×
Haqiqa na leqa cikin wannan littafi Mai anfani wanda akayima suna da mafi alherin guziri na Dan uwa injiniya Hakam Dan Adil zumu Al-Aqily, sai na mayar dashi littafi Mai anfani da amfanarwa, Mai littafin ya tattara ayyuka masu falala ta hanya Mai sauki da dadi... yadda ya koro a cikin sa maganganu, da hadisai da labarai wanda sanya shauki, Haqiqa Qwaqwalwa ta tayi kai komo cikin farfajiyar wannan baituka: Yakai matarran kwakwalan mu da mafi alherin guziri Daga karantarwan mafi alherin manzo zuwa ga bayi Ka hada acikin sa dukkanin Abunda yake da dadawa Na fa'idoji wanda suke haskaka zuciya da shiriya Ubangijin al arshi ya saka maka da Abunda ya fishi Da alheri Duniya da kuma lahira