SAKO DAYA KAWAI!
wagga madda an tarjamata zuwa
- العربية - Arabic
- Ўзбек - Uzbek
- ភាសាខ្មែរ - Khmer
- македонски - Macedonian
- română - Romanian
- lietuvių - Lithuanian
- afaan oromoo - Oromoo
- ಕನ್ನಡ - Kannada
- suomi - Finnish
- தமிழ் - Tamil
- اردو - Urdu
- සිංහල - Sinhala
- ئۇيغۇرچە - Uyghur
- português - Portuguese
- Kurdî - Kurdish
- Kiswahili - Swahili
- Luganda - Ganda
- অসমীয়া - Assamese
- বাংলা - Bengali
- Српски - Serbian
- Nederlands - Dutch
- slovenčina - Slovak
- bosanski - Bosnian
- 中文 - Chinese
- Bahasa Indonesia - Indonesian
- Norwegian - Norwegian
- Shqip - Albanian
- italiano - Italian
- svenska - Swedish
- български - Bulgarian
- हिन्दी - Hindi
- тоҷикӣ - Tajik
- नेपाली - Nepali
- 한국어 - Korean
- Deutsch - German
- polski - Polish
- Français - French
- español - Spanish
- മലയാളം - Malayalam
- English - English
- Wikang Tagalog - Tagalog
- ગુજરાતી - Unnamed
- Tiếng Việt - Vietnamese
- ไทย - Thai
- ελληνικά - Greek
- Türkçe - Turkish
- hrvatski - Unnamed
- Èdè Yorùbá - Yoruba
- پښتو - Pashto
- አማርኛ - Amharic
- čeština - Czech
nau o, i
Full Description
SAKO DAYA KAWAI!
DR. NAJI IBRAHIM AL-ARFAJ
SADAUKARWA
Zuwa ga masu binciken haƙiƙa da gaskiya da ikhlasi.
Zuwa ga ma'abota hankula masu kiyayewa.
Tambayoyi kafin karatu:
1) Me ake nufi da wannan saƙon?
2)Me Littafi abin tsarkakewa yake cewa game da shi?
3)Me Al-ƙur'ani yake cewa game da shi?
4) Menene ra'ayinka a cikinsa bayan hakan?
A cikin ainihin mauru'in:
Bayan halittar Adam, saƙo ne ɗaya mai asali maɗaukaki da aka ɗaukoshi zuwa mutane a tsawon tarihin mutum, saboda gargaɗar da mutane da wannan saƙon, da dawo da su zuwa tsantsar miƙaƙƙiyar hanya, Ubangiji Ɗaya Gaskiya Ya aiko Annabawa da Manzanni kamar: Adam da Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa da Muhammad - amincin Allah ya tabbataba a gare su - don isar da sako ɗaya, shine:
Ubangiji Gaskiya Shi kaɗai yake, to, ku bauta maSa.
Yayi aike don isar da wannan saƙon:
Nuhu " Ubangijinku Ubangiji ne ɗaya, to, ku bauta maSa Shi kaɗai".
Ibrahim " Ubangijinku Ubangiji ne ɗaya, to, ku bauta maSa Shi kaɗai".
Musa " Ubangijinku Ubangiji ne ɗaya, to, ku bauta maSa Shi kaɗai".
Isa " Ubangijinku Ubangiji ne ɗaya, to, ku bauta maSa Shi kaɗai".
Muhammad " Ubangijinku Ubangiji ne ɗaya, to, ku bauta maSa Shi kaɗai".
Haƙiƙa Allah Ya aiko ma'abota haƙuri daga Manzanni da wasunsu daga waɗanda muke sani da kuma waɗanda ba mu sani ba daga Annabawa don isar da manyan al'amura daga cikin su akwai:
1) Karɓar wahayi na Ubangiji, da kuma isar da shi ga mutanensu da kuma mabiyansu.
2) Sanar da muatne Tauhidi da tsarkake bauta ga Allah.
3) Ɗabbaƙa kyakkyawan koyi a faɗa da aiki, don mutane su yi koyi da su a hanyar su zuwa ga Allah.
4) Fuskantar da mabiyansu zuwa tsoron Allah da biyya gareShi da UmarninSa.
5) Sanar da mabiyansu hukunce-hukuncen Addini da kyawawan ɗabi'u.
6) Shiryar da masu saɓo da mushrikai daga cikin masu bautar gumaka da wasunsu.
7) Isarwa muatne cewa za'a tashesu bayan mutuwarsu, kuma za'a yi musu hisabi ranar Al-ƙiyama a kan ayyukansu, wanda ya yi imani da Allah Shi kaɗai ya yi aiki na gari, to, sakamakon sa Aljanna, wanda kuma ya yi shirka da Allah ya saɓa masa, to, makomar sa wuta.
Waɗannan Annabawan da Manzanni Ubangiji ɗaya ne Ya halicce su Ya aiko su. Lallai cewa duniya da abinda ke cikinta na ababen halitta yana furuci da samuwar Allah Mahalicci, kuma yana shaidawa da kaɗaitakarSa, Allah Shi ne Mahaliccin [duk] kasantacce da abin da ke cikinsa na 'yan Adam da dabbobi da ƙwari. Shi ne Mahaliccin mutuwa da rayuwa mai ƙarewa da kuma rayuwa ta har abada.
Lallai littattafai ababen tsarkakewa na Yahudawa da Nasara da musulamai suna shaidawa gaba ɗayansu da samuwar Allah da kaɗaita Shi.
Lallai mai neman gaskiya idan ya karanta ma'anar Ubangiji da karatu da kuma tsarkakewa a cikin littafi abin tsarkakewa da kuma Alƙur'ani mai girma zai iya banbance siffofi makaɗaita waɗanda Allah Ya keɓanta da su, wani ba zai yi tarayya da Shi a cikinsu ba daga iyayen giji na ƙarya. waɗannan su ne wasu daga cikin siffofin.
1) Ubangijin gaskiya Mahalicci ne ba abin halitta ba ne.
2) Ubangijin gaskiya Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, kuma ba mai ƙididdiguwa ba ne, Bai haifa ba, ba'a haifeShi ba.
3) Allah abin tsarkakewa ne daga surantawar halitta, gannai ba sa riskarSa a duniya.
4) Allah ba Shi da farko, ba zai mutu ba, kuma ba ya sauka [jikin wani] , ba ya kamantuwa a cikin kowane abu daga ababen halittarSa.
5) Allah Shi ne abin nufi da buƙata, Mai tabbata ne da zatinSa, Mawadaci daga halittarSa, ba ya buƙatuwa zuwa gareSu, ba Shi da mahaifi ko mahaifiya, ko mata ko ɗa, kuma ba ya buƙatuwa zuwa wani abinci ko abin sha, ko taimako daga wani. Sai dai ababen halittar da Allah Ya haliccesu suna cikin buƙatuwa zuwa gareShi.
6) Allah Shi Mai kaɗaitaka ne da siffar girma da cika da kyau waɗanda wani daga halittarSa ba ya tarayya da Shi a cikinsu, babu wani abu tamkarSa.
Zai yiwu garemu mu yi amfani da waɗannan ma'aunan da siffofin (Da wasunsu daga siffofin da Allah Ya kaɗaita da su Shi kaɗai) wajen rushe da kauda kowane allolin ƙarya.
A yanzu zan dawo dan binciken saƙo ɗaya abin ambata a sama, don kuma in ɗosani sashin nassoshi daga littafi abin tsarkakewa da kuma Alƙur'ani mai girma waɗanda suke ƙarfafa kaɗaitakar Allah. sai dai kafin hakan ina son in yi tarayya da ku a wannan abin mai ɗarsuwa a rai.
Wasu daga cikin Kiristoci za su iya mamaki suna masu tambaya: A bayyane cewa Allah ɗaya ne, mu kuma muna imani da Allah ɗaya, to menene matsala?
Gaskiya cewa ni ta hanyar karatuna mai yawa ga Kiristanci da kuma tattaunawata mai yawa da kiristoci na samu cewa "Allah" a wurinsu (Gwargwadon yadda sashinsu su ke surantawa) ya tattaro abin da ke tafe:
1) Allah uba.
2) Allah ɗa.
3) Allah Shi ne rai abin tsarkakewa.
Lallai sassauƙar baraɓa da mafurta kuɓutacciya suna tura mai bincike na karatu zuwa tambayar waɗannan kiristocin:
Menene ma'anar faɗinku" Allah ɗaya ne" yayin da cewa ku kuna nuni zuwa alloli uku?
Shin Allah ɗaya ne a cikin uku ko uku ne suka sauka a cikin ɗaya (1 a cikin 3 ko 3 a cikin 1) ?
Ƙari zuwa wannan, kuma gwargwadon aƙidun wasu kiristoci, cewa akwai wasu ayyuka da tarayya da surori mabanbanta tare da waɗannan alloli ukun kamar yadda yake tafe:
1) Allah uba = Shi ne Mahalicci.
2) Allah ɗa = Shi ne mai tsamowa ) Mai tseratarwa).
3) Allah rai mai tsarki = Shi ne Mai ɗaukakawa.
Lallai cewa riya cewa Masihu shi ɗan Allah ne, ko cewa shi ne Allah, ko wani yanki ne daga Allah, yana warwara kai tsaye tare da abin da nassoshin Attaura da Injila suka tabbatar, yayin da suka nassanta cewa Allah babu wanda ya ke ganinSa a duniya.
"Lallai cewa ba ku taɓa jin sautinSa ba ko sau ɗaya, kuma ba ku ga fuskarSa ba".
(Injila Yuhanna 5:37).
"babu wanda ya taɓa ganinSa ko sau ɗaya, kuma babu wani da yake da ikon ganinSa".
(Saƙo na farko zuwa Taimusawis 6: 16).
"Babu wani da zai ganni kuma ya wanzu a raye".
(Al-Kharuj: 33: 20).
Gini a kan waɗannan nassoshin da wasunsu, ni ina mamaki ina mai tambaya da dukkanin gaskiya da amana, ta yaya za mu iya haɗawa tsakanin waɗanda suke cewa Isa shi ne Allah, da kuma tsakanin nassoshin Littafi abin tsarkakewa wanda ya ke ƙarfafa cewa ba'a sami wani ɗaya ba da ya ga Allah, ko ya ji sautinSa?!
Shin yanzu Yahudawa ba sa gani a wancan lokacin da iyalan [Annabi] Isa da mabiyan sa, shin ba su ga [Annabi] Isa Almasihu ba (Allah ɗa kamar yadda wasunsu suke ƙudirewa) kuma ba su ji sautin sa ba?
Ta yaya Attaura da Injila suke tabbatar da cewa Allah wani ba ya ganin Sa kuma ba ya jin Sa, sannan mu samu wanda ya ke ƙudirewa cewa [Annabi] Isa wanda suka ga jikin sa kuma suka ji sautin sa shi ne Allah, ko ɗan Allah? Shin akwai wani sirri ne ɓoyayye da yake rataya da haƙiƙanin Allah?
Lallai Attaura tana ƙarfafa akasin hakan yayin da take ciratowa daga faɗin Allah: "Lallai cewa Ni Ni ne Ubangiji, kuma babu wani Allah daban ba Ni ba. Kuma lallai cewa Ni ban taɓa magana a ɓoye ba, kuma ban sanya manufata a ɓoye ba...Lallai cewa Ni Ni ne Allah, kuma lallai cewa Ni ina furta gaskiya, kuma lallai cewa Ni ina bayyana abin da yake gaskiya ne". (Ish'iya'u 45:19).
To meye gaskiya? Yi haƙuri ka karanta nassin da ya gabata da yawa, kuma ka yi tunani a cikinsa tsawon lokaci.
To za mu cirata a yanzu daidai wa daida a cikin wata tafiya don bincike game da haƙiƙanin Allah a cikin Littafi abin tsarkakewa da kuma Al-ƙur'ani mai girma ina mai ƙaunar ba ni ra'ayoyinku da kuma fahimtar ku bayan tuntuntuni a kan ma'anar ayoyin da kuma nassosin da karatun da za ku yi wa wannan ɗan ƙaramin littafin dan gyara na ilimi da adalci.
Don lura da ilimi zan bijiro da dalilai ba tare da taliƙi ba, ina mai fatan yin tuntuntuni a kan ma'anonin su da lura da kuma ilimi wanda surantawa ko wasu hukunce-hukuncen da suka gabata basu cakuɗasu ba.
Allah Ɗaya Gaskiya a cikin Littafi abin tsarkakewa (Tsohon alƙawari):
Ka ji ya kai Isra'il: Ubangiji Shi ne Allan mu Ubangiji ɗaya.
(Al-Tasniya 6:4).
Shin Allah Ɗaya bai halicci ran rayuwa garemu ba, kuma bai azurta mu ba?
(Mulakhy 2:15).
Ku sani kuma ku yi imani da Ni, ku kuma gane cewa Ni Ni ɗin Ni ne Shine Allah, ba'a samu wani Allah ba kafin Ni, kuma ba za'a samu wani Allah ba a bayaNa. Ni Shi ne Ubangiji, kuma babu mai tsamowa in ba Ni ba.
(Ish'iya'u 43: 10-11).
Ni ne Shi Na farko da Na ƙarshe, kuma babu wani Allah in ba Ni ba. Wanene tamkata?
(Ish'iya'u 6:44).
Shin ban zama Ni ne Ubangiji ba, kuma babu wani abin bautawa da gaskiya in ba Ni ba? Mai kuɓutarwa kuma Mai tsamowa, kuma babu wani da ban a nan.
(Ish'iya'u 45: 21).
Shin zaka tuna wasu nassoshin da ban irinsu.
Allah Ɗaya Gaskiya a cikin Littafi abin tsarkakewa (Sabon alƙawari).
Rayuwa ta har abada ita ce su sanKa kai Ubangijin gaskiya kai kaɗai, kuma Yesu Almasihu wanda Ka aiko ne.
(Injil Yuhanna 3:17).
Ku bautawa Allah Ubangijinku, kuma ku gabatar da aiki sabo da Shi kawai.
(Injil Matta 4;10).
Ka ji ya kai Isra'il: Ubangiji Shi ne Allanmu Ubangiji ɗaya...to lallai cewa Allah Shi kaɗai yake, kuma babu wani daban waninSa.
(Injil Mirƙas 12:28-33).
To lallai cewa Allah Shi kaɗai yake, kuma tsani tsakaknin Allah da mutane ɗaya ne, shine mutum Al-Masihu Yesu.
(Saƙo na farko zuwa ga Taimusawis 2: 5).
Ɗayan su ya zo zuwa gareshi sai ya ce masa: "Shugabana na gari, menene abu na gari wanda zan aikata shi dan in samu rayuwa ta har abada?" Sai ya amsa masa (Isa): ((Me ya sa kuke kirana na gari? Ai babu wani na gari sai ɗaya, lallai cewa Shi ne Allah)). (Injil Matta 19: 16-17 kamar yadd yake a kofin sarki Jaimus).
Shin za ka iya tuna wasu nassoshin da ban da suke ƙarfafa cewa Allah Ɗaya ne kawai? (Ba uku ba).
Allah Ɗaya Gaskiya a cikin Alƙur'ani.
((Ka ce Shi ne Allah Ɗaya. Allah Abin nufi da buƙata. Bai haifa ba ba'a haife Shi ba. Kuma babu wani ɗaya da ya zama kini a gareShi)).
(Lambar Surar 112: Aya ta1- 4).
((Babu abin bautawa da gaskiya sai Ni, to, ku bauta miNi)).
(Lambra Surar 21: Aya ta 25).
Lallai ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangiji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su.
(Lambar Surar 5: Aya ta 73).
((Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ɗaya ne)).
(Lambar Surar 37: Aya ta 4).
((Shin akwai wani Ubangiji tare da Allah, to, ku zo da hujjojinku in kun kasance masu gaskiya ne)). (Lambar Surar 27: Aya ta 64).
A haƙiƙa lallai cewa wannan saƙon (Kaɗaita Allah) shi ne mauru'i na asali a cikin Al-ƙur'ani mai girma.
KAMMALAWA
Lallai cewa waɗannan nassoshin da wasunsu daga ɗaruruwan dalilai a cikin Littafi abin tsarkakewa da kuma Alƙur'ani mai girma suna ƙarfafa abin da baya barin wani fage dan kokwanto cewa Allah Ɗaya ne, babu wani Ubangiji waninSa, in da Littafi abin tsarkakewa yake cewa: "Ka ji ya Isra'il: Ubangiji Ubangijimmu Ubangiji ɗaya ne... to, lallai cewa Allah Shi ɗaya ne babu wani daban waninSa. " (Injil Mirƙas 12: 8-33). Kuma Alƙur'ani mai girma yana ambatan wannan umarnin a cikin faɗinSa. (Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci). (Lambra Surar 112: Aya ta1). Littafi abin tsarkakewa ba ya ƙarfafa cewa Allah ɗaya ne kawai, kai yana ƙarfafa cewa Shi ne Mahalicci kuma Mai tsamowa Makaɗaici. Ku sani kuma ku yi imani da Ni, ku gane cewa Ni Ni ɗin Ni ne Shi ne Allah, ba'a samu wani Allah ba kafi Na, kuma ba za'a samu wani Allah ba a bayaNa. Ni Shi ne Ubangiji, kuma babu mai tsamowa in ba Ni ba. (Ish'iya'u 43: 10-11).
Da wannan ne yake bayyana cewa faɗin Allantakar Isa, ko Ran tsarki ko waninsu ba shi da madogara, kuma babu wani dalili a kansa, su ba komai ba ne sai ababen halitta daga halittar Allah, su a al'amari ba komai ba ne, su ba iyayen giji ba ne, kuma ba tajalli ne ga Allah ba, ko jikintaka ko tamka gare Shi. Babu komai tamkar Sa gwargwadan yadda Littafi abin tsarkakewa ya ambata da kuma Alƙur'ani mai girma.
Haƙiƙa Allah Ya yi fushi a kan Yahudawa sabo da ɓatansu da kuma bautarsu wasu Allolin wanin Sa. "Fushin Ubangiji ya yi tsanani akansu". (Adadi 25: 3). Kuma Annabi Musa - aminci ya tabbata a gare shi - ya karya ɗan maraƙinsu na zinari.
Ta wani ɓangaren da ban, wani ɓangare na jama'a masu kaɗaita Allah daga Kiritoci sun sha fama da azaba da takurawa, domin cewa su sunyi imani da kaɗaitakar Allah, kuma sun ƙi canza koyarwar Annabi Isa miƙaƙƙiya (Mai kaɗaita Allah) kuma sun yi inkarin bidi'ar iƙirarin cewa Allah uku ne, wacce ta bayyana a kan hannayen Bolis da mabiyansa.
A taƙaice dai Allah Ya aiko Adam, da Nuhu, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da Muhammad, da dukkanin Annabwa da Manzanni (Tsiran Allah da amincinSa su tabbata garesu baki ɗaya) don kiran mutane zuwa ga imani da tsarkake bauta gare Shi Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya, babu kishiya gare Shi, tsarki ya tabbbatar maSa. Wannan shi ne saƙonsu guda ɗaya.
Ubangiji Gaskiya Shi kaɗai yake, to, ku bauta maSa Shi kaɗai.
Yayin da ya zama cewa saƙon Annabawa da Manzanni ɗaya ne, sabo da haka, to, Addininsu shi ma ɗaya ne. To menene Addinin waɗannan Annabawan da Manzannin?
Lallai cewa jauharin saƙonsu yana tsayawa ne a kan "Miƙa wuya" ga Allah, waccan kalmar wacce ta ke bayyanar da ma'anar "Musulunci", kuma da ma'anar sa a harshen Larabci.
Haƙiƙa Alƙur'ani mai girma ya ƙarfafa cewa Musulunci shi ne Addinin gaskiya ga dukkanin Annabawan Allah da Manzannin Sa, kuma zai yiwu bibiyar wannan haƙiƙar ta Alƙur'ani a cikin Littafi abin tsarkakewa kuma (Zamu bi wannan haƙiƙar a cikin Litttafi abin tsarkakewa a cikin ƙananan littattafai masu gabatowa in sha Allah).
A ƙarshe, yana wajaba a kammu don tabbata a kan tsira karɓar wannan saƙon da imani da shi da gaskiya da tsarkakewa, sai dai wannan aikin kaɗai ba ya isa! kai yana wajaba a kammu yin imani da dukkanin Annabawan Allah da Manzannin Sa (Imani da Annabi - Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tattaro wannan) da bin shiriyarsu da aiki da ita. Wannan shi ne tafarki zuwa rayuwa mai arziƙi ta har abada.
Ya kai wanda ya ke neman gaskiya da ikhlasi kuma yake son tsira, wataƙila za kayi tinani a wannan al'amarin, kuma za ka yi lura a cikinsa a yanzu kafin wucewar lokaci, kafin mutuwar da za ta zo a fuj'a! Waye ya san yaushe ne?
Bayan tunani da sake duba a wannan al'amarin mai muhimmanci mai yankewa, da kuma hankali mai ganewa da zuciya mai gaskiya, za ka iya tabbatar da cewa Allah ɗaya ne, ba Shi da abokin tarayya, kuma ba Shi da ɗa, ka yi imani da Shi, ka bauta maSa Shi kaɗai, kuma ka yi imani da cewa Muhammad Annabi ne kuma Manzo ne irin Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa.
A yanzu zai iya yiwuwa ka furta - idan kaso - waɗannan kalmomin:
Ina shaida cewa lallai babu wani Ubangiji wani abin bautawa da gaskiya sai Allah. kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne
Wannan shahadar ita ce matakin aiki na farko akan hanya zuwa rayuwa ta har abada mai arziƙi, kuma ita ce mabuɗi na haƙiƙa ga ƙofofin Aljanna.
Idan ka tabbatar da riƙon wannan hanyar, to, zai iya yiwuwa gareka ka nemi taimakon abokinka ko maƙocinka musulmi, masallaci mafi kusancin ko cibiya ta Musulunci, ko ka faranta mini ta hanyar yi min waya, ko ta hanyar aiko min da wasiƙa (Zan zama mai farin ciki da hakan).
( Kace (Allah Ya ce) Ya ku bayiNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukansu, kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah, lallai Allah Yana gafarta zunubai baki ɗaya, lallai cewa Shi Shi ne Mai yawan gafara Mai jin ƙai. Ku koma zuwa ga Ubangijinku ku miƙa wuya gare Shi tun kafin azaba ta zo muku sannan ba za'a taimakeku ba. Ku bi mafi kyawun abin da aka saukar gareku daga Ubangijnku tun kafin azaba ba ta zo muku bagtatan ba alhali ku bakwa ji). Alƙur'ani mai girma - lambar Surar 39 ayoyi 53-55.
A nan akwai wani abu da ban...
Mai ɗarsuwa na ƙarshe:
Bayan karantawarka wannan saƙon guda ɗaya karatu na kiyayewa na tuntuntunin ma'anoni, masu gaskiya masu ƙoƙari za su iya tambaya: Menene haƙiƙar? Menene mataki? Menene aiki?
Da sannu zan tattauna waɗannan tambayoyin da wasunsu a cikin rubututtukana masu zuwa in Allah Ya so.
Saboda wasu al'amura na ƙari, ko tambayoyi, ko shawarwari, ina ƙaunar kada ka yi taraddudi a saduwa da mawallafin ta hanyar adireshin nan mai zuwa:
Akawatin gidan waya P.O. Box 418 - Al-Hufuf - Al-Ahsa'i 31982 ƙasar Sa'udiyya / [email protected] [email protected]
Ko ofis...
Muna maraba da dukkanin wani daidaitawa ko gyara.
Allah Ɗaya Gaskiya a cikin Alƙur'ani.