×
Yayi Magana ne akan HUKUNCIN JININ HAIHUWA ( JININ BIKI) ,da sauran mas alolinsa

    HUKUNCIN JININ HAIHUWA ( JININ BIKI)

    [Hausa هوسا-]

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu

    2014 - 1435

    أحكام دم النفاس

    [Hausa هوسا-]

    الشيخ : علي محمد السادس

    2014 - 1435

    HUKUNCIN JININ HAIHUWA ( JININ BIKI)

    Gabatarwa: Da sunan Allah Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna daukene da abinda ya shafi jerin hukunce hukuncen jinin biki wanda ake kira jinin haihua wanda yake da izinin Allah bayanshi za mu kawo a wannan karon bayan da abayanan da suka gabata muka kawo bayanai akan jinin al'ada.

    Menene Jinni Biki: Jinine da yake fitowa daga mahaiffa ta sanadiyyar haihuwa. Kenan shi jinin biki jinine da yake da alaka da haihuwa, idan mace taga jini kwana daya ko biyu kafin haihuwa to shima malamai suna lissafashi cikin jinin haihuwa.

    Mafiyawan Kwanakinsa: Mafi yawan kwanakin da macan data haihu zata ga jinin haihuwa malamai sun karawa juna sani, wadansu sukace kwanaki ar'bainne (40), wadansu kuma sukace kwanaki sittinne (60) kamar yadda mai Akhdari ya bayyana. Sabanin na al'ada shi kwanaki goma sha-biyarne.

    Idan mace ta haihu sai jinin bai dauke ba to zata jira kwanaki arba'in, ko sittin, idan ya dauke a kwanakin shikenan sai ta yi wankan tsarki na daukewar jinin haihuwa ta ci gaba da sallah da kuma sauran ayyuka na ibada, idan kuma bai daukeba to sai a nemi magani ya zama jinin ciwo sai ta yi wankan tsarki ta ci gaba da ibada, idan kuma jinin ya dauke kafin kwanakin kamar ya dauke ranar da aka yi haihuwar to annan ma zata yi wankana ta ci gaba da sallah, laifine maigirman gaske mace jinin haihuwarta ya dauke amma taki yin sallah wai sai ta yi arba'in wannan ba tsari bane na addinin musulunci, domin tsarin musulunci dazarar jinin yananan kafin kwanaki arba'in to dazarar ba za'a yi sallah ba, amma dazarar jini ya dauke ko kafin sunane to dazarar za'a ci gaba da sallah, sai a kiyaye.

    Imam Tirmizi yake cewa: Malamai sun yi ijima'i tun daga Sahabbai da Tabi'ai da wadanda suka zo bayansu (Sun yi ijima'i) akan cewa lalle mace mai haihuwa zata bar salla tsawon kwanaki arba'in sai dai idan ta ga tsarki kafin hakan (kafin kwanaki arba'in din) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah.

    Idan mace ta yi bari sai ya zamana halittar mutum ta bayyana a barin kamar ace ga tsarin halittar ba wai gudan jini bane ya zamana kuma akwai jini day a zuba to anan tana da hukuncin jinin biki jinin haihuwa, gwar gwadon kwanakin da asune ahalittar take bayyana a ciki sune watanni ukune galibi ammadai mafi karanci sune kwanaki tamanin (80).

    Idan ta yi barin gudan jini ko gudan tsoka ta yadda halittar mutum bata bayyanaba to ba'a la'akari da wannan jinin da ya zubo, saboda haka ba zatabar sallah ba kuma ba zatabar azumiba saboda jinin domin bata da hukuncin jinin biki.

    Idan jinin haihuwa ya dauke kafin wadancan kwanakin da aka yi bayaninsu to zata yi wankane ta kuma yi sallah ko da jinin ya daukene a ranar da aka yi haihuwar, to idan jinin ya dauke kafin wadancan kwanakin sai kuma ya dawo to sai mu tsaya mu gani idan tsakani daukewar da dawowar ya kai kwanaki goma sha-biyar zuwa abinda ya yi sama to wanda ya dawodin jinin al'adane bana biki bane, amma idan tazarar batakai kwanaki goma shabiyarba to jinin da ya dawo cikon jinin haihuwane.

    Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai Jinin Bikiba: Mu sani dukkan abuwan da jinin al'ada yake hanawa ayiwa mai al'ada to jinin haihuwama yana hanawa a yi wa mai biki, haka namma abinda jinin al'ada yake hanawa mai al'adar ta yi to jinin haihuwama yana hanawa ta yi, kamar: Saki, saduwa, taba Alkur'ani, zama a masallaci dadai sauransu kamar yadda bayani ya gabata a jinin al'ada.

    Haka namma kamar yadda ya halatta mai al'ada ta yi kunzugu megidanta ya shasshafata ya taba ko ina a jikinta in banda daga cikibiya zuwa gwiwa to haka namma ya halatta ga mai jinin haihuwa.

    Kammalawa: Daga wadannan takaitattun bayanai da suka gabata ya bayyana a fili cewa al'amarin jinin haihuwa ba abune da za'a yi wasa akansaba, watakila hankali ya tafi kan bukukuwa suna maijego kuma bata sallah kuma ga shi jinni ya dauke, kuma mun fahimci munin tsohuwar al'adar nan na cewa maijego sai ta yi arba'in kafin ta fara sallah ashe al'amari da bashi da alaka da addinin.

    Rbutawa :

    Malan Aliyu Muhammad Sadisu