×
Malan yayi bayani akan abubuwan da suke kawo kabliyyah a sallah wanda wajibine kowane musulmi yasansu kuma yakiyayesu.

    ABUBUWAN DA SUKE KAWO KABALIYYAH

    [Hausa هوسا-]

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu

    2014 - 1435

    الأسباب التي توجب السجود قبل السلام

    [Hausa هوسا-]

    الشيخ: علي محمد السادس

    2014 - 1435

    ABUBUWAN DA SUKE KAWO KABALIYYAH

    Gabatarwa: Ayanzu za'a kawo bayanaine akan abubuwan da suke sanya kabaliyyah kadai, sannan bayan haka a kawo bayanai akan abubuwan da suke sanya ba'adiyyah suma su kadai, fatammu a tsaya a karanta bayanan a natse kuma a fahimcesu, idan akwai abninda ya shigewa mutum yana da dama ya yi tambaya, da fatan Allah ya ganar da mu.

    Abubuwan Da Suke Kawo Kabaliyyah: Manyan abubuwan da ke sawa a yi sujjadar Kabaliyyah su ne;

    1. Ragi.

    2. Ragi Da Kari.(Alokaci guda)

    Dukkan mutumin da ya yi ragi a sallar sa to kabaliyyah ta kamashi, kamar:

    1. Karatun Sura: Idan mutum ya manta a raka'ar farko ko a ta biyu bai karanta suraba kawai shi da ya karanta fatiha sai ya yi sujjada, to wannan kabaliyyah ta kamashi.

    2. Asurtawa A Inda Ake Bayyanawa: Duk wanda ya yi karatun sallah sirrance a inda ake bayyanawa, to wannan shima kabaliyyah ta kamashi.

    3. Fadin ''Sami'allu Liman Hamidah'' haka wanda ya manta da fadin wannan kalma kabaliyyah zai yi domin rage.

    4. Tahiyar Farko: Duk wanda ya barta to ya yi ragi a sallarsa kabaliyyah zai yi.

    5. Zama Domin Tahiyyar Farko: Haka duk wanda ya manta da zaman tsakiya shima kabaliyyah zai domin ai shi ya rage manyan sunnonine ma guda biyu. Zama domin tahiyyar da kuma ita kanta tahiyyar.

    6. Tahiyyar Karshe: Itama dukkan wanda ya manta bai yi ta ba to kabaliyyah ta kamashi.

    7. Zama Domin Wannan Tahiyyar Ta Karshe: Shima zaman duk wanda ya manta ya barshi to kabaliyyah zai yi. Kada ku sha'afa zaman da ya karu akan gwargwadon sallama shine ake Magana, amma shi zama gwargwadon sallama wannan wajibine, idan mutum ya barshi kabaliyyah ko ba'adiyyah bata daukeshi.

    Sannan dukkanin wadannan abubuwa da aka bari, ana maganane idan akabarsu da mantuwa ba wai daganganba.

    Ragi Da Kari. (Alokaci guda)

    Hakanan dukkan mutumin da ya yi ragi a cikin sallah kuma ya yi kari a cikin sallar to shima kabaliyyah zai yi, misali mutumin da ya manta bai yi zaman farkoba wato da ya kammala raka'a biyu maimakon ya zauna ya yi tahiyyah sai ya manta ya mike zuwa raka'a ta uku, sannan kuma da ya raka'oin mai makon ya zauna sai ya ci gaba ya kara wata raka'ar ta zama hudu idan a magaribane ko ta zama biyar idan a azaharne ko la'asar ko lisha. To ka ga wannan a sallah guda ya yi ragi domin bai yi zaman farkoba kuma ya yi Karin raka'a to shima kabaliyyah zai yi shikenan ya gyara sallar shi.

    Wanda sujjadar kabaliyyah ta kamashi amma sa ya manta bai tuna ba sai bayan da ya yi sallama, shikenan sai ya yi ta a wannan lokacin ta zama ba'adiyyah kenan kuma sallar ta yi, to amma idan bai tuna da hakanba sai bayan wani lokaci ko ma har ya fita daga masallaci to anan sujjadar ta baci, haka itama sallar zata iya baci idan ya rage sunnonin da suka kai uku ko sama da haka.

    Rafkannuwar da mamu ya yi alokacin yana bayan liman to liman ya dauke masa, saidai idan mamun ya rage farillane kama ya bar sujjada, ko sallama..''.

    Idan mamu ya yi rafkannuwa ko ya yi gyangyadi ko ma aka matse shi bai sami damar yin ruku'i ba sannan kuma ba'a raka'ar farko bace to anan idan ya tabbatar zai iya samin liman kafin ya dago daga sujjada ta biyu ta wannan raka'ar sai ya yi ruku'in ya riski limamin, amma idan ya tabbata ba zai same shi ba, sai ya bar ruku'un, wannan raka'ar kuma sai ya ajiyeta gefe guda sai ya rama wata raka'ar a matsayin wannan din bayan sallamar limamin nasa, babu kabaliyyah ko ba'adiyyah.

    Idan kuma ya yi rafkannuwane ya bar sujjada ko aka matseshi ko ya yi gyangyadi har liman ya tashi zuwa wata sabuwar raka'ar to anan idan ya tabbatar zai riski liman kafin ya yi ruku'i sai ya yi sujjadar, amma idan ya tabbata ba zai iya riskar liman ba sai kawai ya hakura ya ci gaba da bin limamin sai ya rama raka'ar da bai yi mata sujjada ba, bayan liman ya sallame.

    Kada mutum ya yi mamaki ya ji an ce 'an matse shi' ka dauki al'amarin da fadi bawai iya garin ku ba, domin idan Allah ya kaika kasa mai tsarki zaka ga irin cunkoson da ake yi alokutan sallah, musamman idan ya yi daidai alokacin Hajji ka je ko Umarah.

    Kammalawa: Wadannan kadan kenan daga cikin abubuwan da suke sabba sujjadar Kabaliyyah, da mun anfana kuma zamu kara kusantar malamai, a karo na gaba za'a kawo bayanaine akan abinda ya shafi sabuban sujjadar ba'adiyyah, da fatan Allah ya kai mu lokacin ta re da imani, amin.

    Rbutawa :

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu