×
Littafi ne da ya kunshi bayani akan rukunan musulunci da sharuddan Kalmar shahada da kuma tsarin karantar da al’umma, da bayani akan alwala da sallah, da kuma yadda ake shirya janaza da yi mata da tsoratarwa akan shirka, da bayanai akan kyawawan dabi’un musulunci.

HUKUNCE HUKNCE MASU ZURFI

Akan muhimman darussa da suka shafi al'umma baki daya

Wanda ya yi bitar littafin:

Abdulaziz dan Abdullahi dan Baz.

Wallafar:

Abdulaziz dan Daud Fayiz.

Fassarar:

Aliyu Muhammad Sadisu

Wanda Ya Duba

Attahiru Bala Dukku

Gabatarwar Mai Fassara

Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, Dukkan godiya ta tabbata a gareshi, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabimmu Annabi Muhammad da iyalanshi da kuma sahabbansa baki daya.

Bayan haka, hakika wannan littafi mai suna: “Hukunce hukunce masu zurfi Akan muhimman darussa da suka shafi al'umma baki daya". Littafine mai matukar muhimmanci musammamma a wannan lokacin, littafi ne da manyan malamai biyu su ka yi masa aiki tukuru, malami na farko shi ne Shehun malami Abdulaziz Ibnu Baz, Allah ya jikan shi da gafara, wanda shi ne ya wallafa asalin wannan littafi, ya kuma sanya masa suna; “Muhimman Darussa da suka shafi al'umma''. Sai kuma malami na biyu wato Abdulaziz dan Daud Fayiz, wanda ya yi wa littafin Sharhi, ya kuma sanya masa suna; “Hukunce hukunce masu zurfi Akan muhimman darussa da suka shafi al'umma baki daya." Allah madaukakin sarki ya saka musu da alheri bakidayansu.

A rubuta wannan littafi ne akan tsarin darasi-darasi, har yakai darussa goma sha-takwas, darasin farko ya kunshi koyar da karatu daga Fatiha harzuwa surati Zalzala, wato gajerun surori kenan, wanda ake matukar bukatar limamai da malamai su koyar da su ga al'umma baki daya, daki-daki a hankali harkowa ya iya, to haka aka biyo baya da darussa da suka shafi musulunci baki daya, darasi na biyu yana bayani ne akan 'Kalmar Shahada, da kuma rukunanta da sharuddanta'. Darasi na uku kuma akan Shika-shikan Imani, sai kuma darasi na biyar akan 'Karkasuwar Tauhidi', shi kuma darasi na shida akan shika-shikan musulunci.

Amma darasi na shida ya yi bayani ne akan 'Sharuddan Sallah', na bakwai kuma akan 'Rukunan Sallah', na takwas kuma akan 'Wajibabbun Sallah' sai na tara akan 'Tahiya' na goma kuma akan 'Sunnonin Sallah' na sha-daya kuma akan 'Abubuwan da suke bata Sallah'.

Daga darasi na sha-biyu zuwa na sha-hudu duk sun yi bayanin ne kan alwala, Sharuddan alwala, da farillan alwala, da abubuwan da suke warware alwala.

Amma darasi na sha-biyar da na sha-shida an ware su ne domin bayan kyawawa halaye da musulunci ya karanta da kuma nagartattun dabi'un wadanda ake bukatar kowanne mutum musulmi ya su zama halayansa kuma dabi'unsa da zai dabi'untu akan su.

Shi kuma darasi na sha-bakwai ya yi bayani ne kan hatsarin dake cikin shirka da kuma laifuffuka masu halakarwa da ya wajaba kowanne musulmi mace ko namiji ya nisance su.

Darasin karshe shi ne na sha-takwas inda ya yi bayanin yadda ake shirya jana'iza tun daga wanka har sanya likafani har yi mata sallah, har ma da karatun sallar jana'iza din da kuma yadda jera gawarwaki maza da mata ko yara da manya, da kuma in da liman yake tsayawa.

Wannan littafi yana da matukar muhimmanci a koyar da shi a masallatai da makarantu, kuma akoyar a hankali daki-daki, da fatan Allah ya amfanar da mu.

Mai fassara:

Aliyu Muhammad Sadisu,

Minna, Nigeria.

[email protected]

بِسْمِ اِللهِ اِلرَّحْمَنِ اِلرَّحِيمِ

Gabatarwa

Lalle dukkan godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa muna kuma neman gafararsa. Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunammu da kuma munanan ayyukammu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda Allah ya batar da shi to babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai bas hi da abokin tarayya, ina kuma shaidawa da cewar lalle (Annabi) Muhammad bawan Allah ne kuma manzan Allah ne.

- Ya ku dukkanin wadanda suka yi Imani ku ji tsoron Allah hakikanin jin tsoronsa, kuma kada ku mutu sai kuna musulmai''. Suratu Ali Imaran, aya ta:102.

- Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda daya, kuma ya halitta daga ita (wannan ran) matarsa kuma ya watsa daga su biyun maza da yawa da kuma mata, ku ji tsoron Allah wanda kuke tambayar junan da shi kuma (ku ji tsoron yanke) zumunci, lalle Allah ya kasance a gareku mai kulawane''. Suratun Nisa'i, aya ta:1

- Ya ku dukkanin wadanda suka yi Imani! Ku ji tsoron Allah kuma ku fadi Magana maikyau, (in kun yi haka to Allah) zai kyautata muku ayyukanku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya bi Allah da manzanshi to hakkika ya rabauta rabauta mai girman gaske''. Suratul Ahzab, aya ta:70-71.

Bayan haka:

Alokacin dana duba littafi mai suna; 'Muhimman darussa ga al'umma baki daya' na mai girma kuma mahaifi Shehin malami Abdulaziz dan Baz – Allah ya yi mishi rahama- babban mai fatawa na kasar Saudi Arebiya, kuma shugaba na majalisar manyan malamai, sai na yi tunanin in yi masa sharhi saboda irin muhimmanci da yake da shi ga kowanne musulmi gashi karankansa, littafine da ya shafi kowa-da-kowa mace da namiji, malami da maikoyo, sai na ba Allah zabi na kuma shawarci wasu daga cikin malamai masu daraja, sai kuma suka karfafi wannan tunani, to fa daga nan ne sai tunanin ya karfafa (na) himmatu akan fara wannan aiki mai matukar muhimmanci na wadannan darussa masu matukar muhimmanci, sai kuma na nemi izinin malamimmu kuma mahaifimmu sai kuma ya ban izinin, yana madalla da wannan aiki.

Wannan littafi dudda yake ba wani mai yawa bane sai dai ya tara ilimi na addinin musulunci, kama daga abinda ya shafi tauhidi da kuma hukunce hukunce, da kuma irin abinda ya kamata musulmi ya dabi'antu da su na halayya da kuma ladubban musulunci, an kuma kammala shi wannan littafine da tsoratarwa akan shirka da nau'ukan lefuffuka, sai littafin ya kasance a yadda ake so musulmi ya kasance a tauhidi da kuma ibada da halayya da kuma tsari, wannan littafin ya cancanci sunansa na 'Muhimman darussa ga dukkanin al'umma'.

Hakika na sanyawa wannan littafi sharhin da yake ba mai tsawoba balle ya gajiyar ba kuma tsukakkeba ballantana bayanan su kasa gamsarwa, domin hakan ya kasance taimakone bayan datarwar Allah, kuma (ya kasance) wani abune da za'a koma gareshi mai matukar sauki ga dukkan wanda ya yi nufin yin bayanin littafi kama daga cikin limaman masallatai, ko kuma mai gida a gidansa, ko dalibi a unguwarsu ko a garinsu. Hakika na yi kokarin na hada kowanne bayani da dalilinsa gwargwadon iko, na sanya masa sunan '' Hukunce hukunce masu zurfi a muhimman darussa''. Tabbas babban Shehun malami Abdulaziz dan Baz ya yi tsokaci a wasu wurare, sai na sanya layi a kasan wuraran domin a gane su.

Daga karshe ina fata daga dukkan dan'uwa mai daraja da ya duba wannan littafi da kada ya yi mana rowar fadakarwa da tsokaci, shi fa mutum daya yake, amma yana da yawa in ya hadu da 'yan-uwansa.

Wannan kenan, ina kuma rokon Allah da sunayansa kyawawa da siffofinsa madaukaka da ya anfanar da wannan littafin da kuma wanda ya yi sharhin littafin, ya kuma sanya wannan aiki nawa na yi shi domin shi, kamar kuma yadda na ke rokonsa da ya sakanka da alheri ga mawallafi (asalin) littafin da wanda ya yi sharhin littafin ya sakanka da mafi kyawun sakamako, ya kuma sanya mu da kuma shi cikin gida aljanna Firdausi madaukakiya tare da Annabawa da Siddikai da Shahidai, lalle shi majibincin hakane kuma mai iko akan hakan. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu Muhammadu da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.

Abdulaziz dan Daud Fayiz.

Zulfa,

21/5/1415. (27/10/1992)

Darasi Na Farko

Suratul Fatiha Da Abinda Ya Sawwaka Na gajerun Surori.

Daga suratul Zalzalah zuwa suratun Nas za'a dinga biyawa (mutane) kuma ana gyara musu suna haddace su kuma ana musu bayanin abinda ya wajaba su fahimta.

Shehun malami Abdulaziz bin Baz Allah ya ji kansa da gafara, kuma Allah ya anfanar da shi musulunci da musulmai kuma Allah ya saka masa da alheri, yana cewa a darasin farko daga cikin (littafinsa) muhimman darussa ga al'umma baki daya, cewar ya kamata akan kowanne musulmi – gwargwadon ikonsa- da ya koyi (karatun) Suratul Fatiha da kuma abinda ya sawwaka na kananan surori domin koyon karatun suratul fatiha wajibi ne a kan kowanne musulmi, domin sallah bata yiwuwa ga dukkan wanda bai karanta Fatiha ba, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisi ingantacce daga Mustafa –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-.

To ya zama wajibi ga dukkan mai koyar da mutane wadannan surori da yabi wadannan matakai:

Matakin Farko: Ya karanta musu idan sun kasance basu iya karatu ba, idan kuma sun riga su n iya karatu to sai ya wuce zuwa mataki na biyu.

Mataki Na Biyu: Gyaran karatu, sannan sai ya wuce zuwa mataki na:

Mataki Na Uku: Haddatar da su wadannan surori, haddatar da su din ta wadannan hanyoyi:

- Malamin ya karanta ayoyin a hankali da kuma rerawa, kuma ya nemi mahalarta su maimaita tare da shi har su haddace su, sannan bayan haka sai ya yi sharhin ayoyin sharhin da yake fayyatacce gwargwadon fahimtar masu sauraro, sannan bayan haka sai ya ciro wadansu hukunce hukunce daga cikin ayoyin da ya karanta.

Misalin wannan a cikin suratul fatiha ya bayyana musu lalle karatun fatiha rukunice daga cikin rukunan sallah, saboda fadin Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-:

''Babu sallah ga dukkan wanda bai karanta Fatiha ba''. Bukhari da Muslim da Tirmizi suka ruwaito shi.

Hakanan kuma ya ce da su: Lalle yana daga cikin ka'idoji da aka yi ittifaki akan su tsakanin magabata da kuma jagorori magabata; Yin Imani da sunayan Allah da kuma siffofinsa, kuma lalle su suna tabbatar da abinda Allah ya tabbatarwa da kansa, ko kuma Ma'aikinSa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tabbatar masa, kuma su na korewa Allah abinda ya korewa kansa, ko kuma Ma'aikinsa –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yakore masa ba tare da karkatarwa ba kuma ba tare da kamantawa ba, haka kuma ba tare da kamanceceniya ba, kuma ba tare ta kwatantawa ba. Haka kuma ya basu bayanin; Lalle ibada gamamman suna ne da ya tara dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi na zantuttuka da ayyuka na zahiri da kuma na badini.

- Akwai daga cikin hukunce hukuncen da ke cikin Suratul Bakara wanda ya kamata malami ya yi bayanin su; Lalle ita ibada idan shirka ta hadu da ita to fa (ita ibadar) ta baci, haka kuma ya bayyana musu cewar lalle ya wajaba akan kowanne musulmi ya dinga tuna ranar sakamako, kuma lalle rashin manta wannan ranar mai girman gaske yana taimakawa mutum akan ayyukan daidai da kuma nisantar abubuwan da suke haramun.

- To haka zai dinga a sauran surorin yana fada suna fada, kuma yana gyara musu karatun, da kuma haddatar da su da kuma yi sumu bayanin fayyatacce, Allah ne masa ni.

Darasi Na Biyu:

Shaidawa da babu abinbautawa da gaskiya sai Allah, kuma lalle annabi Muhammad Ma'aikin Allah ne.

(شَهَادَةُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اَللهِ)

Malami zai yiwa mutane bayanin ma'anonita (ita Kalmar shahadar) da kuma bayanin sharuddan ( ita لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهِ), kuma ma'anarta (Laa ilaa ha) tana kore dukkan abinda ake bautawa komabayan Allah, (Illallaha) tana tabbatar da ibada ga Allah shikadai bashi da abokin tarayya.

Mawallafin (wannan littafin) Allah madaukain sarki ya yi masa rahama a wannan darasi na:

(شَهَادَةُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اَللهِ ﷺ‬)

Muna matan mu bi abinda muke bukata kamar haka:

Da Farko: Matsayinta.

Wadannan Kalmar shahada biyu su ne rukuni na farko daga cikin rukunan musulunci, hakika dan Umar Allah ya kara musu yarda ya ruwaito daga Annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce:

''An gina musulunci akan abubuwa biyar; Shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai Allah, da kuma (Shaidawa da) lalle (Annabi) Muhammad manzan Allah ne, da kuma tsayar da sallah da bayar da zakkah, da azumin watan Ramadan, da kuma ziyarar dakin Allah mai alfarma (aikin Hajji) ga wanda ya sami iko''.

Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

To ita Kalmar shahada ita ce tushen addini, ita ce kuma katangar addini mai karfin gaske, ita ce farkon wajibin da ke kan bayi, kuma karbar dukkanin ayyuka ya takaitune akan fadarta da kuma aiki da abinda take karantarwa.

Na Biyu: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah. Bai halatta ka (fassara ta) da; ba mahalicci sai Allah, ko ba abinda yake samamme sai Allah ko babu mai azurtawa sai Allah, saboda wadansu al'amurra:

- Lalle su kafiran kuraishawa sun kasance ba sa musun ba mahalicci sai Allah,

Amma duk da haka hakan bai anfane sub a. kuma su suna fahimtar ma'anarta, sabo da haka ne ma suka yi wa Manzon Allah ﷺ‬ musu alokacin da yace musu su fadi:

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ

Wato ''babu abin bautawa da cancanta sai Allah''.

Wato muna matukar mamaki a wannan lokacin dangane da wadanda suke fadin:

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ

Wato ''Ba abin bautawa da acancanta sai Allah''. Amma ba su san ma'anarta ba, suna bautawa Allah tare da sun hada bautar da wasu kamar; waliyyai, da wadanda suke cikin kabari, kuma ka ji suna cewa mu akan tauhidi muke, ga Allah kadai ake neman taimako.

Na Uku: Rukunan Ta.

Ita Kalmar shahada tana da rukunai guda biyu:

Na farko: Korewa, wato idan ka ce: لا إله wato “ba abin bauta da cancanta''.

Na biyu: Tabbatarwa, wato idan kace: إلا الله wato '' Sai Allah kadai''.

To idan kace 'babu abin bauta da cancanta' ka kore dukkan wani nau'I na bauta ga wanin Allah. Idan kace; 'Sai Allah' to anan ka tabbatar da dukkanin nau'ukan bauta ga Allah shi kadai kuma ba shi da abokin tarayya.

Na Hudu: Falalar Ta.

Ita Kalmar shahada tana da falala mai tarin yawa, kuma tana da babban matsayi a wurin Allah, duk wanda ya fade ta da gaske to Allah zai shigar da shi aljanna, duk kuma wanda ya fadeta ba da gaske ba to ta tsare jininsa da kuma dukiyarsa anan duniya a lahira kuma hisabinsa na wurin Allah madaukakin sarki, kuma hukuncinsa shine hukuncin munafukai.

Ita wannan kalma lafuzanta takaitattune, harufanta kuma kadan ne, tana da saukin furtawa a harshe, ta na da nauyi a mizani.

Ita fa wannan Kalmar ta na da falala mai tarin yawa, babban malami Ibnu Rajab ya anbaci wani kaso mai yawa na wadannan falalar a wani littafinsa mai suna:

كلمة الإخلاص

Kuma ya bada dalilai akan kowacce falala, daga cikin wadannan falalar akwai:

- Ita ce 'Kudin aljanna' domin duk wanda karshen maganarsa لا إله إلا الله to ya shiga aljannah.

- Kuma ita tsirace daga wuta.

- Tana sanya mutum ya sami garar Allah.

- Ita ce tafi kowanne kyakkyawan aiki kyau.

- Tana kankare zunubbai.

- Itace ta ke sadar da bawa ga Allah madaukakin sarki.

- Ita ce Kalmar da Allah ya ke gasgata wanda ya fade ta.

- Ita ce abinda Annabawa suka fi fadi.

- Ita ce mafificin zikiri.

- Ita ce mafificin ayyuka.

- Ita ce aka fi nin-ninkawa wanda ya fade ta ladan fadinta da ya yi.

- Ita ce ta ke daidai da 'yanta bayi da mutum ya yi.

- Ita ce ta ke kasancewa (hirzi) wato kariya ga shaidanu.

- Ita ce ta ke amintar da mutum daga kadai takar kabari.

- Ita ce ta ke amintar da mutum daga firgicin ranar saka mako.

- Ita ce kuma babban take na muminai idan sun tashi daga kaburburan su.

- Daga cikin falalarta ita ce fa take budewa wanda ya fadeta kofofin aljannah guda bakwai ya shiga ta wacce ya ga dama.

- Daga cikin falalarta fa dukkanin wadanda suka fade ta to ko da sun shiga wuta saboda wadansu laifuffuka da suka yi to ba za su dawwama a wutar ba, wata rana za su fita daga cinkin ta.

Na Biyar: Shaidawa cewa; Lalle Annabi Muhammadu manzan Allah ne.

kuma hakan ya kunshi:

(1) Gasgatashi cikin duk abinda ya bada labari.

(2) Yi mishi biyayya akan duk umarnin da yabayar.

(3) Nisantar duk abinda ya hana kuma ya tsawatar.

(4) Kuma kada a gabatar da maganar wani ko waye akan maganarsa ﷺ‬.

Na Shida: A sani, cewa; duk wanda ya shaida da babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma lalle (Annabi) Muhammadu bawan Allah ne kuma manzan shi ne, kuma lalle (Annabi) Isah bawan Allah ne kuma manzan Allah ne, kuma zancan Allah ne da ya jefa ta ga (Nana) Maryamu, kuma rai ne daga wurin Allah, kuma (ya shaida) aljanna gaskiyace, wuta ma gaskiya ce, kamar yadda Ubadatu dan Samit ya ruwaito hakan daga wurin ma'aikin Allah ﷺ‬, to Allah zai shigar da shi aljanna abisa gwargwadon aikin sa.

Amma Sharuddan لا إله إلا الله wato Kalmar shahada to su ne;

(1) Sanin ma'anarta wanda ke kore jahiltar ma'anarta.

(2) Tabbas wanda ke kore kokwanto.

(3) Kadaita Allah da ita wanda hakan yake kore shirka da Allah.

(4) Fadarta da gaske wanda hakan ke kore karya.

(5) Son ta wanda yake kore ki.

(6) Sallamawa wanda ke kore bari.

(7) Karba wanda ke kore kin karba.

(8) Kafircewa duk wanda ake bautawa wanda ba Allah ba.

Malamai sun anbaci cewa lalle ita wannan kalma ta tauhidi tana da sharudda guda bakwai, wasu cikin malaman sun lissafa su takwas, kamar yadda malam ya lissafa su anan.

Na Farko: Sanin ma'anarta. Idan bawa ya san lalle Allah maigirma da daukaka shi ne kadai abin bautawa da cancanta, kuma bautawa waninsa ba ibada bace, kuma ya yi aiki da hakan to wannan ya yi aiki da ma'anarta. Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿فَٱعلَم أَنَّهُ لَا إِلَهَ إِلَّا ٱللَّهُ ﴾ محمد: ١٩

Ma'ana: ''To ka sani, lalle yadda yake babu abin bautawa da cancanta sai Allah''. Suratu Muhammad, aya ta: 19. Kuma Allah madaukakin sarki yace:

﴿ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلحَقِّ وَهُم يَعلَمُونَ٨٦﴾ الزخرف: ٨٦

Ma'ana: ''Saidai kawai wadanda suka shaida da gaskiya kuma suna sane''. Suratuz Zukhruf, aya ta: 86.

Kuma ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((مَنْ مَاتَ وَهُوَ يَعْلَمُ أَنَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ دَخَلَ اَلْجَنَّةَ)) رواه مسلم وأحمد

Ma'ana: ''Duk wanda yam utu yana sane da babu abin bautawa da cancanta sai Allah (to wannan) ya shiga aljanna''. Muslim ne da Ahmad suka ruwaito shi.

Na Biyu: Yakini (Tabbas) wanda ke kore kokwanto. Yana zama wajibi ga dukkan wanda ya fadi wannan kalma ya zamana zuciyarsa ta tabbatar da hakan, kuma ya kudurce ingancin abinda yake fadi na cewa Allah madaukakin sarki shi ne kadai wanda ya cancanta a bauta masa, kuma ya kudurce rashin ingancin bautar da aka yi ta ga wanin Allah, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَٱلَّذِينَ يُؤمِنُونَ بِمَا أُنزِلَ إِلَيكَ وَمَا أُنزِلَ مِن قَبلِكَ وَبِٱلأخِرَةِ هُم يُوقِنُونَ٤﴾البقرة: ٤

Ma'ana: ''Kuma wadanda suke yin Imani da dukkan abinda aka saukar maka, da kuma dukkan abinda aka saukar kafin kai, kuma dangane da lahira su masu yakini ne (tabbas)''. Suratul Bakarah, aya ta: 4.

Kuma kamar yadda aka ruwaito daga Abuhuraira t lalle Annabi ﷺ‬ ya ce:

((مَنْ لَقِيتَ خَلْفَ هَذَا اَلْحَائِطِ يَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ مُسْتَيْقِنًا بِهَا مِنْ قَلْبِهِ فَبِشِّرْهُ بِالْجَنَّةِ)). رواه مسلم.

Ma'ana: '' Duk wanda ka hadu da shi a bayan wannan lambun yana shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai Allah, yana da yakinin hakan tun daga zuciyarshi to ka yi mishi bishara da aljannah''. Muslim ne ya ruwaito shi.

Na Uku: Karba wanda ke kore kin karba. Abinda ake nufi shi ne zai karbi dukkanin abinda wannan Kalmar take hukuntawa zai karbane daga zuciyarsa da kuma harshensa. Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿قُولُواْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَينَا ﴾ البقرة: ١٣٦

Ma'ana: '' Ku ce; mun yi Imani da Allah, kuma mun yi Imani da dukkan abinda aka saukar mana''. Suratul Bakarah, aya ta: 136.

Na Hudu: Sallamawa wanda ke kore bari. Hakan kuwa shi ne ya sallama ga wannan Kalmar mai girman gaske, wato sallamawa da mika wuya, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَمَن أَحسَنُ دِينا مِّمَّن أَسلَمَ وَجهَهُ لِلَّهِ وَهُوَ مُحسِن وَٱتَّبَعَ مِلَّةَ إِبرَهِيمَ حَنِيفا وَٱتَّخَذَ ٱللَّهُ إِبرَهِيمَ خَلِيلا١٢٥﴾ النساء: ١٢٥

Ma'ana: ''Babu wanda ya fi kyawun addini kamar wanda ya mika fuskar sag a Allah alhali yana mai kyautatawa''. Suratun Nisa'i, aya ta: 125.

Kuma Allah madaukakin sarki ya ce:

﴿وَمَن يُسلِم وَجهَهُ إِلَى ٱللَّهِ وَهُوَ مُحسِن فَقَدِ ٱستَمسَكَ بِٱلعُروَةِ ٱلوُثقَى وَإِلَى ٱللَّهِ عَقِبَةُ ٱلأُمُورِ٢٢﴾ لقمان: ٢٢

Ma'ana: ''Duk wanda ya sallama fuskar sa ga Allah (kadai) yana mai kyautatawa to hakika ya yi ruko da igiya mai karfi''. Suratu Lukman, aya ta: 22.

Na Biyar: Gaskgatawa. Wannan ko ya na kasancewa ta hanyar yin Imani na gaskiya, hakanan ma akidah ta gaskiya, kuma mai gaskiya a maganganunsa kuma mai gaskiya a Da'awarsa, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَكُونُواْ مَعَ ٱلصَّدِقِينَ١١٩﴾ التوبة: ١١٩

Ma'ana: '' Yaku wadanda suka yi Imani ! ku ji tsoron Allah kuma ku kasance tare da masu gaskiya''. Suratut Taubah, aya ta: 119.

Na Shida: Yi domin Allah, wannan yana faruwane ta yadda dukkanin maganganu da mutum zai fada da ayyukan da zai yi ya zamana ya yi su ne domin Allah kadai, kuma dan neman yardarsa babu wani sofane, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَمَا أُمِرُواْ إِلَّا لِيَعبُدُواْ ٱللَّهَ مُخلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ ﴾ البينة: ٥

Ma'ana: ''Ba'a umarce su da wani abu ba sai domin su bautawa Allah suna masu tsarkake addini dominsa''. Suratul Bayyinah, aya ta: 5.

Kuma kamar yadda y azo a hadisi ingantacce daga Abuhurairata t daga Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((أَسْعَدُ اَلنَّاسِ بِشَفَاعَتِي مَنْ قَالَ: لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ خَالِصًا مِنْ قَلْبِهِ)) رواه البخاري وأحمد

Ma'ana: ''Wanda ya fi kowa cancantar cetona shi ne wanda ya ce: ''Babu abin bautauwa da gaskiya sai Allah, kuma ya fadi hakan tun daga zuciyarsa domin Allah''. Bukhari da Ahmad ne suka ruwaito.

Na Bakwai: So, wato ya so wannan kalma (ta shahada) da kuma duk abinda ta yi nuni akan shi da kuma duk abinda ta kunsa, sai ya so Allah ya kuma so Manzan shir, ya kuma gabatar da son su akan duk wani da yake so, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَتَّخِذُ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَندَادا يُحِبُّونَهُم كَحُبِّ ٱللَّهِ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ أَشَدُّ حُبّا لِّلَّهِ ﴾ البقرة: ١٦٥

Ma'ana: '' Kuma akwai daga cikin mutane wanda yake rikon wani wanda ba Allah ba kishiyoyi ga Allah suna son su kamar yadda suke son Allah, wadanda suka yi Imani suna tsananta so Allah''. Suratul Bakrah, aya ta: 165.

Na Takwas: Kafircewa duk wani abin bauta da ba Allah ba. Kamar yadda ya zo daga ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((مَنْ قَالَ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ وَكَفَرَ بِمَا يُعْبَدُ مِنْ دُونِ اَللهِ حَرُمَ مَالُهُ وَدَمُهُ وَحِسَابُهُ عَلَى اَللهِ))

رواه مسلم.

Ma'ana: ''Duk wanda ya ce: Babu abinda bauta da cancanta sai Allah kuma ya kafircewa dukkan abinda ake bautawa koma bayan Allah to dukiyarsa da jininsa sun haramta, kuma hisabinsa yana ga Allah''. Muslim ne ya ruwaito shi.

Darasi Na Uku: Rukunan Imani.

Su ne kuwa: Ka yi Imani da Allah, da Mala'ikunsa, da Littattafansa, da Manzanninsa, da Ranar karshe, da kuma kaddara alherinsa da dacinsa duk daga wurin Allah ne mai girma da daukaka.

Dalili akan haka shine shahararran hadisin nan na mala'ika Jibrilu lokacin da ya tambayi Annabi ﷺ‬ dan gane da Imani, sai (Ma'aikin Allah ﷺ‬ ) ya ce:

((اَلإِيمَانُ أَنْ تُؤْمِنَ بِاللهِ وَمَلاَئِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ وَالْيَوْمِ اَلآخِرِ وَتُؤْمِنَ بِالْقَدْرِ خَيْرِهِ وَشَرِّهِ))

رواه مسلم

'' Imani, shi ne ka yi Imani da Allah da mala'ikunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar karshe da kaddara ta alheri ko ta sharri''. Muslim ne ya ruwaito shi.

Abu Na Farko: Imani da Allah.

Imani da Allah madaukakin sarki yana kunshe ne da abubuwa guda hudu:

(1)Imani da akwai Allah din. Hakika kyakkyawan tunani da nagartaccan hankali

da tsaftacacciyar shari'a da kyakkyawan motsi duk sun tabbatar da akwai Allah madaukakin sarki.

Amma tabbatuwar akwai Allah ta hanyar kyakkyawan tunani shi ne; cewa dukkan wani da aka halicce shi to an dabi'antar da shi akan ya yi Imani da wanda ya halicce shi, ba tare da ya yi wani dogon tunani ba ko an karantar da shi ba, kamar yadda ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((مَا مِنْ مَوْلُودٍ إِلاَّ وَيُولَدُ عَلَى اَلْفِطْرَةِ فَأَبَوَاهُ يُهَوِّدَانِهِ أَوْ يُنَصِّرَانِهِ أَوْ يُمَجِّسَانِهِ)) رواه البخاري ومسلم.

Ma'ana: ''Babu wani da aka Haifa face ana haihuwarsa ne akan kyakkyawan tafarki, sai iyayansa su yahudantar da shi ko nasarantar da shi ko su majusantar da shi''. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Amma nagartaccan hankali ya yi nuni akan cewa lalle akwai Allah ta cewa; lalle wadannan halittu na da, da na yanzu ba makawa tabbas akwai wanda ya halicce su kuma ya samar da su, domin babu yadda za'a yi rai ta samar da kanta, babu kuma yadda za'a yi ace kawai haka ta samu.

Amma ta fuskar nagartacciyar shari'a kuwa ta tabbatar da akwai Allah madaukakin sarki, domin dukkanin littattafan da Allah ya aiko suna furtawa kuma suna bada labara akan haka, kuma mafi girmansu kuma mafi falalar su shi ne Alkur'ani mai girma, haka nan kuma dukkanin manzanni kuma mafi falalarsu kuma cika makinsu kuma shugabansu shi ne Annabi Muhammad ﷺ‬ dukkanin su kuma sun yi nuni akan hakan kuma sun bayyana.

Amma ta fuskar kyakkyawan motsi kuwa ya tabbata akwai Allah mai girma da daukaka ta fuskoki guda biyu:

Ta farko: Lalle mu muna ji kuma muna ganin amsa addu'ar masu addu'a, da kuma agaji ga wadanda suke cikin matsanancin hali, wanda hakan yake nuni karara akan lalle akwai Allah madaukakin sarki.

Ta Biyu: Lalle ayoyin Annabawa da ake kiransu da Mu'ujiza kuma mutane suke ganinsu ko suke jin labarinsu kwakkwaran daliline akan tabbas akwai mahalicci kuma mai tsara al'amura kuma mai jujjuya duniya wanda yake shi ne kuwa Allah madaukakin sarki.

(2) Imani da cewar shikadaine mahalicci: wato cewa shi kadai ne mahalicci babu wanda ya yi tarayya da shi, kuma ba mai taimako in ba shi ba. Idan akace Ubangiji to shine wanda yake da halitta da mallaka da al'amari, saboda haka babu wani mahalicci in ba Allah ba, kuma ba wani mamallaki in ba Shi ba, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿ أَلَا لَهُ ٱلخَلقُ وَٱلأَمرُ ﴾ الأعراف: ٥٤

Ma'ana: '' Ku saurara! Dukkanin halitta ta sa ce, da kuma al'amari''. Suratul A'araf, aya ta: 54.

Kuma Allah yana cewa:

﴿ ذَلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُم لَهُ ٱلمُلكُ وَٱلَّذِينَ تَدعُونَ مِن دُونِهِ مَا يَملِكُونَ مِن قِطمِيرٍ١٣﴾ فاطر: ١٣

Ma'ana: '' Wannan fa shi ne Allah wanda yake Ubangijinku, dukkanin halitta ta sa ce, wadanda ku ke kira koma bayansa basa iya mallakar zaran igiyar da ke cikin dabino''. Suratu Fadir, aya ta: 13.

(3) Imani da shikadaine abin bauta: cewar shi kadai ne abin bauta da cancanta ba shi da wani abokin tarayya, idan aka ce (الإله) to ma'anarsa (المألوه) wato wanda ake bautawa don ya cancanta ana son sa kuma ana girmama shi, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَإِلَهُكُم إِلَه وَحِد لَّا إِلَهَ إِلَّا هُوَ ٱلرَّحمَنُ ٱلرَّحِيمُ١٦٣﴾ البقرة: ١٦٣

Ma'ana: ''Kuma abin bautarku abin bauta ne daya, babu wani abinbautawa da cancanta sai shi, mai yawan rahama mai yawan jinkai''. Suratul Bakara, aya ta: 163.

Kuma Allah yana cewa:

﴿لَقَد أَرسَلنَا نُوحًا إِلَى قَومِهِ فَقَالَ يَقَومِ ٱعبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّن إِلَهٍ غَيرُهُ ﴾ الأعراف: ٥٩

Ma'ana: '' Hakika mun aika Nuhu zuwa ga mutanan sa sai ya ce: Ya ku mutanena ku bautawa Allah ba ku da wani abin bauta (da cancanta) bayan Sa''. Suratul A'araf, aya ta:59.

(4)Imani da sunayansa da Siffofinsa, wato tabbatar da abinda da Allah ya tabbatarwa da kansa a cikin littafinsa, ko a cikin karantarwar Ma'aikin Allah ﷺ‬ na sunaye da kuma siffofi ta yadda suka dace da shi Allah madaukakin sarki, ba tare da jirkita su ba, ba kuma share su ba, ba kuma tare da an bayyana yadda suke ba, ba kuma tare da an kwatanta yadda suke ba, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿ لَيسَ كَمِثلِهِ شَيء وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلبَصِيرُ١١﴾ الشورى: ١١

Ma'ana: ''Babu wani abu da ya yi kama da shi, kuma shi mai ji ne kuma mai gani ne''. Suratus Shurah, aya ta:11.

Anfanin da ake samu ga dukkan wanda yayi Imani da Allah.

(1) Tabbatar da kadaita Allah madaukakin sarki, ta yadda babu yadda zuciya za ta rataya ga wanin Allah, dan kauna ko don tsoro, kuma ba zai taba bautawa wanin Allah ba.

(2) Cikar son Allah madaukakin sarki, da kuma girmamashi ta hanyar sunayansa kyawawa da kuma siffofinsa madaukaka.

(3) Tabbatar da bauta masa ta hanyar bin abin da ya yi umarni da kuma nisantar abin da ya hana.

Na Biyu: Imani Da Mala'iku.

Abinda ake nufi da mala'iku: Wata duniya ta gaibu da aka halicce su da haske suna bautawa Allah madaukakin sarki ne kadai.

Ba su da wani abu na halittar Allah ko kuma na su ma ayi musu bauta, Allah ya halicce su ne daga haske, kuma ya yi musu baiwa ta su sallama wa umarninsa sallamawa ta gaba daya, da kuma (baiwa) ta karfi wurin zartar da abinda ya sa su, su wadansu al'umma ne masu tarin yawa, babu wanda ya san adadin su sai Allah madaukakin sarki.

Imani da mala'iku ya kunshi abubuwa guda hudu:

(1) Imani da cewar akwai su.

(2) Imani da sunan duk wanda muka san sunansa, kamar Jibrilu, amma wand ba mu san sunansa (ta hanya ingantacciya ba) to za mu yi Imani da shi ne a dunkule.

(3) Imani da abinda muka sani (ta hanya ingantacciya) na siffofinsu.

(4) Imani da abinda muka sani (ta hanya ingantacciya) na ayyukansu da suke yi da umarnin Allah madaukakin sarki, kamar mala'ikan mutuwa wanda aka wakilta shi akan karbar rayuka.

Na Uku: Imani Da Littattafai.

Abinda ake nufi da wadannan littattafai sune wadanda Allah madaukakin sarki ya saukar da su ga manzanninsa domin hakan ya zama rahama ne ga bayi, kuma shiriya ga re su, domin hakan ya kai ga sun rabauta duniya da lahira.

Abinda Imani da littattafai ya kunsa:

(1) Imani da cewar saukar da su ya kasance ne daga wurin Allah madaukakin sarki, kuma hakan gaskiya ne.

(2) Imani da sunan littafin da muka san sunansa (ta hanya ingantacciya) kamar Alkur'ani Wanda aka saukar da shi ga Annabi Muhammadr, da Attaurah da aka saukar da ita ga Annabi musa Alaihissalam.

(3) Gasgata dukkan labaran da aka ji a cikin su, kamar labaran da aka ji daga Alkur'ani da kuma labaran da ba'a canza su ba ko ba'a karkatar da su ba na littattafan da suka gabata.

(4) Aiki da dukkanin hukunce-hukncen da ba'a share su ba, da kuma yarda da su da sallamawa mun fahinci hikimar da ke ciki ko ba mu fahimci hikimar ba, dukkanin littattafan da suka gabata an share hukuncehukncen su da littafin Alkur'ani mai girma, Allah madaukakin sarki na cewa:

﴿وَأَنزَلنَا إِلَيكَ ٱلكِتَبَ بِٱلحَقِّ مُصَدِّقا لِّمَا بَينَ يَدَيهِ مِنَ ٱلكِتَبِ وَمُهَيمِنًا عَلَيهِ ﴾المائدة: ٤٨

Ma'ana: ''Kuma mun saukar maka da littafi cike da gaskiya mai gasgatawane ga littafin da ya gabace shi kuma mai hukunci ne akan shi''. Suratul Ma'aidah, aya ta:48.

Fa'idojin da Imani da littattafai ya kunsa:

(1) Sanin yadda Allah ya ke kula da bayin shi, ta yadda ya saukarwa da kowacce al'aumma littafin da zai shiryar da su.

(2) Sanin hikimomin Allah madaukakin sarki a shari'arsa, ta yadda ya shar'antawa ko wacce al'umma abinda ya yi daidai da halayansu, kamar yadda Allah yake cewa:

﴿ لِكُلّ جَعَلنَا مِنكُم شِرعَة وَمِنهَاجا ﴾ المائدة: ٤٨

Ma'ana: ''A kowanne abu mun sanya muku shari'a da kuma tsari''. Suratul Ma'aidah, aya ta: 48.

Na Hudu: Imani Da Manzanni.

Manzo shi ne wanda aka yiwa wahayin shari'a daga cikin mutane kuma aka umarceshi da ya isar da ita. Farkon manzanni kuwa shi ne Annabi Nuhu na karshensu kuma shi ne Annabi Muhammad tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya.

Babu wata al'umma da Allah madaukakin sarki bai tura mata manzo ba da sabuwar shari'a ba zuwa ga mutanan sa, ko Annabi da ya yi masa wahayi na shari'ar manzannin da suka gabace shi domin ya jaddadata, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَلَقَد بَعَثنَا فِي كُلِّ أُمَّة رَّسُولًا أَنِ ٱعبُدُواْ ٱللَّهَ وَٱجتَنِبُواْ ٱلطَّغُوتَ ﴾ النحل: ٣٦

Ma'ana: ''Hakika mun tayar a cikin kowacce al'umma manzo (abinda muka aike da shi shine ya ce): Ku bautawa Allah kuma ku nisanci dagutu''. Suratun Nahl, aya ta:36.

Kuma Allah madaukakin sarki ya ce:

﴿ وَإِن مِّن أُمَّةٍ إِلَّا خَلَا فِيهَا نَذِير٢٤﴾ فاطر: ٢٤

Ma'ana: ''Babu wata al'umma face sai maigargadi ya wuce musu''. Suratu Fadir, aya ta:24.

Manazanni fa mutanene suna ciki 'yan adam suma halittar Allah ne, ba su da wani abu na hakkin Ubangiji ko na Allantaka, su ma irin abinda da yake samun mutum yana samun su, kamar rahma da mutuwa da bukatuwar abinci da abin sha, da sauran su.

Abubuwan da Imani da manzanni ya kunsa:

(1) Imani da cewar manzancin su gaskiya ne daga wurin Allah madaukakin sarki, duk wanda ya kafircewa manzancin daya daga cikin su to hakika ya kafircewa dukkan su, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿كَذَّبَت قَومُ نُوحٍ ٱلمُرسَلِينَ١٠٥﴾الشعراء: ١٠٥

Ma'ana: ''Hakika mutanan Annabi Nuhu sun karyata manzanni''. Suratush Shu'ara'i, aya ta: 105.

(2) Imani da sunan dukkan wanda muka san sunansa (ta hanya ingantacciya) daga cikinsu, kamar; Annabi Muhammad da Annabi Ibrahim da Musa da Isah da Nuhu tsira da amincin Allah ya tabbata a garesu, wadannan kuma sune manyan a cikin manzanni wato (Ulul Azmi).

Amma duk wand aba mu san sunansa (ta hanya ingantacciya ba) to zamu yi Imani da shi a jumlace, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَلَقَد أَرسَلنَا رُسُلا مِّن قَبلِكَ مِنهُم مَّن قَصَصنَا عَلَيكَ وَمِنهُم مَّن لَّم نَقصُص عَلَيكَ ﴾ غافر: ٧٨

Ma'ana: ''Hakika mun aiko da manzanni tun kafin kai daga cikin su akwai wadanda muka baka labarin su, kuma akwai daga cikinsu wadanda bamu baka labarin su ba''. Suratu Ghafir, aya ta: 78.

(3) Gasgata dukkan abinda ya inganta na labarikan su.

(4) Aiki da shari'ar Annabin da aka aika musu shi daga cikin su, shi ne kuwa cikamakinsu Annabi Muhmmadu ﷺ‬.

Fa'idon Imani da manzanni;

(1) Sanin rahamar Allah madaukakin sarki ga bayinsa da irin yadda yake kula da su, ta yadda ya aiko musu manzanni domin shiryar da su zuwa ga hanyar Allah kuma mikakkiyar hanya, domin su yi musu bayanin yadda za su bautawa Allah.

(2) Yadda za'a godewa Allah akan irin wannan babbar ni'ima.

(3) Son manzanni –tsira da amincin Allah su tabbata a gare su-, da kuma girmama su da yabansu akan irin abinda ya dace da su, domin su manzannin Allah madaukakin sarki ne, kuma sun tsaya wurin yi masa bauta da kuma isar da manzancinsa, da kuma yin nasiha ga bayinsa.

Na Biyar: Imani Da Ranar Lahira.

Ranar lahira itace ranar tashin alkiyama, ranar da Allah zai tayar da mutane a cikinta domin lissafa ayyukan da kowa ya yi da kuma bada sakamakon aikin, an kirata da ranar karshe ne domin babu wata rana a bayanta.

Abinda Imani da ranar karshe ya kunsa:

(1) Imani da tashi daga kabari, shi ko wannan tashin gaskiyane Alkur'ani da Hadisi da ijima'in musulmai duk sun tabbatar da hakan.

(2) Imani da lissafa ayyuka da kuma sakamako, za'a lissafawa mutum aikinsa kuma a bashi sakamako akan hakan, hakika Kur'ani da Hadisi da ijima'in musulmai dun sun tabbatar da hakan.

(3) Imani da cewar akwai aljanna a kwai kuma wuta, kuma su ne makoma na har abada ga al'umma.

Yana shiga cikin Imani da ranar tashin alkiyama dukkanin abinda zai kasance bayan mutuwa, kamara:

(1) Tambayar kabari (2) Azabar kabari ko ni'imar da ke cikin sa.

Faidojin Imani da ranar tashin alkiyama:

(1) Jin tsoron aikata laifuffuka ko yarda da miyagun ayyukan don jin tsoron azabar Allah a wannan ranar.

(2) Kaunar aikata ayyukan alheri da kwadayin hakan, domin ladan da za'a bayar a wannan ranar.

(3) Lallashin mutum mumini don kada ya damu dangane da abinda ya rasa annan duniya saboda abinda yake fatan samu na ni'imar ranar lahira da kuma lada.

Na Shida: Imani Da Kadddara.

Kaddara: Wato kaddarawar da Allah madaukain sarki ya yi wa dukkanin abinda yake wanzanje yadda ilimin Ubangiji ya gabatu akan sa, kuma hikimar Allah ta zartar da hakan.

Abubuwan da Imani da kaddara ya kunsa:

(1) Imani da cewar Allah madaukakin sarki ya san kowanne abu a dunkule ya kuma sanshi a fayyace, yasan wannan tuntuni, sannan wannan abun yana da alakane da ayyukan Allah ne ya sanshi ko yana da alaka da ayyukan bayi, duk Allah ya sansu.

(2) Imani da cewa Shi Allah madaukakin sarki ya ruba ta hakan acikin allon da ya kiyaye komai (Lauhul Mahfuz).

(Akan hakane Allah madaukakin sarki yake cewa:

﴿أَلَم تَعلَم أَنَّ ٱللَّهَ يَعلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَاءِ وَٱلأَرضِ إِنَّ ذَلِكَ فِي كِتَبٍ إِنَّ ذَلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِير الحج ٧٠

Ma'ana: '' Ashe bakasan lalle Allah yana sane da dukkan abinda ke sama da kasa ba? Lalle wannan yana cikin littafi, lalle hakan a wurin Allah abu ne mai sauki''. Suratul Hajji, aya ta:70.

Kuma ya zo a hadisin Amru dan As, Allah ya kara musu yarda, ya ce: na ji ma'aikin Allah ﷺ‬ yana cewa:

((كَتَبَ اَللهُ مَقَادِيرَ اَلخْلَاَئِقِ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ اَلسَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِخَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ)) رواه مسلم.

Ma'ana: ''Allah ya rubuta dukkan abinda ya kaddarawa halittu tun kafin ya halicci sammai da kassai da shekaru dubu hamsin''. Muslim ne ya ruwaito shi).

(3) Imani da cewar dukkanin abubuwan da suke kasancewa basa kasancewa saida ganin daman Allah madaukakin sarki, shin abubuwan da suke da alaka da ayyukan Shi Allah ne, ko ayyukan da suke da alaka da halittu ne, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَرَبُّكَ يَخلُقُ مَا يَشَاءُ وَيَختَارُ ﴾ القصص: ٦٨

Ma'ana: ''Kuma Ubangijinka yana halittar abinda yaga dama kuma yana zaba''. Suratul Kasasi, aya ta:68.

(4) Imani da cewar dukkanin kasantattun abubuwanan halittar Allah madaukakin sarki da asalin halittar ta su da siffofinsu da motsin su, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa:

﴿ٱللَّهُ خَلِقُ كُلِّ شَيء وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيء وَكِيل٦٢﴾ الزمر: ٦٢

Ma'ana: ''Allah shi ne mahaliccin kowanne abu, kuma shi wakiline akan komai''. Suratuz Zumar, aya ta:62.

Imani da kaddara yana da fai'doji masu tarin yawa:

(1) Dogaro ga Allah alokacin da zaka aikata kowanne abu, ta yadda babu yadda zata dogara akan wannan abun kadai, domin kowanne abu da kaddarar Allah madaukakin sarki yake.

(2) Mutum ba zai mamakin kansa ba alokacin da ya sami wani abinda yake so, domin samun wata ni'ima daga wurin Allah madaukakin sarki ne, na abinda Allah ya kaddara mishi na sabubban alheri da kuma samun nasara, alokacin da mutum ya yi mamakin kansa sai ya manta godewa Allah akan wannan ni'imar.

(3) Natsuwa da kwanciyar hankali na abinda suke gudana akanka/ki na cewar Allah ya kaddarasu wanda yake Shi ke da mulkin sammai da kassai, kuma Shi yana nan ba makawa, kamar yadda Allah madaukakin sarki yake cewa:

﴿مَا أَصَابَ مِن مُّصِيبَة فِي ٱلأَرضِ وَلَا فِي أَنفُسِكُم إِلَّا فِي كِتَب مِّن قَبلِ أَن نَّبرَأَهَا إِنَّ ذَلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِير٢٢ لِّكَيلَا تَأسَواْ عَلَى مَا فَاتَكُم وَلَا تَفرَحُواْ بِمَا ءَاتَىكُم وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ مُختَال فَخُورٍ٢٣﴾ الحديد: ٢٢ – ٢٣

Ma'ana: ''Babu wata masifa da zata auku a bayan kasa ko a karankanku face tana cikin littafi (lauhul mahfuz) tun kafin mu halicceta, lalle hakan a wurin Allah abune mai sauki. Domin kada ku yi bakin ciki akan abinda ya kufce muku kuma kada ku yi murna akan abinda ya baku, Allah ba ya son dukkan mai yawan takama mai alfahari''. Suratul Hadid, aya ta: 22-23.

Tabbas kungiyoyi biyu sun bace kan abinda ya shafi kaddara:

(1) Jabariyyah: wadanda suka ce 'lalle bawa an tilasta shi ne akan aikin da ya yi' domin ba shi da nifi kuma ba shi da iko.

(2) Kadariyyah: wadanda suka ce 'bawa ai yana cin gashin kansa ne a duk aikin da ya aikata ta bangaren nifi ne ko iko, ba tare da ganin daman Allah ba kuma ba tare da ikon Allah ba.

Sai suka yi musun cewa Allah ya kaddara abubuwa kuma ya sansu kafin su kasance. Dukkanin maganganun kungiyoyin biyu suna kan bata matuka.

Darasi Na Hudu: Karkasuwar Tauhidi.

(1) Tauhidin Uluhiyyah.

(2) Tauhidin Rububiyyah.

(3) Tauhidin Asma'u Was Sifat.

Tauhidi: Shi ne ((kadaita Allah da ibada)), yana da nau'uka guda uku;

Nau'i Na Farko: Tauhidin Rububiyyah. Shi ne mutum ya sani ya kuma kudurce a zuciyarsa cewa lalle Allah shi ne wanda yake da halitta bakidayanta kuma yake azurtawa yak e jujjuya al'amura. Wannan nau'i na tauhidi maguzawa sun tabbatar da shi amma bai shigar da su musulunci ba, dalili akan haka shi ne fadin Allah madaukakin sarki:

﴿وَلَئِن سَأَلتَهُم مَّن خَلَقَهُم لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُ فَأَنَّى يُؤفَكُونَ٨٧﴾ الزخرف: ٨٧

Ma'ana: ''Kuma tabbas idan ka tambaye su wa ye ya haliccesu wallahi za su ce Allah ne''. Suratuz Zukhruf, aya ta:87.

Nau'i Na Biyu: Tauhidin Asma'u Was Sifat. Shi ne a siffanta Allah da abinda ya siffanta kansa da shi a cikin littafinsa ko manzan shi ﷺ‬ ya siffanta shi da shi akan yadda ya dace da girmansa ma daukakarsa. Wannan nau'i wasu daga cikin mushirikai su yarda da shi, wasu kuma ba su yarda da shi don jahilci da kuma girman kai.

Nau'i Na Uku: Tauhidin Uluhiyyah. Shi ne kadaita Allah da bauta, shi kadai bas hi da abokin tarayya adukkanin nau'ukan ibada, kamar; so, tsoro, kauna, dogaro, addu'a, da wanin hakan na nau'ukan ibada. To wannan nau'i mshirikai sam bas u yarda da shi ba.

Nau'ukan Shirka:

- Babbar Shirka

- Karamar Shirka.

- Boyayyiyar Shirka.

To ita babbar shirka ta na sa dukkan aikin da mutum ya yi ya baci, kuma tana tabbatar da mai ita a wuta, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:

﴿ وَلَو أَشرَكُواْ لَحَبِطَ عَنهُم مَّا كَانُواْ يَعمَلُونَ٨٨﴾ الأنعام: ٨٨

Ma'ana: ''Inda sun yi shirka da duk abinda suka kasance suna aikatawa ya baci''. Suratul An'am, aya ta:88.

Kuma Allah madaukakiin sarki ya ce:

﴿مَا كَانَ لِلمُشرِكِينَ أَن يَعمُرُواْ مَسَجِدَ ٱللَّهِ شَهِدِينَ عَلَى أَنفُسِهِم بِٱلكُفرِ أُوْلَئِكَ حَبِطَت أَعمَلُهُم وَفِي ٱلنَّارِ هُم خَلِدُونَ١٧﴾ التوبة: ١٧

Ma'ana: '' Bai taba kasancewa ga mushirikai ace sun raya masallatan Allah alhalin suna shaidawa akarankansu da kafirci, wadanan ayyukansu sun baci, kuma a wuta su wadanda zasu dawwama ne''. Suratut Taubah, aya ta: 17

Kuma lalle duk wanda ya mutu yana shirka to Allah ba zai taba yafe masa ba, kuma aljanna ta haramta a gare shi, kamar yadda yadda Allah madaukakin sarki ya ce:

﴿إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَغفِرُ أَن يُشرَكَ بِهِ وَيَغفِرُ مَا دُونَ ذَلِكَ لِمَن يَشَاءُ ﴾ النساء: ٤٨

Ma'ana: ''Lalle Allah bay a gafartawa in akai masa tarayya, yana gafarta abinda bai kai shirk aba ga wanda ya so''. Suratun Nisa'i, aya ta:48.

Kuma Allah daukakin sarki ya ce:

﴿ إِنَّهُ مَن يُشرِك بِٱللَّهِ فَقَد حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيهِ ٱلجَنَّةَ وَمَأوَىهُ ٱلنَّارُ وَمَا لِلظَّلِمِينَ مِن أَنصَار﴾ المائدة٧٢

Ma'ana: ''Lalle shi fa duk wanda ya yi wa Allah shirka to hakika Allah ya haramta masa aljanna kuma makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka''. Suratul Ma'idah, aya ta:72.

Yana daga cikin nau'ukan shirka:

Rokon matattu da gumaka da neman agajin su, da yi musu alwashi da yi musu yanka da makamantan haka.

Amma ita shirka karama ita ce: abinda ya tabbata a Kur'ani da Hadisi na anbatonsa da sunan shirka, amma baya cikin jinsin babbar shirka, kamar yin riya a wadansu ayyuka, kamar rantsuwa da wanin Allah, kamar fadin; Haka Allah ya so haka wane ya so', da makamantan haka, saboda fadin ma'aikin Allah ﷺ‬:

((أَخْوَفُ مَا أَخَافُ عَلَيْكُمُ اَلشِّرْكُ اَلأَصْغَرُ، فَسُئِلَ عَنْهُ فَقَالَ: اَلرِّيَا)).

رواه الإمام أحمد والطبراني والبيهقي.

Ma'ana: '' Mafi tsoron abinda nake ji muku tsoronsa shi ne karamar shirka, sai aka tambaye shi dangane da ita, sai ya ce: Riya,(wato yi don agani). Ahmad da Dabarani da Baihaki suka ruwaito.

Da kuma fadinsa ﷺ‬:

((مَنْ حَلَفَ بِشَيْءٍ دُونَ اَللهِ فَقَدْ أَشْرَكَ)). رواه الإمام أحمد.

Ma'ana: '' Duk wanda ya rantse da wani abu to ya yi shirka''. Ahmad ne ya ruwaito shi.

Abu Dauda da Tirmizi sun ruwaito daga hadisin Abdullahi dan Umar –Allah ya kara masu yarda- daga ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

(( مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اَللهِ فَقَدْ كَفَرَ أَوْ أَشْرَكَ)) رواه أبو داود والترمذي.

Ma'ana: '' Duk wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka''.

Kuma Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((لاَ تَقُولُواْ مَا شَاءَ اَللهُ وَشَاءَ فُلاَنٌ، وَلَكِنْ قُولُواْ: مَا شَاءَ اَللهُ ثُمَّ شَاءَ فَلاَنٌ)) أخرجه أبو داود.

Ma'ana: '' Kada ku ce; haka Allah ya so haka wane ya so, saidai ku ce: Haka Allah ya so sannan haka wane ya so''. Abu Dauda ne ya ruwaito.

Wannan nau'i ba ya sa ace mutum ya yi riddah, kuma ba ya sa mai shi ya tabbata a wuta har abada, saidai yana kore wa mai shi cikar tauhidi.

Nau'i Na Uku: wanda yake shi ne buyayyiyar shirka, dalilin wannan kuwa shine fadin ma'aikin Allah ﷺ‬:

((أَلاَ أُخْبِرُكُمْ بِمَا هُوَ أَخْوَفُ عَلَيْكُمْ عِنْدِي مِنَ اَلْمَسِيحِ اَلدَّجَّالِ؟ قَالُواْ: بَلَى،. قَالَ: اَلشِّرْكُ اَلْخَفِيُّ... يَقُومُ اَلرَّجُلُ فَيُصَلِّي فَيُزَيِنُ صَلاَتَهُ لِمَا يَرَى مِنْ نَظَرِ اَلرَّجُلِ إِلَيْهِ)). رواه الإمام أحمد.

Ma'ana: '' Shin ba na baku labarin abinda na fi muku tsoron shi ba sama da jujal?, sai suka ce: Eh. Sai ya ce: Boyayyiyar shirka…. Mutum ne zai ta shi ya kawata sallar sa saboda yadda ya ga wani yana kallonsa''. Ahmad ne ya ruwaito shi.

Kuma zai iya yiwuwa a kasa shirka zuwa ka shi biyu kadai; babba da karama.

Amma boyayyiyar shirka ta na game dukkanin wadannan, tana kasancewa a babbar shirka kamar shirker da munafukai suke yi, domin su suna boye munana akidun su ne, su na kuma bayyana musulunci don again a ce su musulmai ne kuma don jin tsoron kada a gane su. Haka kuma yana kasance wa a shirka karama kamar riya, kamar yadda ya zo a hadisin Mahmud dan Labid mutumin madina da ya gabata da kuma hadisin Abu Said da ya gabata… Allah shi ne mai datarwa.

Darasi Na Biyar: Shikashikan Musulunci

Su ne guda biyar:

1. Shaidawa da 'Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lalle Annabi Muhammad manzon Allah ne.

2. Tsayar da Sallah.

3. Bayar da zakkah.

4. Azumin watan Ramadan.

5. Ziyartar dakin Allah mai alfarma ga dukkan wanda ya sami iko, (aikin Hajji).

Bayan da shehin malami ya kammala bayani akan karkasur tauhidi da kuma rarrabuwar shirka, to zanyu malam ya shiga Magana akan shikashikan musulunci guda biyar. Hakika ya tabbata a ingantaccan hadisin da baban Abdirrahaman Abdullahi dan Umar Allah ya kara musu yarda, ya ce: na ji ma'aikin Allah ﷺ‬ yana cewa:

((بُنِيَ اَلإِسْلاَمُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اَللهِ، وَإِقَامِ اَلصَّلاَةِ، وَإِيتَاءِ اَلزَّكَاةِ، وَحَجِّ اَلْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ)). رواه البخاري ومسلم.

Ma'ana: ''An gina musulunci akan abubuwa biyar ne: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammad manzan Allah ne da tsaida sallah da bayar da zakkah da aikin hajji da azumin watan Ramadan''. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Sai ya kamanta musulunci da gini wanda baya tabbata sai akan turaku biyar babu gini muddinin ba'a sami wadannan turakun ba, sauran kuma abubuwan da suke dabi'une na musulunci sai suka zama kamar cikon ginin ne.

Da ya ce: "Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammad manzan Allah ne''. shi ne Imani da Allah da Manzanshi.

Aruwayar da Muslim ya ruwaito:

((عَلَى خَمْسٍ: عَلَى أَنْ تُوَحِّدَ اَللهَ عَزَّ وَجَلَّ))، وفي رواية: ((عَلَى أَنْ تُوَحِّدَ اَللهَ وَتَكْفُرَ بِمَا دُونَهُ)).

Ma'ana: ''Akan abubuwa biyar: Akan ka kadaita Allah mai girma da daukaka''. A wata riyawar kuma: ''Akan ka kadaita Allah, ka kuma kafircewa duk abinda ba Shi ba''.

Da ya ce: "da tsaida sallah''. Ya zo a ruwayar Muslim daga Jabir t ya ce:

((بَيْنَ اَلرَّجُلِ وَبَيْنَ اَلْكُفْرِ وَالشِّرْكِ تَرْكُ اَلصَّلاَةِ)) رواه مسلم والترمذي.

Ma'ana: ''Tsakanin mutum da kuma shirka (shi ne) barin sallah''. Muslim da Tirmizi suka ruwaito shi.

Hakanan ma a hadisin Mu'azu t daga Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((رَأْسُ اَلأَمْرِ اَلإِسْلاَمُ وَعَمُودُهُ اَلصَّلاَةُ)). رواه الترمذي وابن ماجه.

Ma'ana: ''Kan dukkanin al'amari shi ne musulunci ginshikin sa kuma sallah''.

Abdullahi dan Shakik ya ce: ''Sahabban Ma'aikin Allah ﷺ‬ ba sa ganin wani abu da yake barinsa kafirce ne kamar sallah''.

Da ya ce: '' bayar da zakkah''. Ita ce shisshike ta uku cikin shikashikan musulunci, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوةَ وَٱركَعُواْ مَعَ ٱلرَّكِعِينَ٤٣﴾البقرة: ٤٣

Ma'ana: '' Kuma ku tsaida sallah ku bayar da zakkah''. Suratul Bakarah, aya ta:43.

Kuma Allah madaukakin sarki ya ce:

﴿وَمَا أُمِرُواْ إِلَّا لِيَعبُدُواْ ٱللَّهَ مُخلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوةَ وَيُؤتُواْ ٱلزَّكَوةَ وَذَلِكَ دِينُ ٱلقَيِّمَةِ٥﴾ البينة: ٥

Ma'ana: ''Kuma ba'a umarce su ba sai domin su bautawa Allah su na masu tsarkake addini domin shi, kuma su na tsaida sallah sun a bayar da zakkah, yin hakan (shi ne) mikakken addini''. Suratul Bayyinah, aya ta:5.

Da ya ce: '' da azumin watan Ramadan'' shi ne rukuni na hudu cikin rukunan addinin musulunci. Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيكُمُ ٱلصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبلِكُم لَعَلَّكُم تَتَّقُونَ١٨٣﴾ البقرة: ١٨٣

Ma'ana: '' Ya ku wadanda su ka yi Imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi akan wadanda su ka gabace ku domin hakan zai sa ku ji tsoron Allah''. Suratul Bakarah, aya ta: 183.

Da ya ce: “da aikin Hajji" to wannan kuma shi ne rukuni na biyar daga cikin rukunan aikin Hajji. Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿ وَلِلَّهِ عَلَى ٱلنَّاسِ حِجُّ ٱلبَيتِ مَنِ ٱستَطَاعَ إِلَيهِ سَبِيلا وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَنِيٌّ عَنِ ٱلعَلَمِينَ٩٧﴾

آل عمران: ٩٧

Ma'ana: “Allah ya dorawa mutane aikin Hajji ga dukkan wanda ya sami iko, wandako ya kafirta to lalle Allah mawadaci ne da barin halittu''. Suratu Ali Imrana, aya ta: 97.

Wannan hadisin babban tushe ne kuma mai girman gaske akan fahimatar musulunci.

Darasi Na Shida: Sharuddan Sallah

Su ne kuma guda tara:

(1) Musulunci. (2) Hankali. (3) Wayau

(4) Tsarki. (5) Gusar da najasa. (6) suturce al'aura.

(7) Shigar lokaci. (8) Fuskantar alkibla. (9) Niyyah.

Bayan da malam ya anbaci shika-shikan musulunci guda biyar a darasi na biyar ya yi daidai da ya anbaci sharuddan sallah anan, domin ita sallah ita ce ta fi kowanne rukuni cikin rukunan musuluncin nan in banda Kalmar shahada, kuma ita sallah bata inganta (ace ta yi) sai bayan an cika sharudda, shi ya say a anbaci sharuddan anan.

Farkon sharuddan su ne: Musulunci da hankali da wayau. Sallah ba ta inganta idan kafiri ya yi ta. Haka kuma ba ta inganta daga mahaukaci domin babu wani wuni hukunci akan shi. Haka kuma sallah ba ta inganta daga jinjiri saboda abinda aka fahimta na hadisin:

((مُرُّواْ أَبْنَاءَكُمْ بِالصَّلاَةِ لِسَبعِ)). رواه أبو داود والترمذي وابن ماجة.

Ma'ana: ''Ku umarci yaranku da sallah idan suka kai (shekara) bakwai''. Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah su ka ruwaito.

Sharadi Na Hudu: Tsarki tare da iko, saboda fadin ma'aikin Allah ﷺ‬:

((لاَ تُقْبَلُ صَلاَةٌ بِغَيْرِ طهُورٍ)). رواه مسلم وأبو داود والترمذي.

Ma'ana: “Ba'a karbar sallah ba tare da tsarki ba". Muslim ne da Abu Dawud da Tirmizi su ka ruwaito.

Sharadi Na Biyar: Shigar Lokaci: Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿أَقِمِ ٱلصَّلَوةَ لِدُلُوكِ ٱلشَّمسِ ﴾ الإسراء: ٧٨

Ma'ana: “Ka tsayar da sallah idan rana ta karkace". Suratul Isra'i, aya ta:78

An karbo daga Umar t: “ Sallah tana da wani lokaci da Allah ya sanya mat aba ta inganta sai a ashi". Shi ne hadisin da mala'ika jibrilu a lokacin da ya yi wa Annabi ﷺ‬ limancin salloli biyar, sannan sai mala'ika Jibrilun ya ce:

(( مَا بَيْنَ هَذَيْنِ وَقْتٌ)) رواه أحمد والنسائي.

Ma'ana: “Abinda ke tsakanin wadannan lokutan biyu shi ne lokacin sallah)). Ahmad da Nasa'i su ka ruwaito.

Sharadi Na Shida: Suturta al'aura idan akwai iko da abinda ba ya siffanta jiki, saboda fadin Allah madaukakin sarki:

﴿يَبَنِي ءَادَمَ خُذُواْ زِينَتَكُم عِندَ كُلِّ مَسجِد ﴾ الأعراف: ٣١

Ma'ana: “ Ya ku 'ya'yan Adam! Ku riki adonku a kowanne masallaci".

Suratul A'araf, aya ta:31.

Da kuma fadinsa ﷺ‬:

((لاَ يَقْبَلُ اَللهُ صَلاَةَ حَائِضٍ إِلاَّ بِخِمَارٍ)). رواه الترمذي وأبو داود. وحديث سلمة بن الأكوع قال: قلت: يا رسول الله إني أكون في الصيد وأصلي في القميص الواحد، قال: نَعم وَازْرُرْهُ وَلَوْ بِشَوْكَةٍ)) صححهما الترمذي.

Ma'ana: “Allah bai karbar sallar macen da ta farsa al'ada sai ta yi lillibi". Tirmizi da Abu Dawud ne suka ruwaito. Haka kuma hadisin Salimatu dan Ak'wa'a ya ce: na ce: Ya Ma'aikin Allah “Idan na kasance a halin farauta ina yin sallah da riga guda daya ne, sai ya ce: Eh, Ka daureta ko da da igiya ne''. Tirmizi ya inganta hadisai biyun.

Ibnu Abdulbarri ya hikaito ijima'in malamai akan dukkan wanda ya yi sallah tsirara kuma yana da ikon ya suturce jikinsa sai bai yi hakan ba to sallah batacciyace.

Sharadi Na Bakwai: Nisantar Da Najasa, daga jiki da kuma tufafi da kuma wurin sallah, saboda fadin Allah madaukakin sarki:

﴿وَثِيَابَكَ فَطَهِّر٤﴾ المدثر: ٤

Ma'ana: “Kuma tufafinka ka tsarkake shi". Suratul Mudassar, aya ta:4.

Da kuma fadinsa ﷺ‬ ga Asama'u akan jinin al'ada:

((تَحُكُّهُ ثُمَّ تَقْرِصِهُ بِالْمَاءِ ثُمَّ تَنْضَجُهُ ثُمَّ تُصَلِّي فِيهِ)). متفق عليه.

Ma'ana: “Za ta kankareshi (idan ya bushe) sannan ta wanke shi da ruwa, sannan ta shanya shi sannan sai ta yi sallah da shi". Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.

Sharadi Na Takwas: Fuskantar Alkibla, saboda fadin Allah madaukakin sarki:

﴿ فَوَلِّ وَجهَكَ شَطرَ ٱلمَسجِدِ ٱلحَرَامِ ﴾ البقرة: ١٤٤

Ma'ana: “ To ka juyar da fuskarka tsakiyar masallaci mai alfarma".

Suratul Bakarah, aya ta:144.

Sharadi Na Tara: Niyyah. Saboda fadin zababben Allah ﷺ‬:

((إِنَّمَا اَلأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ)). رواه البخاري ومسلم.

Ma'ana: “Abin sani kawai dukkan ayyuka na ibada sai da niyyah". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

To wannan ne sharuddan sallah suka cika, Allah ne shi ne masani.

Darasi Na Bakwai: Rukunan Sallah.

Su kuma rukunan sallah goma-sha-hudu ne, su ne:

(1) Tsayawa idan akwai iko. (2) Kabbarar Harama. (3) Karatun Fatiha

(4) Ruku'u. (5) Daidaituwa bayan tasowa daga ruku'u.

(6) Yin Sujjada akan gababuwa bakwai. (7) Tasowa daga sujjadar.

(8) Zama tsakanin sujjadu biyu. (9) Natsuwa a dukkanin ayyukan sallah.

(10) Jerantawa tsakanin rukunai. (11) Yin tahiyar karshe.

(12) Zama domin tahiyar. (13) Salati ga Manzan Allahr. (14) Sallama biyu.

Bayanda shehun malamimmu – Allah ya yi masa rahama- ya yi Magana akan abinda ya shafi sharuddan sallah a darasin da ya gabata, domin su sharuddan sallah su na gabatuwa ne kafin sallar, sai ya yi daida da ya anbaci rukunai anan domin rukunan suna tafiya ne tare da sallar.

Rukunin Farko daga cikin rukunan sallah: Tsayuwa idan akwai iko, saboda fadin Allah madaukakin sarki:

﴿ وَقُومُواْ لِلَّهِ قَنِتِينَ٢٣٨﴾البقرة: ٢٣٨

Ma'ana: “ Kuma ku tsaya domin Allah kuna masu biyayyah". Suratul Bakarah, aya ta:238.

Da kuma fadinsa ﷺ‬ a Hasin Imran: ((صَلِّ قَائِمَا)).

Ma'ana:“Ka yi Sallah a tsaye". Bukhari da Tirmizi suka ruwaito shi. Kuma malamai sun yi ijima'i akan haka.

Rukuni Na Biyu: Kabbarar Harama, saboda fadinsa ﷺ‬:

((مِفْتَاحُ اَلصَّلاَةِ اَلطُّهُورُ، وَتَحْرِيمُهَا اَلتَّكْبِيرُ، وَتَحْلِيلُهَا اَلتَّسْلِيمُ)) رواه الخمسة إلا النسائي.

Ma'ana: “Mabudin sallah shi ne tsarki, kuma abinda yake haramta (halas) ita ce: Kabbara, abinda kuma yake halastawa ita ce: sallama". Mutane biyar suka ruwaito inbada Nasa'i. Tirmizi ya ce; Shi ne abu mafi iganci a wannan babin. Kuma saboda fadinsa ﷺ‬ ga wanda ya munana sallarsa:

((إِذَا قُمْتَ إِلَى اَلصَّلاَةِ فَأَسْبِغِ اَلوُضُوءَ ثُمَّ اَسْتَقْبَلِ اَلْقِبْلَةَ فَكَبِّرْ)). متفق عليه.

Ma'ana: “Idan ka tashi zaka je sallah to ka kyautata alwala, sannan ka fuskanci alkibla sai ka yi kabbara". Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.

Rukuni Na Uku: Karatun Fatiha, saboda hadin Ubadata dan Samitt lalle ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((لاَ صَلاَةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ اَلْكِتَابِ)). رواه السبعة.

Ma'ana: “Babu sallah ga dukkan wanda bai karanta Fatiha ba". Mutane bakwai suka ruwaito shi.

Rukuni Na Hudu: Ruku'i. Saboda fadin Allah madaukakin sarki:

﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱركَعُواْ ﴾ الحج: ٧٧

Ma'ana: “ Ya ku wadanda suka yi Imani, ku yi ruku'i". Suaratul Hajji, aya ta:77.

Kamar yadda bayanin ruku'in ya tabbata a hadisin Bukhari da Muslim, daga hadisin Abuhurairah t a hadisin wanda yake munana sallar sa, hakika ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce da shi:

((ثُمَّ اَرْكَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ رَاكِعًا)) رواه البخاري ومسلم.

Ma'ana: “Sannan ka yi ruku'I har sai ka natsu a ruku'in". Bukhari da Muslin ne suka ruwaito shi.

Kuma saboda abinda malamai biyar suka ruwaito daga Abdullahi dan Mas'ud mutumin madina, cewa lalle Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((لاَ تُجْزِئُ صَلاَةٌ لاَ يُقِيمُ فِيهَا اَلرَّجُلُ صُلْبَهُ فِي الرُّكُوعِ وَالسُّجُودِ)).

Ma'ana: “Sallar mutumin da ba ya tsayar da gadon bayansa a ruku'i da sujjada ba ta yi ba".

Rukuni Na Shida: Yin Sujjada da gabobi bakwai; saboda fadin Ma'aikin Allah ﷺ‬:

((أُمِرْتُ أَنْ أَسْجُدَ عَلَى سَبْعَةِ أَعْظُمٍ: عَلَى اَلْجَبْهَةِ، وَأَشَارَ بِيَدِهِ عَلَى أَنْفِهِ، وَالْيَدَيْنِ، وَالرُّكْبَتَيْنِ، وَأَطْرَافِ اَلْقَدمَيْنِ)). متفق عليه.

Ma'ana: “An umarce ni da in yi sujjada a kan gabbai bakwai; akan goshi, sai ya nuna hancinsa da kafafuwa da gwiwowi biyu da gyafan yatsun kafafuwa biyu". Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito.

Rukuni Na Bakwai: Zama tsakanin sujjadu biyu, saboda fadin Ma'aikin Allah ﷺ‬ ga mutumin da ya munana sallarsa:

((ثُمَّ اَرْفَعْ حَتَّى تَعْتَدِلَ جَاِلسًا)). رواه البخاري ومسلم.

Ma'ana: “Sannan ka dago har sai ka daidaita a zaune". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. Saboda kuma fadin da Nana Aisha – Allah ya kara mata yarda- ta yi; Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya kasance idan ya dago kansa daga sujjada ba ya sake komawa sujjadar har sai ya daidaita a zaune''. Muslim ne ya ruwaito shi.

Rukuni Na Takwas: Daidaituwa a sujjada, saboda fadin da ma'aikin Allah ﷺ‬ ya yi ga wanda munana sallar sa:

((ثُمَّ اَرْفَعْ حَتَّى تَعْتَدِلَ جَاِلسًا)). رواه البخاري ومسلم.

Ma'ana: “Sannan ka dago har sai ka natsu a zaune".

Bukari da Muslim ne suka ruwaito.

Rukuni Na Tara: Natsuwa a dukkanin ayyukan sallah, saboda fadin da ma'aikin Allah ﷺ‬ ya yi ga wanda ya munana sallar shi:

((ثُمَّ اَرْكَعْ حَتَّى تَطْمَئِنَّ راَكِعًا)) رواه البخاري ومسلم، وَكَانَ اَلنَّبِيُّ ﷺ‬ يُطْمَئِنُّ فِي صَلاَتِهِ، وَيقولُ: ((صَلُّواْ كَمَا رَأَيْتُمُونِي أُصَلِّي)). رواه البخاري.

Ma'ana: “Sannan ka yi ruku'i har sai ka natsu a ruku'in". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi. Kuma Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya kasance ya na natsuwa a cikin sallar shi ya na kuma cewa: “Ku yi sallah kamar yadda kuka ganni nake sallah". Bukhari ne ya ruwaito.

Rukuni Na Goma: Jeranto wadannan rukunan.

Rukuni Na Goma Sha Daya: Tahiyar karshe.

Rukuni Na Goma Sha Biyu: Zama domin tahiyar.

(dalili kan rukuni na 11-12) fadin Ma'aikin Allah ﷺ‬:

((إِذَا جَلَسَ أَحَدُكُمْ فِي اَلصَّلاَةِ فَلْيَقُلْ: اَلتَّحِيَّاتُ للهِ، وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا اَلنَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكَاتُهُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اَللهِ اَلصَّالِحِينَ...." الخ الحديث متفق عليه.

Ma'ana: “Idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: 'Tsarkakan gaisuwa na Allah ne, da kuma salloli da kyawawan zantuttuka, amincin Allah ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkar sa, amincin Allah ya tabbata a garemu ya kuma tabbata ga bayin Allah na gari….' Har zuwa karshe. Wannan hadisi Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Rukuni Na Goma Sha Uku: Yin salati ga Ma'aikin Allah ﷺ‬ a tahiyar karshe, saboda hadisin Ka'ab dan Ujrah t alokacin da suka tambayi Ma'aikin Allah ﷺ‬ dangane da yadda ake yi mishi salati sai yace; Ku ce:

((اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ)). رواه السبعة.

Ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka yi dadin tsira ga (Annabi) Muhammad da kuma iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi salati ga (Abbabi) Ibrahim da kuma iyalan (Annabi) Ibrahim, lalle kai abin yabo ne kuma mai girma. Ya Allah Ubangiji ka yi dadin albarka ga (Annabi) Muhammad da kuma iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da kuma iyalan (Annabi) Ibrahim, lalle kai abin yabo ne kuma mai girma". Mutane bakwai suka ruwaito shi.

Rukuni Na Goma Sha Hudu: Yin salati ga ma'aikin Allah ﷺ‬ da kuma yin sallama biyu, saboda fadinsa ﷺ‬: “Kuma abinda yake halatta ta shine sallama". Da kuma fadin Nana Aisha –Allah ya kara mata yarda- a siffar sallar Ma'aikin Allah ﷺ‬:

“Ya kasance yana cika sallah da sallama, don ita sallama bayani ne na mutum ya fita daga sallah, ita ce kammaluwar sallah kuma alamace ta an idar da ita".

Darasi Na Takwas: Wajibabbun Sallah.

Su kuma takwas ne.

(1) Dukkannin kabarbari in banda kabbarar harama. (2) Da kuma fadin 'Allah ya amsawa dukkan wanda ya gode masa, ga liman da wanda yake sallah shi kadai. (3) Da fadin: Ya Ubangijin mu dukkanin godiya ta kace, ga kowa da kowa.

(4)Da fadin: Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mai girma, a cikin ruku'i. (5) Da fadin; Tsarki ya tabbata ga Ubangina madaukaki, wannan a sujjada. (6) Da fadin; Ya Allah ka gafarta mini a tsakanin sujjadu biyu. (7) Tahiyar farko (8) Zaman domin tahiyar.

A wannan darasin mawallafin wannan littafi ya fara Magana akan abinda ya shafi wajibabbun sallah, bayan da ya yi bayani akan rukunan sallah, kuma sai ya fara gabatar da rukunan, kafin wajiban domin su rukunai sun fi wajibai karfi, domin su wadannan wajiban sujjadar rafkannuwa ta na gyarasu idan mutum ya bari ne da rafkannuwa, to amma shi rukuni idan mutum ya bari tokan lalle sallar ta baci da rafkannuwa ya bari ko da ganganci.

Wajibi Na Farko: cikin wajibabbun sallah, shi ne dukkanin kabarbari in banda kabbarar harama domin ita rukuni ce kamar yadda bayani ya gabata, da kuma bayanin Abdullahi dan Mas'ud:

“Na ga Annabi ﷺ‬ ya na kabbara a kowacce dagowa da kuma kowacce sunkuyawa, da kuma kowacce tsayuwa da kuma kowanne zama". Ahmad da Nasa'i da Tirmizi, kuma ya inganta shi.

Wajibi Na Biyu: fadin 'Allah ya amsawa dukkan wanda ya gode masa, ga liman da wanda yake sallah shi kadai. Saboda hadisin Abuhurairah t “Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya kasance yana kabbara aduk lokacin da ya fara sallah, sannan kuma ya yi kabbara lokacin da zai yi ruku'i, sannan yace: 'Allah ya na jin dukkan wanda ya yabe shi', adaidai lokacin da yake dago gadon bayansa daga ruku'i, sannan kuma ya ce adaidai lokacin yana tsaye: “Ya Ubangijimmu dukkan godiya taka ce''. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Wajibi Na Uku: fadin; Ya Ubangijimmu dukkanin godiya taka ce, ga kowa-da-kowa (Liman da mamu da wanda yake sallah shi kadai).

Wajibi Na Hudu: Fadin ;Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mai girma, a cikin ruku'i.

Wajibi Na Biyar: Fadin; Tsarki ya tabbata ga Ubangina madaukaki, wannan a sujjada, saudaya. Saboda fadin Huzaifah a hadisin; Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya kasance yana fada aruku'insa :

((سُبْحَانَ رَبِّيَ اَلْعَظِيمِ))

Ma'ana: ''Tsarki ya tabbata ga Ubangijina mai girma".

A sujjada kuma: ((سُبْحَانَ رَبِّيَ اَلأَعْلَى))

Ma'ana: “Tsarki ya tabbata ga Ubangijina madaukaki".

Wajibi Na Shida: fadin; “Ya Allah ka gafarta mini". A tsakanin sujjadu biyu. Saboda hadisin Huzaifah lalle Annabi ﷺ‬ ya kasance yana cewa a tsakanin sujjadu biyu:

((رَبِّ اِغْفِرْلِي، رَبِّ اَغْفِرْ لِي))

Ma'ana: “Ya Allah ka gafarta mini, Ya Allah ka ga farta mini". Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ibnu Majah.

Wajibi Na Bakwai: Tahiyar farko, saboda fadin zababban Allah ﷺ‬:

((إِذَا قُمْتَ فِي صَلاَتِكَ فَكَبِّرْ، ثُمَّ اَقْرَأْ مَا تَسَيَّرَ مِنَ اَلْقُرْآنِ، فَإِذَا جَلَسْتَ فِي وَسطِ اَلصَّلاَةِ فَاطْمَئِن وَافْتَرِشْ فَخِذَكَ اَلْيُسْرَى، ثُمَّ تَشَهَّدْ)) رواه أبو داود.

Ma'ana: “Idan ka tashi za ka yi sallah to ka yi kabbara, sannan ka karanta abinda ya sawwaka na Alkur'ani, idan kuma ka zauna a tsakiyar sallah to ka natsu kuma ka shinfida cinyarka ta hagu, sannan ka yi tahiya". Abu Dawuda ne ya ruwaito shi.

Wajibi Na Takwas: Zaman domin tahiyar farko, saboda hadisin dan Mas'ud da yake marfu'i:

“Idan ku ka zauna a bayan kowacce raka'a biyu to ku ce;

((اَلتَّحِيَّاتُ للهِ)) رواه أحد والنسائي:

Ma'ana: “Dukkanin dadadan gaisuwa na Allah ne". Ahmad da Nasa'i, su ka ruwaito shi.

Haka kuma alokacin da ma'aikin Allah ﷺ‬ ya manta zaman a sallar azahar ya yi sujjada biyu ne kafin ya yi sallama (wato kabaliyyah) maimakon zaman da ya manta.

Darasi Na Tara: Bayani Akan Tahiya.

Bayanin yadda ake tahiya shi ne kamar haka:

اَلتَّحِيَّاتُ للهِ، وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا اَلنَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكَاتُهُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اَللهِ اَلصَّالِحِيَن، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.

Ma'ana: “Tsarkakan gaisuwa na Allah ne, da kuma salloli da kyawawan zantuttuka, amincin Allah ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkar sa, amincin Allah ya tabbata a garemu ya kuma tabbata ga bayin Allah na gari, ina shaidawa babu abinda bautawa da cancanta sai Allah, kuma ina shaidawa lalle (Annabi) Muhammadu bawansa ne kuma manzansa ne.

Ya Allah Ubangiji ka yi dadin tsira ga (Annabi) Muhammad da kuma iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da kuma iyalan (Annabi) Ibrahim, lalle kai abin yabo ne kuma mai girma. Ya Allah Ubangiji ka yi dadin albarka ga (Annabi) Muhammad da kuma iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da kuma iyalan (Annabi) Ibrahim, lalle kai abin yabo ne kuma mai girma".

Sannan sai ya nemi tsarin Allah a tahiyar karshe daga; Azabar jahannama, da kuma azabar kabari, da fitinar rayuwa da kuma mutuwa, da fitinar jujal, sannan sai ya zabe irin addu'ar da yake so ya yi, musamman wacce aka ruwaito daga magabata, daga ciki akwai:

((اَللَّهُمَّ أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ وَشُكْرِكَ وَحُسْنِ عِبَادَتكَ، اَللَّهُمَّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي ظُلْمًا كَثِيرًا وَلاَ يَغْفِرُ اَلذُّنُوبَ إِلاَّ أَنْتَ فَاغْفِرْلِي مَغْفِرَةً مِنْ عِنْدِكَ، وَارْحَمْنِي إِنَّكَ أَنْتَ اَلْغَفُورُ اَلرَّحِيمُ)).

Ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka taimakamin akan anbatonka da gode maka da kyakkyan yi maka ibada, Ya Allah Ubangiji lalle ni na zalinci kaina zalinci kuma mai yawa kuma babu mai gafarta zunubai sai kai, ka gafarta mini gafara ta musamman daga wurinka, ka yi min rahama lalle kai ne mai yawan gafara kuma mai yawan jinkai".

An karbo daga Abdullahi dan Mas'udu t ya ce: Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya juyo ya kalece mu, sai ya ce:

Idan dayanku ya yi sallah to ya ce:

((اَلتَّحِيَّاتُ للهِ، وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا اَلنَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكَاتُهُ، اَلسَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اَللهِ اَلصَّالِحِيَن، أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اَللهُ ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ. ثُمَّ لِيَتَخَيَّرْ مِنَ اَلدُعَاءِ مَا أَعْجَبَهُ إِلَيْهِ فَيَدْعُو)). متفق عليه.

Ma'ana: “Tsarkakan gaisuwa na Allah ne, da kuma salloli da kyawawan zantuttuka, amincin Allah ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkar sa, amincin Allah ya tabbata a garemu ya kuma tabbata ga bayin Allah na gari, ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma ina shaidawa lalle (Annabi) Muhammadu bawansa ne kuma manzansa ne. Sannan ya zabi addu'ar da yake so ya yi))". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito, kuma hadisin Abdullahi dan Mas'ud shi ne mafi ingancin abinda aka ruwaito a tahiya.

An karbo daga baban Mas'ud mutumin badar ya ce: Bashiru dan Sa'ad ya ce: Ya ma'aikin Allah an umarce mu mu yi maka salati to yaya za mu yi mu yi maka salatin? Sa Ma'aikin Allah ya yi shiru, sannan sai ya ce: Ku ce:

((اَللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.)).

Ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka yi dadin tsira ga (Annabi) Muhammad da kuma iyalan (Annabi) Muhammad, kamar yadda ka yi salati ga (Abbabi) Ibrahim da kuma iyalan (Annabi) Ibrahim, lalle kai abin yabo ne kuma mai girma. Ya Allah Ubangiji ka yi dadin albarka ga (Annabi) Muhammad da kuma iyalan (Annabi) Muhammad, kmar yadda ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da kuma iyalan (Annabi) Ibrahim, lalle kai abin yabo ne kuma mai girma. Sai sallama kamar yadda kuka sani". Muslim ne ya ruwaito.

An karbo daga Abuhurairata t ya ce: Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((إِذَا تَشَهَّدَ أَحَدُكُمْ فَلْيَسْتَعِذْ بِاللهِ مِنْ أَرْبَعٍ، يَقولُ: اَللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابِ جَهَنَّمَ، وَمِنْ عَذَابِ اَلْقَبرِ، وَمِنْ فِتْنَةِ اَلْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، وَمِنْ فِتْنَةِ اَلْمَسِيحِ اَلدَّجَّالِ)). متفق عليه.

Ma'ana: “Idan dayanku ya yi tahiya to ya nemi Allah ya tsare shi daga abubuwa hudu, yace: “Ya Allah Ubangiji lalle ni ina neman tsarinka daga azabar jahannama, da kuma azabar kabari, da kuma fitinar rayuwa da ta mutuwa, da kuma fitinar jujal". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

An karbo daga Abubakar Siddiku t lalle shi yace wa Ma'aikin Allah ﷺ‬ koyamin addu'ar da zan dinga yi a salla ta, sai Ma'aikin Allah ﷺ‬ yace: Ka ce:

((اَللَّهُمَّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي ظُلْمًا كَثِيرًا وَلاَ يَغْفِرُ اَلذُّنُوبَ إِلاَّ أَنْتَ فَاغْفِرْلِي مَغْفِرَةً مِنْ عِنْدِكَ، وَارْحَمْنِي إِنَّكَ أَنْتَ اَلْغَفُورُ اَلرَّحِيمُ)). متفق عليه.

Ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka taimakamin akan anbatonka da gode maka da kyakkyan yi maka ibada, Ya Allah Ubangiji lalle ni na zalinci kaina zalinci kuma mai yawa kuma babu mai gafarta zunubai sai kai, ka gafarta mini gafara ta musamman daga wurinka, ka yi min rahama lalle kai ne mai yawan gafara kuma mai yawan jinkai".

Wannan hadisi daliline akan tabbatuwar yin addu'a a cikin sallah a ko'ina, yana daga cikin wuraran bayan tahiya, da kuma yin salati ga Annabi ﷺ‬, da kuma neman tsari daga abubuwa hudu, domin fadinsa ﷺ‬ a hadisin Abdullahi dan Mas'udu: “ Sannan ya zabi irin addu'ar da ya fi so ya yi". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Kuma a cikin wannan hadisin akwai halaccin yin addu'a a cikin sallah da lafazin da aka ruwaito addu'ar da ma wacce ba'a ruwaito ba, idan a cikin addu'ar babu abinda aka hana, a wani lafazi ma:

((ثُمَّ لِيَتَخَيَّرْ مِنَ اَلْمَسَأَلَةِ مَا شَاءَ)). رواه مسلم والنسائي وأبو داود.

Ma'ana: “Sannan ya zabi irin abinda yake so ya roka". Muslim ne da Nasa'i da Abu Dawud su ka ruwaito.

Darasi Na Goma: Sunnonin Sllah

1. Addu'ar bude sallah.

2. Dora tafin hannun dama akan na hagu akan kirji lokacin tsayuwa.

3. Daga hannaye yatsunsu a mike daura da kafada ko daura da kunnuwa a lokacin kabbarar farko, haka kuma lokacin zuwa ruku'i da lokacin tasowa daga ruku'in, da kuma lokacin da aka tashi daga tahiyar farko zuwa raka'a ta uku.

4. Abinda ya karu a nafarko a tasbihin ruku'i da sujjada.

5. Abinda ya karu dangane da abinda ka fada bayan ka taso daga ruku'i na: Ya Allah Ubangijimmu dukkanin godiya ta ka ce'.

6. Abinda ya karu akan guda daya na addu'ar neman gafara a tsakanin sujjadu biyu.

7. Sanya kai daidai da gadon baya a lokacin ruku'i.

8. Nesanta damatsa daga barin jiki, da kuma raba ciki da cinyoyi a lokacin sujjada.

9. Dage sangalin hannu daga kasa a lokacin sujjada.

10. Zaman da masallaci za yi akan kafarsa ta hagu da kuma kafe kafarsa ta dama a zaman tahiyar farko da kuma zama tsakanin sujjadu biyu.

11. Sanya mazaunin mutum a kasa da kuma kafe kafar dama alokacin zaman karshe.

12. Yin salati da kuma nemama ma'aikin Allah ﷺ‬ da kuma iyalanshi da Annabi Ibrahim da iyalanshi a tahiyar farko.

13. Yin addu'a a tahiyar karshe.

14. Bayyana karatu a sallar asuba, da kuma raka'o'I biyun farko na sallar magariba da kuma isha.

15. Sirranta karatu a sallar azahar da la'asar da ra'ar karshe ta magariba, da kuma biyun karshe sallar isha.

16. Karanta abinda ya karu na Alkur'ani bayan karatun fatiha, tare kuma da lura da sauran abinda ya zo na sunnonin sallah banda wadanda aka ambata.

Sunnonin sallah sun kasu zuwa naui biyu:

Naui Na Farko: Sunnoni na maganganu.

Naui Na Biyu: Sunnoni na ayyuka.

Kuma hakika mawallafin wannan littafin ya ambata a kundarin bakin, bawai ance wadannan sunnonin dole sai masallaci ya kawo su, saidai idan ya aikata su ko wasu daga cikin su to kan yana da lada, amma kuma idan ya barsu ko ya bara wasu daga ciki to babu laifi akansa kamar sauran sunnonin.

Saidai ya kamata ga dukkan mutum musulmi ya aikata su kuma ya tuna fadina zababban Allah ﷺ‬:

((عَلَيْكُمْ بِسُنَّتِي وَسُنَّةِ اَلْخُلَفَاءِ اَلرَّاشِدِينَ اَلْمَهْدِيِّينَ عَضُّواْ عَلَيْهَا بِالنَّوَاجِذِ)). رواه الترمذي وابن ماجه.

Ma'ana: “Ku rike sunnata da kuma sunnar Halifofi masu shiryarwa wadanda suke shiryayyu, ku rike ta da fikokin ku". Tirmizi da Ibnu Majah suka ruwaito.

Allah shi ne masani.

Darasi Na Sha-daya: Abubuwan Da Su Ke Bata Sallah.

Su ne kuma guda takwas.

1. Magana dagangan ya tuna cewar yana sallah yana sane ba'a Magana, to amman wanda ya manta ko bai sani ba, to anan sallarsa ba ta baci ba.

2. Dariya.

3. Cin abinci.

4. Shan abin sha.

5. Yayewar al'aura.

6. Karkacewa mai yawa daga fuskar alkibala.

7. Wasa mai yawa kuma a jere a cikin sallah.

8. Warwarewar tsarki.

Bayan da mawallafin wannan littafi ya kamala bayani kan abinda ya shafi sharuddan sallah da kuma rukunanta da wajibabbunta da kuma sunnoninta na magana da kuma na ayyuka, yanzu malam ya fara Magana kana abubuwan da suke bata sallah, domin mutum musulmi ya kasance ya kiyaye daga bata sallarsa daga barin aikata daya daga cikin abubuwan da suke bata sallah guda takwas, su ne kuma kamar haka:

Na Farko: Magana da gangan mutum yana sane ya san ba'a yi, to amma wanda ya manta ko jahilci hakan to sallarshi ba ta baci ba, saboda abinda aka ruwaito daga Zaidu dan Arkam inda yace: “Sai aka umarcemu da yin shiru, kuma aka hanamu yin Magana". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

Na Biyu: Dariya, Ibnu Munzir ya ce: “Malamai sun yi ijma'i akan yin dariya yana bata sallah".

Na Uku Da Na Hudu: Cin abin ci da shan abin sha, Ibnu Munzir ya ce: “Dukkan wanda muka san bayanan su sun yi ijma'i akan dukkan wanda ya ci ko ya sha a sallar farilla da gangan to ya zama wajibi akansa ya sake sallar".

Na Biyar: Yayewar al'aura, domin yana daga cikin sharuddan sallah suturce al'aura, to idan aka rasa wannan sharadin to sallar ta baci.

Na Shida: Karkata mai yawa daga fuskantar alkibla, domin yana daga cikin sharuddan sallah fuskantar alkibla, kamar yadda bayani ya gabata.

Na Bakwai: Wasa mai yawa kuma a jere a cikin sallah, to fa idan ya yi yawa kuma a jeri to wannan ya bata sallah wannan dukkan malamai sun yi ijma'i a kansa, mai littafin Kafi ne ya fadi hakan, ya kuma ce: “Amma idan (aikin) ya zama kadan ne to sallar ba ta baci ba… saboda Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya dauki Umama a cikin sallarsa, idan ya tashi sai ya dauketa idan kuma ya yi sujjada sai ya ajiye ta….kuma ya kara gaba kuma ya dawo baya a sallar kifewar rana".

Na Takwas: Warwarewar alwala, domin yana cikin sharuddan ingancin sallah, to idan alwala ta warware sallah ta baci.

Darasi Na Sha-biyu: Sharuddan Alwala.

Su ne kuma guda goma:

(1) Musulunci. (2) Hankali. (3) Wayau. (4) Niyyah. (5) Tabbatar da hukuncinta, ta yadda kada ya yi niyyar katseta har sai ya kammalata. (6) Yankewar abinda yake sanya alwala. (7) Tsarki da ruwa ko da dutse kafin alwalar. (8) Tsarkakar ruwa da kuma halaccinsa. (9) Gusar da dukkan abinda zai hana ruwa kaiwa ga fata. (10) Shigar lokacin sallah amma akan wanda yake fama da hadasi akoyaushe.

Sharuddan alwala da suke: Musulunci da hankalii da wayau da niyyah, to alwala bata inganta daga wanda yake kafiri domin ba za'a karbeta ba har sai ya musulunta, haka kuma mahaukaci domin shi ba wanda aka dorawa hukunce huknce bane, haka kuma karamin yaro da bashi da wayau, hakan daga wanda bai yi niyyaba, kamar ace ya yi ne domin sanyaya jiki ko ya wanke gabbai domin gusar da najasa ko datti.

An shardanta ga alwalar ruwan ya kasance wanda za'a yi tsarki da shi, idan ya kasance najane to bai yi ba, haka kuma an shardanta ga alwalar ruwan ya kasance halastaccan ruwa ne, to idan fa kwatarshi aka yi ko aka samu ba ta shar'antacciyar hanya ba to bai halatta a yi alwala da shi. Haka nan dai an shardanta ga alwalar cewar tsarki ya gabace ta tsarkin kuma na ruwane ko na dutse, wannanko bayan mutum ya kamala bayan gida/fitsari kenan. Hakanan an shardanta kawar da dukkan abinda zai hana ruwa kaiwa ga jiki, ba makawa ga dukkan mai alwala ya gusar da duk abinda ke gabbansa na tabo ko kulli ko fenti ko siminti domin ruwa ya bi ta kan fatar gaba kai-tsaye ta tare da wani abu ya tsare ba.

Haka nan kuma an shar'anta shigar lokacin sallah amma ga wanda yake fama da hadasi a ko yaushe (kamar mai yoyon fitsari), saboda umarnin da Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya yin a istihala da ta yi alwala a kowacce sallah, Allah shi ne masani.

Darasi Na Sha-uku: Farillan Alwala.

Su ne kuma guda shida:

(1) Wanke fuska, kuma yana cikin wanke fuska: Kuskurar baki da shaka ruwa. (2) Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu. (3) Shafar kai bakidaya, kuma yana cikin hakan: kunnuwa biyu. (4) Wanke kafafuwa zuwa idon sawu. (5) Jerantawa. (6) Yin su a lokaci guda.

Sudai farillan alwala su ne: Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿يَأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ إِذَا قُمتُم إِلَى ٱلصَّلَوةِ فَٱغسِلُواْ وُجُوهَكُم وَأَيدِيَكُم إِلَى ٱلمَرَافِقِ وَٱمسَحُواْ بِرُءُوسِكُم وَأَرجُلَكُم إِلَى ٱلكَعبَينِ وَإِن كُنتُم جُنُبا فَٱطَّهَّرُواْ وَإِن كُنتُم مَّرضَى أَو عَلَى سَفَرٍ أَو جَاءَ أَحَد مِّنكُم مِّنَ ٱلغَائِطِ أَو لَمَستُمُ ٱلنِّسَاءَ فَلَم تَجِدُواْ مَاء فَتَيَمَّمُواْ صَعِيدا طَيِّبا فَٱمسَحُواْ بِوُجُوهِكُم وَأَيدِيكُم مِّنهُ مَا يُرِيدُ ٱللَّهُ لِيَجعَلَ عَلَيكُم مِّن حَرَج وَلَكِن يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُم وَلِيُتِمَّ نِعمَتَهُ عَلَيكُم لَعَلَّكُم تَشكُرُونَ٦﴾ المائدة: ٦

Ma'ana: “Ya ku wadanda suka yi Imani, idan kun tashi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku da hannanyanku zuwa gwiwar hannu kuma ku shafi kawunanku kuma ku (wanke) kafafuwanku zuwa idon sawu". Suratul Ma'idah, aya ta:6

Farali Na Farko: Wanke fuska, baki da hanci na cikin fuska, saboda Allah ya ce: “Kuwanke fuskokinku". Dalili kuwa akan wajibcin kuskurar baki da shaka ruwa domin su suna cikin fuska ne, haka nan kuma dukkan wanda ya siffanta alwalar Ma'aikin Allah ﷺ‬ yana anbaton kuskurar baki da shaka ruwa, ya kuma zo a hadisin Abuhurairata t lalle Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((إِذَا تَوَضَّأَ أَحَدُكُمْ فَلْيَجْعَلْ فِي أَنْفِهِ مَاءً ثُمَّ لينثره)). رواه مسلم.

Ma'ana: “Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan kuma ya face shi". Muslim ne ya ruwaito.

Farali Na Biyu: daga cikin farillan alwala shi ne: wanke hannaye biyu, saboda fadinsa Madaukakin sarki: “Da hannayanku zuwa gwiwar hannu". To ya zama wajibi a shigar da gwiwar hannun cikin wankewar, domin lalle ma'aikin Allah ﷺ‬ ya kasance yana wanke gwiwowin hannusa a alwala.

Farali Na Uku: Shafar kai baki daya, kunnuwa biyu kuwa na ciki, saboda fadinsa madaukakin sarki: “Kuma ku shafa kawunan ku". Kuma Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((الأُذْنَانِ مِنَ اَلرَّأْسِ)). رواه الترمذي وأبو داود وابن ماجة

Ma'ana: “Kunnuwa biyu suna kai". Tirmizi da Abu Dawud da Ibnu Majah suka ruwaito. Kuma saboda ma'aikin Allah ﷺ‬ ya kasance yana shafar kai da kunnuwansa a lokacin alwala.

Farali Na Hudu: Wanke kafafuwa biyu zuwa idon sawu(kuma a shigar da idon sawun ciki), saboda fadin Allah madaukakin sarki: “Da kuma kafafuwanku zuwa idon sawu".

Farali Na Biyar: Jerantawa, domin Allah madaukakin sarki ya ambace su ne a jere, kuma ya shigar inda ake shafawa (ka kenan) tsakanin wuraran da ake wankewa, domin rabe inda ake wankewa (da shafar kai) da dan'uwansa lalle yana fa'idantar da jerantawa, kuma ma'aikin Allah ﷺ‬ ya jeranta alwalane a wannan tsarin, kuma shi ma'aikin Allah ﷺ‬ da maganganunsa da aikinsa ya ke fassara Alkur'ani.

Farali Na Shida: Yin su a lokaci guda, wato kada a jinkirta wanke wata gaba har wacce ta gabaceta ta bushe, dalili kuwa akan haka shi ne lalle Ma'aikin Allah ﷺ‬ shi ne mai shar'antawa kuma mai yiwa al'ummarsa bayanin addininta, kuma dukkan wanda ya siffanta alwalar ma'aikin Allah ﷺ‬ ya siffanta ta ne yana yin ta alokaci guda.

Darasi Na Sha-hudu: Abubuwan Da Suke Warware Alwala.

Su ne kuma guda shida;

(1) Abinda ke fita daga mafita biyu. (2)Abinda ke fita na kazanta da yake najasa daga jiki. (3)Gushewar hankali ta hanyar bacci ko waninsa. (4) Shafar al'aura da hannu gaba ne ko baya (dubura) ba tare da wani shamaki a hannu ba. (5) Cin naman rakumi. (6) Riddah barin musulunci Allah ya tsare mu da sauran musulmi daga haka.

Mawallafin littafin nan ya yi Magana ne a darasin da ya gabata akan binda ya shafi alwala, to anan ya na son ya yi bayanin abinda ya ke warware alwalar, domin mutum musulmi ya kasance akan basira na abinda ya shafi al'amuran addininsa, to anan sai ya ambata mana cewa abubuwan da suke warware alwala sune:

Na Farko: Abinda ya ke fitowa ta mafita biyu kadanne ko maiyawa, ya kuma kasu kashi biyu:

(a)Wanda aka saba da shi, kamar fitsari da bayan gida to wadannan suna warware alwala babu wani sabanin malamai akai. Ibnu Abdulbarr ya ce: Allah madaukakin sarki ya ce:

﴿ أَو جَاءَ أَحَد مِّنكُم مِّنَ ٱلغَائِطِ ﴾المائدة: ٦

Ma'ana: “Ko wani daga cikinku ya je ya yi bayangida". Suratul Ma'idah, aya ta:6

(b)Abinda yake fita da wuya, kamar tsutsa da gashi da tsakuwa, to shi ma yana karya alwala saboda fadin Ma'aikin Allah ﷺ‬ ga mace mai jinin istihala: “Ki dinga yin alwala a kowacce sallah". Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito shi.

Kuma jinin da mai istihala din take fitarwa ai ba jinni ne da aka dabi'antu da shi ba, (kamar jinin al'ada), kuma ai shi abin ya fita ne ta dayan mafita biyu sai ya yi kama da wanda aka saba da shi.

Na biyu: Abinda ke fita na kazanta da yake najasa daga jiki, wannan shi ma ya na karya alwala amma idan yana da yawa, amman kadan dinsa ba ya karya alwala, kamar jinni idan ya yi muni to yana karya alwala, idanko ya kasance ne kadan to baya karya alwala, saboda maganar Abdullahi dan Abbas: “Idan jinin ya yi muni to zai sake", Shi kuma Abdullahi dan Umar ya matse kurji sai kuma ya je ya yi sallah ba tare da ya sake alwala ba, kuma ba'a san cewa akwai wani da ya saba musu ba a cikin sahabban ma'aikin Allah ﷺ‬ sai ya zama ijma'i kenan.

Na Uku: Gushewar hankali ta hanyar bacci ko waninsa, kamar bugun aljani ko suma ko kuma maye, saboda fadin Ma'aikin Allah ﷺ‬:

(( اَلْعَيْنُ وكَاءُ اَلسنه، فَمَنْ نَامَ فَلْيَتَوَضَّأْ)). رواه أبو داود وابن ماجه.

Ma'ana: “…. Duk wanda ya yi bacci to ya sake alwala". Abu Dawud da Ibnu Majah ne suka ruwaito.

Farfadiya da bugun aljani (ko iska) da maye duk sun fi wurin gusar da hankali, kenan alwala ta karye saboda su shi ne ma ya fi.

Na Hudu: Shafar al'aura da hannu gaba ne ko baya (dubura) ba tare da wani shamaki a hannu ba, saboda fadin Ma'aikin Allahr:

(( مَنْ مَسَّ فَرْجَهُ فَلْيَتَوَضَّأْ)) رواه أبو داود وابن ماجه

Ma'ana: “Dukkan wanda ya shafi al'aurarsa to ya yi alwala". Abu Dawud ne da Ibnu Majah suka ruwaito.

Na biyar: Cin naman tsohon rakumi, saboda abinda aka ruwaito daga Jabir dan Samura t lalle wani mutum ya tambayi Ma'aikin Allahr: Shin na yi alwala saboda naman rakumi? Sai ma'aikin Allah ya ce: “Na'am, ka yi alwala saboda naman rakumi". Muslim da Ibnu Majah suka ruwaito.

Na Shida: Riddah barin musulunci Allah ya tsare mu da sauran musulmi daga haka, saboda fadin Allah madaukakin sarki:

﴿ لَئِن أَشرَكتَ لَيَحبَطَنَّ عَمَلُكَ ﴾ الزمر: ٦٥

Ma'ana: (wallahi) har idan ka yi shirka to tabbas aikinka yana baci". Suratul An'am, aya ta: 65.

Fadakarwa mai matukar muhimmanci:

Amma wankan gawa abinda yake shi ne mafi inganci baya karya alwala, wannan kuma shi ne maganar mafi yawan malamai, saboda rashin dalili akan haka, saidai inda hannun mai wankan ya taba gaban mamacin ba tare da wani abu ba(kamar safa) to alwala ta wajaba, abin kuma da yake wajibin shi ne kada a taba al'aurar mamaci sai ansa wani abu a hannu (kamar safa).

Haka kuma shafar mace bai karya alwala da jindadi ko ba da jindadi ba a mafi ingancin maganganu biyu da malamai suka yi muddin wani abu bai fito masa ba, domin ma'aikin Allah ﷺ‬ ya sunbanci wata daga cikin iyalinshi sannan kuma ya yi sallah ba tare da ya sake alwala ba.

Amma fadin Allah madaukakin sarki a ayoyi biyu daya tana Suratun Nisa'i dayar kuma tana Suratul Ma'idah, da ya ce:

﴿ أَو لَمَستُمُ ٱلنِّسَاءَ ﴾النساء: ٤٣

Ma'ana: “Ko kun shafi mata" Suratun Nisa'i, aya ta:43, Ma'ida, aya ta:6 . to abinda ake nufi shi ne saduwa a mafi ingancin maganganu biyun da malamai suka yi, wannan shi ne maganar Abdullahi dan Abbas da kuma wasu jama'a.

Amma abinda ya shafi wankan mamaci da shafar mace to hakika malam ya yi bayanin maganganun malamai tun a gundarin bakin littafin, kuma ya rinjayar da cewa basa karya alwala, Allah shi ne masani.

Darasi Na Sha-biyar Da Sha-shida: Halaye na gari da ake so kowanne musulmi ya siffantu da su, da kuma ladubban musulunci.

Na goma sha-biyar: Halaye Na Gari

Halaye na gari da ake so kowanne musulmi ya siffantu da su, daga ciki akwai:

Gaskiya, amana da kamewa da kunya da karamci da kuma cika alkawari da kin-cin duk abinda Allah ya haramta, da kyakkyawan hali ga makwabta, da taimakawa mabukata gwargwadon iko, da wanin haka na abinda ya shafi kyawawan halaye wdanda Alkur'ani da Hadisi su ka yi nuni akan shar'antuwarsu.

Na goma sha-shida: Dabi'un Musulunci.

Akwai daga cikin dabi'un musulunci: Yin sallama da sakin fuska, da cin abin ci da dama da kuma yin komai da daman, da lizimtar ladubban shara'a a lokacin shiga masallaci ko shiga gida ko kuma fita daga cikinsu, da kuma ladubban tafiya, da kyautatawa mahaifa da dangi na kusa da kuma makwafta da girmama manya da tausayawa yara, da yin barka ga wanda aka yi wa haihuwa, da kuma alakyau (Allah ya kiyaye) ga wanda masibu suka auka masa, da wanin haka na abinda ya shafi ladubban musulunci.

Bayan da malam ya yi bayanin abinda ya shafi babban fikihu (wato tauhidi) da kuma karamin fikhu (wato hukunce hukunce tsarki, sallah…) a darussan da suka gabata to yanzu yana nufin ya bayyanawa al'umma baki daya wani sashi na kyawawan da dabi'u da aka shar'anta su ga kowanne musulmi, da kuma ladubban musulunci, saboda haka ya kai dan'uwa musulmi Allah madaukakin sarki ya datarda mu ga dukkan abinda yake alheri da aiki (da wadannan halaye da dabi'u) domin ka zama babban abin ko yi ga al'umma ta hanyar kyautata wadannan manyan halaye da dabi'un na musulunci masu ban sha'awa da daraja.

Hakika bayanai da Alkur'ani da hadisai sun kwadaitar akan ruko da su dabi'un, gudun tsawaitawa ba to da na anbace su, kuma ya kasance babban abin koyinka wurin aiwatar da wadannan bayanai ya kasance Ma'aikin Allah ﷺ‬ ne, domin tabbas an tambayi Aishah Allah ya kara mata yarda dangane da dabi'unsa, sai ta ce; “Ya kasance dabi'unsa shi ne Alkur'ani". Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, hakika an san shi da gaskiya da amana da jarunta da kuma karamci, kana an san shi da Nisantar abinda Allah madaukakin sarki ya haramta, kuma akan haka sahabbansa masu dara –Allah ya kara musu yarda baki dayansu- suka ta fi.

Hakika musulunci ya yadu a sasannin duniya tun farkon al'amari ta hanyar kyawawan mu'amala da 'yan-kasuwa musulmai suke yi tare da wadanda ba musulmai ba, domin sun kasance masu gaskiya kuma amintattu.

Ina fatan dan'uwa musulmi ka kasance wanda ya siffantu da wadannan manya-manyan siffofin masu daraja, sabo da haka ina horanka da gaskiya a wurin Magana da kuma aiki, da kuma amana aduk abinda za ka yi ko za ka bari, da kuma kamewa da hakura da abinda ke hannunka, ka kasance mai kunya da ladubba da jarumta da cika alkawari da kuma karamci, kuma mai nisantar haram ka zama mai saukin kai, ka kyautata makwabcinka hakkokinsa masu girma ne, kuma ka taimakawa mabukaci, Allah ya na taimakon bawa muddin bawan yana taimakon dau'uwansa.

Ka yi sallama ga dukkan wanda ka sani da wanda baka sani ba, wannan yana cikin karantarwar Ma'aikin Allah ﷺ‬. Ya sanya a so juna kuma yana kau da damuwa da kuma rabuwar kai, ka kasance mai sakin fuska ga 'yan'uwanka musulmai wannan fa yana cikin sadaka.

Ka yi dukkan abinda ma'aikin Allah ﷺ‬ ya karantar da kai, kamar; ci da dama da sha da daman, da lizimta karantawar ma'aikin Allah ﷺ‬ wurin gabatar da kafar dama a lokacin shiga masallaci da kuma karanta addu'ar da aka ruwaito, da kuma (gabatar da kafar) hagu a lokacin fita. Ka kiyaye addu'ar shiga gida da kuma (addu'ar) fita, idan ka yi haka za'a kareka da karewar Allah kuma za'a kiyayeka da kiyayewar sa.

Kada ka manta da addu'ar tafiya a lokacin da zaka yi tafiya. Ka kyautatawa mahaifanka, ka yi musu mu'amala mai kyau, ka fa sani hakkinsu da yake a kanka mai girma ne, Alkur'ani da Hadisi sun yi nuni akan haka, kada ka yi wasa da haka sai ka yi nadama a lokacin da bata da anfani.

Ka da ka manta da kyautatawa 'yan'uwanka na kusa da makwabta manya da kanana wannan fadakarwace daga Allah da Manzanshir, Allah madaukakin sarki yna cewa:

﴿ وَأَحسِنُواْ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلمُحسِنِينَ١٩٥﴾ البقرة: ١٩٥

Ma'ana: “Ku kyautata, lalle Allah yana son masu kyautatawa". Suratul Bakarah, aya ta:195. Kuma Ma'aikin Allah ﷺ‬:

(( إِنَّكُمْ لاَ تَسَعُونَ اَلنَّاسَ بِأَمْوَالِكُمْ، وَلَكِنْ لِيَسَعْهُمْ مِنْكُمْ بَسْطُ اَلْوَجْهِ وَحُسْنُ اَلْخُلُقِ)).

Ma'ana: “Lalle ku ba za ku iya wadatar da mutane da dukiyarku ba, saidai ku wadatar da su da sakin fuska da kuma kyawawan dabi'u".

Kuma Ma'aikin Allah ﷺ‬ ya fadawa Mu'aza, ya ce:

(( اِتَّقِ اَللهَ حَيْثُمَا كُنْتَ وَأَتْبِعِ اَلسَّيِّئَةَ اَلْحَسَنَةَ تَمْحُهَا، وَخَالِقِ اَلنَّاسَ بِخُلُقٍ حَسَنٍ)).رواه الترمذي.

Ma'ana: “Ka ji tsoron Allah a duk inda ka ke, kuma ka bi mummunan aiki da kyakkyawan aiki, kuma ka mu'amalanci mutane da kyakkyawan dabi'a".

Tirmizi ne ya ruwaito shi.

Wani mai hikima ya ce: “Ka kyautatawa mutane za ka mallaki zukatansu, sau dayawa kyautatawa ta na mallake mutum".

Ka yi barka a binda aka haifa, kuma ka yi adu'ar da aka ruwaito akan hakan, ka yi jaje ga 'yan'uwanka da bala'i ya afka musu za ka sami lada akan hakan za ka kwatankwacin ladan su, ka lizimci sauran ladubban musulunci, kuma ka nisanci munanan dabi'u, Allah madaukakin sarki ya sanyamu cikin wadanda za su lizimci kyawawan halaye da shari'a ta karantar da kuma ladubban musulunci kuma za su nisanci batattun dabi'u, lalle shi mai iko ne akan haka, kuma mai amsa addu'a ne. tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabimmu Muhammadu da iyalanshi da kuma sahabbanshi baki daya.

Darasi Na Sha-bakwai: Tsoratarwa Akan Shirka Da Kuma Nau'ukan Laifi.

Tsoratarwa akan shirka da kuma nau'ukan sabo, kamar:

Abubuwa bakwai masu halakarwa, su ne kuma:

(1) Shirka da Allah. (2) Sihiri (Asiri). (3) Kashe ran da Allah ya haramta a kashe ta sai da dalili. (4) Cin riba (5) Cin dukiyar maraya. (6) Juya baya alokaci yaki. (7) Yiwa mata muminai masu kamun kai kazafi. Akwai kuma:

Sabawa mahaifa, da yanke zumunci da shaidar zur (karya), da rantsuwar karya da cutar da makwabci, da zalintar mutane a: Azubar da jinni, dukiya, mutunci da wanin haka daga cikin abinda Allah ya hana ko manzanshir ya hana.

Bayan mawallafin wannan littafin ya kamala bayani kan abinda ya shafi kyawawan halaye da kuma ladubba na musulunci to yana son ya yi bayani a wannan darasin kan abinda ya shafi hadarin shirka, da kuma tsoratrwa akan hakan da kuma dukkanin nau'ukan sabo, kuma yana daga ciki abubuwa bakwai masu halakarwa domin ya tsoratar da al'umma kada su auka musu, ko su aukawa wasu daga cikinsu, an karbo daga Abuhurairah Allah ya kara masa yarda, lalle ma'aikin Allah ﷺ‬ ya ce:

((اِجْتَنِبُواْ اَلسَّبْعَ اَلْمُوبِقَاتِ، قَالُواْ يَا رَسُولَ اَللهِ وَمَا هِيَ؟ قَالَ: اَلشِّرْكُ بِاللهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ اَلنَّفْسِ اَلَّتِي حَرَّمَ اَللهُ إِلاَّ بِالْحَقِّ، وَأَكْلُ اَلرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ اَلْيَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ اَلزَّحْفِ، وَقَذْفُ اَلْمُحْصَنَاتِ اَلْغَافِلاَتِ اَلْمُؤْمِنَاتِ)). رواه البخاري ومسلم.

Ma'ana: “Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa, sai suka ce; Ya Ma'aikin Allah wadannene? Sai ya ce: Yi wa Allah shirka, da Sihiri (asiri) da kashe rai wacce Allah ya haramta a kasheta saida gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya a lokacin yaki, da yiwa mata muminai masu kamunkai kazafi". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

An kira su masu halakarwa ne domin suna halakar da mai aikata su, tun nan duniya na irin nau'ukan ukubar da ka sanya akan duka wanda ya yi, da kuma irin azabar lahira, saidai bayani akan shirka ya gabata tun a darasi na hudu, sai a koma can.

Amma shi sihiri da ake kira damara ko wasu addu'o'I mara kangado, da kuma wasu surkulle da suke tasiri a zukata da kuma gangan jiki, daga ciki akwai me sa rashin lafiya har ma ya yi kisa, akawai mai raba miji da matarsa akwai kuma rufa ido, saidai ba shi da wani tasiri, Allah mai girma da daukaka yana cewa acin Suratu Taha:

﴿قَالُواْ يَمُوسَى إِمَّا أَن تُلقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَن أَلقَى٦٥ قَالَ بَل أَلقُواْ فَإِذَا حِبَالُهُم وَعِصِيُّهُم يُخَيَّلُ إِلَيهِ مِن سِحرِهِم أَنَّهَا تَسعَى٦٦﴾ طه: ٦٥ – ٦٦

Ma'ana: “Suka ce Ya Musa; Kodai ka jefa ko kuma mu kasance farkon wanda zai jefa* sai (Annabi Musa) ya ce: A'a, ku jefa. Sai kawai ga igiyoyinsu da sandunansu ya na mishi rufa idon na asirin na su cewar tana tafiya". Suratu Taha, aya ta:65-66.

Shi asiri haramun ne domin kafircewa Allah ne, kuma yana kore Imani yana kuma korewa mutum tauhidi, Allah madaukakin sarki yana cewa:

﴿ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِن أَحَدٍ حَتَّى يَقُولَا إِنَّمَا نَحنُ فِتنَة ﴾ البقرة: ١٠٢

Ma'ana: “Ba sa koyawa kowa wani (abu) balle har su ce; abin sani kawai mu fitine kada ku kafirce". Suratul Bakarah aya ta: 102.

Hukuncin dukkan mai asiri shi ne kisa, kuma dukkan abinda ya zo da nassin wannan hadisin da kuma abinda malam ya anbata bayan abubuwa bakwai masu halakarwa to duk haramun ne da nassin Alkur'ani da kuma hadisi.

Saboda haka yana zama wajibi akan dukkan mutum musulmi ya nisance su baki daya, idan ko ya samu kan shi cikin wani abu daga cikin su to ya zama wajibi ya tuba, kuma ya yi danasanin aikatawa kuma niyyatu akan ba zai sake aikatawaba anan gaba haka kuma ba zai sake aikata waninsa ban a sauran zunubai da kuma laifuffuka, kuma ya hana duk wanda ke kasansa aikata hakan, kuma ya tsoratar da 'yan'uwansa musulmi da kada su aikata hakan, ya kuma bayyana musu hatsarin dake ciki, domin yin hakan yana cikin taimakekeniya akan bin Allah da kuma takawa, ya na kuma cikin umarni da kyakkyawan aikin da kuma hana mummunan aiki, yana kuma cikin Da'awah akan hanyar Allah, wannan ko ita ce hanyar Annabawa amincin Allah ya tabbata a kan su, Allah madaukakin sarki yana fada akan harshen Annabinsa Muhammadu ﷺ‬ cewa:

﴿قُل هَذِهِ سَبِيلِي أَدعُواْ إِلَى ٱللَّهِ عَلَى بَصِيرَةٍ أَنَا وَمَنِ ٱتَّبَعَنِي وَسُبحَنَ ٱللَّهِ وَمَا أَنَا مِنَ ٱلمُشرِكِينَ١٠٨﴾ يوسف: ١٠٨

Ma'ana: “Ka ce; Wannan ita ce hanya ta da na ke kira zuwa ga Allah akanta, akan basira ni da dukkan wanda ya bini". Suratu Yusuf, aya ta: 108.

Allah madaukakin sarki ya karemu baki daya da dukkanin musulmi daga sauran zunubai da kuma laifuffuka, kuma ya tabbatar da mu da zancen da yake tabbatacce a nan rayuwar duniya da kuma lahira, lalle Ubangijina mai ji ne kuma mai amsar ruko ne, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabimmu Muhammad da kuma iyalan shi da sahabbanshi baki daya.

Darasi Na Sha-takwas: Yadda Ake Shirya Mamaci Da Kuma Yi Masa Sallah.

Bayanai akan haka:

Shirya mamaci:

(1) Idan aka tabbatar da ya rasu sai a rufe masa idanuwa, a kuma daure gemunsa.

(2) Alokaci yi masa wanka: Za'a rufe al'aurarsa, sai a dan daga shi kadan, sai kuma a matsa cikin sa a hankali, sai mai wankan ya sanya wani abu a hannunsa kamar safa ko makamancita sai ya yi masa tsarki, sannan kuma sai ya yi masa alwala irin alwalar sallah, sannan sai ya wanke masa kai da gemunsa za'a yi anfani da ruwane kuma a sanya masa magarya ko makamancinta, sannan sai a wanke masa tsagin jikinsa na dama, sannan sai a wanke na hagu, sannan sai a sake maimaita karo na biyu kenan, sannan kuma a sake na uku kenan, a kowanne idan an zo za'a bi cikinsa a hankali, idan wani abu ya fito sai a wanke shi a kuma toshe wurin da auduga ko makamancin ta, idan wurin bai rike ba sai a sami busasshiyar kasa ko wadansu abubuwa na zamani a likitance.

Sai a sake mi shi alwala, to idan bai wanku a karo na uku ba sai akara zuwa biyar, ko bakwai, sannan sai tsane shi da wani tufafin, sai a sanya turare a boyayyun wuraransa da kuma wuraran sujjadarsa, idan kuma aka sanya masa turare a duk jikinsa ya yi, sai a milke likafanin da turaren 'Bahur', idan gashin bakin sa ko farcansa (akaifa) yana da tsawo sa a rage, ba'a taje masa kai, mace kuma ana tattara gashin kanta sai a kitse shi layi uku a kuma saukeshi a bayanta.

(3) Sanya Likafani: Abinda aka fi so shi ne a sanya mutum namiji likafani uku farare ba riga a cikin su kuma ba rawani, za'a shigar da shi ciki ne kawai, imam kuma an yi masa likafaninne da riga da wando da lifafa babu laifi. Amma mace ana sanya mata likafani biyar ne, da doguwar riga da kuma mayafi (da za'a rufo shi daga kan ta) sai kuma zani da kuma lifafa guda biyu. Ana yiwa karamin yaro da likafani ne da tufafi guda daya ne zuwa guda uku. Karamar yarinya kuma da riga da lifafa guda biyu.

(4) Wanda ya fi kowa cancantar ya yi mamaci wanka, da sallah da binnewa: Shi ne wanda mamacin ya yi wasiyyah da ya yi masa hakan, sannan sai mahaifi sannan sai kaka sannan sai dangi na kusa sai na kusa daga dangin uba.

Wanda ko ya fi cancantar yi wa mace wanka, shi ne wadda ta yi wasiyyah, sannan sai uwa sannan sai kaka sannan sai na kusa sannan na kusa daga cikin mata.

Ma'aurata biyu kowannensu na wanke dayan, domin Sayyidina Abubakar t maidakinsa ce ta yi masa wanka, kuma domin Sayyidin Aliyut shi ya yi Fadima wanka, Allah ya kara mata yarda.

(5) Siffar Sallar Jana'iza: Zai yi kabbara, sai ya karanta Fatiha bayan kabbarar farko, in kuma ya karanta gajeruwar sura ne ko aya daya ko biyu ya yi, saboda hadisin da aka ruwaito akan hakan daga Abdullahi dan Abbas –Allah ya kara musu yarda-. Sannan sai ya yi kabbara ta biyu, sai ya yi salati ga Ma'aikin Allah ﷺ‬ kamar yadda ya yi a lokacin da yake tahiya. Sannan sai ya yi kabbara ta uku sai ya ce:

(( اَللَّهُمَّ اَغْفِرْ لِحَيِّنَا وَمَيِّتِنَا، وَشَاهِدِنَا وَغَائِبِنَا، وَصَغِيرِنَا وَكَبِيرِنَا، وَذَكَرِنَا وَأُنْثَانَا، اَللَّهُمَّ مَنْ أَحْيَيْتَهُ مِنَّا فَأَحْيِهِ عَلَى اَلإِسْلاَمِ، وَمَنْ تَوَفَّيْتَهُ مِنَا فَتَوَفَّهُ عَلَى اَلإِيمَانِ، اَللَّهُمَّ اَغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ وَعَافِهِ وَاعْفُ عَنْهُ ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ وَوَسِّعْ مَدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِمَاءٍ وَثَلْجٍ وَبَرَدٍ، وَنَقِّهِ مِنَ اَلذُّنُوبِ وَالْخَطَايَا كَمَا يُنَقَّى اَلثَّوْبُ اَلأَبْيَضُ مِنَ اَلدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَارًا خَيْرًا مِنْ دَارِهِ وَأَهْلاً خَيْرًا مِنْ أَهْلِهِ وَأَدْخِلْهُ اَلْجَنَّةَ وَأَعِذْهُ مِنْ عَذَابِ اَلْقَبْرِ، وَعَذَابِ اَلنَّارِ، وَافْسَحْ لَهُ فِي قَبْرِهِ وَنَّوِّرْ لَهُ فِيهِ، اَللَّهُمَّ لاَ تُحَرِّمْنَا أَجْرَهُ وَلاَ تُضِلُّنَا بَعْدَهُ)).

Ma'ana: “Ya Allah Ubangiji! ka gafartawa rayayyummu da kuma matattummu, wadanda suke nan da wadanda ba sa nan, da kananammu da manyammu da mazammu da matammu. Ya Allah Ubangiji! duk wanda ka rayarda shi daga cikimmu to ka rayar da shi akan musulunci, duk kuma wand aka dauki ranshi daga cikimmu to ka dauki ranshi yana da Imani. Ya Allah Ubangiji! ka gafarta masa ka yi masa rahama ka kiyaye shi ka yi masa afuwa, ka kyautata makwancinsa ka yalwata kabarinsa, ka wankeshi da ruwa da kankara da sanyi, ka tsaftace shi daga zubunubai da kurakurai kamar yadda ake tsaftace tufafin da yake fari daga datti, ka canza masa gida da ya fi gidansa, da iyalai da suka fi iayalanshi, ka shigar da shi aljanna, ka tsareshi daga azabar kabari, da kuma azabar wuta, ka fadada masa kabarinsa ka kuma haskaka masa shi. Ya Allah Ubangiji kada ka haramta mana ladansa, kuma kada ka batar da mu bayansa. Sannan sai kabbara da hudu, sai iyi sallama guda ta damansa.

An so ya daga hannunsa a kowacce kabbara, amma kuma idan mamaciyar da kasance macece sai yace (alokacin sallah kenan): ((اللهم اغفر لها)) ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka gafarta mata". Idan kuma gawarwakin biyu ne sai kace: ((اللهم اغفر لهما)) ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka gafarta musu". Idan Kuma suna da yawa sai ka ce: ((اللهم اغفر لهم)) ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka gafarta musu".

Amma idan yaro ne sai ka ce:

((اَللَّهُمَّ اَجْعَلْهُ فَرَطًا وَذِخْرًا لِوَالِدَيْهِ، وَشَفِيعًا مُجَابًا، اَللَّهُمَّ ثَقِّلْ بِهِ مَوَازِينَهُمَا، وَأَعْظِمْ بِهِ أُجُورَهُمَا، وَأَلْحِقْهُ بِصَالِحِ اَلْمُؤْمِنِينَ، وَاجْعَلْهُ فِي كَفَالَةِ إِبْرَاهِيمَ – عَلَيْهِ اَلسَّلاَمُ- وَقِهِ بِرَحْمَتِكَ عَذَابَ اَلْجَحِيمِ)).

Ma'ana: “Ya Allah Ubangiji ka sanya shi… wata ajiya ce ga mahaifansa kuma maicetonsu wanda ake amsa masa addu'a, Ya Allah Ubangiji ka nauyaya ma'aunansu (na hakurin rashin) shi ka girmama ladan su da shi, ka hada shi da salihan bayi, ka sanya shi cikin kulawar Annabi Ibrahim, ka tasare shi da rahamarka daga azabar wuta".

Abinda Sunnah takaranta shi ne liman zai tsaya ne daidai kan namiji, idan kuma macece to sai ya tsaya tsakiyarta, kuma namiji ya kasance wanda shi ke dab da liman idan gawarwakin suna da yawa, mace kuma ita ke bin Alkibla.

Idan kuma akwai gawarwakin yara to sai a fara gabatar da yaro kafin mace, sannan sai mace sannan sai yarinya karama, kuma kan karamin yaro ya zama ya jeru da kan babba, sannan tsakiyar mace ya yi daidai da kan namiji, haka nan karamar yarinya kan ta ya kasance daidai da kan mace, kuma tsakiyar ta ya yi daidai da kan namiji. Dukkanin masallata kuma su kasance a bayan liman, saida idan akwai wani mutum guda da bai sami wuri a bayan liman ba to anan sai ya tsaya a daman liman.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kadai, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabimmu Muhammad da iyalanshi da kuma sahabbansa.