×
Malan yayi bayani akan abubuwan da suke kawo ba adiyyah a sallah wanda wajibine kowane musulmi yasansu kuma yakiyayesu.

    ABUBUWAN DA SUKE KAWO BA'ADIYYAH A CIKIN SALLAH

    [Hausa هوسا-]

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu

    2014 - 1435

    الأسباب التي توجب السجود بعد السلام

    [Hausa هوسا-]

    الشيخ: علي محمد السادس

    2014 - 1435

    ABUBUWAN DA SUKE KAWO BA'ADIYYAH A CIKIN SALLAH

    Gabatarwa: Ayanzu za'a kawo bayanaine akan abubuwan da suke sanya ba'adiyyah kadai, da fatan Allah ya an fanar da mu.

    Manyan abubuwan da suke haifar da ba'adiyyah, abubuwane kamar haka:

    1. Kari (Da mantuwa)

    2. Kokwanto

    Wadannan sune manyan abubuwan da suke kawo sujjadar ba'adiyyah, kuma akan su za muyi bayani a wannan karon da izinin Allah.

    Idan mutum ya yi kari a sallah da rafkannuwa ba wai daganganba to ba'adiyyah zai yi, kamar mutumin da ya kara raka'a a asuba ta zama uku, ko a magariba ta zama hudu, ko kuma a azahar ko la'asar ko kuma lisha ta zama biyar to hukuncinshi anan ya yi sujjadar ba'adiyyah domin ya yi kari.

    Haka mutumin da ya kara sujjada a raka'a ta zama uku ko ya kara ruku'i ya zama biyu, amma da mantuwa shi ma ba'adiyyah zai yi.

    Wanda ya yi Magana a cikin sallah da mantuwa shima ba'adiyyah zai yi, ko ya sallame daga raka'a biyu da mantuwa, saida ya sallame ya tuna to anan sai ya ciko ragowar raka'o'in sannan ya yi ba'adiyyah.

    Wanda ya karanta surori biyu ko sama da biyu a raka'a guda, ko ya fita daga surar da yake karantawa zuwa wata surar ko kuma ya yi ruku'i kafi ya kammala karatun surar duk anan ba komai akan shi, wato ba kabaliyyah kuma ba ba'adiyyah, haka kuma wanda ya yi nuni da hannusa ko da kansa kuma yana cikin sallah, saidai yana rage lada.

    Wanda ya maimaita karatun fatiha a raka'a duga da rafkannuwa to shima zai yi ba'adiyyah.

    Amma wanda ya tuna cewar bai karanta suraba bayan kuma ya sunkuya zuwa ruku'u to anan bazai koma tsaye domin ya karantaba, saidai bayan sallama ya yi kabaliyyah, saidai idan ya tuna asurtawane ko bayyanawa kafin ya yi ruku'i to anan zai sake karatun, idan karatun surane zai sake karatunne ba wata kabaliyyah ko ba'adiyyah, amma idan karatun fatihane zai sake din amma kuma zai yi ba'adiyyah.

    Wanda kuma ya mike bayan ya yi raka'a biyu amma kuma bai zauna ba sai ya tuna kafin hannayansa da gwiwowinsa su bar kasa shikenan sai ya koma ya zauna ba komai akansa, in ko ha ya rabu da kasane to sai ya ci gaba ba zai dawo ya zaunaba saidai zai yi kabaliyyah domin ya rage wani abu a sallarshi, idan kuma bayan ya mikedin ya dawo ya zauna bayan kuma ance da shi ya wuce to anan sallarshi ta yi sai dai zai yi ba'adiyyah ne saboda ya yi kari na wannan mikewar.

    Wanda ya yi atishawa a cikin sallah baya cewa ''Alhamdu Lillah'' idan kuma har ya fadadin sallah shi nanan kuma ba komai akanshi, sannan kuma baya maida gaisuwa ga wanda ya gaida shi saboda yana cikin sallah.

    Wanda kuma ya yi hamma yana cikin sallah sai ya rufe bakinsa shikenan.

    Wanda kuma ya sa wata kalma alokacin da ya karatu wacce ba ta Kur'ani ba zai yi ba'adiyyah ne, amma idan ta Kur'anice babu komai akanshi, saidai idan ya canza lafazi ko ya bata ma'ana to anan sai ya yi ba'adiyyah. Lalle wadannan bayanai za su sa mutsaya mu gyara karatummu na sallah da kuma limamammu, domin ana tafka kurakurai a karatuttukan sallah.

    Amma kuma wanda ya manta da ruku'i saida yana sujjadah ya tuna to sai ya koma tsaye, sannan an so ya sake wani abu na karatun sallah, sannan sai ya yi ruku'in ya kuma ci gaba da sallar, bayan ya kammala sai ya yi ba'adiyyah.

    Sannan wanda ya manta sujjada guda bai yi ta biyun ba, saida ya mike sannan ya tuna to kawai zai dawo ya zaunane sannan ya yi wannan sujjadar, saidai idan ya yi wannan zaman kafin ya mike to kawai sai ya wuce zuwa gabatar da wannan sujjadar kai-tsaye, bayan ya kammala saii ya yi ba'adiyyah.

    Wanda kuma ya manta da sujjadu biyu sai bayan ya mike sannan ya tuna to kawai zai tafi zuwa gabatar da wadannan sujjadunne ba tare da ya zauna ba, sannan ya yi ba'adiyyah.

    Abu na biyu daga cikin abubuwan da suke janyo ba'adiyyah a cikin sallah shine :-

    Kokwanto:

    Idan mutum ya yi kokwanton sallarshi ta cika ko bata cika ba sai ya kawo abinda ya yi kokwanton sannan ba'adiyyah, misali; Idan ya yi kokwanton shin ya yi sujjadar ta cika ko bata cika ba, sai ka cika sannan ka yi ba'adiyyah.

    Idan mutum ya yi kokwanton wannan raka'ar itace ta hudu ko itace ta uku sai ya barta itace tau kun sai ya kawo cikon ta hudun sannan ya yi ba'adiyyah.

    Mutum mai yawan wasuwasi to abinda da ake so daga gareshi shine yabar wasuwasin ya kakkabeshi daga zuciyarsa ba zai kawo abinda ya yi kokwanton akanshi ba, sai bayan ya sallame sai ya yi ba'adiyyah, shin kokwanton akan karine ko akan ragi. Wannan yana nuna mana mafita daga mutanan da suke da yawan kokwanto da wasuwasi, Allah ya yaye musu mu kuma ya tsaremu, amin.

    Idan mutum ya yi shakkun yana da hadasi ko bai da shi? Sannan sai ya dan yi tunani kadan sai kuma ya samu tabbas akan yana da tsarki to ba komai akanshi, dudda ya yi hakan ne a cikin sallah.

    Yin rafkannuwa a sallolin da ake ramakwansu daidaine da wadanda ake yin su cikin lokaci ba banbanci, kenan suma kabaliyyah da ba'adiyyah tana shiga cikinsu.

    Idan mamu ya yi lafkannuwa alokacin yana bayan liman to liman ya dauke masa, misali; da aka yi zaman tahiya na farko kawai sai ka yi sallama ka dauka an gama sallar, ko kuma kuna sujjada sai ka ji wani ya yi kabbara sai ka taso daga sujjadar ka dauka liman sai ka ga ba haka bane sai ka koma sujjadar duk bakomai akanka, saboda kana bayan liman.

    Idan masabuki (wanda yake ciko sallarsa bayan sallamar liman) ya yi rafkannuwa a lokacin da yake kawo raka'o'in da suka wuce masa bayan sallamar liman to fa anan hukuncinsa hukuncin mai sallah ne shi kadai saboda haka ba'abinda liman ya dauke masa domin tuni liman ya sallame shi, saboda haka idan kabaliyyah ta kamashi a wannan lokacin sai ya yi ta hakama idan ba'adiyyah ce.

    Idan kabaliyyah ko ba'adiyyah ta kama liman to ta shafi mamu ko tare dashi abin ya faru ko ba tare da shi bane.

    Idan kabaliyyah ta kamaliman to mamu zai yi tare da liman, sannan idan liman ya sallame sai ya mike ya kawo ragowar raka'o'insa. Amma idan ba'adiyyah ce to bazaka yi tare da liman ba har sai ka ciko ragowar abinda ake binka ka yi sallama sannan ka yi ta, kasan dalilin da liman ya yi ta ko baka saniba.

    Idan mutum ba'adiyyah ta kamashi ta bangaran liman, sannan da ya tashi yana kawo abinda ya saura akansa sai kuma kabalillah ta same shi to anan idan ya yi kabaliyyar ta wadatar, ba sai ya yi ba'adiyyar ba.

    Wanda ya yi kokwanton ''shin yanzu yana wuturine ko yana raka'a ta biyun shafa'ine''? to sai ya barta itace raka'a ta biyun shafa'in, sannan bayan ya sallame sai ya yi ba'adiyyah sai kuma ya mike ya kawo wuturin.

    Idan kuna sallah tare da liman sai shi limamin ya yi rafkannuwa ta yadda ya yi kari ko ya rage to mamu tasbihi zai yi, sai kace ''Subhanallahi'', idan liman ya kara sujjada ta zama uku to abinda zaka yi shine tasbihi ba zaka yi sujjadar ta uku tare da shi ba.

    Idan liman ya tashi zuwa raka'a ta biyar to duk wanda ya tabbatar itace ta hudun sai ya bishi, haka kuma duk wanda yake kokwanto; shin ta biyarce ko ta hudu, to shima zai mike ya bishi. Amma duk wanda ya tabbatar wannan raka'ar itace ta biyar to ba zai bi shi ba sai ya yi zamanshi.

    Idan liman ya sallame kafin sallah ta cika, to wadanda ke bayansa sai su yi masa tasbihi wato su ce ''Subhanallah'', idan liman ya gasgata wanda ya yi tasbihin sai ya mike ya ciko sallar, sai kuma a yi ba'adiyyah, idan kuwa liman yana kokwanto akan hakan, sai ya tambayi mutane biyu adilai, kuma ya halatta su yi Magana anan, idan kuwa shi liman yanada yakini akan sallar ta cika to sai ya yi aiki da yakinin na sa, ya ajiye tanbayar, saidai idan mutanen dake bayansa sun ta tasbihi sai ya bar yakinin na sa, ya koma zuwa ga abinda suke a kai, kamar yadda mai Akhdari ya zayyano.

    Kammalawa: Wannan shine gwargwadon abinda ya samu na bayani akan rafkannuwa a cikin salloli na farilla, ko na ramuwa ko wadanda ake yin su a lokacinsu, da fatan zamu kara kusantar inda malamai suke. Akaro na gaba da izinin Allah madaukakin Sarki zamu kawo bayanaine dangane da rafkannuwa a cikin salloli na nafilfili. Ga dukkan mai tambaya kofa a bude take, fatammu shine Allah ya karbi ayyukammu ya kuma sanya mu cikin wadanda ya yiwa rahama.

    Kammalawa: Adaidainan zamu dakata kan abinda ya shafi yin ba'adiyyah ta sanadiyyar kari da mantuwa, a karo na gaba bayanai za su zo akan ba'adiyyah ta sanadiyyar kokwanto, da fatan mun anfana.

    Rubutawa :

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu