuma cikinsa akwai abinda ya wajaba Mutum ya sanshi kuma ya kudurce shi na abubuwan da suka shafi kadaita Allah, da kuma Tushen Addini da wasu abubuwan da suke da alaka da shi wadanda aka samo su daga litattafan Tauhidi na Manyan Malaman Mazhabobin nan guda Hudu.

Iman Abu hanifa, Imam Malik, Imam Shafi'i, Imam Ahmad bn Hanbal, da kuma mabiyansu - Allah ya yi musu Rahama, kuma su ne wadanda Mutane suka hadu kan cewa Akidar su tana kan Akidar Ahlusunnah da Jama'a babu wanda kuma ya saba kan hakan. Kamar littafin Alfiqh Al'akbar na Abu Hanifa Allah ya yarda da shi wanda ya rasu a shekarar 150 Hijira Aqidat Al'tahawiyya Na Attahhawy wanda ya rasu a shekarar 321Hijira da Sharhinta na Babban Malami Abul Izz Alhanafi wanda ya rasu a shekarar 792 Hijira Da Muqaddimat Al'risala na Abu Zaid Alqairawani Almaaliky wanda ya rasu a shekarar 386 Hijira Da Usoul Al'sunnah Na Abu Zamanain Almaliky wanda ya rasu a shekarar 399 Hijira Da Al'tamhed Sharhin Muwatta na ibn Abdulbarri wanda ya rasu a shekarar 463 Hijira

Kuma wannan littafi a cikin Akidar Ahlul Hadith na Al'sabouni Al'Shafi'a wanda ya Mutu a shekarar (449) bayan Hijira Da Sharhussunnah Na Al'muzni Dalibin Shafi'a wanda ya rasu a shekarar 264 Da kuma Usoul Al'sunnah Na Imam Ahmad bn Hanbal wanda ya rasu a shekarar 241 Da littafin Al'sunnah na Dansa Abdullahi wanda ya rasu a shekarar 290 Da kuma littafin Al'sunnah na Khallal Al'hanbali wanda ya rasu a shekarar 311 Hijira Da kuma littafin Bida'a da hani akanta na Ibn Wadhah Al'andalusi wanda ya rasu a shekarar 287 Hijiriyya Da littafin Al'hawadith wal bid'aa Na Abu Bakr Al'tartousi Al'maliky wanda ya rasu a shekarar 520 Hijira. Da kuma littafin Al'bai'th Ala inkari Albida'a walhawadith Na Abu Shamah Al'maqdisi Al'shafi'a wanda ya rasu a shekarar 665Hijira Da waninsu na litattafan Usoul da Akida wadan da wadan nan Malamai suka Wallafa da Almajiransu, don kira ga gaskiya, da kuma kariya ga Sunnah da Akida, da kuma Raddi ga yan Bidi'a da karyayyaki da kuma tatsunuyoyi.

Kuma tunda dai - Dan uwana Musulmi kana mai bi ga daya daga cikin limaman Mazhabobi, to wannan Akidar Imaminka ce, to kamar yadda kake binsa a Hukunce Hukunce to haka ya kamata ka bishi a Akida.

Kuma hakika naga tsara wannan littafin kan hanyar Tambaya da Amsa don saukin isar da sako da kuma tabbar da shi

kuma Allah nake roko da ya datar da baki daya don karbar gaskiya da kuma Iklasi da biyayya -sau da kafa- ga tafarkin Manzon Allah tsira da Aminci a gare shi,

Tsira da Aminci su tabbata ga Annabi Amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayansa da Sahabbansa ka Amince su Amincewa.

Tambaya: Idan akace da kai, wanene ubangijinka?

Amsa: to kace Allah shi ne ubangijina, mamallaki, mai halitta, mai juya al'amura, mai suranta halitta, mai tarbiyyantar das u mai gyara bayinsa, wanda yake tsaye waajen lura da al'amuransu. Kuma babu wani abu da zai samu ba tare da umarninsa ba, kuma motsin komai yana faruwa ne da izininsa da nufinsa

Tambaya: idan akace maka da wame abu ka san ubangijinka. ?

Amsa: sai kace: nasan ubangijine ne da ilmin day a halicce ni dashi, da kuma yanayin halittar dan Adam na yarda da, samuwar Allah da girmanshi da jin tsoronsa Hakanan na sanshi ta hanyar duba da lura da alamominsa da halittunsa, kamar yadda ya fada: 'Daga alamomin (samuwar Allah akwai dare da wuni da rana da wata) (suratu Fussilat) sannan wadannan muhimmn halittu da suke irin wannan tsari da kuma kyawun gaske ba zai yiwu su samar dasu bayan da babu su Kenan suma dalilai ne masu karfi akan samuwar wani mai halitta, wanda yake da iko da girma da hikima Wannan yasa dukkan halitta in banda baudaddu marasa addini –suna da alaqa da mamallakinsu mai arzuta su, mai juya al'umarsu, wanda daga cikin cikin abubuwan day a halitta akwai sammai bakwai da kassai bakwai da abin da ke cikinsu da wanda ya san adalchinsu da ainihin yadda suke sai Allah, wanda yake basu komai, rayayye tsayayye, mahalicci, mai girma Allah yana cewa: ubangijinku shine Allah wanda ya halicci sammai da kasa a cikin kwana shida, sannan ya daidaita a al'arshi, shi yake sa dare ya rufe yini, yana nemansa da gaggawa, kuma da rana da wata da taurari ababan horewa ne da umarninsa, kuji da kyau duk halitta da umarni nasa ne, Albarkar allah Ubangijin talikai ta yawaita (A'araf 54)

Tambaya: idan akace da kai menene Addininka?

Amsa :sai kace: Addinina shine musulunci, kuma yana nufin mika wuya ga Allah da dayantawa, das akin kai don biyayya ga Allah, da yin hannun riag da shirka da mushrikai, kamar yadda Allah yace: hakika addini (na gaskiya) a wajen Allah shine musulunci. (Ali Imran 19) ya kuma cewa 'duk wanda ya nemi wani addi ba musulunci ba to ba za'a karba daga gareshi, sannan a ranar lahira yana daga masu asara (Ali Imran) 85. Don haka Allah baya karbar wani addinin sai addininsa daya aiko Annabinmu Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam Saboda ya shafe ko wane addini daya gabata wanda yabi wanin musulunci to ya bata, kuma a lahira yana daga asararru da zasu shiga jahannama. Tur da wannan makoma.?

Tambaya: Idan akace dakai menene rukunnan Imani?

Amsa; sai kace: rukunan Imani guda shida ne sune: Imani da Allah, imani da mala'ikunsa imani da litattafansa, imani da manzanninsa, imani da ranar lahira da qaddara mai kyau da mara kyau duka daga Allah suke.?

kuma imani ba zai cika ba sai anyi imani dasu baki dayansu kamar yadda Alqur'ani da hadisi suka nuna, duk wanda kuma yayi musu da daya daga ciki to ya fita daga farfajiyar imani Saboda fadin Allah ta'ala: ba fuskantar gabas da yamma ne kyautayi ba, amma kyautayi shine wanda yai Imani da Allah da ranar lahira da mala'iku da littafi da annabawa sannan ya bayar da dukiya abisa yana sonta ga makusanta da 'yanta bayi kuma ya tsayar da sallah, ya bayar da zakka, da kuma masu cika alkawarinsu da suka dauka da masu hakuri a lokacin tsanani da cuta da lokacin yaki, wadanan sune sukayi gaskiya, kuma wadannan sune masu tsoron Allah' (Bakara 177) da kuma fadin Manzon Allah tsira da aminchin Allah a gareshi lokacin da aka tambayeshi akan imani Imani shine kayi imani da allah da mala'ikunsa da litattafansa da manzannninsa da ranar lahira, kuma kayi imani da Qaddara, alherinsa da sharrinsa

Tambaya: idan akace dakai yaya imani da Allah yake?

:Amsa sai ka ce Imani da Allah shi ne gasgatawa da shi da kuma Imani da kuma Ikirari da samuwar Allah da kadaitakarsa cikin Allahntaka, da Sunayensa da Sifofinsa

Tambaya: Idan aka ce da kai yaya Imani da mala'iku yake?

Amsa: sai ka ce: shi ne gasgatawa da Amincewa da samuwarsu da siffofinsu da ikonsu da ayyukansu da abubuwan da ake umartarsu das u. da kuma cewa su halittu ne masu girma da daraja da Allah ya halicce su daga haske. Kamar yadda yake cewa: basa sabawa Allah abin day a sasu cesu, kuma suna aikata duk abin da aka umarcesu (Surah Taharim 6) kum suna da fikafikai biyu –biyu, uku-uku wasu hudu-hudu wasu fiye da haka. Kuma suna da yawan gaske kuma babu wanda yasan adadinsu sa Allah.Sannan ayi imani da cewa Allah ya dora musu wasu muhimman ayyuka. Akwai masu dauke da al'arshi akwai wadanda aka wakilta a mahaifar mace, da masu rubuta ayyukan talikai, da masu gadin bayin Allah, da masu tsaron Aljanna da masu tsaron wuta da wasunsu da kma. Wanda yafisu duka shine Jibril wanda yake kawo wahayi ga annabawa. Don haka sai muyi wani dasu a dunkule da kuma a rarabe, kamar yadda Allah ya sanar damu a cikin Alqur'ani, da kuma yadda yazoa sunnar annabinmu tsiran Allah da ainci a gareshi. Duk wanda yayi musun samuwar mala'iku to ya fadi wani abu daban da wanda Allah ya fada to ya zama kafiri don ya karyata abinda Allah da Manzon Alah suka fada

Tambaya: idan akace da kai yaya imani da saukakkun litattafai yake?

Amsa: Sai ka ce: Shi ne ka ka sakankance kuma ka shaida cewa lallai Allah Madaukakin Sarki ya saukar da Litattafai ga Annabawansa da Manzanninsa Amincin Allah ya tabbata a garesu kuma ya fadi wasu daga cikinsu a littafinsa : Kamar Suhufu Ibrahim da Attaura ga Annabi Musa da Linjila ga Annabi Isa da Zabura ga Annabi Daud da kuma Alqurani ga Mafificin Annabawa Amincin Allah a gare su.

Kuma mafificinsu shi ne Al'qur'ani wanda shi ne zancen Allah kuma wanda yayi magana da shi a Hakika kuma Lafazinsa kuma Ma'anarsa daga Allah ta ke kuma ya jiyar da Jibirilu shi kuma ya Umarce shi da isar da sakonsa ga Annabinsa Muhammad Allah Madaukaki Sarki yace: "Ruhi Amintacce ya saukar da shi"(l'shura'a:198) kuma Allah "Mu ne Lallai muka sauka maka da Al'qurani Saukarwa:(Al'Insan:23( da kuma fadinsa: "to ka basu Mafaka har yaji zancen Allah" (Attaubah6)

kuma Allah ya kiyaye Alqur'ani daga gurbatawa ko kari ko ragi.Sannan an kawwameshi a takardu da kiraza har izuwa lokacin da Allah zai karbi rayukan muminai kafin a tashi alkiyama a karshen duniya, lokacine Allah zai dauke shi zuwa gareshi baa bin da zai saura nasa

Tambaya: idan aka ce da kai: yaya imani da Annabawa da Manzannin yake?

Amsa: sai kace: zuciya ta yanke da kudirin cewa annabawa mutane ne zababbu a cikin yan Adam, Allah ne ya zabe su don su isar da sakon shari'ah ga bayinsa, da za su kirasu izuwa bautar Allah shi kadai ba shiraka. Da kuma fandarewa duk wata shirka da masu yenta. Kuma uta annabta zabi ne daga Allah, ba a samunta saoda kokari ko dagewa da bin Allah ko nagarta ko karfin basira. Allah yace: Allah ne yafi sanin a wurinda yake sanya manzaicinsa' (Anam 124)

kuma farkon Annabawa shi ne Adam, farkon Manzo kuma shi ne Nuhu, cikamakinsu, kuma shine Muhammad dan Abdullahi bakuraishe – bahaushe, Allah ya yarda dasu baki dayansu. Duk wanda yayi inkarin wani annabi to ya zama kafiri, wanda kuwa yace shi annabi ne bayan Annabi Muhammad tsira da amincin Allah a gare shi to kafiri ne, mai karyata Allah a fadinsa: Muhammad bai zamo uba ga dayan mazajenku ba, sai dais hi manzon Allha ne kuma cikamakin annabawa. Kuma Manzon Allah yana cewa 'babu wani Annabi bayana'

Tambaya: Idan aka ce dakai yaya Imani da ranar lahira yake?

Amsa: sai ka ce : shi ne a gaskata kuma a sakankance ba tare da kokwanto ba, da yin furuci da duk abin da Allah ya bayar da labarin zai faru bayan Mutuwa, tun daga Azaba ko ni'ima dake cikin kabari, da tashi daga kabari da taruwa don hisabi da hukunci har izuwa abubuwan da zasu faru a farfajiyar alkiyama na doguwar tsayuwa da kusantowar rana kwatankwacin mil daya kuma tafki da sikelin awo da raba takardun aiki da kafa sira a aman wutarJahannama da sauran abubuwan tashin hankali da zasu faru a wannan babbar Rana. Har da 'yan Aljanna su shiga Aljanna 'yan wuta si shiga wua kamar dai yadda yazo dalla dalla a kur'ani da hadizi. Hakanan a karkashin imani da ranar lahira akwai gasgata abinda ya tabbata na alamomin alkiyama kamar yawaitar fitina da kasha – kasha da girgizar kasa da kisfewar rana da zuwan Dujal da saukar Annabi Isa da fitowar Yajuju da Majuju da hudowar rana ta mafadarta sda makamantansu.

kuma dukkan wadan nan sun tabbata daga irin ingantattun Hadisai daga Manzon Allah tsira da aminci a gareshi ya bayar kuma aka rubutasu a manyan litattafan hadisi masu inganci.

Tambaya: idan akace dakai: shin azabar kabari dani'imomin cikin sa sun tabbata a Kur'ani da Hadisi?

Amsa: sai kace: kwarai kuwa, domin Allah ya fadawa mutanen fir'auna cewa: wuta ce da aka bijiro dasu gareta da safe da yamma. Sannan a ranar Alkiyama (sai ace da mala'iku ku shigar da jama'ar fir'auna mafi tsananin azaba (Gafir 46) da fadinsa 'da kaga lokacin da Mala'iku suke karbar rayukan kafirai, suna bugun fuskokin da bayansu, (sannan ace) ku dandani azabar kuna. (Anfal 5) da fadinsa: Allah zai tabbatar da muminai abisa tabbatacciyar Magana a rayuwar duniya da ta lahira ( Ibrahim 27) hakanan wani a dogon hadisi kudsi da Barra yazo cewa: wani mai kira zai yi kira daga aljanna, kuyi masa sutura daga aljannan, kuma ku bude masa kofa zuwa aljanna sai ya jiyo iskarta da kanshinta kuma a yalwata masa fadin kabarinsa iya ganinsa.Amma kafiri kuwa sai a dawo masa da ransa izuwa jikinsa, sannan mala'iku biyu su zo su zaunar da shi sai su ce masa wanene Ubangijinka sai yace wayyo! Ban sani ba. Sai su ce menene addininka sai wayyo! Wayyo! Ban sani ba. Sai su ce da shi: Ina labarin mutumin da aka aiko muku (da Annabta) sai yace wayyo! Wayyo! Bai sani ba, sai wani mai kira yayi kira daga sama yace: qarya yake ku yi masa shinfixa ta wuta, kuma ku saka masa tufafi na wuta, sannan ku buxe masa qofar wuta sai ya jiyo zafinta da iskarta, kuma kabarinsa ya yi masa qunci har sai gavovinsa sun sava da junansu. (A wata ruwayar ya qara cewa sai a haxa shi da (Mala'ika) da baya ji ba ya magana yana xauke da wani madoki na baqin qarfe wanda da za a bugi dutse da shi da sai ya zama garin qasa. Sai ya buge shi dukan da duk abin da yake gabas da yamma sai ya ji qararsa ban da mutum da aljan). Abu dawud ya ruwaito shi. Wannan dalili ne ya sa aka umarce mu da mu dinga neman tsari daga azabar qabari a kowacce sallah

Tambaya . Idan aka tambaye ka shin muminai za su ga Allah ranar lahira?

Amsa: Kace kwarai kuwa Zasu ga ga Ubangijinsu a Lahira kuma daga cikin Dalilan hakan fadinsa: "Wasu Fuskoki a wannan Rana suna cikin walwala suna Kallon Ubangijinsu" (Alkiyama:22-23)Lallai ku zaku ga Ubangijinku da kuma fadin Annabi : "Buhari da Muslim Suka rawaito shi, kuma Hadisai da yawa sun zo wadanda suke tabbatar da ganin Muminai ga Ubangijinsu kuma Sahabban Annabi duk sun hadu kan hakan da kuma wadanda suka biyo bayansu to duk wanda ya karyata da ganinsa to hakika ya karyata Allah da Manzonsa kuma ya sabawa Hanyar Muminai na Sahabai da wadanda suka zo bayansa, amma a Duniya ba zai yiwu a ganshi ba sabida fadin Annabi : "Lallai cewa ba zaku taba ganin Ubangijinku ba har sai kun Mutu" kuma Annabi Musa ya nemi hakan a Duniya kamar yadda ya zo a fadin Allah Madaukaki: "Kuma yayin da Musa ya zo don ganawa da mu kuma Ubangijinsa yayi Magana da shi ya ce Ubangiji ka nunana mun in ganka ya ce: ba zaka taba iya gani na ba" (Surat Al'a'araf: 143)

Idan aka ce da kai yaya Imani da Hukuncin Allah da kuma qaddara yake?

Sai ka ce ta Hanyar tabbatarwa da cewa kowanne abu yana gudana ne akan Hukuncin Allah da qaddararsa, babu abin da zai faru sai da yardarm Allah, shi ya halicci duk ayyukan bayi masu kyau da marasa kyau. Kuma ya halicci bayi a bisa alheri da karvar gaskiya, kuma ya basu hankula da za su tantance abubuwa, ya basu ikon da za su yi zavi, ya bayyana musu gaskiya ya tsoratar da su daga bin vata, ya shiryar wanda ya so da falalarsa, ya avatar da wanda ya so da Adalcin sa, shi ne mai hikima, masani, mai jin qai, ba a tambayar dalilin da ya sa ya yi wani abu, amma su (Jama'a) ana tambayarsu.

Kuma ita Kaddara mataki hudu ce su ne Kamar haka:

Mataki na fakro shi ne imani da cewa sanin Allah ya kewaye dukkan komai, Allah ya san duk abin da ya faru da wanda yake faruwa, da ma yadda abin da bai faru ba, zai kasance

Mataki na biyu: Imani da cewa Allah ya rubuta komai da komai

Mataki na uku: Imani da cewa babu abin da zai faru sai da yardar Allah.

Mataki na Hudu: Imani da cewa Allah shi ya Halittawa komai jikkuna da Ayyuka da maganganu da motsi da rashin motsi da siffofi a duniyoyin da suke sama ko qasa, kuma dalilan duk waxannan suna da yawa a Alqur'ani da hadisai

Idan aka ce da kai shin mutum xora shi ake yi akan ayyukansa ko yana da zabi?

Sai ka ce ba a faxa kai tsaye a ce Allah ne yake dora mutum akan aiki ko kuma a ce yana da zabi. Duk kkan wannan kuskure ne, bayanai daga Alqur'ani da hadisi sun tabbatar da cewa mutum yana da iko da ganin dama, kuma a haqiqa shi ne yake aikata ayyukana da kansa sai dai duk wannan bai fita daga sanin Allah da ikonsa ba, kuma fadin Allah da ya nuna haka shi ne duk wanda ya ga dama zai iya daidaituwa amman dai abin da kuka ga dama ba zai faru ba sai Allah Ubangijin talikai ya so (Surat Takwir 28 – 29). Da fadinsa: wanda ya so sai ya tuna shi, amma abu abin da za su tuna sai abin da Allah ya so, shi ne ma'abocin taqwa kuma ma'abocin gafara (Muddassir 55-56)

Tambaya: Idan aka ce da kai: Ko ya Imani ya Inganta ba tareda Aiki ba?

Amsa: Ka ce: Bai Inganta ba Imani ba tare da aiki ba aa dole ayi aiki domin aiki ginshiki ne na Imani kamar yadda furta shi wani bangare ne na Rukuninsa kuma wan nan shi ne abin da Malamai suka hadu akansa cewa imani Furuci ne da kuma aiki dalin haka kuma shi ne fadin Allah: "Kuma duk wanda yaje masa yana Mumini yayi Ayyukana gari to wadan nan suna da Darajoji Madaukaka(Taha:75) sai Allah yaShardma anta Imani da kuma Aiki baki daya don shiga Aljannah.

Tamabaya: Idan aka ce da kai menene rukunan musulunci?

Sai ka ce: guda biyar ne shaidawa babu macancancin bauta sai Allah kuma Muhammad manzonsa ne, da tsayar da sallah da azumin watan ramadhan, da bayar da zakkah da hajjin xakin Allah mai a gare shi yace: 'An gina musulnci a bisa aubuwan guda biyar: shaidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne, da tsyar da sallah da bayar da zakka da hajji da azmin watan Ramadan (Bukhari da muslim).

Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: 'angina Musulunci kan abubuwa guda biyar:Sai ka ce: guda biyar ne shaidawa babu macancancin bauta sai Allah kuma Muhammad manzonsa ne, da tsayar da sallah da azumin watan ramadhan, da bayar da zakkah da hajjin xakin Allah mai a gare shi yace: 'An gina musulnci a bisa aubuwan guda biyar: shaidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne, da tsyar da sallah da bayar da zakka da hajji da azmin watan Ramadan (Bukhari da muslim)

Tambaya: Idan aka ce dakai menene shidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne?

Sai ka ce: Shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah shi ne: babu abin bauta da gaksiya sai Allah kamar yadda Allah yace: “Tuna lokacin da Ibrahim yace da babansa da mutanensa, ni dai na yi hannun riga da abin da kuke bautawa. Sai dai wanda ya halicce ni (zan bautawa) don shi ne zai shiryar da ni. Kuma sai ya sanyata ta zama wata kalma ce da za ta wanzu a bayansa, ko me yi wuwa za su dawo. (Zukhruf 28) da kuma fadinsa. “Wannan kuwa saboda Allah shi ne gaksiya, abin da suke bautawa kuma shi ne qarya, sannan Allah shi ne madaukaki mai girma (Luqmana 29)

Ma'anar shaidawa cewa Muhammad manzon Allah ne shi ne mu sakankance, mu yi furuci cewa shi bawan Allah ne kuma manzonsa, sannan shi bawa ne ba a bauta masa shi Annabi ne ba a qaryata shi, ana yi masa biyayya ne cikin abin da yai umarni, ana gasgata shi cikin abin da ya bada labari, ana nisantar abin da yai hani ga barinsa kuma ya tsawatar, kuma ba a bautawa Allah sai da abin da ya shar'anta

Kuma haqqin manzon Allah akan al'ummarsa shi ne su mutuntashi, su girmama shi, sannan soyayya ita ce biyayya ta kai tsaye a kowanne lokaci gwagwadon iyawa. Allah maxakakin sarki ya ce: “ka ce (da su) in ai kun kasance kuna san Allah, to ku yi min biyayya, sai Allah ya so ku ya kuma gafarta muku zunubanku (Ali Imran 31).

Tambaya: Idan aka ce da kai waxannan sharuxan Kalmar shahada.

Amsa: sai ka ce: Kalmar shahada ba kalma ba ce da za a faxa kawai ba tare da qudircewa ba, ture da dagewa wajen aiki da abin da ta qunsa da nisantar abin da ya sava mata. Har ma tana da wasu sharaxai guda bakwai da malamai suka fito da su daga cikin hujjojina shari'ah, sannan suka rubuta su tare da dalilansu daga qur'ani da hadisi; su ne.

1-sanin ma'anar abin da take korewa da wanda take tabbatarwa wato sanin cewa Allah shi kaxai ne babu abokin tarayya tare da shi, kuma shi ya cancanta a bauta masa da kuma abin da (Kalmar) take nunawa na koruwar duk wani abin bauta ba Allah ba tare da sanin abin da take hukuntawa da abubuwan da suke xanfare da ita da masu warwareta, da suke kore jahilci. Allah yace: “ka sani babu abin bauta a bisa cancanta sai Allah (Muhammad 19) da faxinsa “sai wanda suka shaida da gaskiya kuma suna sane (da abin da suka shaida) (zukhruf 86) kuma manzon Allah tisra da amincin Allah a gare shi yace “wanda ya mutu yana sane da cewa babu abin bauta sai Allah to zai shiga aljanna? (Muslim ne ya ruwaito shi.

2-Sakankancewa: shi ne qudircewa ta gaske wadda take kore kokwanto da kaikawo, wato tabbatacce a zuciya. Allah yana cewa “kaxai muminai su ne waxanda suka yi imani da Allah da manzonsa sannan a su yi kokwanto ba, kuma suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu cikin tafarkin Allah. Waxannan sune masu gaskiya (Hujrat 25). Kuma manzon Allah yace: “Wanda yace na shaida cewa babu abin bauta da gaksiya sai Allah kuma ni manzon Allah ne, to babu wani bawa da zai gamu da Allah da su (waxannan kalmomin) kuma baya kokwanto face ya shiga aljannan. (Muslim ne ya ruwaito).

3-Tsarkake niyya da take kore shirka, a hanyar rairaye ibada da tsarkaketa daga dukkan xauxar shirka ko riya Allah mai girma yana cewa: “Ku ji da kyau! Tsarkakakken addini na Allah ne" (Zumar 3) da faxinsa “Kuma ba a umarce su ba sai don su bautawa Allah suna masu tsarkake zuciya gare shi da addini" kuma manzon Allah tsira da aminci a gare shi yace: “Mafi arzuta da cetona a cikin mutane ranar alqiyama shi ne wanda yace: “Babu abin bauta sai Allah yana mai tsarkake niyya a ziyarsa da ransa" (Bukahri ne ya ruwaito).

4-Soyayya ga wannan kalma da abin da take nufi, da farin ciki da hakan da qaunar a halitta da jivintar al'amuranshi da qin abin da yake warwareta, da barranta daga kafirai. Allah yace “daga cikin mutane akwai wanda yake riqon wasun Allah kishiyoyi, yana son su kamar yadda yake son Allah, amma waxanda suka yi imani sun fi son Allah. (Baqarah 165) manzon Allah tsira da amincin allah a gare shi yace “abu uku, duk wanda suka kasance tare da shi to ya sami xanxanon imani. Ya zama ya fi son Allah da manzonsa fiye da waninsu, kuma ya qaunaci mutum ya zama baya qaunarsa sai don Allah, sannan ya qyamaci cikin kafirci kamar yadda yake qyamar a jefa shi a wuta (Muslim ne ya rawaito shi)

5- Gaskiya wadda ta ke kore qarya, tare da dacewar zuciya da gavovi da harshen da ya yi furuci da kalmar tauhidi, sai ya zama gavovi sun gasgata abin da zuciya ta faxa sai su dinga yin ayyuka na zahiri da na voye. Allah mai girma yace “lallai Allah zai bayyana waxanda suka yi gaskiya, kuma lallai zai bayyana wanxa suka yi qarya, (Ankabuta 3) Allah yana cewa “wanda ya zo da gaskiya kuma ya wanda ya gaskata da ita, to waxannan sune masu taqwa (zumar 33) kuma manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace “wanda ya mutu yana shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta, kuma Muhammad Manzon Allah ne, yana mai gasgatawa a zuciyarsa, to zai shiga aljanna. (Ahmad ne ya ruwaito).

6- Jawuwa izuwa qasqantar da kai ga Allah, da xayanta shi da ibadada da zuwa da haqoqin ibada da suka shafi umarni da nisantar abubuwan hani cikin tsarkake niyya da kwaxayi da kyakkyawan fata da tsoron Allah mai girma, wanda yake cewa kuma ku kama zuwa ubangijinku kuma ku miqa wuya gare shi. (Zumar 54). Allah ya kuma cewa “duk wanda ya miqa kansa izuwa ga Allah, alhali yana mai kyautatawa to babu shakka yayi ruqo da igiya mai qwari. (Luqman 22)

7- Karva wanda yake kore juyarwa. Wato karvar kalma da zuciya da kuma duk abin da take nufi, amma kada ya qi karvarta daga wanda ya kira shi izuwa gareta, kawai saboda baya cikin mutanensa ko saboda girman kai. Allah mai girma yace “su sun kasance idan aka ce da su babu abin bauta bisa cantnata sai Allah sai su yi girman kai" (Saffat 35) mai yin wannan ba musulmi ba ne

Tambaya:. Idan aka ce da kai wanenen Annabinka?

Amsa: Sai kace: shi ne muhamamd xan Abdullahi xan Abdul muxxalib Xan hashim xan Abdu Manaf, wanda Allah ya zava daga quraishawa, su kuma sune zavavu a cikin zuriyar Annabi Isma'il Xan Ibrahim amincin Allah a garesu. Kuma Allah ya aiko shi ne, zuwa aljanu da mutane, ya saukar masa da littafi da hikima, ya sanya shi mafi alherin Annabawa kuma fiyayyensu aminci da tsiran Allah a gare su

Tambaya: Idan aka ce da kai wane abu ne farkon abin da Allah ya wajabta akan bayinsa?

Amsa: A. sai ka ce farkon abin da Allah ya fara wajabta wa shine imani da shi da kafircewa xagutu (duk abin da ya xauke hankali ga barin Allah) kamar yadda Allah mai girma ya ce “haqiqa mun aiko manzon ga kowacce al'umma (yana ce musu) ku bautawa Allah, ku nisanci xagutu daga cikinsu akwai waxanda Allah ya shiryar akwai kuma wanda vata ta tabbata a are shi. Ku yi tafiya a bayan qasa don ku ga yadda qarshen maqaryata ya zama (nahl 36). Xagutu shi ne abin da bawa zai qetare iyaka saboda shi ko bauta masa yake ko goyon baya, ko biyayya gare shi.

Idan aka ce da kai: don wane abu ne Allah ya halicce ka?

Amsa: Sai ka ce Allah ya bayyana wannan dalla-dalla, cewa ya halicci halitta, mutane da aljanu don su bauta masa shi kaxai ba tare da shirka ba, da yi masa biyayya ta hanyar kwatanta aikata abin a yai umarni da shi da gujewa abin da yai hani da shi. Allah ya ce “Ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta min (Zariyat 56) Allah yace “Ku bautawa Allah kada ku yi shirka da his da komai. (Nisa'I 36).

Tambaya: Idan aka ce da kai menene ma'anar Ibada?

Amsa: Sai ka ce: Ita ce dukkan abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi, na daga maganganu da ayyuka na voye da na fili, ko mu furtasu ko mu aikata su, kamar tsoronsa da fatan alheransa da qaunarsa da neman taimakonsa da neman agajinsa da sallah da azumi.

Idan aka ce da kai: shin addu'a Ibada ce?

Amsa: Sai ka ce: Addu'a tana daga cikin manyana ibadu, kamar yadda Allah yace: “kuma ubangijinku yace: ku roqe ni zan amsa muku, lallai waxanda suke girman kai da barin bauta ta, to za su shiga jahannama sun a qasqantattu (Gafir 60) a cikin hadisi manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace addu'a itace ibada (tirmidhi ne ya ruwaitoshi. Kuma saboda muhimmancinta da girmanta a addini akwai ayoyi fiye da xari uku da suka zo a alqur'ani akanta. Ita addu'a nau'I biyu ce: addu'a ta ibada da addu'a ta roqo, kuma kowacce daga ciki tana Damfare da 'yar uwarta

Addu'ar Ibada itace: bin Hanya izuwa ga Allah mai girma don neman afkuwar wani abin da ake nema ko ije wani abin baqin ciki ko yaye cuta ta hanyar tsarkake ibada gare shi, shi kaxai. Allah mai girma yace: da kuma zun nun lokaci da ya tafi yana mai fushi, har ya yi zaton ba za mu yi ikon mu akansa ba, sai ya yi kira a cikin duffai ya ce babu abin bauta sai kai, tsarki ya tabbata a gareka, lallai ni ina cikin azzalumai, sai muka amsa masa, muka tserar da shi daga baqin ciki, kuma kamar haka muke tseratar da muminai. (Anbiya 87 -88)

Addu'ar roqo: ita ce roqon abin da zai amfani mai roqon na daga jawo wani amfani ko yaye wata cuta. Allah mai girma yace: ya ubangijinmu lallai mu mun yi imani, ka gafarta mana zunubanmu kuma ka kiyaye mu Azabar wuta (Ali Imran 16).

Addu'a da kowanne irin nau'I aka yi ta, ita ce tsantsar ibada, kuma tafi kowacce ibada ibada sauqin yi, da kuma girma matsayi ta amfani, ita ce hanya mafi qarfi wajen tare abin qi da samun abin nema da yardarm Allah.

Tambaya: Idan aka ce da kai waxanne ne sharuddan karvar aiki a wajen Allah.

Amsa: Sai ka ce Allah ba ya karvar aiki har sai ya cika sharaxai biyu, na farko aikin ya zama don Allah a ka yi shi, don Allah yace ba a umarce su ba sai don su bautawa Allah suna masu tsarkake niyya da addini a gare shi, kuma masu tsarkake niyya da addini a gare shi, kuma masu karkacewa vata. (Bayyinah 5) da faxina Maxaukakain Sarki “Duk wanda yake fatan ya gamu da Allah (lafiya) to sai ya aikata aiki mai kyau kuma kada ya haxa kowa da Allah a ibada (Kahfi 110).

Sharadi na biyu shi ne lallai aikin ya dace da shari'ar da manzon Allah tsira da amincin Allah ya zo da ita. Kuma dalilin haka shine faixn Allah mai girma ka ce (musu) idan dai kuna son Allah to ki yi biyayya a gare ni, sai Allah ya so ku. (Ali Imran 31).Da kuma faxin manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi “duk wanda ya aikata aikin da babu umarnin mu a cikinsa to za a juyar masa da shi" (Muslim ne ya rawaito shi) don haka idan aiki ai dace da shiryarwar manzon Allah tsira da amincin a gare shi ba to ba za a karva ba ko da kuwa mai yinsa ya tsarkake niyyarsa.

Tambaya: Idan aka ce da kai shin kyawun niyya ba tare da aiki ba zai wadatar?

Amsa: Sai ka ce a'a, dole ne kyawun niyya wato ikhlasi da aiki su dace da shari'ar manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi, hujjar haka itace faxin Allah “Duk wanda yake fatan ya gamu da Allah (lafiya) to sai ya aikata aiki mai kyau kuma kada ya haxa kowa da Allah a ibada (Kahfi 110) Allah ya sharxanta a cikin wannan ayar cewa ba za a karvi aiki a sai da kyakykyawar niyya, da kuma dacewarsa da shari'ar manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi

Tambaya: Idan aka ce da kai Tauhidi nau'I nawa ne?

Amsa: sai ka ce: nau'I uku ne: 1). Tauhidin rububiyya: shi ne qudurcewa da gakse cewa Allah ne mai halitta mai arzutawa mai jujjuya al'amuran talikai baki xaya babu abokin tarayya a tare da shi, ba shi da mataimaki. Wato wannan shi ne kaxaita Allah a cikin ayyukansa. Allah Madaukakin Sarki, yace: “Shin akwai wani mai halitta da ba Allah ba wanda yake arzutaku daga sama da qasa babu abin bauta sai shi, to ta yaya ake juyar da ku" (fadir 3). Kuma Allah ya ce Allah shi ne mai Arzutawa, mai ikon yi mai matabbacin qarfi (Zariyat 58) kuma Allah ya ce yana juya ikon yi al'amari daga sama zuwa qasa (Sajadah 5) haka nan Allah ya ce: “Ku ji da kyau, da halitta da umarni duk na Allah ne, albarkatun Allah ubangijin talikai sun halitta' (a'araf 54)

Na biyu: Tauhidin sunaye da siffofi shine qudurce wa cewa Allah yana da sunaye maus tsarki da siffofi cikakku tabbatattu a Alqur'ani da hadisi ba tare da kwatantawa ko misaltawa ko canjawa ko kyalewa ba kuma babu waqni au kamar shi.allah malukakin sarki yana cewababu wani kamar allah kuma shi mai jine mai mai ganine(shura'11)kuma alllah mai girma yace allah yan suna ye masu kyau ko roke shi dasu, (A araf 180)

Na Uku: tauhidin kuluhiyy'shine dayanta Allah da ibada shi kadai da shi da abokai tarayya a wanin shi ne dayanta Allah ta hanyar ayyukan bayi na bauta allah mai suna masu tsar kake niyya a addini kuma masu karka cewa varna (bayyinah 5)kuma Allah y ace bamu aiko wani annabi baya gabaninka face muna yin wahayi gareshi cewa babu abinda bauta sai ni (don haka)ku bauta min (Anbiya 25)

Tambaya: Idan aka ce da kai wane zunubi ne mafi girma da aka yiwa Allah

Amsa: to kace wannan shi ne Shirka Allah Madaukakin Sarki ya ce: " "Tabbas wadanda suka ce Allah shi Almasihu Dan Maryam kuma Almasihu ya ce da su:ya ku Bani Isra'i'la ku bautawa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku kuma cewa Lallai duk wanda yayi Masa Shirka to hakika Allah ya haramta masa shiga Aljanna kuma Makomarsa Wuta kuma Azzalumai basu da Mataimaka"(Ma'ida72) da kuma Fadinsa: "Lallai Allah baya gafartawa idan akai masa Shirka kuma yana gafarta abinda yake koma bayanta ga wanda ya so" (Alnisaa"48) to kasancewarsa Madaukakin Sarki baya gafarta shi to wannan Dalili nena girman Zunubin, kuma hakan yana bayyane cikin fadinsa tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayin da aka tambaye shi wane zunubi ne yafi girma sai ya ce: "Kasanya kishiya ga Allah alhalin shi ya halicce ka" Buhari da Muslim suka rawaito shi

Shirka ita ce a sanya wani yazama dai dai da Allah ko Malaika ne ko Manzo ko waliyi ko makamantansu. Ta yadda mutum zai qudurce wani abu na siffofin Ubangiji ko wani abin da Allah qevan ce shi da shi kamar halitta ko mulki ko sarrafa ko kuma ya dinga neman kusanta izuwa gareshi (abin taraya) sai ya dinga kiransa (da neman buqata) ko qaunar wani abu awajensa ko tsoronsa ko dogaro da shi ya dinga kwaxayi awajansa banda allah ko a wajensa da wajen Allah. sai ya sarrafar da wani ibada zuwa gareshi ko da dukiya ko da jiki a fili ko a Boye

Tambaya: Idan aka ce dakai nawa ne rabe-raben shirka

Amsa: Kace kashi biyu ce:

1-Shirka babba: Ita ce juyar da wani nau'I na ibada zuwa ga wanin Allah, kamar dogaro ga wanin Allah, ko neman taimako daga matattu, ko yin yanka don wanin Allah, ko bakance ga wanin Allah, ko sujjada da neman agaji daga wanin Allah a abin da babu mami iya yinsa sai Allah, kamar neman agaji daga wanda ba ya nan ko matacce babu wanda zai yi wannan jahilcin sai wanda ya qudurce cewa za su iya amsa masa addu'arsa, kuma za su iya aikata abin da babu wanda zai iya sai Allah. To wannan ya xorawa abin halitta siffofin ubangiji, don haka sai ya qasqantar da kai gare shi,kuma ya wulaqanta gare shi irin wulaqantar bauta, ya zama yana dogaro akansa, yana neman agajinsa da kiransa yana roqonsa abin da wani halitta da zai iya yinsa. Wannan ya isa abin mamamki a ce wai a nemi agaji da gajiyayye, wanda ba zai iya cutar da kansa ko ya amfanar da shi da komai ba, bai mallaki mutuwa ko rayuwa ko tashi ba, wanda ba zai iya hana cuta ta same shi ba yaya zai iya hana tag a waninsa, misalin wannan shi ne kamar wanda ruwa ya ciwo ne ya dinga neman taimako daga wanda shima ruwan ya ciwo shi, Allah sarki! Amma ta yaya basirar wasu take shafewa, hankulansu su tafi, har su dinga aikata irin wannan shirka da ta savawa sharia, ta savawa hankali ta ci karo da abin da shi ne haqiqa.

2- Shirka qarama: itace kamar 'yar qaramar riya. Manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace mafi girman abin da nake jiye muku tsoronsa shine qaramar shirka. Da aka tambaye shi sai yace ita ce riya (Muslim ne ya ruwaito shi). Hakanan kamar rantsuwa da wanin Allah. Kamar yadda Manzon Allah tara da amincin Allah yace duk wanda ya rantse a wanin Allah to ya kafirta ko yayi shirka Tirmizi ne ya rawaito).

Tambaya: Idan Aka ce da kai nawa ne rabe-raben kafirci?

Amsa: Kace kashi biyu ne>

1-Karamin kafirci: shi ne wanda dalilai na shari`ah suka ambace shi da suna kafirci, amma ba babban ba, kuma ana kiran sa da kafircewa ni`ima ko kuma karamin kafirci kamar yakar musulmi, da korewa kai nasaba, da kukan mutuwa, da kwatankwacin haka daga dabi`u na jahiliyya. Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (zagin musulmi fasikanci ne yakar sa kuma kafirci ne) Bukhari ne ya rawaito. Kuma manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: ( mutm biyu cikin mutane akwai kafirci tare da su: masu suka cikin nasaba, da masu koke-koken mutuwa). Muslim ne ya rawaito. Wadannan ayyuka basa fitar da mutum daga addini saidai su suna cikin manyan kaba`irai, muna neman tsari daga Allah. i

2-Karamin kafirci: shi ne wanda dalilai na shari`ah suka ambace shi da suna kafirci, amma ba babban ba, kuma ana kiran sa da kafircewa ni`ima ko kuma karamin kafirci kamar yakar musulmi, da korewa kai nasaba, da kukan mutuwa, da kwatankwacin haka daga dabi`u na jahiliyya. Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (zagin musulmi fasikanci ne yakar sa kuma kafirci ne) Bukhari ne ya rawaito. Kuma manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: ( mutm biyu cikin mutane akwai kafirci tare da su: masu suka cikin nasaba, da masu koke-koken mutuwa). Muslim ne ya rawaito. Wadannan ayyuka basa fitar da mutum daga addini saidai su suna cikin manyan kaba`irai, muna neman tsari daga Allah. i

Tambaya/ To idan aka ce da kai : munafurci kala nawa ne?

Amsa : to ka ce : kala biyu ne: Babban munafurci, da karamin munafurci.

Amma shi babban munafirci : shi ne bayyanar da imani da kuma boye kafirci , wannan shi ne mafi girman alamomin sa yin gaba da addinin musulunci da nuna kiyayya ga cin nasarar sa da gaba da ahalin sa musulmai, da kuma tashi tsaye don yakar su da bata musu addinin su

Shi kuma karamin Munafirci : Shi ne yin kamanceceniya da ayyukan munafikai ba tare da boye kafirci a cikin zuciyar sa ba , kamar wanda idan zai yi Magana zai yi karya, idan kuma ya yi alkawari sai ya saba, idan kuma aka amince da shi sai ya yi ha`inci ; Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce : (Alamar munafiki guda uku ce : Idan zai yi Magana sai ya yi karaya , kuma idan aka amince masa sai ya yi ha`inci , idan kuma yayi alkawari sai ya saba ). Bukhari ne ya rawaito shi.

Tambaya / Idan aka ce da kai : menene abubuwan da suke warware musulunci ?

Sai ka ce : Mai warwarewa shi ne mai lalatawa kuma mai batawa , duk lokacin da ya hau kan wani abu zai lalata shi kuma zai bata shi , kamar abubuwan da suke warware alwala wadanda daga aikata su alwalar sa ta lalace, kuma dole ne ya sake maimaita ta , kwatankwacin su ne irin abubuwan da suke warware musulunci wadanda idan bawa ya aikata su to musuluncin sa ya baci ya lalace, mai aikata su kuma ya fice daga kwaryar musulunci zuwa kafirci , kuma hakika malamai sun ambaci nau`ika da yawa a cikin babuka na ridda da hukuncin mai yin ridda daga abubuwan da za su iya fitar da musulmi daga addinin sa kuma jinin sa da dukiyar sa su halasta, kuma mafi hadarin su mafi girmansu da mafi yawan wanda suka fi faruwa, da wanda malamai suka hadu akan su; su ne masu warwarewa guda goma : Na farkon su : Yin shirka a cikin bautawa Allah madaukaki, Allah madaukaki ya ce: Lallai ne Allah baya gafarta ayi shirka da shi, kuma yana gafarta abinda ya ke bayan wannan, (an-nisa`I : 116). Kuma Allah madaukakin sarki ya ce: Lallai ne shi wanda ya yi shirka da Allah to tabbas Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomar sa wutam kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai. (al-ma`ida: 72.). yana daga abinda ke warware musulunci shi ne kiran wanin Allah, da neman agaji da kuma neman tsarin su, da yin bakance da yin yanka a garesu kamar wanda zai yiwa aljani yanka ko ga wani kabari, ko ga wani waliyyi rayayye ne ko matacce domin neman janyo wani alheri ko tunkude wata cutuwa kamar yanda jahilai wadanda aka yaudare su da karyace-karyace da shubuhohin shaidanu batattu suke aikatawa.

Na biyu : Wanda ya sanya wani tsani tsakanin sa da tsakanin Allah yana rokar su, yana kuma rokon su ceto, yana kuma dogaro da su cikin neman biyan bukatun sa da abubuwan da yake so na duniya da lahira, to hakika ya kafirta da ijima`in malamai. Allah madaukaki ya ce: Kuma ka ce: kadai ni ina kiran ubangiji na kuma ba na hada shi da kowa a bauta. ( Al-jinn: 20)

Na uku : Duk wanda bai kafurtar da mushirikai ba , ko ya yi kokwanto a cikin kafircin su, ko yake ganin ingancin hanyar da suke tafiya akanta, to ya kafurta, Allah madauakaki ya ce: Kuma yahudawa suka ce: Uzairu dan Allah ne, kuma nasaara suka ce masihu dan Allah ne, wancan zancen su ne da bakunan su, suna kama da maganar wadanda suka kafirta gabanin su, Allah ya la`ance su , ta yaya aka karkatar da su. (Suat Attauba: 30). Saboda yadda da kafirci shima kafirci ne, kuma addini baya ingantuwa sai da kafircewa dagutu ta hanyar kudurce bacin duk addinin da ba na musulunci ba da yin gaba da shi, da kaurace masa da kuma kauracewa ahalinsa, da yakar su gwargwadon iko.

Na hudu : Duk wanda ya kudurce cewa wanin shiryarwar annabi mai tsira da aminci ta fi shiryarwar sa cikar kamala, ko kuma cewar Hukumcin wanin sa ya fi nasa hukumcin kyautatuwa, kamar wanda ya ke fifita hukumcin dagutai da kuma tsarin dokokin da mutane suka kirkiroma kansu da hukumce-hukumcen su akan hukumcin Allah da manzon sa, Allah madaukaki ya ce: To a`aha ! Ina ratsuwa da ubangijin ka, ba za su yi imani ba sai sun yadda da hukuncin ka cikin abin da ya saba a tsakanin su, sa`annan kuma basu sami wanu kunci a cikin zukatan su ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama cikakkiyar sallamawa. (an-nisa`i : 65). Kuma duk wanda ya gabatar da darikun shehunnan bata da abubuwan da suka kago da bidi`o`insu akan ingantacciyar sunna alhali yana sane cewa ita sunnar annabi ce, duk wanda ya aikata wannan to shi kafiri ne da Haduwar malamai

Na biyar : Wanda duk ya fusata da wani abu daga cikin abinda manzon Allah mai tsira da aminci ya zo da shi ko da ya yi aiki da shi to hakika ya kafurta, Allah madaukaki ya ce : Wannan saboda cewa lallai su, sun ki abin da Allah ya saukar, domin haka ya bata ayyukan su. ( Suarat Muhammad: 9)

Na shida : wanda duk ya yi Izgili da wani abu na daga addinin manzon Allah mai tsira da aminci- kamar wanda yake yin izgilanci da sashin Hukunce-hukuncen sa da shari`o`in sa da sunnonin sa ko abinda ya bada labarin su, ko kuma ya rika izgilanci da abin da Allah ya tanadar da shi na daga lada ga masu yi masa da`a, ko kuma ukubar da ya tanadar ga masu sabo daga abinda Allah da manzon sa mai tsira da Aminci suka bada labari gameda shi to hakika ya kafirta, dalili kuwa shi ne fadin Allah madaukaki : ka ce shin da Allah da ayoyin sa da manzon sa kuka kasance kuna yiwa izgilanci? Kada ku kawo wani uzuri hakika kun kafirta a bayan imanin ku. (Suat Tauba: 65-66.)

Na bakwai : Sihiri, kuma baya kasancewa sai ta hanyar amfani da aljanu da shaidanu da kuma yin tarayya da su da aikata ayyukan kafirci domin neman yaddar su , daga ciki akwai jujjuyawa da tausasawa mai tasiri a cikin jikkunan mutane, da kuma cikin hankulan su, duk wanda ya aikata shi ko ya yadda da shi to hakika ya kafirta, dalilin haka shi ne fadin Allah madaukaki : kuma basu sanar da kowa har sai sun ce : mu fitina ce kawai, saboda haka kada ka kafirta. (Suat Al-bakara:102).

Na takwas : Taimakawa mushirikai da kuma yin taimakekeniya da su, da taimakon su wajen cin Nasara akan Musulmai, dalili kuwa shi ne fadin sa Allah madaukaki : Kuma wanda ya jibince su daga gare ku, to lallai ne shi yana daga gare su, lallai Allah baya shiriyar da mutane azzalumai. (Suat Al-ma`ida : 51).

Na tara : Wanda duk ya kudurci cewa wasu sashin mutane zasu iya fita daga karkashin shari`ar annabi Muhammad mai tsira da aminci- kamar yadda ya yalwaci khidr ficewa daga shari`ar annabi musa amincin Allah ya tabbata a gareshi to shi kafiri ne saboda fadar Allah madaukaki : Duk wanda ya nemi wani addinin da ba na musulunci ba to baza a karba daga gareshi ba kuma shi a lahira yana daga cikin asararru . (Suat Alil-imrana: 85)

Na goma: Bijirewa daga Addinin Allah (musulunci), baya koyar sa kuma baya aiki da shi, dalili kan haka fadin sa Allah madaukaki: Kuma wanene yafi zalunci bisa ga wanda aka tunantar da ayoyin ubangijin sa, sa`annan ya bijire daga barin su, lallai mu masu daukar fansa ne daga masu laifi. (As-sajdah : 22) . Abin nufi da bijirewa daga addinin Allah shi ne : Rashin koyon abin da ya zamar masa dole na daga abinda Addinin sa baya ingantuwa sai da sanin shi daga ginshikan Addininsa

Bayan ambaton wadannan abubuwan masu warware musulunci; ya kyautu a garemu da mu yi tambihi guda biyu masu muhimmanci su ne :

1- Cewa Amabaton wadan nan abubuwa masu warware musulunci domin a tsorata daga garesu, kuma a tsoratar da mutane da su guje su, domin shedanu da mataimakan su masu gurbatar hankali masu batarwa suna zaman dako wajen hana musulmi bin hanya mai kyau, sai su ribaci sakacin wasu daga cikin su kuma su ribaci jahilcin su domin su fitar da su daga cikin kwaryar gaskiya zuwa batacciyar hanya, kuma domin su juyar da su ga barin hanyar aljanna zuwa wuta

2- Cewa saukar da wadan nan abubba masu warware Addini bisa hakikanin yadda suke yana daga aikin manyan malamai masu zurfi cikin ilimi, sune wadanda suke sanin dalilai da hukunce-hukunce da kiyayewa ga saukakken hukunce-hukuncen da ke kan mutane, ba kowa ne yin hakan yake halasta a gareshi ba

Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin ana iya yanke Hukunci ga wani daga cikin Musulmi da cewa shi dan Aljanna ne ko Dan wuta?

Amsa / Sai a ce : Ba`a yiwa wani Hukunci da wuta ko aljanna sai wanda nassoshi suka zo cikin yimusu hukunci, saidai ana fatan samun lada ga mai kyautata aiki kuma ana jin tsoron ukuba ga mai munana aiki, kuma muna cewa duk wanda ya mutu akan imani to makomarsa zuwa aljanna ce, kuma duk wanda ya mutu akan shirka da kafirci to shi dan wuta ne kuma tur da makoma.

Tambaya/ Idan aka ce da kai : shin za`a iya yiwa Musulmi Hukunci da kafirci saboda ya aikata sabo?

Amsa/ Sai a ce: ba`a yiwa Musulmi Hukunci da kafirci saboda aikata zunubai da sabo ko da kuwa manya ne, matukar dai basu daga cikin lafuka masu kafirtarwa wadanda nassoshin shari`a na cikin kur`ani da sunna suka yi nuni a kansu kuma Sahabbai da manyan malamai suka fadesu , zai zamo akan imanin sa kuma ya kasance daga masu sabo na ahalin tauhidi matukar bai afka cikin babban kafirci ko babbar shirka ko kuma babban Munafurci ba

Tambaya/ Idan aka ce da kai : Shin tuntuben harshe da munanan kalmomin sa suna yin tasiri bisa tauhidi, kuma shin suna zamiya da mai fadarsu ga barin mikakken tafarki? Ko kuma su suna daga cikin kananan zunubai ?

Amsa: Lamarin Harshe yana da girma domin da kalma ce mutum yake shiga musulunci kuma yana iya fita daga cikin sa da furta kalma, muna neman tsarin Allah Tuntuben harshe da zamiyar sa mataki-mataki ne, daga cikin su akwai Kalmar kafirci wadda ta ke bata imani kuma ta ke rusa ayyuka, kamar zagin Allah, ko zagin manzon sa mai tsira da aminci, ko wadansu kalmomi da zai siffanta wasu masu girma da waliyyai da siffofin rububiyya, da neman agajin su da kuma jingina duk wani alheri da abinda zai faru ga mutum zuwa garesu daga cikin su akwai lafazan da ake yabon su wanda ake wuce gona da iri a cikin sa, tare da sanya su sama da matsayin su na `yan adantaka, da kuma yin rantsuwa da su, ko kuma yin izgilanci da shari`a da batanci ga hukunce-hukuncen ta, daga cikin su akwai kalmomi na yin fushi da hukunce-hukuncen Allah da ya shar`anta, ko kuma yin fushi tare da bijirewa bisa abin da kaddara ta hukuntar masu radadi na daga abubuwan ki masu faruwa anan duniya daga masifun da suke samun jikin dan adan da dukiya da `ya`ya, da wasun su

Yana daga cikin manyan kaba`iran da suke cutar da imani kuma suke tauye shi: Giba da annamimanci , lallai mu kiyayi kanmu matukar kiyayewa kuma mu tsare harsunan mu ga barin duk wani lafazi da ya sabawa shari`ar Allah da sunnar annabin sa mai tsira da aminci , Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: ( Lallai wallahi bawa yana furta Kalmar da zata janyo masa yaddar Allah wadda baya bata kulawa amma sai Allah ya daga shi da ita (Kalmar) zuwa wasu darajoji , kuma lallai cewa bawa wallahi zai yi Magana da Kalmar da zata janyo masa fushin Allah wadda baya damuwa da ita amma zai fada cikin wutar Jahanna saboda ita) . Bukhari ne ya rawaito

Tambaya / Idan aka ce da kai : A yaushe ne aikin mumini ya ke yankewa?

Sai ka ce : Aikin Mumini baya yankewa sai da Mutuwa , dalilin haka shi ne fadin Allah madaukaki : Kuma ka bautawa ubangijin ka har mutuwa ta zo maka . (al-hijr : 99) . abin da ake nufi da yakini anan shi ne mutuwa, saboda dalilin fadin manzon Allah mai tsira da aminci daga usman dan maz`un yayin da ya rasu : (amma shi usman wallahi hakika mutuwa ta zo masa). Bukhari ne ya fitar da shi. kuma saboda annabi mai tsira da aminci bai rabu da yin aiki cikin tsawon rayuwar sa ba , anan ba ana nufi da ma`anar yakini wata daraja daga imani da mumini zai kai daga kan ta ya tsaya da yin aiki ba ko kuma ace an dauke masa yin aiki ba, kamar yanda wasu karkatattu su ke riya shi

Tambaya: Idan aka ce da kai: Waye yake gudana da Mulkin Sammai da Kasa da abinda ke tsakaninsu?

Amsa/ sai ka ce: wanda ke jijjuya al-amarin sammai da kasa da wadanda ke cikin su da abinda ke tsakanin su shi ne Allah shi kadai ne ba shi da abokin tarayya, babu wani mamallakin da ba shi ba, kuma ba shi da abokin tarayya babu mai taimakon sa kuma babu mataimaki a gareshi, tsarki da godiya sun tabbata a gareshi, Allah madaukakin sarki ya ce: Ka ce: ku kirayi wadanda kuka riya (cewa abubuwan bautawa ne) ba Allah ba, ba sa mallakar kwatankwacin kwayar zarra a cikin sammai kuma basa mallakarsa a cikin kasa, kuma basu da wani rabon tarayya a cikin su (sammai da kasa) kuma ba shi da wani mataimaki daga garesu. (saba`a: 22)

Tambaya: Idan aka ce: Menene Hukuncin wanda yake kudurtar cewa halittar nan wadansu akdabu ne su hudu ko su bakwai suke tafi da al-amuran su, ko kuma akwai wadansu autadu ko gausi da ake fukantar sa da bauta koma bayan Allah? Ko kuma a hadasu tare da Allah?

To kace : Duk wanda ya kudurce wannan (a zuciyar sa) to hakika malamai sun hadu akan kaficin sa, saboda yayi kuduri da samuwar abokin tarayya ga Allah a cikin rububiyyar sa

Tambaya: Idan aka ce da kai shi Waliyyai sunsan Gaibu kuma suna aya Matattu?

Amsa / sai ka ce: Babu wanda ya san gaibi sai Allah babu kuma mai rayar da matattu sai Allah , dalilin haka shi ne fadin Allah madaukaki : Kuma da na kasance ina sanin gaibi, da lallai ne na yawaita daga alheri, kuma cuta baza ta shafeni ba . (al-a`araf : 188) . Yayin da manzon Allah mai tsira da aminci ya kasance shi ne mafificin halitta bai san gaibi ba to wanda yake koma bayan sa shi ne mafi cancanta kuma mafi dacewa da ace bai san gaibi ba

Kuma limaman nan guda hudu (Abu Hanifa, Imamu Malik, Imamu shafi`I, da Imamu Ahmad) sun hadu bisa cewar duk wanda ya kudurce a zuciyar sa cewa manzon Allah mai tsira da aminci yana sanin gaibi ko yana rayar da matattu, to shi mai ridda ne daga musulunci, saboda ya karyata Allan nan da ya umurci manzon sa mai tsira da aminci da ya fadawa mutane da aljanu : Ka ce: ba zan ce muku a wurina taskokin Allah suke ba, kuma ba na sanin gaibi, kuma ba na gaya muku cewa ni mala`ika ne, ba na bin komai sai abinda ake yin wahayi zuwa gareni. (al-an`am: 50). Allah madaukakin sarki kuma ya ce: Lallai Allah a wurinsa kawai sanin sa`a yake (tashin alkiyama), kuma shi yake saukar da ruwan sama, kuma shi ya san abinda ke cikin mahaifannai, kuma babu wata rai da ta ke sanin me zata aikata gobe, kuma babu wata rai da ta ke sanin a wace kasa zata mutu, Lallai Allah masani ne mai kididdigewa (lukman: 34). To manzon Allah mai tsira da aminci baya sanin komai daga gaibi sai kawai abinda Allah yayi wahayi da shi zuwa gareshi, kuma ya sanar da shi shi kadai, kuma manzon Allah mai tsira da aminci babu wata rana da yayi da`awar cewa shi ya rayar da daya daga cikin sahabban sa ko daya daga cikin `ya`yansa wadanda suka rasu kamin shi. To kuma ta yaya wadanda suke komabayan annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi

Tambaya / Idan akace da kai : Shin ita walittaka kebantacciya ce a cikin wani sashi na Muminai ban da wasu?

Amsa: Sai ka ce: Duk wanda ya kasance mumini mai tsoron Allah to shi waliyyi ne a wurin Allah, dalilin haka fadin sa Allah madaukaki: To, lallai ne masoyan Allah babu tsoro a kansu, kuma baza su kasance suna yin bakin ciki ba, Wadanda suka yi imani kuma suka kasance suna yin takawa. (Yunus: 62-63). Ba kebantacciya ba ce ga wani daga cikin muminai banda wani, saidai matakan ta suna tserewa juna (wani yana iya fin wani), kuma takawa tana nufin: aikata abinda Allah da manzon sa mai tsira da aminci suka yi umurni da kuma nisantar abinda Allah da manzon sa mai tsira da aminci suka yi hani ga barinsa, kuma kowane mumini yana da walittaka gwargwadon imanin sa da Biyayyarsa.

Tambaya: To idan aka ce da kai : Shin fadin sa Allah madaukaki : To, lallai ne masoyan Allah babu tsoro a kansu, kuma baza su kasance suna yin bakin ciki ba, tana nufin halascin kiran waliyyai?

Amsa: Sai ka ce: Ayar ba ta nufin halascin rokar su ko neman agaji ko neman tsari da su, amma dai a cikin ta akwai bayanin matsayin su, da kuma cewa su babu tsoro akan su a duniya da lahira, kuma baza su yi bakin ciki a lahira ba, a cikin ta akwai kira da siffantuwa da samun walittaka ta hanyar dayanta Allah da kuma yimasa da`a da manzon sa mai tsira da aminci, domin samun babban rabo saboda fadin sa Allah madaukaki: babu tsoro a kansu, kuma baza su kasance suna yin bakin ciki ba, kuma rokon wanin Allah shirka ne kamar yadda bayanin sa ya gabata

Tambaya / Idan aka ce da kai: Shin wadan da ba annabawa ba daga waliyyai kubutattu ne daga aikata manya da kananan laifuka?

Amsa/ Sai ka ce: Duk wanda ya kasance waliyyi ba daga cikin annabawa ba to shi ba kubutacce ba ne daga afkawa cikin kanana da manyan laifuka, hakika hakan ya faru ba sau daya ko sau biyu ba daga manyan waliyyai da salihan bayi wasu daga cikin zame-zame da tuntube da zurme-zurme, saidai cewa su suna gaggauta tuba da komawa ga Allah, sai Allah ya gafarta musu

Tambaya: Idan aka ce da kai : Shin khidr amincin Allah ya tabbata a gareshi yana nan a raye?

Amsa: To sai ka ce: Ingantaccen zance shi ne cewa shi khidr annabi ne daga Annabawan Allah, ya rasu gabanin Haihuwar Annabi mai tsira da aminci- saboda Allah madaukaki ya ce: Kuma bamu sanya dauwama ga wani mutum ba a gabanin ka, shin to, idan ka mutu to, su ne madauwama?. (Al-anbiya: 34). Kuma da ace ya kasance a raye da ya bi manzon Allah mai tsira da aminci- kuma yayi yaki tare da shi, saboda annabin mu mai tsira da aminci an aiko shi zuwa mutane da aljanu baki daya, Allah madaukaki yace : kace ya ku mutane lallai ni jakadan Allah ne zuwa gareku baki daya. (Al-a`araf: 158) Kuma Annabi mai tsira da aminci ya ce: (Yanzu baku ga wannan daren naku ba, hakika a duk karshen shekara dari daga gareta, babu daya daga cikin wanda ke a ban kasa da zai wanzu). Bukhari ne ya rawaito. Kuma wannan shi ne dalilin da ke nuni bisa cewa khidr matacce ne daga cikin Matattu, akan haka ne to shi baya jin kiran wanda duk ya kirashi, kuma baya shiriyar wanda ya bace ga barin hanya ta kwarai a yayin da ya nemi da ya shiryar da shi. Kuma abinda ake ambatawa ga wasu mutane na labirin haduwa da shi da kissoshin ganin sa da zama da shi da daukar ilimi daga gare shi, wannan duk rudu ne da karyace-karyace a fili wanda basa rudar da wanda Allah ya Azurta shi da ilimi da lafiyayyen hankali da Basira

Tambaya/ Idan aka ce da kai: Shin matattu suna ji ko su bayar da amsa ga mai kiran su?

Amsa: Sai kace: Matattu basa ji saboda fadin Allah Madaukaki: Kuma kai baka kasance mai jiyarwa ba ne ga wadanda ke cikin kaburbura. (Fadir:22). Da kuma fadin sa: Lallai kai (ya Muhammad) baka jiyar da matattu. (an-namli:80) Kuma basu iya bada amsa ga wanda ya kira su, Allah madaukaki ya ce: Kuma wadanda kuke kira wanda ba shi ba, ba su mallakar ko bawon kwallon dabino. Idan kun kira su ba za su ji kiranku ba, kuma ko sun ji ba za su amsa muku ba, kuma a ranar kiyama za su kafircewa shirkarku, kuma babu mai baka labari kamar wanda ya sani (faadir:13-14) Da kuma fadin Allah madaukaki: Kuma wanene mafi bata daga wanda ke kiran wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba har ranar kiyama, alhali su (wadanda ake kiran) Shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu (Ahkaf 5)

Tambaya: Idan aka ce da kai: Menene wannan abin da akeji a wasu lokuta a wasu daga cikin kabur-buran matattu wadanda jahilai ke girmama su?

Amsa: Sai ka ce: Su wadan nan Muryoyin Shaidanun Aljanu ne, suna Rudar Jahilai da cewa wannan sautin ma`abicin kabarin ne ta yadda har sai sun fitinance su sun cakuda musu addinin su sun batar da su, alhali su ma`abota kabarin basa ji kuma basa amsawa ga wanda yake rokon su ko mai kiran su da nassin kur`ani mai girma, Allah madaukaki ya ce: Hakika lallai ne kai baka jiyar da matattu.(An-namli: 80). Allah madaukaki ya kuma cewa: Idan kun kira su basa jin kiran naku. (Fadir: 14) Allah madaukaki ya kuma fada: Kuma kai ba mai jiyar da wadanda ke cikin kabur-bura ba ne.(Fadir: 22) To ta yaya za su amsa musu alhali su suna wata duniyar ta barzahu, basu da wata alaka da ahalin wannan duniyar tamu Allah madaukaki ya ce: alhali su (wadanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu (Ahkaf 5)

Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin waliyyai da wadansun su suna amsawa ga wanda ke neman agajin su da kuma neman taimako daga wajen su ?

Amsa: Sai ka ce: Su basa amsawa ga wanda ya kira su, kuma basu da iko bisa amsawa wanda ya kira su ko ya nemi agajin su, Allah madaukaki ya ce: : Kuma wadanda kuke kira wanda ba shi ba, ba su mallakar ko bawon kwallon dabino. Idan kun kira su ba za su ji kiranku ba, kuma ko sun ji ba za su amsa muku ba, kuma a ranar kiyama za su kafircewa shirkarku. (Faadir:13-14). Yaa tabewar wanda shaidanu da masu kira zuwa bata suka yaudare shi ! sai gashi sun kawata masa rokon matattu da wadanda ke cikin kabur-bura daga annabawa da waliyyai da salihan bayi, Allah madaukaki ya ce : Kuma wanene mafi bata daga wanda ke kiran wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba har ranar kiyama, alhali su (wadanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran da ake yi musu (Ahkaf 5).

Tambaya: To idan aka ce da kai: Menene ma`anar (Rayayyu) a cikin fadin Allah madaukaki: Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a cikin hanyar Allah Matattu ne, a`a! rayayyu ne su a wurin Ubangijin su ana ciyar da su

Amsa: Sai ka ce: Hakika Ma`anar Rayayyu acikin wannan Ayar cewa su ana rayar da su wata rayuwa ta ni`imomi irin ta barzahu wadda ba irin rayuwar duniya ba, domin su rayukan shahidai ana ni`imtar da su a cikin alajnna, saboda haka ne Allah mai tsarki ya ce: a wurin ubangijin su ana ciyar da su. To su suna cikin wani gidan daban suna da wata rayuwa da wani yanayi wanda ba irin rayuwar su da kuma yanayin su na cikin wannan duniyar ba. Domin cewa su ba sa jin wanda ya kira su kuma ba sa amsawa a aresu kamar yadda ya gabata cikin ayoyi, babu cin karo tsakanin su, saboda hakan ne ayar ta kasance : ana ciyar da su, ba (suna ci ba)

Tambaya/ To idan aka ce da kai: Menene hukuncin yin yanka ga wanin Allah domin neman kusanci ga wanda aka yiwa yankan?

Amsa: Sai ka ce: wan nan Babbar shirka ce saboda fadin sa madaukaki : Kayi salla ga ubangijin ka kuma ka yi yanka. (Al-kauthar:2). Da fadar sa madaukaki: Ka ce : lallai ne salla ta da yanka na da rayuwa ta da mutuwa ta na Allah ne ubangijin halitta. Babu abokin tarayya a gareshi, kuma da wancan ne aka umurce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa. (Al-an`aam: 162-163). Da fadin sa manzon Allah mai tsira da aminci- (Allah ya la`anci wanda yayi yanka ga wanin Allah) muslimu ne ya rawaito.

Kuma ka`ida tana cewa: (Duk abin da ya kasance aiwatar da shi zuwa ga Allah ibada ne, to aiwatar da shi zuwa ga wanin Allah shirka ne)

Tambaya: To idan aka ce da kai: Mene ne Hukuncin yin bakance ga wanin Allah Madaukaki?

Amsa: sai ka ce: Yana daga babbar shirka saboda fadar sa mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi: (Duk wanda yayi bakance zai yiwa Allah biyayya to lallai ne ya yimasa da`ar, kuma duk wanda ya yi bakancen zai sabawa Allah to kada ya kuskura ya saba masa) Bukhari ne ya rawaito. To bakance wata ibada ce ta Magana ko dukiya ko yi da jiki, gwargwadon yadda mai yin bakance ya ke yin bakancen, shi ne lizimtawa kai abinda bai zama wajibi akan sa a shar`ance ba domin kaunar samun abinda ake nema ko ije wani abin tsoro ko godiya ga wata ni`ima, da ta faru ko wata azaba da ta gushe, su wadannan suna daga cikin ibadun nan da bai halasta a aiwatar da su ga wanin Allah ba. Saboda Allah ya yi yabo ga masu cika alkawarin bakance , Allah madaukaki ya ce: Suna cikawa da alwashin bakancen da suka dauka, kuma suna tsoron wani yini wanda sharrin say a kasance mai tartsatsi ne. (Al`insan: 7)

Kuma ka`ida tana cewa : Dukkan aikin da Allah ya yi yabo akan mai aikata shi to shi mai shiga ne cikin ayyukan ibada, duk abin da kuma ya kasance Ibada ne to aiwatar da shi ga wanin Allah shirka ne.

Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin zamu iya neman tsari da wanin Allah Madaukaki ?

Amsa: Sai ka ce: Amsar tana bayyana ne ta hanyar sanin nau`ikan :neman tsari guda uku su ne

1- Neman tsari na tauhidi kuma na ibada: shi ne neman tsari da Allah daga dukkanin abin da kake jin tsoro, Allah Madaukaki ya ce:Ka ce: ina neman tsari ga ubangijin Mutane, mamallakin mutane, abin bautawar mutane, Daga sharrin mai sanya wasuwasi a cikin kirazan mutane, Daga Aljannu da Mutane.

2- Neman tsari wanda aka halasta: Shi ne neman tsari da abin halitta wanda yake a raye a gaban ka yana da iko cikin abin da aka kaddara zai iya aiwatarwa bisa abin da ya kasance abin kaddarawa ne a shari`ance, manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (Duk wanda ya sami wata mafaka ko wata matsara to ya yi aiki da ita) muslimu ne ya rawaito

3- Neman tsari na shirka: Shi ne neman tsari ga wanin Allah a cikin abin da babu mai kio akan sa sai Allah, Allah madaukaki ya ce: (Kuma lallai ne shi cewa wasu maza daga cikin mutane, sun kasance suna neman tsari da wasu maza daga cikin aljannu, saboda haka sai suka kara musu girman kai. (Al-jinni: 6)

Tambaya / Idan aka ce da kai: Me zaka fada idan ka sauka a wani Masauki ?

Amsa / Sai ka ce: Zan fadi abin da manzon Allah mai tsira da aminci ya shiyar da ni zuwa gareshi- ya ce: (Duk wanda ya sauka wani masauki sai ya ce: Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin nashi). Muslim ne ya Rawaito

Tambaya/ Idan aka ce da kai : Shin za`a iya neman agaji da wanin Allah cikin abin da babu mai iko akan sa sai Allah domin janyo alheri ko tunkude sharri?

Amsa: Sai ka ce: Wan nan yana daga babbar shirka mai ruguza ayyuka mai fitarwa daga addini mai kaiwa ga halaka dauwamammiya ta har abada ga wanda ya afaka cikin sa kuma bai tuba daga gareshi ba kafin mutuwa, saboda fadin Allah madaukaki: Ko wanene yake amsawa mai tsananin bukata idan ya kira shi, kuma ya yaye masa bakin cikin (an-namli: 62). Yana nufin babu mai amsa masa sai Allah kuma babu mai yaye masa damuwa sai Allah, sai Allah tsarkakakken sarki ya zargi wanda ke neman agajin wanin sa da sigar tambaya saboda shi neman agaji da neman taimako ga Allah ibada ne, Allah madaukaki ya kuma fada: Ku tuna yayin da kuke neman agajin ubangijin ku. (al-anfal: 9). Kuma hakika ya tabbata a cikin littafin sahihul bukhari daga abi hurairata Allah ya masa yadda, cewa annabi mai tsira da aminci ya ce: (Kada na sami dayan ku ya zo ranar alkiyama alhali ya dauko rakumi akan wuyan sa yana kukan rakuma sai ya ce: ya manzon Allah ka agajeni, sai na ce masa: hakika na isar maka da sako, don haka ba na mallakar komai a gareka daga Allah, kada na sami dayan ku ya zo ranar kiyama akan wuyan sa yana dauke da doki yana ta haniniya, sai ya ce: ya manzon Allah ka agajeni, sai na ce: bani mallakar komai a gareka daga Allah hakika na isar maka da sako) Bukhari da muslimu sun fitar da shi. Kuma sanannen abu ne cewa ya halasta a garemu da munemi agajin wanda yake rayayye ne kuma munagin shi gamu-ga-shi, ba wanda baya nan ba, kuma wannan ya halasta ne cikin abin da yake da iko akan sa, neman agaji ga abin halitta rayayye yana nufin neman taimako daga gareshi cikin abin da dan`adam yake da ikon yin sa, kamar yanda abokin annabi musa ya nemi taimakon annabi musa amincin Allah ya tabbata a gareshi akan makiyin su, Allah madaukaki ya ce: Sai wannan da yake daga jama`ar sa ya nemi agajin sa akan wannan da yake daga makiyan sa. (Al-qasas:15). Amma neman agajin wadanda basu nan daga mutane da aljannu da ma`abota kabur-bura, sai limaman malamai suka hadu akan bacin sa da haramcin sa da kuma cewa hakan yana daga shirka

Tambaya/ to idan aka ce da kai: Shin ya halasta a bautar da sunaye ga wanin Allah kamar (ace) Abdun-nabiyi ko Abdul-husaini da kuma kwatankwacin haka?

Amsa/ sai ka ce: Bai halatta ba, ta yanda dukkanin limaman malamai sun hadu bisa haramcin dukkanin sunan da aka bautar da shi ga wanin Allah, kuma yana wajaba da a canza sunan da aka bautar da shi ga wanin Allah kamar Abdun-nabiyi, ko Abdur-rasuli, ko Abdul-Husaini, ko Abdulka`abati (Bawan ka`aba) da wanin su daga sunayen bautarwa ga wanin Allah madaukaki . kuma mafi soyuwar sunaye a wurin Allah sune: (Abdullahi, da kuma Abdur-rahman) kamar yadda yake cikin hadisi daga manzon Allah mai tsira da aminci : (Hakika mafi soyuwar sunanye a wurin Allah (sune) Abdullahi da Abdur-rahman) Muslimu ne ya rawaito. Kuma yana wajaba a canza sunaye ababan bautarwa ga wanin Allah wannan kuma ya rataya ne ga wadanda suke a raye ana kiran su da sunaye ababan bautarwa ga wanin Allah

Tambaya/ To idan aka ce da kai : Menene hukuncin sanya rataya, ko zare a hannu ko a wuya ko a sanyawa dabba (da mota) ko wanin su domin tunkude kambin baka ko hassada, ko wani bala`i da sharri, ko kuma don dauke shi?

Amsa/ sai ka ce: Wannan yana daga shirka saboda fadin sa mai tsira da aminci-: (Wanda ya rataya laya hakika yayi shirka) Ahmad ne ya rawaito a cikin musnadin sa, da kuma fadin sa mai tsira da aminci -: (Babu wani maratayi mai wutiri da zai wanzu a wuyan rakumi ko wani maratayi na daban fa ce sai na yanke shi) Bukhari ne ya rawaito. Da fadin sa mai tsira da aminci : (Wanda ya kulla gemun sa ko ya rarrataya wutiri, ko ya yi tsarki da kashin dabbobi ko wani kashi to hakika annabi Muhammad (mai tsira da aminci) ya barrantu daga gareshi) Ahmad ne ya rawaito shi. Da kuma fadin sa mai tsira da aminci: (Hakika tofe-tofe da layu da kuma guru shirka ne) Abu Dawud ne ya rawaito shi. Da kuma fadin sa mai tsira da aminci : (Duk wanda ya rataya laya to kada Allah ya cika masa burin sa) Ibn Hibban ne ya rawaito a cikin sahihin sa. Kuma duk wanda ya rataya al-amuran sa da rudani da kuma tatsuniyoyi hakika ya tabe, Ya zo cikin hadisi : (Wanda duk ya rataya da wani abu to an kyale shi da wannan abin)

Abin nufi da At-tiwala: wani tsafi ne da ake yin sa suna kudurtar cewa yana sanya soyuwar miji ga matar sa ko kuma yana raba tsakanin su, kuma suna yin amfani da shi wurin jefa gaba a tskanin masoya da kuma makusanta na jini

Abin nufi da At-tama`im: wani abune da ake ratayawa kananan yara saboda tunkude musu kambin baka ko Hassada

Kuma ma`anar Laya, Imamul munziri ya ce: (Wani rufi ne na fata da aka dinke shi da zare da allura, su kasance su rataya ta suna ganin cewa ita zata tunkude musu aibubbuka), wannan kuma jahilci ne da bata, saboda ba sababi ba ce a shar`ance ko a kaddarance, kuma wannan ya hada da sanya kambu da kuma rataya tsumma da kuma makarai ga mutum, da dabbobi, da mota, da kuma gida

Tambaya/ Idan aka ce da kai: menene ma`anar tabarruki ?

Amsa: Sai ka ce : Shi ne neman albarka da alheri ta hanya kamun kafa da wasu sababai da mutum zai aikata su domin kaunar samun alheri a gareshi da samun abin da yake nufin sa da kuma abin da yake so

Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin neman tabarraki nau`i daya ne ko sama da haka ne?

Amsa/ sai ka ce : Neman tabarruki kasha biyu ne

1- Neman tabarraki shar`antacce, Kur`ani da sunna sun yi nuni bisa shar`antuwar sa da kuma amfanuwar mai aikata shi da shi, kuma baya halatta a kudurci neman Albarka a cikin komai sai idan da dalili daga kur`ani da sunna babu wata dama da za`a shigar da hankali ko kyautata zato a cikin ta, bamu iya sanin cewa wannan abin akwai albarka ko da akwai albarka a cikin sa sai da labari daga mahalicci gwani mai albarkar suna da daukaka, ko daga manzon sa mai tsira da aminci, kuma albarka da alheri dukkanin su suna cikin biyayyar kur`ani da hadisi, daga cikin su ne muke sanin abubuwan da suke da albarka da kuma yadda zamu yi tabarraki da su kamar neman tabarraki da zatin Manzon Allah mai tsira da aminci- da abin da ya rabu daga gareshi na yawu da kuma gashi, da abin da yake like da jikin sa na tufafi, wannan kuma kebantacce ne da shi mai tsira da Aminci- da kuma duk abin da ya tabbata yana da alaka da shi, daga ciki akwai gashi da tufafi, kuma ma`abota tatsuniya suna yin karya suna riya cewa akwai wani daga cikin gashin sa a wurin su, da wani tufafi daga tufafin sa, duk wannan suna yi ne domin wasa da hankulan wasu daga cikin Musulamai, da kuma bata musu Addinin su, da karbe musu abin Duniya

2-Kashi na biyu: Neman Tabarrukin da aka haramta, wanda yake kai Mutum zuwa ga Shirka kamar naiman Tabarruki da Zatin Mutanen kirki da kuma abinda yake futa daga cikinsu, da neman tabarruki da Kaburburansu da Sallah da yin Addu'a a wurinsu, da kuma neman Albarka da Kasarta da kudurcewa wannan Magani ne, kwatan kwacinsa neman Albarkarka ko Dawafi ko Rataya musu wani kyalle a wani guri ko Dutse ko wata Bishiya da ake canfa Albarkarta, kuma hakika babu wani abu da aka shar'anta Sunbantarsa ko shafarsa sai Hajarul Aswad da ke Ka'aba da Rukunanta kuma bayanta Haramun ne a shafi wani abu ko a sunbance shi ko ayi masa Dawafi, kuma wannan shirka ce Babba ga wanda ya Kudurce cewa yana bada Albarka a zatinsa ko kuma yana daga cikin Karamar Shirka ga wanda ya canfa cewa wannan shi Sababin samun Albarka.

Tambaya/ Idan aka ce da kai : Shin ana bibiyar gurabun salihan bayi, da kuma neman albarka da zatin su da gurabun abubuwan da suka bari aiki ne shar`antacce, ko kuma bidi`a ce da bata ?

Amsa: Sai ka ce : Wannan kuduri ne da kuma aiki kirkirarre kagagge saboda sahabban annabin mu Muhammad mai tsira da aminci- sune mafi sanin al`umma kuma mafi falalar ta kuma mafi fahimtar ta kuma mafi kwadayin ta bisa alheri kuma mafi sanin ta da falalar ahalin falalar, amma ba su nemi tabarraki da gurabun Abibakr da umar da usman Aliyu Allah ya kara yadda a garesu, amma kuma basu bibiyi gurabun su ba alhalin sune mafifitan al-umma bayan annabawa, saboda su suna sane da cewar hakan kebantacce ne ga annabi mai tsira da aminci-, kuma hakika umar Allah ya kara yadda a gare shi ya yanke bishiyar da aka yi bai`ati ridwan saboda jin tsoron a rika wuce gona da iri akan ta. Kuma magabata na kwarai sune mafi kwadayin mutane bisa aikin alheri, kuma da ya kasance bibiyar gurabin na su yana da alheri kuma a cikin sa akwai falala to da sun rigaye mu zuwa gare shi

Tambaya: To idan aka ce da kai : Shin yana halatta ayi tabarraki da bishiyu ko duwatsu ko Turbaya?

Amsa: Sai ka ce: Wannan yana daga shirka, Hakika imamu Ahmad da Tirmizi sun rawaito daga Abi wakidil-laithiy, ya ce: Mun fita tare da manzon Allah mai tsira da aminci zuwa Hunaini, alhali bamu jima da barin kafirci ba, kuma su mushirikai suna da wata bishiyar magarya suna zama a wurin ta, kuma suna rataye makaman su a jikinta, ana kiran ta da suna: zatu anwadin (ma`abociyar rataya), ya ce: sai muka wuce ta wannan magarya, sai muka ce: ya manzon Allah muma ka sanya mana ma`abociyar rataya, sai manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (Allahu Akbar ! hakika ita sunnoni ne! na rantse da wanda rayi na ke hannunsa kun fada kamar yanda banu isra`ila suka fada: (Ka sanya mana abin bauta kamar yanda suke da abin bauta, sai ya ce:lallai ku mutane ne jahilai). (Al-a`araf: 138). Wallahi sai kun hahhau tafarkin wadan da suka gabace ku

Tambaya: Idan aka ce da kai : menene Hukuncin rantsuwa da wanin Allah ?

Amsa: sai ka ce: Baya halatta yin rantsuwa da wanin Allah madaukaki, manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (Duk wanda ya kasance zai yi rantsuwa to ya rantse da Allah ko kuma yayi shiru) Bukhari ne ya rawaito. Kuma manzon Allah mai tsira da aminci yayi hani ga barin rantsuwa da wanin Allah kamar yanda yake cikin fadin sa mai tsira da aminci: (Kada ku rantse da iyayenku kuma kada ku rantse da dagutai) muslim ne ya rawaito. Kuma al-dawagi: jam`i ne na dagutu. Kai bama haka ba- manzon Allah mai tsira da aminci ya sanya yin hakan daga cikin shirka, kamar yanda yake cikin fadinsa mai tsira da aminci-: (Duk wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko kuma yayi shirka), kuma manzon Allah mai tsira da aminci ya ce-: (Duk wanda ya rantse da amana to baya daga cikin mu) Imamu Ahmad da ibn hibban da Al-Hakim ne suka rawaito da Isnadi Ingantacce

To lallai ne musulmi ya kiyayi kansa da yin rantsuwa da annabi, ko waliyyi, ko da daukaka, ko da amana, ko da ka`aba, da kuma wanin su daga ababan Halittu

Tambaya: To idan aka ce da kai: Shin yana halatta mu kudurce cewa taurari suna da tasiri bisa abubuwan da suke faruwa(a Duniya) da kuma mutane a cikin janyo alheri da dacewa da kuma samun rayuwa mai kyau ko kuma tunkude wani sharri da abubuwan ki da Bala`o`i ?

Amsa: sai ka ce: Baya halatta a kudurci hakan kwata-kwata saboda babu wani tasiri a garesu cikin yin hakan, kuma babu mai gaskata shugabannin shirme sai masu raunin hankulla da kuma masu bin hauma-hauma, kuma kudurce hakan yana daga shirka saboda fadin sa mai tsira da aminci- a cikin hadisi kudusi: (Hakika Allah yana cewa: Duk wanda ya ce an yimana ruwa da falalar Allah da rahamar sa, to wannan mai yin imani da ni ne mai kafircewa tauraro, wanda kuma ya ce: anyi mana ruwa da nau`i kaza da kaza to wannan mai kfircewa da ni ne, mai yin imani da tauraro ne) Bukhari da muslimu ne suka rawaito. Sai mutanen jahiliyya suke kudurce cewa taurarin nan suna da wani tasiri cikin zuwan ruwan sama.

Tambaya: Idan aka ce da kai: Shin yana halatta ayi kudurin cewa akwai wani tasiri ga burujai kamar burujin(ad-dalwu) ko wanin sa ko kuma manyan taurari da kananan taurari bisa abin da yake afkuwa ga mutum a cikin rayuwar sa na daga jin dadi ko tabewa, kuma shin zai yiwu a iya yaye abin da yake na gaibi wanda zai faru anan gaba ta hanyar su (taurarin) ?

Amsa: sai ka ce: Baya halatta ayi kudurin cewa akwai wani tasiri ga burujai da kuma manyan taurari da kananan taurari bisa abin da yake afkuwa ga mutum a cikin rayuwar sa, kuma ba`a gano abin da zai faru anan gaba da su,saboda sanin gaibi kebantacce ne ga Allah, Allah madaukaki ya ce: Ka ce: Babu wanda ya san gaibi a cikin sammai da kasa fa ce Allah. (suratu-Namli: 65). Kuma saboda Allah shi kadai ne mai janyo alheri kuma mai tunkude sharri, duk wanda ya kudurci cewa akwai wani tasiri garesu (taurarin) cikin gano abubuwa na gaibi da kuma arziki ko tabewar wanda aka Haifa a cikin lokacin wannan buruji ko a zamanin bullowar kaukabi, ko kuma cewa taurari suna da tasiri cikin azurtar da shi ko tabar da shi to hakika ya sanya su masu tarayya tare da Allah a cikin abin da shi yana daga hakkokin sa da kuma kebantacciyar rububiyyar sa duk wanda ya aikata wannan hakika ya kafirta, muna neman tsarin Allah

Tambaya: To idan aka ce da kai: Shin yana wajaba akan mu yin Hukunci da abin da Allah ya saukar ?

Amsa/ Sai ka ce: Yana wajaba akan musulmai baki dayansu yin hukunci da abin da Allah ya saukar, saboda fadin sa madaukaki: Kuma ka yi hukunci a tsakanin su da abin da Allah ya saukar, kuma kada ka bibiyi son zuciyoyin su, kuma ka kiyaye hanuwar su fitine ka daga sashen abin da Allah ya saukar zuwa gare ka. To idan sun juya baya, to ka sani cewa kawai Allah yana nufin ya samesu da masifa ne saboda sashen zunuban su. Kuma lallai hakika mafiyawa daga mutane hakika fasikai ne.(suratul-ma`ida: 49). Kuma hakika Allah ya zargi kundin tsari na dan adam da fadin sa: Shin hukuncin jahiliyya suke nema? Kuma wanene mafi kyawu ga hukunci daga Allah ga mutane wadanda suke yin yakini? (tabbataccen imani). (al-ma`ida: 50)

Tambaya: Idan aka ce da kai Maye Ceto?

Amsa: Sai ka ce: Ceto shi ne shiga tsakani ko kamun kafa da wani domin janyo wani amfani da kuma alheri, ko tunkude wani sharri da cuta

Idan aka ce da kai: Menene nau`ikan ceto ?

Amsa/ Sai ka ce: Nau`ika uku ne :

1- Ceto tabbatacce wanda ba`a neman shi sai daga Allah, Allah madaukaki ya ce: Ka ce ceto na Allah ne baki dayan sa. (Az-zumar: 44). Shi ne ceto domin kubuta daga azbar wuta da kuma rabauta da ni`imomin aljanna

a- Yin izini ga mai ceto da ya yi ceton, kamar yanda Allah madaukaki ya fada: Wanene wannan da zai yi ceto a wurin sa fa ce sai da izinin sa. (Aal-bakara: 255)

b- Yadda ga wanda za`ayi ceto gareshi, kamar yanda Allah madaukaki ya ce: Kuma basu yin ceto sai ga wanda ya yadda. (a-anbiya`i: 28). Kuma hakika Allah tsarkakakken sarki madaukaki ya tattare su da fadin sa: Akwai mala`iku da yawa a cikin sammai ceton su baya wadatar da komai face bayan Allah yayi izini ga wanda ya so kuma ya yadda (da shi wajen ceton) (An-najmi: 26). To wanda yake son ceton ya shafe shi, to lallai ya roki Allah tsarkakakken sarki, domin shi ne mamallakin sa kuma mai yin izini da shi, kuma ba`a rokon wanin sa, saboda fadin sa mai tsira da aminci -: (Idan za kayi rook to ka roki Allah) tirmizi ne ya rawaito. Sai ka ce: Yaa Allah ka sanya ni daga cikin wadanda annabinka mai tsira da aminci- zai cece su ranar kiyama

2-Ceton da ba'a yarda da shi shi ne wanda ake neman taimakon wanin Allah cikin abinda bawanda zai iya sai Allah shi ne ceto na shika

3- Ceto na Duniya a tsakanin halittu, shine ceto tsakanin ababan halitta rayayyu a cikin Duniya cikin abinda suke da iko a kansa, kuma sashinsu yake da bukatarsa daga sashi a cikin bukatun Duniya , kuma wannan mustahabbi ne idan ya kasance a cikin Alherine, kuma haramunne idan ya kasance a cikin sharri ne, kamar yadda yake cikin fadinsa Madaukakin sarki: ( wanda ya yi ceto, ceto mai kyau zai sami rabo daga gare shi kuma wanda ya yi ceto, ceto mummuna zai sami ma'auni daga gare shi (al nisa'i: 85).

Tambaya: idan aka ce da kai: shin ana nema daga Manzan Allah - Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da Salihai da Shahidai ceto domin cewa su suna yin ceto a ranar kiyama?

Amsa: sai ka ce: Ceto mulki ne na Allah madaukaki, kamar yadda Allah madaukaki ya fada: ( ka ce ga Allah ceto baki daya yake) azzumar :44)Sai mu roketa a wajan Allah mamallakinta da kuma izini da ita, saboda da'a ga Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- wanda ya ce: ( idan zaka yi roko ka roki Allah) Tirmizi ne ya rawaito shi , sai mu ce : ya Allah ka sanya mu cikin wadanda Manzanka- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yake ceta ranar kiyama

Tambaya: Idan aka ce da kai Mene ne Hukuncin wanda ya sanya Mamata su zamanto masu ceto tsakaninsa da Allah wajen neman biyan bukatarsa.

Amsa: wannan yana daga shirka babba, saboda Allah Madaukaki ya zargi wanda ya sanya tsakaninsa da Allah masu ceto Allah Madaukaki ya fada a kansu (kuma suna bautawa baicin Allah abinda baya cutar da su kuma baya amfanar da su, kuma su na cewa wadannan sune masu cetonmu a wajan Allah, ka ce shin kuna baiwa Allah labari ne abinda bai sani ba a cikin sammai ko kasa? Tsarkinsa ya tabbata kuma ya daukaka ga abinda suke shirki da shi. (Yunus: 18), sai ya ambace su da shirka sai mai tsarki da daukaka y ace: ( ga abinda suke shirka da shi) sannan ya yi hukunci a kansu da kafirci sai y ace: ( lalle ne Allah ba ya shiriyar wanda yake makaryaci kuma kafiri(azzumar: 3)

Tambaya : idan aka ce da kai: shin ana iya fahimta daga fadinsa Madaukaki ( kuma da dai cewa su a lokacin da suka zalunci kansu sun zo maka sa'annan suka nemi gafarar Allah kuma Manzo ya nema musu gafara, hakika da sun sami Allah mai karbar tuba mai jin kai) (alnisa'i: 64). Neman gafara daga wajan Manzo- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- har bayan mutuwarsa?

Amsa: hakika neman gafara daga gare shi ya kebanta da lokacin rayuwarsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, ba bayan mutuwarsa ba, bai tabbata daga sahabbai ba Allah ya yarda da su, ko ma'abotan karnika masu falala wani labari ingantacce daga gare su cewa su sun kasance suna nema daga Manzo- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – cewa ya nema musu gafara bayan mutuwarsa, saboda cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yayinda A'isha ta nema daga gare shi Allah ya yarda da ita addu'a kuma ya nema mata gafara bayan mutuwarta sai y ace da ita: (wancananki da zai kasance alhali ina raye sai na nema miki gafara kuma na yi miki addu'a) Bukhari ne ya rawaito shi, to hadisin yana fassara ayar, domin cewa neman istigfari daga Manzo- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kebantacce ne a cikin rayuwarsa ba wai bayan mutuwarsa ba,neman istigfari daga gare shi bayan wafatinsa bai afku ba face daga sashin wadanda suka zo daga baya, bayan karewar karnika masu falala, da kuma watsuwar muhaddasai,da galabar jahilci, sai wasu sashinsu suka aikata haka saboda sabawa hanyar magabata nagari tabbatattu a ilimi, da kuma shugabanni shiryayyu daga sahabbai da kuma wadanda suka bisu da kyautayi.

Tambaya: idan aka ce da kai: menene ma'anar fadinsa Madaukaki (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoran Allah kuma ku nemi tsani izuwa gare shi) (suratul alma'ida: 35) ?

Amsa: sai ka ce: ma'anarta kusantuwa izuwa gareshi da yi masa biyayya Da kuma bin Manzansa- tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi to Wannan shi ne tsanin da Allah yayi umarni das hi domin kusancinmu zuwa gare shi Madaukaki, kuma cewa tsanin shi ne abinda zai sadar izuwa abin nema kuma ba 'a saduwa da abin nema face da abin da Allah ya shara'anta da Manzansa na daga tauhidi da aikata da'a ba tsani bane fuskantar waliyyai da wadanda aka binne to wannan yana daga juyar da ababan Ambato, da kuma ambatar abubuwa ba tare da sunansu ba, kuma wannan ba komai bane face yaudara daga Shaidanun mutane da Aljanu don su batar da mutane ga barin hanyar shiriya mai sadar da su ga Aljanna

Tambaya: idan aka ce da kai: Menene Tawassuli?

Amsa: sai kace: Asalin Tawassuli shi ne kusanci, a kuma shari'a shi ne kusantar Allah Madaukaki da biyayya da kuma bauta, da kuma bin Annabinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- , da kuma aikata Duk abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi.

Tambaya: idan aka ce da kai: nawa ne nau'o'in Tawassuli?

Amsa: sai ka ce: Tawassuli nau'I biyu ne: wanda aka shara'anta ,da kuma Wanda aka hana.

Tambaya: idan aka ce da kai: wannene tawassulin da shari'a ta shara'anta?

Amsa: sai ka ce: (a) Tawassuli izuwa ga Allah da sunayensa Allah Madaukaki y ace:( kuma Allah yana da sunaye mafiya kyau to ku kira shi Da ita), da kuma siffofinsa, kamar yadda yake cikin fadinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a are shi-:( ya rayayye ya mai tsayuwa da komai Da rahamarka nake neman taimako), to wannan tawassuli ne izuwa ga Allah da siffarsa ta rahama

(b) Tawassuli izuwa ga Allah da kyakkyawan aiki wanda aka yi shi saboda Allah wanda ya dace da sunnar Manzan Allah- tsira da amincin Allah su Tabbata a gare shi-, kamar wanda yake cewa: ya Allah don tsarkakewar Aiki na a gare ka, da kuma biyayyata ga Annabinka – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ka bani lafiya kuma ka arzurta ni, kamar Imani da Allah Mai tsarki da Manzansa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Allah Madaukaki ya ce:(ya Ubangijinmu lalle ne mu mun ji mai kira zuwa imani cewa ku yi imani da Ubangijinku, sai muka imani ya Ubangijinmu to ka gafarta mana zunubanmu ka kuma kankare miyagun Aiyukanmu daga garemu. Kuma ka karbi rayukanmu tare da mutanen Kirki) (ali imran: 193) kuma bayan wannan tawassuli sai suka roki Allah Suka ce: ya Ubangijinmu ka bamu abin da ka yi mana alkawari a kan Manzanninka, kuma kada ka tozartamu a ranar kiyama lalle ne kai baka Karya alkawari) (ali imran 194) da kuma kamar yadda Ma'abota Dutse Suka yi tawassuli da Allah da kyawawan aiyukansu domin ya yaye musu Abinda suka shiga cikinsa na damuwa kamar yadda yake a hadisin dan Umar Allah ya yarda da shi wanda yake cikin Bukhari da Muslim, cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya zantar da mutane game da labarin mutanen nan su uku wadanda fan Dutse ya rufesu a cikin kogo, sai suka roki Allah da aiyukansu kyawawa don ya yaye ta daga gare su har sai da ta yaye.

(c) Tawassuli da Addu'ar bawa salihi wanda yake nan mai iyawa, kamar Wanda ya nemi wani mutumin kirki da ya roka masa Allah kamar yadda Sahabbai Allah ya yarda da su suka nema daga Abbasu ya roka musu Allah ya yi musu ruwa, kuma Umar Allah ya yarda da shi ya nema daga Uwaisul alkarni ya yi masa addu'a, da kuma kamar neman da 'ya'yan Ya'akuba suka yi daga gare shi Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Allah Madaukaki y ace: ( suka ce: ya babanmu ka nema mana gafarar zunubanmu lalle ne mu mun kasance masu kuskure) (suratu Yusufa 97).

Tambaya: Idan aka ce da kai: menene Tawassuli wanda aka hana?

Amsa:sai ka ce: shi ne tawassulin da shari'a ta bata shi, kamar wanda yaKe tawassuli da matattu kuma yake neman ceto daga gare su,to wannan Tawassuli ne na shirka bisa ga haduwar malamai,kuma ko da ababanTawassalin da su Annabawa ne ko Waliyyai, Madaukaki y ace: (kuma Wadanda suka riki wasu majibinta ba shi ba: ba mu bauta musu ba face Domin su kusantar da mu zuwa ga Allah kusantar daraja (azzumar 3), Sannan ya biyar da siffarsu da hukunci a kansu, sai Madaukaki ya ce:(lalle Allah na yin hukunci a tsakaninsu ga abinda suka kasance suna sabawa a cikinsa. Lalle Allah ba ya shiryar da wanda yake mai karya mai kafirci(azzumar: 3) sai ya hukunta kafirci a kansu da kuma fita daga Addini,haka nan yana daga cikin tawassulin da aka hana abinda shari'a tayi shiru ga barinsa, domin tawassuli ibada ne kuma ita ibada tsayayyiya ce kamar yin tawassuli da Alfarma ko da zatina ko da watanta, kamar fadin wasu sashin mutane : ya Allah ka gafarta min saboda alfarmar masoyi, ko kuma ya Allah lalle ne mu muna rokanka da Annabinka ko da alfarmar managartan bayi ko da kasar wane…,domin cewa wannan Allah bai shara'anta shi ba da Manzansa, sai ya zama bidi'a ce wacce ya wajaba a nuisance ta, kuma ba'a san wannan nau'I ba da wanda ya rigaye shi daga salihan magabata ban a daga sahabbai da tabi'ai, da shugabannin shiriya ababan shiryarwa Allah ya yarda da su baki daya

Tambaya: idan aka ce da kai: menene nau'ikan ziyarar kabari ga Mazaje?

Sai ka ce: nau'I biyu ce:

1- Ziyara Wacce shara'antawa wacce ake sakawa ma'abocinta saboda illoli guda biyu sune

(a) tana tunar da Lahira, saboda fadinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ( na kasance ina hanaku ziyarar kabarai ku saurara to ku ziyarce ta domin cewa ita tana tunatar da lahira) Muslim ne ya rawaito shi

b) sallama ga mamata da kuma yi musu addu'a, sai mu ce: (Aminci ya tabbata a gare ku ya ahalin gidaje na daga muminai… zuwa karshe) sai mai ziyara ya amfana da wanda aka ziyara

2- Ziyara wacce ba'a shara'anta ba wanda mai yinta yake yin sabo, kuma ita ce wacce aka nufi addu'a a wajan kaburburansu, ko kuma fuskanta izuwa Allah da su, wannan bidi'ace da take sadar da ma'abocinta izuwa shirka, ko kuma neman taimako da matattu da kuma neman ceto da su da neman madadi daga gare su, kuma wannan shi ne shirka babba saboda fadin Allah Madaukaki :Wancanenku shi Allah Ubangijinku Mulki nasa ne kuma wadan da koma bayansa basu Mallaki ko da bawon kwallon Dabino ba kuma in kuka kuka kirasu basa jin kiranku kuma koda sunji ba zasu iya amsa muku ba kuma a Ranar Alkiyama zasu kafirce da Shirkarku kuma babu Mai baka Labari Kamar Allah" (Fadir:13-14)

Tambaya: Idan aka ce da kai: me zaka ce yayin Ziyarar Makabartu?

Amsa: sai ka ce: zan fadi abinda Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya shiryar da sahabbansa da shi idan suka ziyarci makabartu su ce: ( amincin Allah ya tabbata a gare ku gidan Jama'ar muminai kuma abinda aka yi muku alkawari da shi zai zo muku gobe kuma muma in Allah ya so masu haduwa ne da ku) Muslim ne ya rawaito shi, sannan na rokar musu rahamar Allah da gafara da daukakar daraja, da watanta daga Addu'oi tsarkaka.

Tambaya: Idan aka ce da kai: shin muna iya kusantuwa izuwa ga Allah da Addu'a a wajan kaburburan salhai?

Amsa: sai ka ce: Hakika rokan Allah a wajan kaburburan Salihai Bidi'a ce fararriya, kuma ita tsani ne izuwa shirka, hakika ya zo daga Aliyu dan Husain Allah ya yarda das hi cewa shi ya ga wani mutum yana rokon Allah a wajan kabarin Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ya hana shi, kuma y ace lalle ne cewa Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce:( kar ku riki kabarina wurin Bauta) biya'ul makdisi ya fitar das hi a cikin almukhtar: 428) Kuma mafi girman kabarurruka kabarin da ya tare mafi tsarki da alfarmar jiki da kuma mafificin mutane kuma maafi girman halitta ga Allah shi ne kabarinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma ba'a taba sanin wani isnadi ingantacce daga daya daga cikin sahabbai ba Allah ya yarda da su cewa shi ya kasance yana zuwa kabarinsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya roki Allah a wajansa, haka kuma wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa ba su kasance suna kirdadon addu'a a wajan kabarin sahabbai da kuma manyan shugabannin al'umma ba, sai dai cewa ita rudi na shaidan wanda ya raunani hankulan sashin majinkinta da ita sai suka kyautata abinda magabatansu na kwarai suka munana kuma suka nuisance shi suka yi hani ga buransa saboda saninsu da muninsa da kuma bacin makomarsa, kuma sai majinkirtan suka gafala ga wancananka mafiya karancin ilmi da hankali da fahimta da falala, sai suka fada cikin tarkunan shaidan sai ya ja su da kyautata bidi'a izuwa bidi'a manisaciya, muna neman tsarin Allah.

Tambaya: idan aka ce da kai: menene ma'anar guluwwi, kuma yana da Nau'ika?

Sai ka ce: Wuce iyaka shi ne ketare iyakar shari'a da ketare abinda Allah ya yi umarni das hi, kuma guluwwi yana kasancewa da dadi abisa abin nema a shari'a da kuma abinda aka yi izini a cikinsa, kuma yana kasancewa da bari abisa hanyar bauta

Kuma yana daga cikin nau'ikan wuce iyaka mai halakarwa:guluwwi a cikin Annabawa da Salihai ta wajan daukakasu sama da matsayinsu, da kuma dadi cikin abinda suka cancance shi daga so da girmamawa da basu siffofin ubangiji ko kuma juyar da wani abu na ibadu zuwa garesu, da kuma isa mutuka cikin yabonsu da godiya a gare su da abinda zai sanya su cikin matsayin Ubangiji

Kuma yana daga guluwwi: bauta ga Allah da bari dauwamamme ga abubuwan da Allah ya halatta wacce Allah madaukaki ya halicceta don maslahar mutane na daga abinci da abin sha da kuma abinda mutum yake bukatarsa na daga Barci da Aure.

Kuma yana daga guluwwi abin ki: hukunci abisa musulmi masu dayanta Allah da kafirtawa da kuma abinda yake bin bayan haka na daga bara'a, da kauracewa, da yaka, da Zalunta, da halatta mutunci da Dukiya da Jini.

Tambaya: idan aka ce da kai: ka ambaci wani abu daga nassoshin shari'a wacce take tsoratarwa daga guluwwi?

Amsa: sai ka ce: hakika dalilai sun yawaita a cikin Alkur'ani da sunna wacce suke hani ga barin guluwwi, da kuma tsoratarwa daga gare shi, kamar abinda yake cikin fadinsa Madaukaki: (kuma bana cikin masu kakalen fadarsa) (suratul sad 86), kuma Mai girma da daukaka ya hani bani isra'ila ga barin guluwwi a cikin addini, Madaukaki ya ce: (kada ku yi guluwwi a cikin Addininku) ( suratu alnisa'i 171), kuma Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- y ace: ( ina yi muku kashedi da guluwwi domin cewa abinda ya halaka wadanda suke kafin ku shi ne guluwwi) Ahmad ne ya fitar da shi, kuma y ace:- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: (masu guluwwi sun halaka, masu guluwwi sun halaka, masu guluwwi sun halaka) Muslim ne ya fitar da shi.

Tambaya: Idan aka ce da kai: shin ya halatta a yi dawafi ba'a ka'aba ba?

Amsa: sai ka ce: bai halatta a yi Dawafi ba'a ka'aba ba, domin Allah madaukaki ya kebance dakinsa da dawafi, sai mai tsarki ya ce: ( kuma sai su yi dawafi ga dakin nan 'yantacce) (Al hajj: 29), kuma Ubangijinmu bai yi mana izini da wanin wannan ba, domin cewa dawafi ibada ne, kuma hakika ya tsoratar damu daga farar kowace irin ibada, domin babu wata ibada face da wani dalili ingantacce daga Kur'ani ko sunna, farar wata ibada ba tare da dalili na shari'a ba, karkata ne, kuma juyar da ita ga wanin Allah shirka ne mai bata aiki mai fitarwa daga hanya hanifiyya zuwa ga kafirci muna neman tsarin Allah.

Tambaya: idan aka tambaye ka: shin ya halatta daura sirada( tafiya) don girmama wani bigire ko wani guri banda masallatai uku ( masallaci mai alfarma da masallacin Annabi da masallacin Al aksaa)?

Amsa: sai ka ce: bai halatta daura sirada saboda girmama wani bigire ko wani guri da kudirta falalarsa da kuma falalar tafiya izuwa gare shi ba face ga masallatai uku, saboda fadin Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- : ( ba'a daura sirada sai dai izuwa masallatai uku: masallaci mai alfarma, da masallacina wannan, da masallacin Al aksaa) Muslim ne ya rawaito shi.

Tambaya: idan aka ce da kai: shin wadan nan Hadisan masu biyowa ingantattu ne, ko kuma karya aka yiwa Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- :(idan al'amura suka yi muku kunci to ina umartarku da ziyarar kabarurruka), da (wanda ya yi hajji bai ziyarce ni ba to hakika ya yi min bakin ciki), da (wanda ya ziyarce ni kuma ya ziyarci babana Ibrahim a shekara daya zan yi masa lamini a wajan Allah na aljanna), da ( wanda ya ziyarce ni bayan mutuwa ta kamar wanda ya ziyarce ni ne a cikin rayuwata), da ( wanda ya yi kudiri cikin wani abu zai amfane shi), da ( ku yi tsani da matsayina domin matsayina a wajan Allah mai girma ne), da (Bawana ka bi ni sai na sanya ka daga cikin mai cewa da wani abu kasance sai ya kasance), da ( lalle cewa Allah ya halicci halitta daga hasken Annabinsa Muhammadu –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-).

Amsa: sai ka ce: dukkan wadan nan Hadisan karya aka yiwa Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma 'yan bidi'a sune kadai suke korjantatada masu bautar kabarurruka, wanda yaka cewa da abu kasance sai ya kasance ai shi ne Allah shi kadai bas hi da abokin tarayya kuma ba shi da kini kuma ba shi da makamanci, tsarki ya tabbatar masa da gode masa, ba wanda zai iya wannan kuma babu daya da ya mallake shi daga halitta Annabawa ne ko waliyyai, Allah Madaukaki ya ce:( umarninsa idan ya nufin wani abu sai y ace masa kawai kasance sai yana kasancewa) (suratu yasin: 82). Kuma Madaukaki ya ce: ( to shi ne da halittar da kuma umarnin albarkar Allah Ubangijin talikai ta bayyana) (Al'a'araf : 54) ya gaatar da abinda hakkinsa jinkirtarwa don ya fa'idantar da iyakancewa kuma shi ya iyakance halitta da kuma tsarawa gareshi shi kadai bas hi da abokin tarayya.

Tambaya: idan aka ce shin ya halatta binne matattu a cikin masallatai, da kuma gina masallatai a kan kabarurruka?

Amsa: sai ka ce: shi yana daga ababan Haramtawa masu girma, da kuma bidi'o'I masu hadari, kuma yana daga cikin manyan tsanika masu sanyawa a afka cikin shirka, an karbo daga Aisha Allah ya yarda da ita ta ce: Manzan Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya fada cikin rashin lafiyar da ya mutu a cikinsa: ( Allah ya la'anci Yahudu da Nasara sun riki kaburburan Annabawansu masalatai) A'isha ta ce:Allah ya yarda da ita: (yana tsoratarwa abisa abinda suka aikata) Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi, kuma an karbo daga Jundubi dan Abdullah Allah ya yarda das hi daga Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- cewa shi ya ce kafin ya mutu da kwana biyar: ( ku saurara cewa wadanda suka zo kafin ku sun kasance suna rikon kaburburan Annabawansu da salihansu masallatai ku saurara kada ku riki kaburbura masallatai, domin cewa ni na hane ku da wannan) Muslim ne ya rawaito shi. Kuma masallatan da aka gina abisa kaburbura bai halatta a yi salla a cikinsu ba, kuma idan aka gina masallaci a kan wani kabari ko kabarurruka ya wajaba a rushes hi, amma idan aka gina masallaci ba akan kabari ba, sannan daga baya aka binne mamaci a cikinsa to baza a rushe masallacinba, sai dai za'a bude kabarin sannan a cire wanda aka binne a cikinsa daga masallacin izuwa makabartar jama'a

Tambaya: idan aka ce da kai: menene Hukuncin gini a kan kabarurruka?

Amsa: sai ace: yin Gini a kan kabarurruka bidi'a ce a bar ki saboda abin day ake cikinta na guluwwi cikin girmama wanda aka binne a cikin wannan kabarin,kuma ita mai kaiwa ce zuwa shirka, saboda haka ya wajaba a gusar da abinda aka yi gini da shi a kan kabarin da kuma daidaita ta domin kawar da wannan bidi'ar da kuma toshe hanyar shigowar shirka, hakika Muslim ya rawaito a cikin sahihinsa daga Abil hayyajil asadi Hayyan dan Husain y ace: Aliyyu y ace da ni Allah ya yarda da shi: bana aikaka ba abisa abinda Ma'aikin Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- :( cewa kada ka bar wata sura face ka shafeta ko kuma wani kabari mai tudu face ka daidaita shi).

Tambaya: idan aka ce da kai: shin an binne Ma'aikin Allah-tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- da farko a cikin Masallaci?

Amsa: sai ka ce: an binne shi a cikin dakin A'isha Allah ya yarda da ita kuma ya kai mafi yawa da shekaru tamanin a bisa kabarinsa a wajan masallacin, kuma daya daga cikin halifofin Umawiyawa ne ya yalwata masallacin Annabi sai dakin ya zama kamar a cikin masallacin, kuma Halifan bai karbi hanin Malaman cikin zamaninsa da kuma tsawatarwarsu daga shigar da dakin cikin masallacin ba. Kuma hakika Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya fada yana mai tsawatarwa daga gina masallatai a kan kabarurruka: ( ku saurara cewa wanda suka kasance kafinku sun kasance suna rikar kabarurruka masallatai, ku saurara to kada ku riki kabarurruka masallatai domin cewa ni na hane ku ga barin wannan) Muslim ne ya rawaito shi, kuma Ma'aikin Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya tsinewa wadanda suka rika akan kabarurruka masallatai da fitilu kamar yadda yake cikin hadisin da ma'abota sunan suka rawaito shi. Kuma abinda yake tsoransa ya afku-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a bisa al'umarsa kuma abinda yake gargadi a kansa ya faru, saboda rinjayen jahilci, da kuma rikitarwar shehunan karya da bidi'a, sai suka zama suna kusantuwa izuwa Allah da abinda shi yana daga karkata a gare shi,da kuma sabawa ga Manzan Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- daga sanya kabarurruka da ginin kabari a cikin masallaci, da kuma sanya mata sutura akanta,da sanya musu fitilu, da kuma yi mata dawafi,da sanya akwatinan bakance a kanta, sai shirkoki da bacebace suka watsu da sunan soyayyar salihai da girmamasu da fuskanta da su ga Ubangijin talikai don ya amsa addu'ar masu rokon, kuma dukkan wannan yana daga gadon batattu marigaya, Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: lalle tabbas za ku bi Hanyoyin wadanda suka zo kafinku

Tambaya: idan aka ce da kai: shin Manzan Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana raye a kabarinsa, kuma cewa shi yana fitowa a bisa mutane lokacin maulidin Annabi da abinda ake cewa halartowa kamar yadda sashinsu yake kudircewa?

Amsa: sai ka ce: Limaman mazahaba hudu sun hadu kai duk al'umma baki daya a bisa cewa sahabbai Allah ya yarda da su ba su binne Ma'aikin Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ba har said a Ruhinsa ya rabu da jikinsa, domin cewa ba zai yiwu a hankalce su binne shi ba alhali yana da rai !! kuma saboda cewa su sun sanya halifarsa a bayansa, kuma 'yarsa Fadima Allah ya yarda da ita ta nemi gadonta daga gare shi, kuma ba'a ciro daga wani daya daga sahabbai ba ko tabi'ai ko wadanda suka bisu daga shugabannin nan hudu cewa Manzan Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya taba fitowa ga mutane bayan mutuwarsa da kuma binne shi, wanda kuma yake da'awar cewa shi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana fitowa ga mutane daga kabarinsa to shi makaryaci ne shaidanu sun yi wasa da shi mai kirkirar karya ne a bisa Allah da kuma Manzan Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- takaka bayan Allah maitsarki da daukaka yana cewa: ( kuma Muhammadu bai zama ba face Manzo Hakika Manzanni sun shude kafin shi, ashe idan ya mutu ko aka kasha shi, zaku juya akan dugaduganku) da fadinsa Madaukaki: (lalle ne kai mai mutuwa ne kuma lalle suma masu mutuwa ne), sai Allah Mai tsarki da daukaka ya hada labarin mutuwarsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- , da mutuwar mutane don ya bayyana cewa shi mutuwa c eta hakika da kuma ciruwa daga wannan gida zuwa gidan barzahu wanda ba mafita daga gar eta face zuwa fagen kiyama don hisabi da sakamako bayan tashi da rayawa da fitowa daga kabarurruka, yana daga abinda ya dace cikin martini abisa jahilai da makaryata wadanda suke kudirta fitowarsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- daga kabarinsa abinda Imamul kurdubi bamalike ya fada wanda ya mutu a cikin shekara ta (656) cikin rubutu na fahimta a bisa karyata fitowarsa-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- daga kabarnsa:( kuma wannan ana riskar barnarsa da farkon hankali,kuma yana lazimta a gare shi cewa ba wani daya da zai ganshi face abisa surarsa wacce ya mutu a kanta , kuma cewa masu gani su biyu bazasu ganshi ba cikin lokaci guda a guri biyu, kuma cewa ya rayu yanzu ya kuma fito daga kabarinsa, kuma ya dinga tafiya cikin kasuwanni ya kuma dinga hira da mutane kuma suma su dinga hira das hi, kuma wannan yana lazimta cewar kabarinsa zai wofunta daga jikinsa, kuma ba abinda zai wanzu a cikin kabarinsa, sai a ziyarci mujarradin kabari kuma a dinga sallama a bisa wanda baya nan,domin cewa shi ja'izi ne a ganshi cikin dare da rana tare da haduwar lokuta abisa hakikaninsa ba'a cikin kabarinsa ba, to ka ga wannan jahilci ne wanda mafi koma bayan hankali ba zai lazimce shi ba) ya kare>

Tambaya: idan aka ce da kai : mecece bidi'a? kuma menene nau'inta? Kuma menene hukuncin kowane nau'i? kuma shin a cikin musulunci akwai bidi'a kyakkyawa?

Amsa: sai ka ce: bidi'a ita ce abin da bawa yake bautawa Allah da shi ba tare da Dalili na shari'a ba, kuma nau'I biyu ce: bidi'a mai kafirtarwa kamar wanda yake kewaya kabari don neman kusanci ga a'abocinsa, da kuma bidi'ar da me yinta yake sabo ba tare da kafirci ba, Kamar wanda yake tsayawa maulidin annabi ko waliyyi in bai hada shi da abubuwan shirka da abubuwan kafirciba. Kuma babu wata bidi'a kyakkyawa a cikin musulunci, domin dukkan bidi'a bata ne, saboda fadinsa –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- (ina yi muku kashedi da fararrun al'amura domin cewa kowane fararre bidi'a ne kuma kowace bidi'a bata ce), a cikin wata riwayar: (kuma dukkan bata yana cikin wuta) Imamu Ahmada da Nasa'i ne suka rawaito shi, kuma bai kebance -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -daga bidi'a wani abu ba, kuma bidi'a dukkanta abar haramtawa ce kuma mai yenta ba za'a bas hi lada ba domin cewa ita riskarwa ne ga mai shara'antawa da kuma dadi a cikin Addini bayan kammaluwarsa da cikarsa, kuma ita abar mayarwa da ma'abocinta ne,saboda fadinsa- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- :(wanda ya aikata wani aiki wanda babu umarninmu a gare shi to shi juyayye ne) Muslim ne ya rawaito shi, da fadinsa: ( wanda ya farar da wani abu a cikin umarninmu abinda baya daga cikinsa to shi juyayye ne) Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi, da fadinsa( al'amarinmu) yana nufin Musulunci

Tambaya: idan aka ce da kai: me ake fahimta daga fadinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-: ( wanda ya sunnanta wata sunna to yana da sakamakonta da kuma sakamakon wanda ya aikatata ta) ?

Amsa: sai ka ce: ( wanda duk ya sunnanta sunna kyakkyawa) ana nufin wanda ya aikata wani aiki wanda musulunci ne ya zo da shi alhali mutane sun manta da shi, ko kuma ya yi kira izuwa abinda Alkur'ani da sunna ya zo das hi, daga abinda mutane suka jahilce shi to yana da ladan wanda ya bi shi, domin cewa wannan hadisin sababinsa kira izuwa sadakoki abisa fakirai da suka kasance suna tambaya, kuma wanda ya ce ( wanda ya sunnanta sunna kyakkyawa) shi ne wanda ya ce :( dukkan bidi'a bata ce), ita sunna asalinta Alkur'ani da sunna, kuma bidi'a bata da wani asali a cikin Alkur'ani da sunna, kawai ita tsantsar halartawar wani sashi ne na hankalanwasu yan zamani

Tambaya: Idan aka ce da kai: me za'a fahimta daga fadin Umar Allah ya kara yadda a gare shi a cikin sallar tarawihi : ( madalla da bidi'a), da kuma farar da kiran salla na biyu cikin zamanin Usman Allah ya yarda da su?

Amsa: sai ka ce: lalle cewa fadin Umar Allah ya yarda da shi ( madalla da bidi'a) yana nufin ma'anarta ta yare ba wai ma'anarta ta shari'a ba, domin cewa Umar Allah ya yarda das hi bai fadi wannan kalma ba sai dai a sallar tarawihi wacce Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya sunnantaba, to aikinsa mai dacewa ne da abinda Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi –ya aikata, kuma abinda ya kasance raya aikin Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ne to ba bidi'a ba ne kadai shi jaddada da tunasarwa ga mutane da abinda aka mance aka bari kuma kira izuwa aiki na shari'a Manzan Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya yi kira izuwa gare shi kuma ya aikata shi, amma kuma aikin Usman Allah ya yarda das hi to shi yana daga cikin wanda Manzan Allah –tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi kira da a yi koyi da sunnarsa tare da sauran halifofi shiryayyu yayinda yace- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace: ( ina horarku da sunnata da sunnar halifofina shiryayyu), wadanda ba halifofi ne shiryayyu ba bas u zamo kamar haka ba domin cewa Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya tsare sunna das hi da kuma halifofi shiyayyu, kuma bai ambaci waninsu ba, hakika sahabbai sun kasance Allah ya yarda da sumafiya tsananin mutane fadakarwa daga bidi'a da fararrun al'amura, yana daga ciki wannan cewa dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya fada ga wasu mutane da suka kirkiri wani abu a cikin addini yayinda suke ambaton Allah da zikiri na jama'a da wani yanayi ayyananne fararre kuma alhalin su suna nufin alheri:( kun rigayi Muhammad –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ne, ko kuma kun zo ne da wata bidi'a don zalunci) , yayin da kuma suka ce da shi:( alhairi muka nufa), sai ya ce da su : ( ba kowa ne mai neman alhairi ba ne yake samunsa) Darimi ne ya rawaito shi a cikin sunan nasa, da yawan lokaci kuma yakan maimaita a mazaunansa ga sahabbansa :( ku bi kada ku kirkiro) kuma dan Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: (kowace bidi'a bat ace koda mutane suna ganinta kyakkyawa)

Tambaya: idan aka ce da kai: shin Taron haihuwar Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sunna ce ko bidi'a?

Amsa: biki da haihuwar Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi -bai zo a Alkur'ani ba ko kuma sunna kuma bas hi da wani dalili na shari'a, kuma bai tabbata ga daya daga cikin sahabbai ba Allah ya yarda das u, kuma babu wani daga cikin shugabanni hudu da ya fade shi, da kuwa ya kasance alheri dad a kuma da'a da sun rigaye mu izuwa gare shi Masu yin bikin suna ambatar cewa su suna bikin haihuwar annabi ne –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – saboda soyayyarsa, soyayyar Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- farilla ce aini a bisa dukkan musulmi imaninsa ba zi inganta ba sai da sonsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kuma tana kasancewa ne da da'arsa ba da bikin maulidinsa ba, kuma farkon wadanda suka fara yin wannan bidi'ar su ne yan adiniyya zindikai wadanda ake kira da fadimiyyuun, kuma wannan ya faru bayan mutuwar Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da karni hudu, kuma masu bikin maulidi da shi cikin ranar litinin kuma ita ranar mutuwarsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma a gaskiya cewa bikin maulidinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ba wani abu bane face kwaikwayon aikin nasara cikin bikinsu da haihuwar Annabi Isa aminci ya tabbata a gare shi, kuma Allah ya wadata mu ga barin bidi'o'I da farefare da kirkire kirkiren al'umomi batattu da shari'a cikakkiya tatacciya tsarkakakkiya kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin Talikai

Tambaya: idan aka ce da kai: menene hukuncin koyar sihiri, ko kuma aiki da shi?

Kuma suka bi abin da shaiɗãnu ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani.

Aljubt: an fassara shi da sihiri, sai Allah ya gwama shi da dagutu, kamar yadda yake imani da dagutu kafirci ne, to hakanan aiki da sihiri kafirci ne, kuma yana daga lazimammun kafirci da dagutu a kudirce bata sihiri ,domin cewa shi ilimi ne mara kyau mai bata addini da Duniya, kuma ya wajaba a nuisance shi, da kuma kubuta daga gare shi da kuma Ahalinsa.

Madaukaki ya ce: ( da sharrin mata masu tofi a cikin kulle kulle) (Alfalak: 4), kuma –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce:( ku nisanci zunubai bakwai masu halakarwa) sai ya ambaci sihiri daga cikinsu, kuma acikin hadisin: (wanda ya daura wani kulli sannan ya yi tofi a cikinta to ya yi sihiri, kuma wanda ya yi sihiri to ya yi shirka) Al nasa'I ne ya rawaito shi, kuma Bazzar ya rawaito: (ba ya tare da mu wanda ya yi shu'umci ko ya nemi a yi masa shu'umci ko ya yi bokanci ko ya nemi a yi masa bokanci ko ya yi sihiri ko ya nemi a yi masa sihiri), kuma ukubar mai sihiri ita ce kisa, hakika Umar dan Khaddab Allah ya yarda da shi ya rubuta ga gomnoninsa:(cewa ku kashe duk wani boka namiji da boka mace) Bukhari ne ya rawaito shi, kuma an karbo daga Jundubi Allah ya kara yarda a gare shi Manzan Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -ya ce: ( haddin sihiri kisa da takobi) Tirmizi ne ya rawaito shi kuma hakika Hafsa Allah ya yarda da ita ta kashe wata baiwarta da ta yi mata sihiri

Tambaya : to idan aka ce da kai: shin abin da masu rufa ido suke yi na daga sukar kansu da kuma cin abubuwa masu kaifi, sihiri ne da rufa ido ko karama ce?

Amsa: sai ka ce: abinda masu rufa ido suke yin a daga abinda aka ambata shi yana daga abinda shaidanu suke taimaka musu das hi wajan aikatashi, kuma wani sashin yana daga abinda suke sihirce idon mutane das hi, sais u dinga ganin abinda ban a gaske ba kamar cewa shi gaske ne, kamar yadda masu sihiri suka yiwa Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi da mutanensa wadanda suka ga abinda ya afku wanda Allah ya ambatata a Alkur'ani, hakika an surantawa Musa cewa igiyoyin masu sihiri tana tafiya, amma a hakika ba tafiya suke ba, kamar yadda Allah Madaukaki ya ce: ( ana surantasu agare shi daga sihirinsu lalle tana tafiya da sauri) (daha : 66), da cewa za'a karanta a wajan masu rufa idon ayatul kursiyyi da surorin falaki da nasi da fatiha da karshen bakara da wasunsu na daga ayoyi da sai sihirin y abaci da rufa idon da izinin Allah Madaukaki, da kuma karyar masu rufa idon ta yaye kuma batansu da karyarsu ta bayyana ga mutane.

Kuma karama bata kasancewa face ga salihai masu kadaita Allah kubutattu daga bidi'a da karyarsu, kuma ita karama itace samiwar alhairi ga mumini ko ije sharri ga barinsa ba wannan yana nufin cewa shi yafi waninsa daga muminai ba na daga wadanda karama bata afku a kansu ba, shi sha'anin karama a boye kada a bayyana, ba kuma a ci da ita kuma ba'a yaudara Mutane da ita.

Tambaya: idan aka ce da kai: menene hukuncin zuwa wajen mai sihiri saboda neman magani?

Amsa: sai ka ce: bai halatta tafiya zuwa wajen mai sihiri namiji ko mai sihiri mace ba don tambayarsu da kuma neman magani daga gurinsu ba, saboda hanin Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ga barin hakan, kuma dalili cewa shi lokacin da aka tambayi Manzan Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a game da nushra kuma itace warware sihiri da sihiri kwatankwacinsa ya ce: ( ita tana daga aikin shaidan) yana nufin nushra Abu dawuda ne ya rawaito shi, kuma wani abu bai halatta ba daga aikin shaidan kuma ba'a amfani a cikinsa, kuma babu wani alhairi da ake fata da shi.

Tambaya : Idan aka ce da kai: mecece rigakafi daga sihiri kafin afkuwarsa kuma yaya za'a yi maganinsa bayansa?

Amsa: sai ka ce: kiyayewa abisa zikiran safe da yamma, kuma musamman ( da sunan Allah wanda babu wani abu da zai cutar tare da sunansa a kasa ko kuma a sama kuma shi ne Mai ji Masani) sau uku safe da dare, da fadin :( ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta), da kuma nemawa iyali da yara:( ina nema muku tsari da kalmomin Allah cikakkiya daga kowane shaidani da kuma dabba mai cutarwa da kuma daga kowane ido mai zargi) kamar yadda yake a hadisi, da kuma karanta surorin kul huwallahu da falaki da nasi sau uku safe da yamma, da kuma ayatul kursiyyi, da kuma ayoyi na karshe daga suratul bakara da daddare, da kuma cin dabino guda bakwai da safe.

Kuma bayan afkuwar sihirin kuma: yiwa wanda aka yiwa sihirin karatu kai tsaye da ayoyin Alkur'ani, da addu'o'I wadanda suka zo a cikin sunnar Annabi, da kuma kaho, da kuma bata abubuwan da aka yi sihiri da ita yayin da ta bayyana, kuma da sannu sihiri zai faci kuma wanda aka yiwa sihiri ya ji sauki da izinin Allah Madaukaki.

Tambaya: to idan aka ce da kai: shin ya halatta zuwa wajan bokaye day an duba da matsafa da masu duba tafi, da kuma masu da'awar sanin ilimin gaba da taurari da kuma sanin burujan sama?

Sai ka ce: zuwa gurinsu da tambayarsu da kuma saurarar karairayinsu abin haramtawa ne a gare mu sai dai ga wanda yake nufin bayyana karyarsu da kunya ta su da kuma yaye bace bacensu daga malamai wadanda zasu iya hakan, kuma ya wajaba a fadakar daga duk wani mai da'awar sanin gaibu, da kuma fadakarwa daga karairayinsu da yaudarorinsu ga gafalallu, kuma kaiton tabewar wanda ya gasgata karyace karyacensu da batansu, ya ce: (wanda ya je wajan dan duba ko boka sannan ya gasgata shi da abinda ya fada to lalle ya kafirta da abinda aka saukar a bisa Muhammad- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ma'abota sunan ne suka rawaito shi. Kuma ya ce- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- (wanda ya je wajan Dan duba kuma ya tambaye shi wani abu ba za'a karba daga gare shi sallar dare Arba'in ba) Muslim ne ya rawaito shi.

Tambaya: to idan aka ce da kai: me zaka ce a cikin wannan hadisin:( ku koyi sihiri kuma kada ku yi aiki da shi)?

Amsa: sai ka ce: wannan hadisi ne na karya a bisa Manzan Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ta kaka zai hani ga barin sihiri kuma sannan ya yi kira izuwa koyarsa

Tambaya : to idan aka ce da kai: wanene mafificin mutane bayan Annabawa?

Sai ka ce: Sahabbai ne Allah ya yarda da su kuma wannan cewa shi yayinda Annabinmu Muhammadu – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance mafificin Annabawa sai Sahabbansa suka zama su ne wadanda suka fifici baki dayan sahabban Annabawa, kuma mafificinsu Abubakar tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: rana bada fito ba kuma bata fadi ba a bayan Annabawa da Manzanni abisa mafifici daga Abubakar) sannan Umar sannan Usman sannan Aliyu Allah ya yarda da su, sannan sauran goman. Kuma sahabbai sashinsu suna son sashi, kuma saboda haka Aliyyu- Allah yarda da shi ya ambaci 'ya'yansa da sunayen halifofi da suka zo kafin shi, to yana daga sunayan 'ya'yansa Abubakar da Umar da Usman, kuma ya karyata wanda y ace: cewa Sahabbai ba sa son muminai daga alul baiti kuma cewa ahlul baiti ba sa son sahabbai, to wannan tana daga karyace karyacen makiya ahlul baiti da sahabbai Allah ya yarda da su.

Tambaya: idan aka ce da kai: menene wajibinmu a bangaren sahabbai Allah ya yarda das u, menene hukuncin zagin dayansu?

Amsa: sai ka ce: ya wajaba sonsu da girmamasu baki dayansu da kuma yarda da su baki daya, saboda Allah ya yarda da su, kuma be kebance ko mutum daya daga cikinsu ba, kamar yadda Allah Madaukaki ya ce:( Kuma mãsu tserewa na farko daga Muhãjirina da Ansar da waɗanda suka bi su da kyautatãwa, Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare Shi, kuma Ya yi mãsu tattalin gidãjen Aljanna; Ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, suna madawwamã a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma) ( al tauba : 100) kuma Allah Madaukaki ya ce:( lalle ne hakika Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke maka mubaya'a a karkashin itaciyar nan ( Al fath : 18), kuma Allah ya ce agame da su:( kuma dukkansu Allah ya yi musu alkawarin sakamko mai kyau), kuma ya wajaba son iyayen muminai da kuma girmamasu, kuma ya haramta zagin daya daga cikinsu domin cewa hakan yana daga manyan zunubai , Allah Madaukaki ya ce: ( Matayensa iyayensu ne) ( suratul Ahzab: 6), to dukkan matayen Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- iyayen muminai ne domin cewa muminai be kebance ko guda daya daga cikinsu ba , hakika kuma ya zo a cikin hadisin Abi sa'id al hudri Allah ya yarda da shi, ya ce:Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – ya ce: ( kada ku zagi sahabbaina da cewa dayanku zai ciyar da dinare misalign girman dutsen uhudu, ba zai kai misalin mudu daya na dayansu ba ko kuma rabinsa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

Kuma babu mamaki daga wan nan matsayi mai girma a gare su, to su ne wadan da suka bada kansu da dukiyoyin su saboda Addinin Allah, kuma suka yaki makusanci da manisanci daga wadanda suke mu'araba da kiran Manzan Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- , kuma suka kauracewa Ahali, kuma suka kauracewa garuruwansu a cikin tafarkin Allah, kuma su ne sababin dukkan alheri da fifiko wanda al'umma suke samu har zuwa tashin kiyama, kuma suna da misalin sakamakon duk wanda ya zo bayansu daga muminai zuwa Allah ya gaje kasa da wadanda suke kanta, ba su misali cikin al'umman da suka rigaye su kuma ba za'a sami misalinsu ba a cikin na bayansu, Allah ya yarda da su kuma ya yardar da su, kuma boni ya tabbata ga wanda yake gaba da su kuma yake zaginsu kuma yake suka a cikinsu,

Tambaya: Idan aka ce da kai Menene Ukubar wanda ya zagi daya daga Sahabban Annabi tsira da Aminci a gare su ko ya zagi daya daga cikin Iyayen Muminai (Matan Annabi)

Amsa: sai ka ce:ukubarsa tsinuwa da kora da nisa ga rahamar Ubangiji mai tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- y ace: ( wanda ya zagi sahabbaina to la'anar Allah da Mala'ikunsa da mutane baki daya ta tabbata a gare shi) Dabarani ne ya rawaito shi, kuma abinda yake wajibi inkari mai tsanani a bisa wanda ya zagi daya daga sahabbai ko ya zagi daya daga cikin iyayen muminai yardarm Allah ta tabbata a gare su baki daya, ya wajaba ga shugaba da kuma bangarori kyabantattu ladabtar da ukubantar da wanda yake afka wannan daga gareshi ladabtarwa mai tsanani.

Tambaya: idan aka ce da kai: shin ya halatta fadin Gamayyayar Addinai?

Sai ka ce: bai halatta wannan fadin da kudirce shi ba, kuma shi yana daga cikin mafiya girman nau'ikan kafirci kuma shi karyata Allah ne da kuma raddi ga hukuncinsa, kuma daidaitawa ne tsakanin kafirci da imani da gaskiya da karya, kuma ta kaka mai hankali zai kokonta bacin daidaito da kuma hadawa tsakanin addinin Allah da kuma addinin dagutai? Kuma takaka tauhidi zai hadu da shirka da kuma gaskiya da karya?! Shi fa addinin musulunci shi ne gaskiya kuma abinda yake bas hi ba shine karya, kuma hakika Allah ya cika addininsa kuma ya cika ni'imarsa, Madaukaki yace: (a yau na kammala muku addininku kuma na cika a gareku ni'imata kuma na yardar da musulunci shi ne addini) ( Al ma'ida: 3), bai halatta a tauye daga gare shi ba, ko a kara a cikinsa, ko kuma a daidaita shi da waninsa daga hanyoyi kafirci da kuma addinan dagutai ko a hada tare da ita, ba wani musulmi mai hankali da zai kudirta haka, babu wani da ya mallaki daidai da kwayar zarra na daga hankali da imani da zai tafi izuwa haka , Madaukaki ya ce: ( kuma wanda ya bi wanin musulunci addini to ba za'a karba daga gare shi ba kuma shi a lahira yana daga masu hasara) ( ali imrana : 85), kuma ya fada-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- (na rantse da wanda raina yake hannunsa babu wani daya daga cikin wannan al'umma bayahude ko banasare da zai ji daga gareni, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba face ya kasance daga yan wuta) Muslim ne ya rawaito shi.

Tambaya: idan aka ce da kai: mene ne dadin Imani da Allah da tauhidinsa, da kuma istikama abisa sunnar Manzonsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-?

Amsa: sai ka ce: yana tabbata da imani ga mutum daya da jama'a da al'umma dukkan alheri a cikin duniya da lahira na daga budin albarkatu daga sama da kuma kasa, Madaukaki ya ce:(Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa (suratul Aaraf: 96).

Kuma haka nan yana samu da tabbatuwar imani nutsuwar zuciya da hutun rai da yalwar kirji, Madaukaki y ace: ( wadanda suka yi imani kuma zukatansu takan samu nutsuwa da ambaton Allah to da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa( suratul ra'ad 28). Kuma mumini mai dayanta Ubangijinsa mai bi ga sunnar Manzansa da tabbaci da gaskiya zai dinga rayuwa rayuwa mai dadi kuma ba zai sami nutsuwar rai ba zai firgice ba, ba zai bakin ciki ba, kuma shaidanu ba za su salladu akansa da wasiwasi da tsoratarwa dab akin ciki ba, kuma ba zai tsiyata a duniyarsa ba, kuma zai azurta a cikin aljannatun ni'ima a lahirarsa, Madaukaki ya ce: (Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa.(al nahl 97).

To ka yi kokari Dan Uwana Musulmi da 'yar uwata musulma ku kasance daga masu rabauta da wannan bishara masu shiga cikin ahalin wannan alkawarin na Ubangiji mai karamci.

Kammalawa

Ya dan uwana mai girma … ya 'yar uwata mai girma

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya cika mana addini, kuma ya cika ni'ima a kanmu, kuma ya shiryar da mu ga addinin musulunci addinin gaskiya da kuma tauhidi da rabon duniya da na lahira,

Yana daga abu mai muhimmanci__ya kai mai girma__ tafiya don kari daga ilimin shari'a mai samuwa daga Alkur'ani da sunna da kuma fahimtar wadanda Allah ya yarda da su kuma suma suka yarda das hi, don mu kasance daga cikin masu bautawa Allah a basirance, kuma mu kubuta daga afkawa cikin shubuhohi da kuma fitintunu masu batarwa, kuma duk wani mutum duk inda martabarsa takai abin yiwa umarni ne da Karin ilimi kuma mai bukatuwa ne zuwa gare shi,

To ga dai shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ubangijinsa ya umarce shi da karawa da ilimi, Madaukaki ya ce: (ka sani cewa shi babu abin bautawa da gaskiya face Allah) (Muhammad :19) kuma ya shiryar das hi da tambayar Ubangijinsa dadi daga gare shi, Madaukaki y ace: (kuma ka ce ya Ubangijina ka kara min ilimi) (daha:114).to ka tafi__ ya kai mai dace da shiryarwa Annabinka kuma shugabanka Muhammad- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- , kuma ka yi bushara da alhairi da girma a cikin gidajenbiyu, Madaukaki y ace: (Allah yana daukaka wadanda suka yi imani daga cikinku da kuma wadanda aka bawa ilimi da darajoji) ( almujadala:11).

Kuma bayan saninka ka kasance tare da masu aiki da abin da suka sani, kuma ka yi kokari wajan yada alhairi da ilimi don ka riski mahayar salihai masu gyara, kuma don ka sami ladan wadanda ka kiraye su, kuma a rubuta maka ladan wanda ya amsa maka, kuma babu wani abu bayan tsayar da farillai da ya fi yada ilimi da kuma kira ga alhairi

Mamakin girman ladan masu kira izuwa gaskiya ga mutane, su ne masu tsamo su da izinin Allah ga wanda ya nitse cikin duffan jahilci da bata da karyace karyace, masu ruko da hannunsu izuwa hanyar aminci da haske da shiriya da hanyar aljanna kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai