×
SHAHARARRUN SUNNONIN DA SUKA YADU NA AKIDAR RABAUTACCIYAR TAWAGA MAI NASARA

 SHAHARARRUN SUNNONIN DA SUKA YADU NA AKIDAR RABAUTACCIYAR TAWAGA MAI NASARA

Hafiz Bn Ahmad Alhakami

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa kuma ya sanya duffai da haske, sa’an nan kuma wadanda suka kafircewa Ubangijinsu suke karkacewa. Shi ne wanda ya halicceku daga laka, sa’an nan kuma ya yanka wani Ajali, alhali wani ajalin ambatacce yana gurinsa. S’an nan kuma ku kuna yin shakka. Kuma shi ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin kasa, yana sanin asirinku da bayyananku, kuma yana sanin abin da kuke yi na tsiwurwuta

Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya Makadaici ne wanda ake nufi da bukata bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba kuma babu daya da ya kasance tamka a gare shi bari ma abin da yake cikin sammai da kasa duka ga re shi suke da’a shi ya kirkiri sammai da kasa kuma idan ya nufi wani al’amari to sai kawai ya ce da shi kasance sai yana kasancewa kuma Ubangijinka ne yake halittar abin da ya so kuma ya zaba, zabi bai kasance a wajansu ba tsarki ya tabbata ga Ubangiji kuma ya daukaka ga abin da suke yin shirka, ba a tambayarsa game da abin daya aikata kuma su ne ababan tambayar.Kuma ina shaidawa cewa shugaban mu kuma Annabin mu Muhammad Bawansa ne kuma Manzansa ne kuma ya aiko shi da shiriya da kuma Addinin gaskiya domin ya rinjayar da shi a kan Addinai dukansu kuma koda Mushirikan sun ki hakan.Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa wadanda suka yi hukunci da gaskiya kuma da shi ne suka kasance suna adalci, da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa wadanda ba sa kaucewa ga barin sunna bari dai ita kadai suke bibiya kuma da ita ne suke ruko kuma a kanta suke soyayya kuma suke kiyayya kuma a wajanta ne suke tsayawa, kuma ga barinta suke korewa kuma suke kariya da kuma dukkan wanda ya bi hanyarsu har zuwa ranar da za a tashe suBayan haka to wannan wani abin takaitaccen littafi ne mai girmma kuma mai anfani, mai girman fa’ida mai tarin abubuwan amfani,wanda yake tattare da ka’idojin addini, kuma yana kunshe da asalan tauhidi wanda Manzanni suka yi kira izuwa gare shi kuma aka saukar da littattafai da shi kuma babu tsira ga wanda yake yin addini da waninsa, kuma yana shiryarwa izuwa ga bin hanya mai haske kuma tsarin gaskiya ne mabayyani na yi bayanin al’amuran imani da dabi’unsa a cikinsa, da kuma abin da yake gusar da shi baki daya koma ya kore cikarsa.kuma na ambaci kowace mas’ala a cikinsa tare da dalilanta, domin al’amarinta ya bayyana kuma hakikaninta ya fito sarari kuma hanyarta ta bayyanu, kuma na takaita a cikinsa abisa matafiya ta sunna kuma na wofantu da maganganun ‘yan bin son zuciya da ‘yan bidi’a, domin ita ba a ambatonta face don yin raddi a gare ta, da kuma harba kibiyar sunna a kanta, kuma hakika manyan shuwagabanni sun toshe ga yayewar aibinta, kuma suka rubuta littattafai masu zaman kansu a cikin raddinta da nisantata tare da cewa ana gane kishiya da kishiyarsa kuma ya fita da gane hakikaninsa shi kadai, to idan Rana ta fito yini baya bukatuwa zuwa mai kafa Dalili da ita.kuma idan gaskiya ta bayyana ta fito sarari to babu abin da yake bayanta face bata kuma na tsara shi a bisa hanyar tambaya domin Dalibi ya farka kuma ya fadakuSannan na raba masa da amsa wacce Al’amarin zai bayyana da ita kuma ba zai rikitar ba kuma na Saka Masa suna "Futattun Sunnoni da suka yadu, don kudircewar tawagar da ta ke cin Nasara"Kuma Allah nake roko ya sanya shi don Girman sa mafi daukaka, kuma ya amfane mu da abin da muka sani, kuma ya sanar da mu abin da zai amfane mu saboda ni’ima daga gare shi da falala cewa shi a bisa dukkan komai mai iko ne kuma ga Bayinsa mai tausasawa ne masani, kuma makoma tana izuwa gare shi kuma shi ne majibincinmu to madalla da Majibinci kuma madalla Mataimaki.

 Farkon abin da ya wajaba akan bayin Allah

Farkon abin da yake wajaba a kan Bayi sanin al’amuran da Allah ya haliccesu da shi, kuma ya riki alkawari da shi a kansu kuma ya aiko Manzanninsa da shi izuwa gare su, kuma saboda shi ne ya halicci Duniya da Lahira da Aljann da Wuta da shi ne za a yi kiran gaskiya kuma mai afkuwa ta afku kuma a cikin sha’aninsa ne za a kafa Ma’aunai kuma takardu su dinga tashi kuma a cikinsa tsiya da arziki take kasancewa kuma a bisa hisabinsa ake raba haskeKuma duk wanda Allah bai sanya masa Haske ba to bashi da wani guri da zai samo Hasken

 Al’amarin da Allah ya halicci halittu saboda shi

wane abu shi wancan al’amarin da Allah ya halicci halitta saboda shi?

Allah Madaukaki ya cekuma ba mu halicci Sammai da kasa da kuma abin da yake tsakaninsu wasa ba bamu halicce su ba face da gaskiya kuma sai dai mafi yawansu ba su sani bakuma Allah Madaukaki ya cekuma ba mu halicci Sama da Kasa da abin da yake tsakaninsu ba da gaskiya ba wancan zato ne na wadanda suka kafircekuma Allah Madaukaki ya ceKuma Allah ya halicci Sammai da Kasa da gaskiya kuma don a sakawa kowace rai abin da ta tsiwurwurta kuma su ba za a zalunce su bakuma Allah Madaukaki ya ceKuma bamu halicci Mutum da Aljan ba sai don su Bautamun

 Ma’anar Bawa

me ake nufi da Bawa?

Bawa idan ana nufi da shi abin bautarwa wato ababan kaskantarwa to shi da wannan ma’anar ya tattare dukkan ababan halitta na daga talikai na sama da na kasa mai hankali da waninsa da danye da busashshe da mai motsi da mara motsi da bayyanane da boyayye da mumini da kafiri da managarci da fajiri da wadansun wadannan duka ababan halitta ne na Allah mai girma da daukaka ababan bauta ne gare shi mai horewa ne da horewarsa mai tsari ne da tsarawarsa, kuma kowanne daga cikinta wata alama ce da ya tsaya a gare shi kuma iyaka ce da ake tikewa izuwa gare shi kuma kowanne yana tafiya saboda wani ajali abin Ambato ba zai tsallake shi ba gwargwadon nauyin kwayar zarraWannan kaddarawar Mabuwayi ne Masanitsari ne na Adalci na mai Hikima, kuma idan ana nufi da shi mai ibada abin so an kebance wannan da muminai su ne Bayinsa ababan girmamawa, kuma masoyansa masu takwa, wadanda babu tsoro a kan su kuma ba za su kasance suna bakin ciki ba.

 Ma'anar Ibada

Mecece Ibada?

Ibada it ace: suna ne wanda ya game dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi na daga fadi da aiyuka na zahiri da na badini da kuma kubuta daga abin da yake kore wancan kuma yake kishiyantarsa.

 Yaushe ne aiki yake kasancewa Ibada

?Yaushe ne aiki yake kasancewa ibada

Idan abubuwa biyu suka cika a cikinsa kuma sune cikar so tare da cikar kaskanciAllah Madaukakin Sarki ya cekuma wadanda suka yi imani su suka fi tsananin soyayya ga Allahkuma Allah Madaukaki ya ceLalle ne wadanda suke masu sauna sabo da tsoran UbangijinsuKuma Hakika Allah ya tattare wadan nan a fadinsaLalle ne su, sun kasance suna gudun tsere zuwa ga ayyukan alheri. Kuma suna kiranmu a kan kwadayi da fargaba. Kuma sun kasance masu saunar (aikata sabo) gare Mu.

 Alamar soyayyar Bawa ga Ubangijinsa Mai girma da daukaka

Mecece Alamar soyayyar Bawa Ubangijinsa Mai girma da daukaka?

Alamar hakan : ya so abin da Allah Madaukaki yake so kuma ya yi fushi da abinda yake fusatar da shi kuma ya dinga misalta abubuwan da ya yi umarni da shi kuma ya nisanci hane hanensa kuma ya so masoyansa kuma ya yi ki ga makiyansa, kuma da wannan ne ya kasance mafi karfin imani shi ne so saboda Allah da kuma ki saboda shi.

 yadda Bayi za su gane abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi

Da wane abu ne Bayi za su gane abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi?

Za su gane shi Madaukaki ta hanyar aiko da Manzanni kuma da saukarwarsa littattafai yana mai umartarsu da abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi yana mai hana su ga barin abin da yake kinsa kuma da wancan ne hujjojinsa masu karfi suke tsayawa a kansu, kuma Hikimominsa isassu suka bayyana

Allah Madaukakin Sarki ya ceManzanni masu bayar da bushara kuma masu gargadi domin kada wata hujja ta kasancega mutane a kan Allah bayan manzanninkuma Allah Madaukaki ya ceKa ce: in kun kasance kuna son Allah to ku bi ni sai Allah ya so ku kuma ya gafarta muku zunubanku kuma Allah mai gafara ne mai jinkai ne

 Sharadan Ibada

Nawa ne sharadan ibada?

Uku ne:na farko: gasgata niyya kuma shi sharadi ne a cikin samuwarta, kuma na biyu: tsarkake niyya, kuma na uku: dacewar shari’a wanda Allah madaukaki ya yi umarni da kada a yi masa addini sai da shi, kuma su ne sharadai biyu a cikin karbarta

 Gaskiyar Niyya

Menene shi gaskiyar Niyya?

Shi ne barin kiwa da kuma jinkiri da yin matukar kokari wajen gasgatawar fadinsa da Aikinsa

AllahMadaukakin Sarki ya ceyaku wadanda suka yi imani don me kuke fadin abin dab a ku aikatawa? Ya girma ga zama abin kyama a wurin Allah, ku fadi abin da ba ku aikata.

 Ma’anar tsarkake Niyya

menene ma’anar tsarkake Niyya?

Shi ne nufin Bawa ya kasance baki dayan fadinsa da aikinsa na zahiri da na badini don neman yardar Allah Madaukaki

Fadin Allah maigirma da Daukaka:Kuma ba'a Umarce mu ba sai Mu bautawa Allah muna masu tsarkake Addini a gare shimuna masu kaucewa Bata, kuma mu tsaida Sallah kuma mu bada Zakka.kuma Allah Madaukaki ya ceKuma babu wani a wurinsa yake da bashin wata Ni'ama da zai saka Masa Kawai sai dai neman yardar Ubangijinsa Madaukakikuma Allah Madaukaki ya ceMuna ciyar da ku ne kadai domin neman yardar Allah kawai, ba mu nufin neman wani sakamako daga gare ku, kuma ba mu Neman godiya

kuma Allah Madaukaki ya ce

wanda duk ya kasance yana nufin noman Lahira za Mu kara masa a cikin nomansa, wanda kuma ya kasance yana nufin noman duniya za Mu sam masa daga gar eta,alhali kuwa ba shi da wani rabo a cikin Lahira

 Shari’ar da Allah ya yi umarnin kada a bauta masa sai da ita

Mecece shari’ar da Allah ya yi umarnin kada a bauta masa sai da ita?

Ita ce Al-hanifiyya wato hanyar Annabi Ibrahim

Allah Mai tsarki da daukaka ya ce

Lallai kadai Addini a wajen Allah shi ne Musulunci

kuma Allah Madaukaki ya ce

To wanin Addinin Allah suke zaba? kuma fa gare shi duk abin da yake sama da Kasa ya mika Wuya yana Mai bi cikin Yarda ko Tilastawa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma Babu wanda zai kyamaci Tafarkin Annabi Ibrahim, face wanda ya wawaitar da kansa

kuma Allah Madaukaki ya ce

kuma wanda ya zabi wanin musulunci ya zama addini, ba za a karba daga gare shi ba kuma shi a Lahira yana daga cikin masu hasara

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ko suna da wasu Abokan Tarayya ne da suke Shar'anta musu Addini abin da Allah bai musu Izini da shi ba

 Matakan Addinin musulunci

nawa ne Matakan Addinin musulunci?

yana Matakai uku ne: musulunci da imani da ihsani kuma kowa ne daya daga gar eta idan aka sake shi sai ya tattare Addinin baki dayansa

 Ma’anar musulunci

Menene ma’anar musulunci?

Ma'anarsa shi ne mika wuya ga Allah da kadaitawa, da kuma bin dokokinsa da yi masa biyayya, da kuma kubuta daga Shirka.

Allah ya yi masa Rahama

Kuma wane ne ya fi kyau ga Addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wanda ya mika fuskarsa zuwa ga Allah, alhali kuma yana mai kyautatawa to lalle ya yi riko ga igiya amintacciya

kuma Allah Madaukaki ya ce

Sa’an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne guda daya sai ku mika masa wiya. Kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai.

 Dalili a bisa gamewar musulunci addini dukkansa ya yin da aka saki

Menene dalili a bisa gamewar musulunci addini dukkansa ya yin da aka saki?

Allah Madaukaki ya ce:

Lallai kadai Addini a wajen Allah shi ne Musulunci

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Musulunci ya fara bako kuma da sannu zai koma yana bako kamar yadda ya fara

Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce

Mafificin musulunci shi ne imani da Allah

 Ma'anar musulunci da rukunansa biyar

Menene dalili a bisa arrafa shi da rukunansa biyar a wajan rarrabewa?

Fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin hadisin tambayar da Jibrilu ya yi masa ga addini

Musulunci shi ne ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa Annabi Muhammadu manzansa ne kuma ka tsaida salla kuma ka ba da zakka kuma ka azimci ramadana kuma ka ziyarci dakin Allah idan ka sami ikon tafarki izuwa gare shi

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

An gina musulunci a bisa abubuwa biyar

sai ya ambaci wannan sai dai cewa shi ya gabatar da hajji a bisa azimin ramadana kuma dukkanninsu suna cikin Bukahari da Muslim.

 Matsayin Kalmomin Shahada biyu daga addini

menene mahallin shahada biyu daga musulunci?

Bawa ba zai shiga addini ba face da su

Allah Madaukaki ya ce

kadai Muminai wadanda suka yi imani da Allah da Manzonsa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

An umarce ni na yaki mutane har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa Muhammadu Bawansa ne kuma Manzonsa ne

 Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

Menene dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?

Fadin Allah Madaukaki

Allah ya shaida cewa shi babu abin bautawa face shi kuma Mala’iku da ma’abota ilimi sun shaida, yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face shi, Mabuwayi, Mai hikima

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

To ka sani, cewa babu abin bautawa face Allah

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

kuma babu wani abin bauta face Allah

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Allah bai riki wani abin haihuwa ba kuma babu wani abin bauta tare da shi

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Ka ce da akwai wadansu abubuwan bautawa tare da shi, kamar yadda suka fada a lokacin,da sun nemi wata hanya zuwa ga ma’abocin Al’arshi

 Ma’anar shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

Menene dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?

Ma’anarta: korewa cancantuwar ibada ga duk wanda ba Allah ba da tabbatar da ita ga Allah Mai girma da daukaka shi kadai ba shi da Abokin tarayya a cikin bautarsa kamar inda kuma cewa ba shi da abokin tarayya a cikin mulkinsa

Allah Madaukakin Sarki Yace

ذلك بأن الله هو الحق وأن ما يدعون من دونه هو الباطل وأن الله هو العلي الكبير

 Sharadan cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

Menene sharadan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wacce ba ta amfanar mai fadinta face da haduwarta a cikinsa?

Sharadanta bakwai ne:

Na farko: sanin ma’anarta halin korewa da tabbatarwa

kuma na biyu: yakinin zuciya da ita

na uku: jawuwa a gare ta a zahiri da badini

na hudu: karbarta alhalin ba za a komar da wani abu daga abubuwan da ta lazimta ba da kuma ta hukuntar

na biyar: tsarkaka a cikinta

Na shida: Gaskiya daga cikin kokon zuciya ba kawai fada da Baki ba

na bakwai: soyayya a gare ta da kuma ahalinta, da kuma jibinta da gaba saboda ita.

 Dalilin sharadanta sani da La’ilaha illallahu

menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?

Fadin Allah Madaukaki

face wanda ya yi shaida da gaskiya

Yana nufin Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

kuma su suna sani da zukatansu ma’anar abin da harsunansu suka yi furuci da shi

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

da kuma fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

 Dalilin sharadanta sani da La’ilaha illallahu

menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?

Fadin Allah maigirma da Daukaka: Cewa kadai Muminai sune wadanda suka yi imani da Allah da Manzonsa sannan kuma basu yi kwakwanto ba

Zuwa fadin sa:Wadannan sune masu gasgatawa

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa ni Manzon Allah ne ba wani Bawa da zai hadu da Allah da su baya kokonto a cikinsu face Allah ya shigar da shi Aljanna

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ga Abu Huraira

wanda ka hadu da shi a bayan wannan shingen yana mai shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma zuciyarsa tana mai yakini da ita to ka yi masa bushara da Aljanna

Dukaninsu biyun suna cikin sahihul Bukhari.

 Dalilin sharadanta sani da La’ilaha illallahu

menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?

Allah ya yi masa Rahama

Kuma wanda ya mika fuskarsa zuwa ga Allah, alhali kuma yana mai kyautatawa to lalle ya yi riko ga igiya amintacciya

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Imanin dayanku ba zai cika ba har sai son zuciyarsa ya kasance mai bi ga abin da na zo da shi

 Dalilin shardanta karbar Kalmar Shahada

menene dalilin sharadanta Karbar Kalmar Shahada daga Kur’ani da sunna?

Allah Madaukaki ya ce cikin sha’anin wanda bai karbeta ba

Ku tara wadanda suka yi zalunci, da abokan hadinsu, da abinda suka kasance suna bautawa

Zuwa fadin sa:

Lalle su sun kasance idan an ce musu babu abin bautawa face Allah sais u dora girman kai kuma suna cewa shin mu lallai masu barin gumakanmu ne saboda fadin wani mawaki mahaukaci?

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

kwatankwacin abinda Allah ya aiko ni da shi na Shiriya da Ilimi kamar Ruwan Sama ne da ya sauka a kasa wacce ta kasan ce kyakkyawa kuma sai ta karbi Ruwan ta futo da ciyawa da tsirrai Masu yawa kuma ya kasance da kwarurruka a cikinsa wanda zai tare Ruwa sai Allah ya amfanar da Mutane da wannan Ruwan sai suka sha kuma suka shayar kuma sukai Shuka kuma ya Ruwan ya samu wata Kasar kuma Fako wacce bata rike Ruwa kuma bata futo da tsiro, to wannan kwatankwacin wanda yayi Ilimin Shari'a ne kuma ya Amfana da shi abinda Allah ya aiko ni da shi sai ya sani kuma kwatankwacin wanda bai ko daga kai ga wannan ba, kuma bai karbi shiriyar Allah ba da ya aiko ni da shi ba.

 Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

To Addini tsarkakakke na Allah ne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Saboda haka ka bautawa Allah kana mai tsarkake addini a gare shi.

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Mafi rabautar mutane da cetona wanda ya ce La’ilaha illallahu yana mai tsarkaka daga zuciyarsa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Lalle Allah Madaukaki ya haramtawa wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu yana mai neman yardar Allah da ita

 Dalilin shardanta gaskiya cikin Kalmar Shahada

menene Dalilin shardanta gaskiya cikin Kalmar Shahada daga Kur’ani da sunna?

AllahMadaukakin Sarki ya ce:

A. L .M. Ashe mutane sun yi zaton a bar su su ce, mun yi imani alhali kuwa ba za a fitine su ba? Kuma lalle mun fitini wadanda ke a gabaninsu, domin Allah ya san wadanda suka yi gaskiya, kuma lalle ya san makaryata

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Babu wani Bawa da zai shaida babu abin bauta wad a gaskiya sai Allah kuma cewa Muhammad Manzon Allah ne halin kasancewarsa mai gaskiya daga zuciyarsa face Allah ya haramta masa shiga wuta

Kuma ya fada ga wani mutumin kauye wanda ya sanar da shi shari’o’in musulunci izuwa fadinsa na rantse da Allah ba zan dada ba kuma ba zan rage ba daga gar eta sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce

Ya rabauta idan ya yi gaskiya

 Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Yak u wadanda suka yi imani wanda ya bar addininsa daga ku to Allah zai zo da wasu mutane yana sonsu su kuma suna sonsa

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Abu uku wanda suka kasance tare da shi ya samu zakin imani da su: Allah da Manzansa su kasance mafi soyuwa a gare shi daga waninsu, kuma ya so mutum ba yana sonsa ba ne sai dan Allah, kuma ya ki komawa cikin kafirci bayan Allah ya tserar da shi daga cikinsa kamar yadda yake ki a jrfa shi cikin wuta

 Dalilin jibinta Saboda Allah da gaba saboda shi

Menene dalilin jibinta don Allah da gaba saboda shi?

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

ya ku wadanda suka yi imani kada ku riki yahudu da nasara majibinta sashinsu majibincin sashi ne kuma wanda ya jibince su daga gare ku to lalle ne shi yana daga gare su.

Zuwa fadin sa:

Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da Manzonsa da kuma wadanda suka yi imani

kuma Allah Madaukaki ya ce

yak u wadanda suka yi imani kada ku riki iyayenku da ‘yan uwanku majibinta idan sun so kafirci a kan imani

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ba za ka sami mutane masu yin imani da Allah da ranar lahira suna soyayya da wanda ya sabawa Allah da Manzonsa ba

kuma Allah Madaukaki ya ce

Yaku wadanda suka yi imani kada ku riki makiyina kuma makiyinku masoyi

 Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah

Menene dalilin shaidawa cewa Muhammad Manzan Allah ne?

Fadin Allah Madaukaki

Lalle ne hakika Allah ya yi babbar falala a kan muminai, domin ya aika a cikinsu Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinsa a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su littafi da hikima

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Lalle ne hakika Manzo daga cikinku ya je muku, abin da kuka wahala das hi mai nauyi ne a kansa. Mai kwadayi ne saboda ku. Ga muminai mai tausayi ne mai jin kai

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma Allah yana sane da lalle kai, hakika Manzansa ne

 Menene ma’anar shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne?

Menene ma’anar shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne?

Shi ne gasgatawa yankakke daga cikin zuciya mai dacewa da fadin harshe da cewa Muhammad Bawansa ne kuma Manzansa ne izuwa baki dayan mutane mutanensu da AljanunsuMai shaida ne kuma Mai bushara ne kuma Mai gargadi ne kuma Mai kira ne izuwa Allah da izininsa kuma fitila Mai haskakawaTo ya wajaba a gasgata shi cikin gaba dayan abin day a bada labara das hi na daga labaran abin da ya gabata da kuma labaran abin da zai zo da kuma cikin abin da ya halatta daga halal kuma ya haramta daga haram da kuma misaita da jawuwa ga abin day a yi umarni das hi da kuma kamewa da hanuwa ga abin day a yi hani ga buransa da kuma bin shari’arsa da kuma lazimtar sunnarsa a boye da sarari tare da yarda da abin da hukunta da mika wuya a gare shi kuma da’arsa ita ce da’ar Allah kuma saba masa sabawa Allah nedomin cewa shi mai isar da sakon Allah ne kuma Allah bai karbe shi ba har sai da ya cika addini da shi ya kuma isar da sako mabayyani kuma ya bar al’ummarsa a bisa hanya mai haske darenta kamar yininta babu wanda zai karkace ga buranta a bayansa sai dai halakakke kuma a cikin wannan babi akwai mas’aloli da sannu za su zo in Allah ya so.

 Menene ma’anar shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne?

Sharadan shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne

Menene sharadan shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzon Allah ne kuma shin za a karbi shaidar farko ba tare da ita ba?

 Dalilin Salla da Zakka

menene dalilin Salla da Zakka?

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Sa’an nan idan sun tuba kuma suka tsayar da salla kuma suka bada zakka to ‘yan’uwanku ne a cikin addini

kuma Allah Madaukaki ya ce

Sa’an nan idan sun tuba kuma suka tsayar da salla kuma suka bada zakka to ‘yan’uwanku ne a cikin addini

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma ba'a Umarce mu ba sai Mu bautawa Allah muna masu tsarkake Addini a gare shimuna masu kaucewa Bata, kuma mu tsaida Sallah kuma mu bada Zakka.

 Dalilin Azumi

Menene dalilin Auzimi?

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Ya ku wadanda suka yi imani ! An wajabta azimi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke gabaninku

kuma Allah Madaukaki ya ce

To wanda ya ga wata daga cikinku, sai ya Azumce shi

da kuma Hadisin Mutumin kauye: ka bani labarin abin da Allah ya wajabta min na daga azimisai ya ceWatan Ramadana sai dai in kayi tadauwu’in wani abu

 Dalilin Hajji

Menene dalilin azimi?

Allah Madaukakin Sarki ya ce

kuma ku cika hajjin da umara domin Allah

kuma Allah Madaukaki ya ce

kuma akwai hajjin Dakin domin Allah akan mutane ga wanda ya sami ikon zuwa a gare shi

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Lalle ne Allah Madaukaki ya wajabta a kanku Hajji

Hadisin yana cikin Bukhari da Muslim kuma hadisin Jibrilu ya gabata da kuma Hadisin

An gina musulunci a bisa abubuwa biyar

 Hukuncin wanda ya musa daya daga cikin rukunan musulunci

Menene hukuncin wanda ya musa daya daga cikin su ko kuma ya tabbatar da shi kuma ya yi girman kai ga buransa?

Mene ne hukuncin wanda ya musa daya daga cikin su ko kuma ya tabbatar da shi kuma ya yi girman kai ga buransa?

 Hukuncin wanda ya yayi Ikirari da Rukunan Musulunci sannan kuma ya barsu sabida Kasala ko wani Tawili

Mene ne Hukuncin wanda ya yayi Ikirari da Rukunan Musulunci sannan kuma ya barsu sabida Kasala ko wani Tawili?

Amma salla duk wanda ya jinkirta tag a barin lokacinta da wannan sifar to shi ana neman tubansa idan ya tuba idan kuma ba haka ba sai a kashe shi kisan haddi, saboda fadinsa Madaukaki:

Sa’an nan idan sun tuba kuma suka tsayar da salla kuma suka bada zakka to ‘yan’uwanku ne a cikin Addini

An umarce ni na yaki Mutane

Amma zakka idan mai hanata ya kasance yana daga wadanda ba makami a gare shi sai shugaba ya karbeta da rinjaye, kuma ya yi masa horo da karbar wani abu daga dukiyarsa, saboda fadin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi

kuma dukkan wanda ya hanata to mu zamu karbeta da wani yanki na daga dukiyarsa tare da ita

In kuma sun kasance jama’a ne kuma suna da makami ya wajaba a bisa shugaba yakarsu har sai sun bada ita saboda ayoyi da hadisan da suka gabata da wasunsu da kuma aikinsa Abubakar da sahabbai Allah ya yarda da su baki daya.

Amma azimi babu wani abu da ya zo a cikinsa sai dai kuma shugaba zai ladabtar da shi ko wakilinsa da abin da zai kasance tsawatarwane gare shi da kuma misalinsa

Amma Hajji to dukkan rayuwar bawa lokacinsa ne bay a tserewa sai da mutuwa kuma abin da yake wajibi a cikin sa gaggautawa, kuma hakika narko na lahira ya zo a cikin wulakantawa a cikinsa, kuma wata ukuba a kebe a cikinsa a duniya bai zo ba.

 Dalilin Imani da Manzan ni

Menene ma’anar Imani da Allah?

Imani fadi ne da kuma aiki fadin zuciya da harshe da kuma aikin zuciya da harshe da gabobi, kuma yana karuwa da da’a yana kuma raguwa da sabo kuma ahalinsa suna da fifiko a cikinsa

 Dalili a bisa kasancewar imani fadi ne da kuma aiki

Menene dalili a bisa kasancewarsa fadi da aiki?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Kuma amma Allah ya soyar da imani a gare ku, kuma ya kawata shi a cikin zukatanku

kuma Allah Madaukaki ya ce

to ku yi imani da Allah da Manzansa

Kuma wannan shi ne ma’anar shahada biyu wadanda Bawa ba zaishiga addini ba sai da su, kuma ita daga aikin zuciya ne a kudiri, kuma aikin harshe ne a furuci bata amfani said a dacewa da su

kuma Allah Madaukaki ya ce

kuma Allah bai kasance mai bata imaninku ba

yana nufin sallarku izuwa baitil makdisi kafin juya alkibla, an ambaci salla dukkanta imani kuma ita ta tattare aikin zuciya da kuma na harshe da na gabobi.

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanya jihadi da tsayuwar daren lailatul kadri da azimin ramadana da tsaya masa da bada khumusi da wasunsu daga imani, kuma an tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: wane aikin ne ya fi falala? Ya ce imani da Allah da Manzonsa

 Dalili a bisa karuwar imani da tawayarsa

Menene dalili a bisa karuwar imani da tawayarsa?

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Domin su kara imani tare da Imaninsu

Kuma muka kara musu shiriya

kuma Allah yana karawa wadanda suka nemi shiryuwa da shiriya

kuma wadanda suka nemi shiriya zai kara musu shiriya

Kuma wadanda suka yi imani su kara Imani

To amma wadanda suka yi imani to ta kara musu Imani

Don haka ku ji tsoransu sai (wannan Magana) ta kara musu Imani

Kuma wannan bai kara musu komai ba face imani da sallamawa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Da cewa ku zaku dinga kasancewa a cikin kowane hali kamar halinku a gurina da Mala’iku sun dinga yi muku musafaha

kokamar yadda ya ce

 Dalili a bisa fifikon ma’abota imani a cikinsa

Dalili a bisa fifikon ma’abota imani a cikinsa

Allah Madaukaki ya ce

Da wadanda suka tsere. Su wadanda suka tseren nan, wadancan su ne wadanda aka kusantar

Da mazowa dama. Mene ne mazowa dama?

kuma Allah Madaukaki ya ce

To amma idan ya kasance daga makusanta, sai hutawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni’ima, kuma amma idan ya kasance daga mazowa dama, sai( a ce masa) aminci ya tabbata gare ka daga mazowa dama

kuma Allah Madaukaki ya ce

Sa’an nan daga cikinsu akwai mai zalunci ga kansa kuma a cikinsu akwai mai tsakaitawa, kuma daga cikinsu akwai mai tserewa da aiyukan alheri da izinin Allah

Kuma a cikin hadisin ceto

Cewa Allah zai fitar daga wuta wanda ya kasance a cikin zuciyarsa akwai nauyin dinare na daga imani, sannan wanda a cikin zuciyarsa akwai rabin dinare na daga imani

Kuma a cikin wata riwaya za a fitar daga wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu kuma ya kasance a zuciyarsa akwai na daga alheri abin da zai kai nauyin kwayar sha’ir sannan za a fitar daga wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu kuma a cikin zuciyarsa akwai na daga alheri abin da zai kai nauyin kwayar alkama sannan za a fitar daga wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu kuma ya kasance a cikin zuciyarsa akwai na daga alheri abin da zai kai nauyin kwayar zarra

 Dalili a bisa cewa imani ya tattare Addini baki daya

Menene dalili a bisa gamewar musulunci addini dukkansa ya yin da aka saki?

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: wanda ya rataya wani abu to an jingina shi a gareshi

Ina umartarku da imani da Allah shi kadai ya ce: kun san menene imani da Allah shi kadai? Suka ce: Allah da manzonsa ne suka fi sani. Ya ce: shaidawa babu abin bauta wad a gaskiya sai Allah kuma cewa Muhammad Manzan Allah ne, da kuma tsayar da salla, da bada zakka, kuma ku bayar daga abin da aka samu na ganima daya bisa biyar

 Dalili a bisa bada imani da rukunai shida

Menene dalili a bisa arrafa shi da rukunansa biyar a wajan rarrabewa?

Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yin da Jibrilu aminci ya tabbata a gare shi ya ce: ba ni labari ga imani

ya ce:ka yi Imani da Allah da Mala’ikunsa da littattafansa da Manzanninsa kuma ka yi imani da kaddara alherinsa da sharrinsa

menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?

Fadin Allah Madaukaki

Bai zama addini ba domin kun juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da Mala’iku da littattafan sama da Annabawa

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Lalle mu, kowane irin abu mun halitta shi a kan tsari

Kuma da sannu in Allah ya so za mu ambaci kowanne a bisa kadaitakarsa

 Ma’anar imani da Allah Mai girma da daukaka

Menene ma’anar imani da Allah Mai girma da daukaka?

Shi ne gasgatawa yankakkiya daga cikin zuciya da samuwar zatinsa Madaukaki wanda bai rigayu da kishiya ba kuma ba zai yi karshe da ita ba ,shi ne na farko kafin shi ba kowa, kuma shi ne na karshe bayan shi ba kowa kuma shi ne Bayyananne burbushinsa babu kowa kuma Boyayye koma bayansa babu kowa Rayayye Makadaici abin nufi da bukata

bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba kuma babu daya day a kasance tamka a gare shi

Kuma kadaita shi da Allantakarsa da rububiyyarsa da sunayensa da siffofinsa.

 Kadaitarwar Allantaka

menene kadaitarwar Allantaka?

Shi ne dayanta shi Mai girma da daukaka da ga baki dayan ibada ta zahiri da ta badini, fadi da kuma aiki da kuma kore bauta ga duk wani ba Allah ba Madaukaki kuma ko wanene, Allah Madaukaki ya ce

Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa face shi

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma Bautawa Allah kuma kada kuyi masa shirka ko daya

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lalle ni, Ni ne Allah. Babu abin bautawa face ni. Sai ka bauta mini, kuma ka tsayar da salla domin tuna ni

kuma wannan hakika cewa Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya face Allah ta cika da shi

 kishiyar kadaita Allah

menene kadaitarwar Allantaka?

Kishiyarsa shirka kuma shi nau’I biyu ne: mafi girma yana kore shi baki daya da kuma karami yana kore cikarsa.

 Shirka mafi girma

menene shirka mafi girma?

Shi ne Bawa ya riki wanin Allah tamka ya dai dai ta shi da Ubangijin Talikai ya dinga sonsa kamar yadda yake son Allah ya kuma dinga jin tsoransa kamar yadda yake tsoran Allah kuma ya dinga fakewa izuwa a gare shi kuma ya dinga rokonsa kuma yana jin tsoransa kuma yana kwadayi a wajansa kuma ya din dogaro da shi ko ya yi masa da’a a cikin sabon Allah ko ya bi shi a bisa abin da ba yardar Ubangiji ba, da kuma wadansunsu

Kuma Madaukaki ya ce

Lalle ne, Allah ba ya gafarta a yi shirka game da shi, kuma yana gafarta abin da yake bayan wannan ga wanda yake so, kuma wanda ya yi shirka da Allah, to lalle ne ya kirkiri zunubi mai girma.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wanda ya yi shirka da Allah to hakika ya bace bata mai nisa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wanda ya yi shirka da Allah to hakika Allah ya haramta Aljanna a gare shi kuma makomarsa wuta ce

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yana kamar abin da ya fado daga sama, sa’an nan tsuntsaye su cafe shi, ko iska ta fada da shi a cikin wani wuri mai nisa

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Hakkin Allah a bisa Bawa su bauta masa kada kuma su yi shirkar wani abu da shi kuma hakkin Bayi a bisa Allah ba zai azabtar da wanda bai shirkar wani abu da shi ba

kuma shi yana cikin Bukhari da Muslim, kuma yana dai dai acikin fita daga wannan shirkar ga barin addini wanda ya bayyana da shi kamar kafiran kuraishawa da wasunsu, da kuma wanda ya boye a gare shi kamar munafukai mayaudara wadanda suke bayyana musulunci kuma suke boye kafirci.

Allah ya yi masa Rahama

Lalle ne, munafukai suna a magangara mafi kaskanci daga wuta. Kuma ba za ka sama musu mataimaki ba. Sai wadanda suka tuba, kuma suka gyara , kuma suka nemi fakuwa ga Allah , kuma suka tsarkake addininsu domin Allah,to wadannan suna tare da muminai

 Shirka karama

Menene shirka karama?

Shi ne riya mai sauki mai shiga cikin kyautata aiki wanda Allah ake nufi da shi

Allah ya yi masa Rahama

Saboda haka wanda ya kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa,to, sai ya yi aiki na kwarai. Kuma kada ya hada kowa ga bauta wa Ubangijinsa.

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Mafi tsoran abin da nake tsoro a kanku shirka karama

An tambaye shi a kanta sai ya ce riya

Sannan ya fassara shi da fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi

Mutum zai tashi yin salla sai ya kawata sallarsa saboda abin da ya gani na daga kallon wani mutum izuwa gare shi

kuma yana daga ciki yin rantsuwa da wanin Allah kamar rantsuwa da iyaye da kishiyoyi da Ka’aba da amana da wasunsu

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:

kada ku rantse da iyayenku maza ko kuma da iyayenku mata ko kuma da kishiyoyi

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:

kada ku ce na rantse da ka’aba sai dai ku ce da Ubangijin ka’aba

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:

kada ku rantse face da Allah

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce

wanda ya rantse da amana to ba shi daga gare mu

:Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce

Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka a cikin wata riwayar kuma ya yi shirka

kuma yana daga gare shi fadin Allah ya so ka so. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada ga wanda ya fada masa wannan

ka sanya ni kishiya ga Allah kadai ka ce Allah ya so shi kadai

kuma yana daga ciki fadin ba don Allah da kai ba, da kuma me ke gare ni sai Allah da kai da kuma ni zan shiga don Allah don kuma kai da misalin wancananka,

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:

Kada ku kuskura kuce: Allah ya yarda wane ma ya yarda, kuce: Allah ne ya yarda Sannan kuma wane kuma ya yarda.

Ma’abota ilimi sun ce kuma ya halatta a ce ba don Allah ba sannan wane, kuma bai halatta a ce ba don Allah da wane ba

Menene banbanci tsakanin da da kuma sannan a cikin wadannan lafazan?

Domin cewa hadawa da da yana hukunta hadawa da daidaitawa sai ya kasance wanda ya ce Allah ya so da kai ya hade soyayyar Allah da soyayyar Bawa daidaice da ita sabanin ya yi hadin da sannan wacce take hukuntar da bi, to wanda ya ce Allah ya so, sannan kuma ka so to hakika ya tabbatar da cewa soyayyar Bawa mai bi ce ga soyayyar Allah Madaukaki bata kasancewa face bayanta kamar yadda Madaukaki ya ce

kuma ba za ku so ba face sai Allah ya so

Kuma haka nan sauran

 Tauhidin Kadaita Allah

maye kishiyar kataita allah

Shi ne tabbatarwa yankakkiya da cewa Allah Madaukaki Ubangijin komai kuma mamallakinsa kuma mahaliccinsa kuma mai tsara shi kuma mai sarrafa shi ba shi da abokin tarayya a cikin mulkin,

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa, kuma ya sanya duffai da haske

kuma Allah Madaukaki ya ce

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ka ce wane ne Ubangijin sammai da kasa? Ka ce Allah. Ka ce Ashe fa kun riki wadansu masoya baicin shi, wadanda ba su mallaka wa kansu wani amfani ba, kuma haka ba su ture wata cuta? Ka ce shin makaho da mai gani suna daidaita? Ko shin, duhu da haske suna daidaita? Ko sun sanya ga Allah wadansu abokan tarayya wadanda suka yi halitta kamar halittarsa, sa’an nan halittar ta yi kama da juna a gare su? Ka ce, Allah ne mai halittar komai, kuma shi ne Makadaici, Marinjayi

kuma Allah Madaukaki ya ce

Allah ne wanda ya halicce ku, sa’an nan ya arzurta ku, sa’an nan ya matar da ku, sa’an nan ya rayar da ku. Ashe daga cikin abubuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga wadannan abubuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma ya daukaka bisa ga abin da suke yi na shika

kuma Allah Madaukaki ya ce

Wannan shi ne halittar Allah. To ku nuna mini, mene ne wadannan da ba shi ba suka halitta?

kuma Allah Madaukaki ya ce

Shin an halitta su ne ba daga komai ba, ko kuwa su ne masu yin halitta? Shin sun halitta sammai da kasa ne? A’a ba su dai yi imanin yakini ba

kuma Allah Madaukaki ya ce

Shi ne Ubangijin sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu to sai ka bauta masa, kuma ka yi hakuri ga bautarsa. Shin ka san wani takwara a gare shi

kuma Allah Madaukaki ya ce

Da Babu abinda yayi kama da Allah kuma shi ne Mai ji kuma mai gani

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma kace godiya ta tabbata ga Allah wanda Bairiki da ba baida abokin tarayya cikin mulkinsa kuma baida wani majibincin al amarinsa kaskanci baikasance agare shi ba ka girmama ubangijin ka girmamawa.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kukirayi wadan da kuke zatan abubuwan bautawa ne ba Allah ba basu mallaki komaibadaidai da kwayar zarra ba cikin sammai da kassai kuma cikin su basu da wani abokin tarayya kuma bashi da wani mataimaki daga garesu ,ba wani ceto da zai amfani a wajansaba sai dai wanda akayimasa izini harsai

 kishiyar kadaita Allahntakar

maye kishiyar kataita Allah

Shi ne Kudurcewa Allah mai girma da Daukaka shi ne mai juya komai na gudanar da Halittu wajen Samar da su ko kashe su ko raya su ko kashe su, ko samar musu da amfanuwa ta Alkairi ko ije Sharri ko wanin hakan daga cikin Ma'anonin Allahntaka, ko kudurce wani wanda zai ja da Allah a cikin wani abu na abubuwan da ya hukunta ko sunayensa ko Sifofinsa Kamar Ilimin Gaibu, da kuma kamar Girma da kuma daukaka, da mai kama da shi.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Duk abin da Allah ya bayar ga Mutane na Rahama to babu mai iya hana ta kuma duk abinda ya hana babu wanda ya isa ya bayar da su bayansa kuma shi ne Mabuwayi kuma mai Hikima ya ku Mutane ku tuna ni'amar Allah akanku shin bayan Allah akwai wani mai Azurtaku daga Sama da Kasa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Idan Allah ya sama wata cuta babu mai yayema saishi Allah kuma idan yana nufinka dawani alkhairi babu wanda zaimayal da falalarSa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kace bakwa ganin abinda kuke bautawa koma bayan Allah in Allah ya nufe ni da Cuta shin akwai mai iya yaye mun Cutar in ba shi ba ko kuma ya Nufeni da Rahama shin akwai wanda ya isa ya tare Rahamar ta sa, kace Allah ya Ishe ni kuma gare shi masu Dogara suke Dogara.

Allah Mai tsarki da daukaka ya ce

Kuma mabudan gaibu suna gurinsa ba wanda ya sansu sai daishi…

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ka ce: wanda suke sammai da kassai basu san gaibu ba sai Allah

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma babu wanda ya isa yakewaye da Iliminsa sai abinda ya so

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Allah Madaukaki ya ce Girman kai Kwajalle na ne kuma Daukaka Mayafi na ne to duk wanda yayi Jayayya dani cikin daya daga cikinsu to zan saka shi a Wuta

Hadisin ya zo a cikin Sahih

 Kadaita Allah cikin sunayensa da siffofinsa

menene kishiyar tauhidin sunaye da siffofi?

Hadisin ya zo a cikin Sahih

yana sanin abin da yake tsakanin gabansu da kuma abin da yake bayansu kuma su ba su kewaye sani da shi ba

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

da Babu abinda yayi kama da Allah kuma shi ne Mai ji kuma mai gani

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Hadisin ya zo a cikin Sahih

kuma acikin Tirmizi daga Ubayyu dan Ka’abu Allah ya yarda da shi cewa mushirikai sun ce da Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – yana nufin yayin da ya ambaci Allolinsu- ka sifanta mana Ubangijinka sai Allah madaukakin sarki ya saukar da

Kul huwa Allah Ahad “ka ce shi ne Allah Makadaici”Allah wanda ake nufinsa da bukatakuma Assamad shi ne wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba

Domin cewa shi babu wani abu da za’a Haifa face sai ya mutu kuma babu wani abu da zai mutu face an gaje shi kuma lalle Allah Madaukakin sarki ba zai mutu ba kuma ba za’a gaje shi ba

kuma babu daya da ya kasance tamka a gare shi

Allah ya ce babu wanda ya kasance mai kama da shi ko kuma kwatankwacinsa, kuma babu wani abu da yayi tamkarsa.

 Dalilin sunayansa kyawawa daga Alkur’ani da kuma sunna

Menene dalilin sunayansa kyawawa daga Alkur’ani da sunna?

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

Kuma Allah yana da sunaye masu kyau sai ku roke shi da su ku bar wadanda suke yin ilhadi a cikin sunayensa

Kuma tsarki ya tabbatar masa ya ce

Ka ce, ku kirayi Allah ko kuwa ku kirayi Mai rahama. Kowanne kuka kira, to yana da sunaye masu kyau

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

Allah babu abin bautawa face shi. Yana da sunaye mafiya kyau.

Da wasun su daga Ayoyi.

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

lalle Allah yana da sunaye casa’in da tara duk wanda ya kiyayesu zai shiga Aljanna

kuma shi yana cikin Bukhari. Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce

ina rokanka ya Allah da kowane suna naka, wanda ka ambaci kanka da shi, ko ka saukar das hi a cikin littafinka, ko ka sanar das hi da wani daga cikin halittarka, ko ka kebance kanka da saninsa a cikin ilimin fake dake wurinka daka sanya Alkur’ani mai girma ya zama kaka ga zuciyata

 Misalin sunayen Allah masu kyau daga Alkur’ani

Menene misalin sunayen Allah mafiya kyau daga Alkur’ani?

Misalin faxin Allah Madaukakin Sarki:

Lalle Allah ya kasance Madaukaki Mai girma

Lalle Allah ya kasance Mai tausasawa Mai labartawa.

Lalle Allah ya kasance Masani Mai iko

Lalle Allah ya kasance Mai ji Mai gani

Lalle Allah ya kasance Mabuwayi Mai hikima

Lalle Allah ya kasance Mai gafara Mai jin kai

Lalle shi ne Mai tausayi Mai jin kai gare su.

kuma Allah Mawadaci ne Mai hakuri

Lalle shi abin godewa ne, Mai girma

Lalle Ubangijina a bisa dukkan komai Matsari ne

Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karbawa

Lalle Allah ya kasance Mai dako ne a kanku

kuma Allah ya isa ya zama Wakili

kuma Allah ya isa Mai lissafi

Kuma Allah ya kasance a kan dukkan komai Mai kayyade lokaci

Lalle shi a bisa dukkan komai Mai shaida ne

Lalle shi ga dukkan komai Mai kewayewa ne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Allah babu wani abin bautawa sai shi Rayayye Mai tsayuwa da komai

kuma Allah Madaukaki ya ce

Shi ne na farko, Na karshe Bayyananne, Boyayye, kuma shi Masani ne ga dukkan komai

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Shi ne Allah wanda babu wani abin bautawa face shi, Masanin fake da bayyane shi ne Mai rahama Mai in kai. Shi ne Allah wanda babu abin bautawa face shi, Mai mulki Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai tilastawa, Mai nuna isa. Tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke yin a shirka da shi. Shi ne Allah Mai halitta, Mai ginawa, Mai surantawa, yana da sunaye masu kyau

Da wasun su daga Ayoyi.

 Misalin sunayen Allah masu kyau daga Sunnah

Menene misalin sunayen Allah mafiya kyau daga Sunnah?

Faxar Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ta gabata

babu wani abin bautawa face Allah Mai girma Mai hakuri babu wani abin bautawa face Allah Ubangijin Al’arshi mai girma, babu wani abin bautawa da gaskiya face Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa kuma Ubangijin Al’arshi mai yawan baiwa

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

ya Rayayye ya Mai tsayuwa da komai ya Ma’abocin daukaka da girma ya Makagin sammai da kasa

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

da sunan Allah wanda da sunansa wani abu a sama ko a kasa baya cutarwa. Kuma shi ne Mai ji Masani

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

ya Ubangiji masanin fake da bayyane Mahaliccin sammai da kasa Ubangijin dukkan komai kuma mamallakinsa

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

ya Allah Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al’arshi mai girma ya Ubangijinmu kuma Ubangijin dukkan komai mai tsaga kwayar hatsi da ta dabino wanda ya saukar da Attaura da linjila da Alkur’ani ina neman tsarinka daga dukkan sharrin mai sharri wanda kai kake rike da makwarkwadarsa.kai ne na farko babu wani abu kafin ka, kuma kai ne na karshe babu wani abu bayanka, kuma kai ne bayyananne babu komai birbishinka kuma kai ne boyayye babu wani abu da yake boyuwa a gareka

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

ya Allah godiya ta tabbata a gareka kai ne hasken sammai da kasa da kuma abin da yake cikinsu kuma godiya ta tabbata a gareka kai ne mai tsai da sammai da kasa da abin da yake cikinsu

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

ya Allah ina rokanka, saboda ni na shaida cewa kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai,kai kadai tal,wanda ake nufa da dukkan bukatu, wanda bai Haifa ba kuma ba’a haife shi ba, kuma babu wani tamka a gare shi

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Ya Mai juyar da zukata

Da wasun haka masu yawa:

 Da wadansun wadannan masu yawa

a bisa nau’i nawa sunayen Allah mafiya kyau suke shiryarwa da shi?

ita tana shiryarwa ne a bisa nau’ika uku: shiryarwarta a bisa zati a dacewa, da kuma shiryarwarta a bisa siffofi ababan cirowa daga gareta a kunshe, da kuma shiryarwarta a bisa siffofi wacce ba’a ciro daga gareta ba a lazimtawa

Menene misalin wancananka?

Misalin wancananka: sunansa Madaukaki Mai rahama Mai jin kai yana shiryarwa a bisa zatin abin Ambato shi ne Allah Mai girma da daukaka a dacewa da kuma a bisa siffa abar cirowa daga gareta ita ce Rahama a kunshe kuma a bisa watanta daga siffofi wacce ba’a cira daga gareta ba kamar Rayuwa da iko a lazimtawaHakanan kuma sauran sunayensa,to wannan sabanin ababan halitta ne domin akan ambaci wani da mai hikima alhali kuma jahili ne ko kuma mai hukunci alhali kuma Azzalumi ne ko kuma mai isa alhali makaskanci ne ko kuma mai alfarma alhali kuma mara alfarma ne ko kuma mai karamci alhali kuma mara karamci ne ko kuma managarci alhali kuma ba managarci ba ne ko kuma mai arziki alhali kuma matsiyaci ne ko a kira shi da Zaki ko kuma mai daci amma kuma ba haka yake ba, tsarki ya tabbata ga Allah da kuma gode masa shi kamar yadda ya siffanta kansa yake kuma sama da yadda halittarsa suka siffanta shi

 Shiryarwar sunayensa mafiya kyau ta fuskar kunsa

a bisa kaso nawa shiryarwar sunayen Allah mafiya kyau suka kasu ta fuskar kunsa?

ita ta kasu kaso hudu:

Shi ne Allah Mahalicci Mai ginawa Mai surantawa

Shi ne Allah Mahalicci Mai ginawa Mai surantawa

da kuma makamancin wannan, kuma bai taba zuwa mai bi ga waninsa ba daga sunayen

Na biyu: abin da ya kunshi siffar zatin Allah Mai girma da daukaka kamar sunansa Mai ji wanda ya kunshi jinsa mayalwaci ga dukkan saututtuka, daidai ne a gurinsa boyayyiyarta da bayyananniyarta kuma sunansa Mai gani wanda ya kunshi ganinsa mai zarcewa a cikin dukkan gannai daidai ne zurfafanta da mabayyananta kuma sunansa Masani wanda ya kunshi saninsa mai kewayewa wanda

Masanin gaibi gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare shi a cikin sammai kuma bata nisanta a cikin qasa kuma babu mafi girma face yana a cikin Littafi bayyananne

Gwargwadon zarra bat a nisanta daga gare shi a cikin sammai, kuma bat a nisanta a cikin kasa, kuma mafi karanci daga wancan kuma babu mafi girma

kuma sunansa Mai iko wanda ya kunshi ikonsa a bisa dukkan komai a samarwa da rasantarwa da wasun wadannan

Na uku: abin da ya kunshi siffar aikin Allah kamar Mahalicci Mai azurtawa Mai ginawa Mai surantawa da wadansun wadannan.

 Na hudu: abin da ya kunshi tsarkinsa Madaukaki daga dukkan tawaya kamar sunansa Mai tsarki, Mai aminci.

Kaso nawa sunayen mafiya kyau ta fuskar sakinsu a bisa Allah Mai girma da daukaka suka kasu?

daga cikinta akwai wanda ake sakinsa a bisa Allah kadai ko tare da waninsa kuma shi ne wanda ya kunshi siffar cika ta kowace fuska kamar Rayayye Mai tsayuwa da kome Makadaici Abin nufi da bukata da makamantansu, kuma yana daga cikinta abin da ba’a sakinsa a bisa Allah face tare da mukabilinsa shi ne wanda idan ya kadaita zai wahamtar da tawaya kamar Mai cutarwa Mai amfanarwa, Mai kaskantarwa da Mai daukakawa da Mai bayarwa da Mai hanawa da Mai buwayarwa da Mai kaskantarwa da makamancin wadan nan To bai halatta sakin Mai cutarwa ko kaskantarwa ko hanawa kowanne a bisa kadaituwarsa ba, ba’a taba sakin wani abu daga gare taba a cikin wahayi hakanan babu a cikin littafi babu ma a cikin sunna, kuma yana daga ciki sunansa Madaukaki Mai ramuwa ba’a sake shi a cikin Alkur’ani ba face tare da muta’allikinsa kamar fadinsa Madaukaki

Lalle mu masu yin azabar ramuwa ne ga masu laifi

ko da raba Ma’aboci a sifa abar cirowa daga gare ta kamar fadinsa Madaukakin sarki

kuma Allah shi ne Mabuwayi Ma’abocin ramuwa

 Misalin siffofin zati daga Alkur’ani

ya gabata cewa siffofin Allah Madaukaki akwai na zati da kuma na aiki to menene misalign siffofin zatin daga Alkur’ani?

Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:

Misalin fadinsa Madaukakin sarki

Kowanne abu mai halaka ne face Fuskarsa

Kuma Fuskar Ubangijinka Mai girman jalala da karamci ita ce take

Kuma domin a rike ka da kyau a kan idoNa

Menene ya yi ganinsa da jinsa

Hakika nai ina tare da ku ina ji kuma ina gani

yana sanin abin da yake tsakanin gabansu da kuma abin da yake bayansu kuma su ba su kewaye sani da shi ba

Kuma Allah yayi magana da Musa Magana sosai

kuma a lokacin da Ubangijinka ya kira Musa kajewa mutanan nan azzalumai

kuma Ubangijinsu ya kira su shin ban hana ku ba daga waccan itaciya,

kuma ranar da yake kiran su, sa’annan ya ce, mene ne kuka karba wa manzanninku

da kuma wadansunsu.

 ? Misalin siffofin zati daga Alkur’ani

Menene misalin siffofin zati daga sunna?

Kamar fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Hijabinsa haske ne da zai yaye shi da jalalar Fuskarsa ta kone abin da ganinsa ya tuke a gare shi na daga halittarsa

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Daman Allah a cike take,ciyarwa bazata tauyeta ba mai yawan baiwa ne dare da rana ba kwa ganin abin day a ciyar tun lokacin day a halicci sammai da kasa, cewa shi babu abin da zai tauye abin da ke cikin damansa kuma Al’arshinsa yana kan ruwa kuma a daya hannun nasa baiwa take ko kuma rikewa yana daukakawa kuma yana kaskantarwa

Kuma faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a cikin Hadisin Dujal

Lalle Allah ba zai buya daga gare ku ba cewa shi ba mai Ido daya ba ne

sai yayi nuni da hannunsa izuwa idonuwansa, haka kuma a cikin hadisin istihara

Ya Allah lalle ni ina neman zabinka da iliminka ina neman iyawarka da ikonka kuma ina rokanka daga falalarka mai girma domin cewa kai kake da iko ni bani da iko kuma kai mka sani ni bani da wani sani kuma kai ne Masanin abubuwan da suke fake

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

cewa ku ba kurma kuke kira ba ko kuma fakakke kuna kiran Maiji Maigani Makusanci

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

‘’Idan Allah Madaukakin Sarki ya yi niyyar wahayi kan wani abu sai yayi magana da wahayi‘’

Kuma a cikin hadisinTashi daga Kabari

Allah Madaukakin sarki zai ce: Ya Adamu sai ya ce amsawarka

da kuma hadisan zancan Allah ga bayinsa a cikin matsaya, da kuma maganarsa ga ‘yan Aljanna da wadansu wadannan wanda baza su kididdigu ba.

 Misalin siffofin aiyuka daga Alkur’ani

Mene neMisalin siffofin aiyuka daga Alkur’ani?

Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:

sannan ya daidaita zuwa sama

Sannan fadinsa

shin suna jira face dai Allah ya je musu

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

kuma ba su kaddara Allah a bisa hakikanin ikon yinsa ba, kasa kuma duka damkarsa ce, ranar kiyama kuma sammai abubuwan nadewa ne ga damansa.

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

me ya haneka ka yi sujjada ga abin da na halicce shi da hannaye na?

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

kuma muka rubuta masa a cikin alluna daga kowa ne abu

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

yayin da Ubangijinsa ya kuranye zuwa ga dutsen, ya sanya shi nikakke

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

lalle Allah yana aikata abin da ya so

Da wasun su daga Ayoyi.

 ? Misalin siffofin Ayyuka daga Alkur’ani

Menene misalin siffofin Ayyukai daga sunna?

Fadar Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi misali ce

Ubangijinmu yana sauka a kowane dare izuwa saman duniya lokacin da daya bisa ukun karshe ya yi

Kuma faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a cikin Hadisin Ceto

sai Allah ya zo musu cikin surarsa wacce suka sani sai ya ce nine Ubangijinku sai su ce kai ne Ubangijinmu

kuma muna nufi da siffar aiki a nan zuwa ba sura ba kawai ka fahimta. Da fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Lallai Allah yana danke Kasa a Ranar Alkiyama kuma Sama ta kasance a Hannun Damansa, sannan ya ce: Ni ne Sarki

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

yayin da Allah ya halicci halitta sai ya rubuta da hannunsa a bisa kansa cewa rahmata ta rinjayi fushi na

A cikin Hadisin jayayyar Annabi Adam da Musa: "Sai Adam ya ya kai Musa Allah ya zabeka da Zancensa kuma ya rubuta maka Attaura da Hannunsa to zancensa Madaukaki da kuma Hannunsa siffifi ne na Zati kuma Maganarsa Sifa ce ta Zati kuma da aiki hade kuma Rubuta Attaurarsa Sifa ce ta aiki Fadin Annabi Amincin Allah a gare shi:

Lalle ne Allah Madaukaki yana shimfida hannunsa da dare domin masu lefi da rana su tuba kuma yana shimfida hannunsa da rana domin masu lefi da dare su tuba

da wadansunsu da yawa.

 Sunayen Allah dukkansu tsayayyu ne

Shin ana cirar wani suna daga dukkan siffofin aiki ko kuma sunayen Allah dukkansu tsayayyu ne?

A’a bari dai sunayen Allah Madaukaki dukkansu tsayayyu ne ba’a ambatonsa sai da abin da ya ambaci kansa da shi a cikin littafinsa ko kuma Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sakar masa shi kuma dukkan wani aiki wanda Allah Madaukaki ya sakar ma kansa da shi to shi acikinsa yabo ne da kuma cika amma kuma ba dukkan su ne Allah ya siffanta kansa da shi ba kai tsaye kuma ba dukkanninsu ne ake cirar wani suna daga gare su ba, kadai dai akwai daga cikin su wadanda yake siffanta kansa da shi kai tsaye.kamar fadinsa Madaukaki:

Allah ne wanda ya halicceku sannan kuma ya azurta ku sannan kuma ya matar da ku sannan kuma ya raya ku

kuma ya ambaci kansa da Mahalicci Mai arzurtawa Mai rayawa Mai matarwa Mai tsarawa, kuma daga cikinsu akwai wasu aiyukan wadan da Allah madaukaki ya sakar ma kansa ta hanyar sakamako, da kabaltawa kuma ita a cikin abin da aka koro dan shi yabo ne da kamala, kamar fadinsa Madaukakin sarki:

suna yaudarewa da Allah, alhali kuwa shi ne mai yaudararsu

Kuma sun yi makirci, Allah kuma ya yi musu makircin,kuma Allah ne mafi alherin masu saka wa makirci

sun mance Allah sai ya manta da su

sai dai kuma bai halatta a saketa a bisa Allah ba cikin wanin abin da aka koro a ayoyin, ba za’a ce Allah Madaukaki yana makirci ba ko yana yaudara ko yana isgili ba da makamantan wadannan,,kuma hakanan ba za’a ce Makiri Mayaudari Mai isgili ba kuma Musulmi da mai hankali ba zasu fadi haka ba,to hakika Allah Mai girma da daukaka bai siffanta kansa da Makiri ba ko Mayaudari face ta fuskar sakayya ga wanda ya aikata hakan ba tare da gaskiya ba, kuma bayan tabbas ya sani cewa sakayya a bisa haka da adalci aiki ne mai kyau daga ababan halitta to kaka ga Mahalicci Masani Adali Mai hikima.

 me sunansa Al-Aliyyul A’alaa ya kunsa

me sunansa Al-Aliyyul A’alaa ya kunsa da abin da yake a ma’anarsa kamar Al-Zahiru da Al-Kahiru da Al- Muta’aali?

sunansa Al-Aliyyul A’alaa yana kunshe da siffarsa abin cirowa daga gare ta shi ne tabbatar da daukaka a gare shi Mai girma da daukaka da dukkan ma’anoninsa, daukakar bisansa Madaukaki a bisa Al’arshinsa,ya daukaka bisa dukkan halittarsa Manisanci daga gare su Mai lura da su yana sanin abin da suke ciki hakika saninsa ya kewaye dukkan komai, babu wani abu daga gare su boyayye da zai buya a gare shi

da kuma daukakar rinjayensa babu wani mai rinjayarsa babu kuma wani mai jayayya ko mai kishiyanta ko mai hanawa a gare shi, bari dai dukkan komai mai kaskantar da kai ne ga girmansa, kuma wulakantacce ne ga buwayarsa, kuma kowa yana katkashin tasarrufinsa da rinjayensa ba’a kufcewa daga kamunsa.

kuma daukakar sha’aninsa, dukkan siffofi na kamala sun tabbata a gare shi kuma dukkan wata tawaya korarriya ce ga buransa ya girmama kuma ya daukaka kuma ya tsarkaka, kuma dukkan wadannan ma’anoni na daukaka mai lazimtuwa ce babu wata ma’ana daga gare ta da za ta rabu da wata.

 dalilin daukakar bisa daga Alkur’ani

menene dalilin daukakar bisa daga Alkur’ani?

dalilan a sarari suke a kansa ba za su kirgu ba kuma ba za su kididdugu ba yana daga cikin su wannan sunayen da wadanda suke da ma’anarsu, kuma yana daga ciki fadinsa Madaukakin sarki:

Mai rahama ya daidaita a kan Al’arshi

cikin gurare bakwai daga Alkur’ani kuma yana daga cikinsu fadinsa Madaukakin sarki:

shin ko kun amince cewa wanda ke cikin sama

Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:

suna tsoran Ubangijinsu daga bisansu

Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:

Zuwa gare shi Magana mai dadi ke hawa, kuma aiki na kwarai yana daukarta

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Mala’iku da Ruhi suna takawa zuwa gare shi

Sannan faxinsa

yana tsara lamari daga sama izuwa kasa

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

ya Isa lalle ni mai karbar ranka ne, kuma mai daukeka ne zuwa gare ni

Da wasun haka masu yawa:

 dalilin daukakar bisa daga sunna

menene dalilin wancananka daga sunna?

dalilansa daga sunna suna da yawa ba za su kididdugu ba, yana daga ciki fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cikin hadisin Al-au’aal

kuma Al’arshi yana bisan wancananka kuma Allah yana bisan Al’arshi kuma shi ya san abin da kuke a kansa

Da fadinsa ga Sa’adu cikin kissar bani kuraiza, "Hakika kayi musu Hukunci da Hukuncin Sarkin da yake Saman Bakwai“ da fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shiga kuyanga: ina Allah? Sai ta ce: cikin sama Sai ya ce: ka ‘yanta ta don cewa ita Mumina ce

da hadisan Mi’irajin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cikin hadisin zuwan Mala’iku

sannan wadanda suka kwana a cikinku sai su hau, sai ya tambaye su alhali shi ne mafi sani da su

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

wanda ya yi sadaka da kwatankwacin dabiniya na daga tsuwurwuri tsarkakakke domin Allah babu abin da yake hawa zuwa gare shi sai tsarkakakke

Kuma faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a cikin Hadisin Wahayi

idan Allah ya nufi zartar da lamari a cikin sama sai Mala’iku su yi bugu da fikafikansu suna masu kaskan da kai saboda fadinsa kai ka ce shi sarka ce a bisa fan dutse

kuma hakika dukkan ababan halitta sun tabbatar da wannan sai dai yan jahamiyya

 Mas’alar istiwa’i

me shugabannin Addini daga magabata na kwarai suka fada a cikin mas’alar istiwa’i?

fadinsu baki dayansu Allah Madaukaki ya jikansu: istiwa’i ba abin jahilta ba ne kuma kaifiyyarsa ba abin hankalta ba ne kuma imani da shi wajibi ne kuma tambaya game da shi bidi’a ne kuma daga Allah sako yake, kuma a bisa Manzo isarwa take mu kuma a kanmu gasgatawa da mika wuya yake, haka kuma da fadinsu cikin dukkan ayoyi

mun yi imani da shi dukansa daga wajan Ubangijinmu yake

mun yi imani da Allah kuma ka shaida da cewa mu masu mika wuya ne

 Dalilin daukakar Rinjaye daga Alkur’ani

menene dalilin daukakar tilastawa daga Alkur’ani?

Akwai dalilai ma su yawa daga ciki akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki:

kuma shi ne tankwasa a kan bayinsa

kuma shi ne wanda ya kunshi daukakar tilastawa da kuma bisantaka.

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Mai tsarki shi ne Allah shi kadai kuma Mai Rinjaye akan kowa

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Mulki ga wa yake a yau? yana ga Allah Makadaici, Mai Rinjaye

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Yace Ni ba kowa bane sai mai gargaxi haqiqa babu wani Allah face Allah Madaukakin Sarki

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Babu wata dabba face shi ne mai riko ga makwarkwadarta

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

ya jama’ar aljanu da mutane idan kuna iya zarcewa daga sasannin sammai da kasa, to ku zarce. Ba za ku iya zarcewa ba face da wani dalili

Da wasun waxannan daga ayoyi.

 Dalilin daukakar bisa daga sunna

menene dalilin wancananka daga sunna?

dalilansa daga sunna suna da yawa yana daga ciki fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:

ina neman tsarinka daga sharrin dukkan dabbar da kake rike da makwarkwadarta

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

ya Allah lalle ni bawanka ne kuma dan bawanka kuma dan baiwarka makwarkwadata tana hannunka Hukuncinka zartacce ne a kaina,kuma kaddararka gare ni mai Adalci ce

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

lalle kai ne kake hukunci babu wanda yake Hukunci a kanka, tabbas wanda ka jibince shi ba zai wulakanta ba wanda kuma ka ki shi ba zai daukaka ba

Da wasun haka masu yawa:

 dalilin daukakar sha’ani

menene dalilin daukakar sha’ani kuma me ya wajaba a kore shi ga barin Allah Mai girma da daukaka?

Ka sani cewa daukakar sha’ani shi ne abin da sunansa AlkuddusAssalaam Alkabiir Almuta’aal ya kunsa da kuma abin da yake cikin ma’anarta da kuma dukkan siffofin cikarsa ya lazimta shi da siffofin daukakarsa ya daukaka a ce a cikin kadaitakarsa ya kasance waninsa yana da wani mulki ko wani yanki daga gare shi ko wani mataimaki ya kasance a gare shi ko wani mai ceto a gurinsa ba tare da izininsa ba ko yayi zalunci a gare shi

kuma ya daukaka cikin girmansa da mallakewarsa da rinjayensa a ce wani mai jayayya ko wani mai rinjaye ko wani masoyi saboda wulakanci ko kuma wani mataimaki ya kasance a gare shi

kuma ya daukaka cikin wadatuwarsa ga mata ko kuma da ko kuma uba ko tanka ko kuma mataimaki

kuma ya daukaka cikin cikarsa da rayuwarsa da tsayuwarsa da ikonsa ga mutuwa da gengedi da gajiya da wahala

Kuma ya daukaka cikin cikar iliminsa ga gafala da mantuwa da kuma fakuwar daidai da kwayar zarra ga iliminsa a cikin kasa ko a cikin sama

kuma ya daukaka cikin cikar hikimarsa da godiyarsa gay a halicci wani abu da wasa da kuma ya bar halitta sasakai ba tare da umarni da kuma hani da tashi da sakamako ba

kuma ya daukaka cikin cikar adalcinsa ga ya zalinci wani daya ko da kwatankwacin kwayar zarra ne ko ya cinye wani abu daga kyawawansa

kuma ya daukaka cikin cikar wadatarsa ga ciyarwar ko arzurtarwar ko bukata cikin wani abu izuwa ga waninsa ba

kuma ya daukaka cikin dukkan abin da ya siffanta kansa da shi kuma Manzansa ya siffanta shi da shi ga wofuntarwa da kamantawa kuma tsarki ya tabbatar masa da godiyarsa kuma ya buwaya ya daukaka

kuma ya daukaka ya tsarkaka ga dukkan abin da zai kore Allantakarsa da rububiyyarsa da kuma sunayensa kyawawa da siffofinsa madaukaka

kuma yana da misali wanda yafi daukaka a cikin sammai da kasa, kuma shi ne Mabuwayi Mai jin kai

nassoshin wahayi daga Alkur’ani da sunna cikin wannan babin sanannu ne kuma fahimtattu tare da yawanta da shahararta

Kuma faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi game da Sunayen Allah

mafiya kyau wanda ya kiyayesu zai shiga Aljanna

menene ma’anar fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cikin sunayensa mafiya kyau wanda ya kiyaye su zai shiga Aljanna?

hakika an fassara wannan da wasu ma’anoni yana daga cikinsu kiyaye ta da kuma rokon Allah da ita da godiya a gare shi da dukkansu. Kuma yana daga cikinsu cewa abin da ya halatta a yi koyi da shi kamar Mai jin kai da kuma Mai karamci to sai bawa ya bibiyi kansa a bisa ya inganta insafi da ita a kansa cikin abin da ya rataya da shiKuma wanda a cikinsa akwai ma’anar alkawarin narko kamar Mabuwayi Ma’abocin fansa Mai tsananin ukuba Mai gaggawar hisabi, to sai ya tsaya daga gare shi wajan tsoro da firgicikuma wanda a cikinsa akwai ma’anar alkawarin narko kamar Mabuwayi Ma’abocin fansa Mai tsananin ukuba Mai gaggawar hisabi, to sai ya tsaya daga gare shi wajan tsoro da firgici

kuma yana daga cikinta shaidar bawa a kanta da kuma bata hakkinta a ma’arifa da kuma ubudiyya misalinsa wanda ya shaida daukakar Allah Madaukakin sarki a bisa halittarsa da kuma bisansa a kan su da kuma daidaitonsa a kan al’arshinsa manisanci daga halittarsa tare kuma da kewayewarsa da su da ilimi da iko da wadansu wadannan kuma ya bauta masa da abin da wannan siffa ta hukuntar ta yadda zai zama da zuciyarsa mabukaciya yana hawa izuwa gare shi yana mai munajati da shi yana mai kwankwasawa kuma yana mai tsayuwa nan gaba gare shi tsayuwar bawa kaskantacce nan gaba ga Sarki Mabuwayi kuma ya dinga jin cewa zancansa da aikinsa mai hawa ne izuwa gare shi mai bijirowa ne a gare shi sai ya dinga jin kunyar cewa kada wani daga zancansa ko aikinsa da zai kunyata shi ya dinga hawa izuwa gare shi a can, kuma ya shaida saukar lamarin Ubangiji izuwa sassan duniyoyi a kowane lokaci da nau’o’in tsari da tasarrufi na daga kashewa da rayawa da daukakawa da kaskantarwa da bayarwa da hanawa da yayewar bala’u da kuma aikensa da kuma jujjuyawar kwanaki tsakanin mutane izuwa wadansun wadannan na daga tasarrufu a cikin daular da take ba mai tasarrufi a cikin ta in ba shi ba sai shugabancinsa ya zamo zartacce a cikinta kamar yadda yake so

Yanã shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasã, sa'an nan ya tãka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shekaru dubu ne ga abin da kuke lissafãwa.

to wanda ya cikawa wannan mash’hadi hakkinsa a halin sani da kuma bauta to hakika ya wadatu da Ubangijinsa kuma ya isar masa, kuma haka nan wanda iliminsa makewayi ya shaida da jinsa da ganinsa da rayuwarsa da tsayuwarsa da waninta kuma ba kowa ne yake arzurta da wannan mash’hadi ba face marigaya makusanta.

 Kadaita Allah cikin sunayensa da siffofinsa

menene kishiyar tauhidin sunaye da siffofi?

kishiyarsa shi ne ilhadi cikin sunayen Allah da siffofinsa da ayoyinsa, kuma shi nau’i uku ne

na farko: ilhadin mushirikai wadanda suka karkatar da sunayen Allah Madaukaki daga yanda suke kuma suka kira da ita gumakansu sai suka kara kuma suka rage sai suka ciri laata daga Al-ilaah da kuma uzzaa daga Al-Aziiz da kuma manaata daga Al-Mannaan.

na biyu: ilhadin masu kamantawa sune wadanda suke kwaikwaita siffofin Allah Madaukaki kuma suke siffanta shi da irin siffofin halittarsa kuma shi ne mukabilin ilhadin mushirikai to wadannan sun daidaita ababan halitta da Ubangijin talikai, kuma wadannnan sun sanya shi matsayin jukkuna ababan halitta kuma suka siffanta shi da ita ya daukaka kuma ya tsarkaka abisa haka.

na uku: ilhadin masu korewa kuma su kaso biyu ne: kason da suka tabbatar da lafazan sunayensa Madaukaki kuma suka kore gare shi abin da suka kunsa na daga siffofin cika sai suka ce: Mai rahama Mai jin kai ba tare da rahama ba Masani ba tare da sani ba Mai ji ba tare da jib a Mai gani ba tare da gani ba Mai iko ba tare da kudura ba, kuma suka kore sauranta hakanan, da kuma kason da suka bayyana kore sunayen da abin da suka kunsa baki daya, sai suka siffanta shi da rashi tsantsa wanda ba shi da suna kuma ba shi da siffa tsarki ya tabbata ga Allah kuma ya daukaka ga abin da azzalumai masu musu masu ilhadi suke fada daukaka mai girma

Ubangijin sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu to sai ka bauta masa, kuma ka yi hakuri ga bautarsa. Shin ka san wani takwara a gare shi

Babu abinda yayi kama da Allah kuma shi ne Mai ji kuma mai gani

yana sanin abin da yake tsakanin gabansu da kuma abin da yake bayansu kuma su ba su kewaye sani da shi ba

 Dukkan nau’o’in tauhidi malizimta ne

shin dukkan nau’o’in tauhidi malizimta ne sai ya koreta dukkanta abin da yake kore wani nau’i daga gareta?

hakane ita malizimciya ce wanda yayi shirka cikin wani nau’i daga gare ta to shi yayi shirka a sauran, misalin wannan shi ne kiran wanin Allah da rokonsa cikin abin da ba mai iko akansa face Allah,to kiranta ita kadai ibada ne kai tsantsar ma ibada wacce ya juyar da ita ga wanin Allah ba Allah ba to wannan shirka ce cikin Ilahiyya.kuma rokonsa shi kadai wannan bukata ta samin alheri ko ije wani sharri yana mai kudirta cewa shi mai iko ne a bisa bada wannan, wannan shirka ce cikin rububiyyarsa ta yanda ya kudirce cewa shi mai tasarifi ne tare da Allah cikin mamallakarsa,sannan cewa shi bai roke shi wannan Addu’a daga koma bayan Allah ba face tare da kudirinsa cewa shi yana jinsa a bisa nesa da kuma kusa a cikin kowane lokaci ya kasance da kuma kowane guri kuma suna bayyanawa da wancananka kuma shi shirka ne cikin sunayen da siffofin ta yadda ya tabbatar masa da ji mai kewayewa da dukkan majiyai kusanci ba ya yi masa hijabi hakana nisa sai wannan shirka ta lazimta a cikin uluhiyya shirka cikin rububiyya da sunaye da kuma siffofi.

 Dalili bisa imani da Mala’iku daga Alkur’ani da sunna

menene dalili a bisa imani da Mala’iku daga Alkur’ani da sunna?

Dalilan suna da yawa daga Alqur’ani da kuma Sunnah daga cikinsu akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki

dalilan wancananka daga Alkur’ani suna da yawa yana daga ciki fadinsa Madaukakin sarkai:

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Lalle ne, waɗanda ke wurin Ubangijinka bã su yin girman kai ga bauta Masa, kuma sunã tsarkake shi da tasbĩhi, kuma a gare shi suke yin sujada.

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Wanda ya kasance maƙiyi ga Allah da malã'ikunSa da manzanninSa da Jibirĩla da Mĩkã'ĩla to, lalle ne, Allah Maƙiyi ne ga kãfirai.

kuma imani da su ya gabata daga sunna cikin hadisin Jibrila da waninsa, da kuma cikin sahihi Muslim cewa Allah Madaukakin sarki ya halicce su daga haske, kuma hadisai cikin sha’aninsu suna da yawa.

 ma’anar imani da Mala’iku

menene ma’anar imani da Mala’iku?

shi ne ikrari yankakke da samuwarsu kuma cewa su halitta ce daga halittun Allah horarru kuma bayi ne masu girma

Bã su gabãtarSa da magana, kuma su da umurninSa suke aiki.

ba sa sabawa Allah ga abin da ya umarce su kuma suna aikata abin da ake umartarsu

Kuma waɗanda suke wurinSa (watau malã'iku), bã su yin girman kai ga ibãdarSa. kuma bã su gajiya.

kuma ba sa kosawa kuma ba sa gajiya.

 nau’o’in Mala’iku ta izina da yadda Allah ya tanade su gare shi kuma ya wakilta su da shi

ka ambaci sashin nau’o’insu ta izina da yadda Allah ya tanade su gare shi kuma ya wakilta su das hi?

su ta izina da wancananka kashe kashe ne masu yawa, yana daga cikinsu wanda aka wakilta da kaiwa Manzanni wahayi, shi ne Ruhi amintacce Jibril Aminci ya tabbata a gare shi

kuma akwai daga cikinsu wanda aka wakilta da ruwa, shi ne Mika’il amincin Allah ya tabbata a gare shi.

kuma akwai daga cikinsu wanda aka wakilta da ruwa, shi ne Mika’il amincin Allah ya tabbata a gare shi.

kuma akwai daga cikinsu wanda aka wakilta da karbar rayuka, shi ne Mala’ikan mutuwa da mataimakansa.

kuma akwai daga cikinsu wanda aka wakilta da aiyukan bayi, sune masu girma Marubuta

kuma akwai daga cikinsu wadanda aka wakilta da kiyaye bawa daga gaba gare shi da kuma bayansa, su ne masu lura.

kuma daga cikinsu akwai wadanda aka wakiltawa Aljanna da ni’imominta, su ne Ribwan da wadanda suke tare da shi.

kuma akwai daga cikinsu wadanda aka wakiltawa wuta da azabarta, su ne Maliku da wadanda suke tare da shi daga Zabaniyawa kuma shugabanninsu goma sha tara ne.

kuma akwai daga cikinsu wadanda aka wakilta da fitinar kabari, su ne Munkar da Nakiir.

kuma suna daga cikinsu masu dauke da Al’arshi

kuma daga cikinsu akwai karubiyawa.

kuma akwai daga cikinsu wadanda aka wakilta da digon maniyyi a cikin mahaifa da kuma halittata da kuma rubuta abin da ake nufi da ita.

kuma akwai daga cikinsu wasu Mala’iku wadanda suke shiga baitul ma’amuri a kowace rana Mala’ika dubu saba’in ne suke shigarsa kuma ba sa dawowa izuwa gare shi,da kuma wasu Mala’iku das uke yawo suna bibiyar guraren zikiri.

kuma akwai daga cikinsu masu sahu suna tsaye ba sa kosawa.

kuma akwai daga cikinsu masu ruku’u ba sa dagowa

kuma akwai daga cikinsu wadanda ba wancananka ba

Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.

kuma nassoshin wannan kashe kasha daga Alkur’ani da sunna ba ya buya.

 dalilin imani da littattafai

menene dalilin imani da littattafai?

Akwai dalilai ma su yawa daga ciki akwai faxin Allah Madaukakin Sarki:

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ĩmãni da Allah da Manzonsa, da Littãfin da Ya saukar ga ManzonSa da Littãfin nan wanda Ya saukar daga gabãni.

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Ku ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabewa a tsakãnin kõwa daga gare su

kuma ya isa cikin wancananka fadinsa Madaukakin sarki:

kuma ka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi.

 shin an ambaci gaba ki dayan littattafan nan a cikin Alkur’ani

shin an ambaci gaba ki dayan littattafan nan a cikin Alkur’ani

Allah ya ambata daga cikinsu a cikin Alkur’ani shi da Attaura da Linjila da Zabura da suhufiIbrahim da Musa kuma ya ambaci sauran a jumlace sai ya ce:

Allah, bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Rãyayye Mai tsayuwa da kõme Yã sassaukar da Littãfi a gare ka da gaskiya, yana mai gasgatãwa ga abin da ke gaba gare shi, kuma Allah Yã saukar da Attaura da Linjĩlã a gabãni

kuma Allah Madaukaki ya ce

kuma mun bawa Dawuda littafin Zabura

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari?

kuma Allah Madaukaki ya ce

Haƙĩƙa, lalle Mun aiko ManzanninMu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikeli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci

to abin da Allah ya fada daga cikinsu a warware to ya wajaba a kanmu mu yi imani da shi a warwaren, kuma wanda ya ambata daga cikinsu a jimlace to ya wajaba a kanmu imani da shi a jimlacesai mu fada a cikinsa abin da Allah ya yi umarni da shi da Manzansa

kuma ka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi.

 Menene ma’anar imani da Litattafan Allah Mai girma da daukaka?

Menene ma’anar imani da Litattafan Allah Mai girma da daukaka?

ma’anarsa gasgatawa yankakkiya da cewa dukkansu ababan saukarwa ne daga Allah Mai girma da daukaka kuma cewa Allah yayi zance da ita a hakika akwai daga cikinta abin ji daga gare shi Madaukakin sarki daga bayan hijabi ba tare da wasidar Manzo Mala’ika ba, kuma akwai daga gare ta wanda Manzo Mala’ika zai isar da shi izuwa Manzo Mutum, kuma akwai daga gare ta abin da Allah Madaukakin sarki ya rubuta da hannunsa kamar yadda Allah Madaukaki ya fada:

Kuma bã ya kasancewa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so

Allah Maxaukakin Sarki yace akan Annabi Musa

ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa

Kuma Allah yayi magana da Musa Magana sosai

Kuma Ubangiji madaukaki ya fada acikin Maganar Attaura:

Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabewa ga dukan kõwane abu

Ya ce akan Annabi Isa

kuma mun bashi Linjila

kuma Allah Madaukaki ya ce

kuma mun bawa Dawuda Zabura

kuma ambatonta ya gabata da lafazin saukarwa

Allah Madaukakin Sarki yana cewa acikin Sha'anin Alkur'ani:

Amma Allah Yanã shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yã saukar da shi da saninSa. Kuma malã'iku sunã shaida. Kuma Allah Yã isa Ya zama shaida.

Allah Madaukakin Sarki yace acikin ta

Kuma yanã abin karãtu Mun rarraba shi dõmin ka karanta shi ga mutane a kan jinkiri kuma Mun sassaukar da shi sassaukarwa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijin halittu ne. Rũhi amintacce ne ya sauka da shi. A kan zũciyarka dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi Da harshe na Larabci mai bayãni.

Allah Madaukakin Sarki yace acikinta

Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi. Ɓarna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde.

da wadansunsu da yawa.

 matsayin Alkur’ani daga sauran littattafan

menene matsayin Alkur’ani daga littattafan da suka gabata?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wannan Alƙur'ãni bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabãninsa da bayãnin hukuncin littãffan Allah, Bãbu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Bai kasance wani ƙirƙiran lãbãri ba kuma amma shi gaskatãwa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukan abũbuwa, da shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suka yi ĩmãni

ma’abota tafsiri sun ce: Muhaiminan Mai amintarwa kuma Mai shaida a bisa abin da ya zo kafinsa na daga littattafai kuma mai gasgatawa da ita, yana nufin yana gasgata abin da yake cikinta na daga inganci, kuma yana kore abin da ya ya afku a cikinta na daga canji kuma yana hukunci a kanta da shafewa ko tabbatarwa, saboda haka ne duk wani mai ruko da littattafan da suka gabata yake kaskantar da kai a gare shi daga cikin wadanda basu juya masa baya ba kamar yadda Allah Madaukaki ya ce:

wadanda muka ba su littafi kafin shi su suna yin imani da shi kuma idan aka karanta a gare su sai su ce: mun yi imani da shi lalle shi gaskiya ne daga ubangijinmu lalle mu mun kasance kafin shi masu mika wuya.

 abin da ya wajaba a lazimce shi cikin hakkin Alkur’ani

menene ya wajaba a lazimce shi cikin hakkin Alkur’ani a bisa dukkan al’umma?

shi ne binsa a zahiri da badini da ruko da shi da kuma tsayawa da hakkinsaAllah Madaukaki ya ce

kuma wannan littafi ne da muka saukar da shi mai albarka to ku bi shi kuma ku ji tsoro

kuma Allah Madaukaki ya ce

ku bi abin da aka saukar izuwa gare ku daga Ubangijinku kuma kada ku bi wasu masoya koma bayansa

kuma Allah Madaukaki ya ce

kuma wadanda suke ruko da littafin kuma suka tsaida salla lalle mu ba ma tozarta ladan managarta

kuma ita ta hade komai cikin kowane littafi da ayoyi cikin wancananka masu yawa, kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi wasiyya ga littafin Allah sai ya ce:” ku kama littafin Allah kuma ku yi ruko da shi” kuma a cikin hadisin Aliyyu marfu’I “ cewa da sannu wasu fitinu za su kasance” na ce : menene mafita daga gare ta ya ma’aikin Allah? Ya ce:” littafin Allah” kuma ya ambaci hadisin

 menene ma’anar rook da Alkur’ani da kuma tsayawa da hakkinsa?

menene ma’anar rook da Alkur’ani da kuma tsayawa da hakkinsa?

kiyaye shi da karanta shi da tsayuwa das hi dare da rana da yin tadabburi ga ayoyinsa da kuma halarta halalinsa, da kuma haramta haram dinsa da kuma jawuwa ga umarninsa, da tsawatuwa daga abin da ya tsawatar da kuma lura da misalansa, da wa’aztuwa da kissoshinsa da aiki da muhkaminsa, da mika wuya ga mutashabihinsa da tsayawa ga iyakokinsa, da korewa ga barinsa canzawar

 Hukuncin wanda ya ce Alkur’ani halitta ne

menene Hukuncin wanda yace Alkur’ani halitta ne?

Alkur’ani zancan Allah ne Mai girma da daukaka tabbas harafansa da ma’anoninsa ba wai zancansa harafai ne banda ma’anoni ba kuma ba ma’anoni ne ba banda harafai Allah yayi Magana da shi Magana kuma ya saukar da shi a bisa Annabinsa a wahayi kuma muminai sun yi imani da shi tabbas to shi duk da cewa an rubuta shi da yatsu kuma an karanta shi da harshe kuma an hadda ce shi da a zuciya kuma ana jinsa da kunnuwa kuma idanuwa biyu suka ganshi hakan ba zai fitar da shi daga kasancewarsa zancan Mai rahama ba,To ‘yan yatsu da tawwadu da takardu abin halitta ne abin da kuma aka rubuta da ita baa bin halitta ba ne kuma harsuna da sautuka abin halitta ne abin da ake karantawa da ita a bisa sabaninta baa bin halitta ba ne, kiraza abin halitta ne amma kuma abin da ake haddacewa a cikinta baa bin halitta ba ne, kuma majiyu abin halitta ne amma abin da ake jin baa bin halitta ba ne

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja. A cikin wani littafi tsararre

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ã'a, shĩ ãyõyi ne bayyanannu a cikin ƙirãzan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma bãbu mai musun ãyõyinMu fãce azzãlumai

kuma Allah Madaukaki ya ce

ka karanta abin da aka yi wahayi izuwa gare ka daga littafin Ubangijinka babu mai canzawa ga kalmominsa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah

Kuma dan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: “ku dauwamar da ganinku cikin mus’hafi, kuma nassoshi a cikin wannan ba za su kidanyu ba

Duk wanda yace Alqur’ani ko wani abu daga cikin Alqur’ani halitta ne to ya kafirta kafici mai girma wanda zai fitar da shi daga musulunci gaba daya ,saboda Alqur’ani zancen Allah Maxaukakin Sarki ne da shi ya fara gare shi kuma yake komawa zancen sa kuma siffara sa ne wanda duk yace wata siffa ta Allah halitta ce to shi kafiri ne yayi ridda za’a bijiro mai da komawa Musulunci ,idan ya koma shikenan idan kuma yaqi sai a kasha shi a kafiri bas hi da wata dangantaka da hukunce hukuncen da suka hau kan Musulmi

 siffar zance zati ce ko aiki ce

Shin siffar zance zati ce ko aiki ce?

Wajen bayyana cewa siffar zancen Allah da jingina shi da Zatin Allah Maxaukakin Sarki da kuma siffanta Allah Maxaukakin Sarki da shi daga cikin siffar Zatin Allah akwai Iliminsa ya saukar da shi da iliminsa kuma shine mafi sanin abinda ya saukar ,amma wajen bayyana zancensa da ikonsa da qudirarsa siffarsa aiki ce kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yake cewa

‘’Idan Allah Madaukakin Sarki ya yi niyyar wahayi kan wani abu sai yayi magana da wahayi‘’

Hadisi

Da wannan ne Magabata na qwarai Allah yayi musu rahama suke cewa akan siffar zancen Allah Madaukakin Sarki cewa shidin siffa ce ta zatin Allah tare da aikinsa a tare ,Allah Madaukakin Sarki bai gushe ba kuma ba zai gushe ba ana siffanta shi da zaance ba har abada ,kuma yin zance dashi da zancen shi da ikonsa ne da qudurarsa yana yin zance a lokacin da ya so da yadda ya so yin zancen wanda kadai ya so ne zai iya sauraronsa ,haka kuma zancen sa ba shi da maqura ba shi da qarshe.

Da kogi zai zamo Tawwada da zai rubuta kalmomin Ubangiji Na da Kogin ya qafe kafin Kalmomin Ubangijina su qare ko da kuwa za’a karo kwatankwacin sa

Da za’a mayar da duk wata Bishiya Alqalami kogi kuma a mayar da shi Tawwada bayan shi da akwai wasu Koguna guda bakwai a rinqa qarawa Kalmomin Allah ba za su qare ba ba

Kuma kalmomin Ubangijinka sun cika da gaskiya da kuma adalci babu wani da ya isa ya canja kalmomin sa haqiqi shine Mafi ji kuma mafi Sani

 Al Wafiqa kuma mene hukuncinsu?

Su wane Al W afiqa me ne kuma hukuncinsu?

Al Wafiqa sune wadan da suke cewa akan Alqur’ani ba zamu ce Alqur’ani zancen Allah ne ba kuma ba zamu ce abin halitta ne ba ,Imam Ahmad Allah yayi masa rahama yana cewa

Duk wanda ya kasance yana kyautata zancen to shi Dan Jahamiyya ne wanda kuma ya kasance baya kyautatawa to ya zamo jahili hujja zata tsaya akansa da bayani tare da hujja, sai dai idan ya tuba ya kuma yi Imani da cewa Aqur’ani zancen Allah ne ba halitta ba ne ,in bahaka ba kuma to shi wani sharri ne daga Jahamiyya"

 Hukuncin wanda ya furta cewa Alqur’ani halitta ne

Mene ne Hukuncin wanda ya furta cewa Alqur’ani halitta ne

Wannan maganar bai halatta abarta ba haka kawai a sakewajen hani ko tabbatarwa; saboda lafazin a ma’anarsa ya haxu ne tsakanin furta lafazin wanda shi aikin Bawa ne,da abinda aka urta lafazin akan shi wanda shine Alqur’ani idan aka saki maganar kan cewa halitta ne sai ya dauki ma’ana ta biyu, ya koma kaga fadin Jahamiyya, idan kuma aka ce shi Alqur’anin ba halitta ba ne shi kuma ya hada ma’anar farko wanda shine aikin Bawa ,shi kuma wannan yana daga cikin Bidi’ar Ittihadiyya da wannan ne Magabata na qwarai suke cewa: ’’Duk wanda a furta cewa Alqur’ani halittane to shi Dan Jahamiyya ne ,wanda kuma yace ba halitta bane ta shi kuma Dan Bidi’a ne

 Dalilin Imani da Manzanni

Me ne ne dalilin Imani da Manzanni?

Dalilan suna da yawa daga Alqur’ani da kuma Sunnah daga cikinsu akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki

Lallai Wadan da suka kafircewa Allah da Manzonsa kuma suke son su raba tsakanin Allah da Manzonsa suna faxin mun yi Imani da wani sashi na Littafi mun kuma kafircewa wani sashin suna son su samu a tsakanin haka wata hanya waxannan su kafirai na gaske kuma haqiqa mun tanadarwa kafirai azaba ta wulaqanci; Waxanda suka yi Imani da Allah da Manzonsa basu kuma yi qoqarin raba tsakaninsu ba wadannan haqiqa zamu basu sakamakonsu

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Nayi Imani da Allah da Manzonsa

 Maanar Imani da Manzanni

Mene ne Imani da Manzanni?

Shi ne gasgatawa da kuma tabbatarwa haqiqa Allah Madaukakin Sarki ya aikowa kowacce Al’ummah daga cikinsu akwai wadanda suka kira su zuwa ga bautawa Allah shi kadai ,da kuma kafircewa bautawa wani abu ba Allah ba kuma daukkaninsu sun yi Imani da sun gasgata sun kuma zamo masu biyayya shiryayyu,masu karamci tsarkaka masu tsoron Allah Shiryayyu masu shiryarwa ,da hujjoji mabayyana da Ayoyi baiyanannu daga Ubangijinsu tabbatattu, cewa Su haqiqa sun isar da gabaki dayan abinda Allah ya aiko su su Boye ba ba su kuma canja ba ba su qara komai a ciki ba dai dai da harafi kuma basu rage shi ba.

Haqiqa babu komai akan Manzanni sai isar da saqo

Dukkaninsu sun kasance akan gaskiya bayyananniya ,Allah Madaukakin Sarki ya zabi Annabi Ibrahim Badadinsa ,Ya kuma zavi Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Badaxi ya kuma yi zance da Annabi Musa zance , Ya daga Annabi Idris zuwa wuri madaukaki , sannan Annabi Isa Bawan Allah ne kuma Kalmarsa ne Ya jefa ta izuwa ga Maryama kuma Ruhi ne daga gare shi kuma Allah ya fifita sashensu bisa wani Sashen Ya daukaka darajar wasunsu akan wasu.

 Da’awar Manzanni gaba daya ta hadu ne kan abinda suke umarni da kuma hani

Shin Da’awar Manzanni gabadaya ta hadu ne kan abinda suke umarni da kuma hani?

Gabaki dayan Da’awarsu ta hadu ne tun daga kan na farkon su har zuwa na qarshensu kan asalin ibada da tushenta shi ne Tauhidikan kadaita Allah a dukkanin nau’o’in bauta daga kan qudurcewa da Magana da kuma aiki tare da kuma kafircewa bautawa duk wani abu ba Allah ba.

Wajiban da aka wajabta yin bauta dasu sune Sallah da Azumi da wasunsu ba’a wajabta kan sauran ba ,an haramta akan su abinda aka halatta akan sauran jarrabawa ce daga Allah Madaukakin Sarki:

Dan ya jarrabe ku ya ga Waye mafi kyautata aiki daga cikin ku.

 Dalili kan haxuwar Manzanni kan asalin Ibada

Me ne ne dalilin haduwar Manzanni kan Aslin bauta wacce aka ambata ?

Dalili akan haka daga Littafi nau’I biyu ne Mujjamal da Mufassal

A dunkule shi ne misalign fadin Allah Madaukakin Sarki:

Haqiqa mun aiko ga kowacce Al’ummah Manzo ku bautawa Allah ku kuma guji bautawa Dagutu

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Bamu tura gabaninka ba wani Manzo face mun yi masa wahayi cewa babu wani Allah face Ni ku bauta mi ni

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Ka tambaa kan waxanda muka turo gabaninka daga Manzannin mu shin mun sanya musu komabayan Allah wani abin bauta

A bayyane kuma shi ne misalin fadin Allah Madaukakin Sarki:

Haqiqa mun aika da Annnabi Nuhu zuwa ga mutanen sa yana mai cewa dasu yak u mutane na ku bautawa Allah ba ku da Allah bayan shi

Mun aika zuwa ga Samudawa Dan uwansu Salih yace yaku mutane na ku bautawa Allah ba ku da wani Allah bayan shi

Mun aika zuwa ga Adawa Dan uwansu Hud yace yak u mutane na ku bautawa Allah ba ku da wani Allah bayan shi

Mun aika zuwa ga Mutanen birnin Madyana Dan uwansu SHu'aib yace yak u mutane na ku bautawa Allah ba ku da wani Allah bayan shi

Kuma ku tuna lokacin da Annabi Ibrahim yana cewa babansa da mutanensa haqiqa Ni na barranta daga abinda kuke bautawa sai ga wanda ya halicce ni

Musa yace hakika Allah shi ne Ubanginku babu wani Allah bayan shi saninsa ya mamaye dukkan komai

Al'masihu kuma ya ce: :

Ya ku Banu Isra’ila ku bautawa Allah Ubangiji na kuma Ubangijinku hakika duk wanda ya hada shi da abokin tarayya haqiqa Allah ya haramta masa Aljannah sannan mokomarsa wuta

Ya ce Ni ba kowa bane sai mai gargadi hakika babu wani Allah face Allah Madaukakin Sarki

Da wasun su Ayoyin

 Dalilin sabanin shari’o’insu kuwa yana daga rassan ta na daga Halal da kuma Haram

Me nene Dalilin sabanin shari’o’insu ta vangaren rassan ta daga Halal da kuma Haram?

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

Ga kowanne mun sanya muku shari’ah da kuma hanya da Allah ya so da ya sanya ku Al’ummah guda xaya amma sai dai dan ya jarabceku cikin abinda aka baku kuyi rigegeniya wajen aikata Alheri

Ibn Abbas Allah ya yi masa rahama ya na cewa ‘’Shari’ah da Hanya’’hanya ce da Sunnah misalign hakan Mujahid da Ikramata da Hasanul Basri da qatada dDihak da Sudai da Abu Ishaq Assubay’,a cikin Sahihul Bukhari Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa: ’’Mu Annabawa yan uwa ne saboda munufar addinmu daya ne ‘’yana nufin Tauhidi wanda Allah ya aiko dukkannin Manzanni da shi kuma kowanne Littafi da aka saukar ya qunshe shi ,amma shari’o’I sun banbanta a umarni da kuma hani da kuma cikin Halal da kuma Haram

Dan ya jarrabe ku ya ga Waye mafi kyautata aiki daga cikinku.

 Shin Allah ya bada labarin dukkanin Annabawa a cikin Alqur’ani

?Shin Allah ya bada labarin dukkanin Annabawa a cikin Alqur’ani

Hakika Allah Madaukakin Sarki ya bamu labarin kissoshin su abinda zai ishe mu ya kuma zamo wa’azi da kuma darasi a gare mu sai Allah Madaukakin Sarki y ace:

Wasu Manzannin mun baka labarin su tun a farko wasu kuma bamu baka labarinsu ba

Zamu yi Imani da dukkanninsu a rabe a wajen da aka raba ,a kuma hade a wajen da aka hade.

 Annabawan da aka ambaci sunan su a Qur’ani

Nawa ne Annabawan da aka ambaci sunan su a cikin Alqur’ani?

Daga cikin wadan da aka ambaci sunan su akwai :Adam,da Nuh da Idris da Hud da Salih da Ibrahim da Isma’il da Ishaq da Ya’aqub da Yusuf da Lud da Shu’aib da Yunus da Musa da Haruna da Ilyas da Zakariya da Yahya da Yasa’ da Zal kifil da Dawud da Sulaiman da Ayyub an ambaci Al’Asbad a jumlace da Isa da Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi tare da su baki daya

 Ulu-Azm na Manzanni

Su waye Ulu-Azm daga Manzanni

Su biyar ne Allah ya ambace su daya bayan daya a wurare guda biyu a cikin Alqur’ani ,wuri na farko cikin Suratul Ahzab shi ne fadin Allah Madaukakin Sarki

A lokacin da muka kulla alkawari da Annabawa tare da kai da Nuh da Ibrahim da Musa da Isa Dan Maryam

Wuri na biyu kuma a Suratus Shura shine fadin Allah Madaukakin Sarki:

An shar’anta muku a cikin addini abinda aka y Nuhu wasiyya da shi da abinda muka yi maka wahayi da abinda muka yi wa Ibrahim da Musa da Isa wasiyya da shi Su tsaya akan addini kada Su rarraba a cikinsa

 farkon Manzanni

Wa ne ne na farkon Manzanni:

Na farkon su bayan sabanin da aka samu shi ne Nuh amincin Allah ya tabbata a gare shi kamar yadda Allah madaukakin Sarki yace:

Hakika mun yi wahayi gare ka kamar yadda muka yi wahayi zuwa Nuh da Annabawan da suka zo bayan shi

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kafin su mutanen Nuh sun karyata shi tare da jama’ar da suka zo bayansu

Yaushe ne sabanin ya faru?

Ibn Abbas yardarm Allah ta tabbata a gare shi yana cewa :tsakanin Annabi Nuh da Annabi Adam Karni goma ne dukkaninsu sun kasance akan shari’a ta gaskiya sai suka yi sabani

Sai Allah ya aiko Manzanni masu bushara da gargadi

 Cika makin Annabawa

Wa ne ne cikamakin Annabawa?

Cika makin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Me ne ne dalili akan haka?

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Annabi Muhammadu bai zamo Uban daya daga cikin mazajenku ba sai dai shi Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Hakika a bayana zai kasance a sami wasu mutane Makaryata su talatin dukkaninsu zasu zo suna da’awar Annabta kuma ni ne cikamakin Annabawa babu wani Annabi baya na

Yazo a cikin Sahihul Bukhari maganarsa ga Aliyu Allah ya yarda dashi

Shin ba zaka yarda ka zamo min kamar yadda Annabi Haruna yak e ga Musa ba sai dai babu wani Annabi bayan ni

Kuma fadin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a cikin Hadisin Dujal

Ni ne cikamakin Annabawa babu wani Annabi baya na

 Abinda Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya kebanta da shi daga sauran Annabawa

Abin da Annabi tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kebanta da shi daga sauran Annabawa?

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana da abubuwa masu yawa da ya kebanta da su daga cikinsu akwai: kasancewarsa cikamakin Annabawa kamar yadda muka ambata ,sannan kuma akwai kasancewar sa Dan Annabi Adam kamar yadda fadin Allah Madaukakin Sarki ya fassara:

Wadan can Annabawan mun fifita sashensu akan sashe daga cikin su akwai wanda Allah ya yiwa Magana ya Daukaka darajar wadansunsu

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa ‘’ Ba ina alfahari ba ne Nine shugaban yayan Adam’’daga cik kuma an aiko Annabi trira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi zuwa ga mutane baki daya Aljanunsu da kuma mutanensu kamar yadda Allah Madaukakin Sarki y ace:

Ya ku mutane ni manzon Allah ne zuwa gare ku baki Daya

kuma Allah Madaukaki ya ce

Bamu aiko ka ba sai zuwa ga mutane baki daya Mai gargadi kuma Mai bushara

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba)wata daya gabanin haduwar mu, kuma aka sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah na kuma abar yin tsarki,don haka duk wanda salla ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai, Ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane gaba daya

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Na rantse da wanda raina ya ke hannunsa babu wani a cikin wannan Al’ummah Bayahude ko Nasara da zai ji wani abu game dani,sannan ya mutu bai yi Imani da abinda aka aiko ni da shi face sai ya zamo daga cikin yan wuta

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana da abubuwan da ya kevanta dasu da yawa waxanda bamu ambata ba ka bibiye su cikin nassoshi

 Mu’ujizar Annabawa

Me ce ce Mu’ujizar Annabawa?

Mu’ujiza wani abu ne da ya sabawa Al’ada ba’a saba ganin shi ba wanda yake hade da qalubale ,imam dai ta kasance abinda ido zai iya gani ce ko abinda za’a iya ji kamar fitar Taguwa daga dutse da kuma juyewar Sanda ta zamo Micijiya da maganar abubuwan da su da rai da wasun haka ko kuma wanda shi ba jiki bane da za’a iya gani da ido kamar Mu’ujizar Alqur’ani

Duk wadan nan an bawa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi babu wata Mu’ujiza da wani Annabi yake da ita face an bashi ita shima mafi girmanta daga cikinsu tsagewar Wata da begen kututturen Dabino da bulbular ruwa daga tsakankanin yanyatsun sa masu daraja da maganar karfata da tasbihin Abinci da wasun hakan wadan da suka zo cikin Labarai masu inganci sai sub a kamar sauran Mu’ujizozin Annabawa bane wadan da aka hada su da wadan su abubuwan ba.

Babu abinda yayi saura daga gare sai ambatonta ,Mu’ujizar da ta wanzu itace Mu’ujizar Alkur’ani wacce abubuwan mamakinta basa Karewa sannan vata bata shigarsa ta dukkanin geffansa ta gabansa ko ta bayansa saukakke ne daga Mai Hikima abin Godewa

 Dalilin Mu’ujizar Alqur’ani

Mene ne Dalilin Mu’ujizar Alqur’ani?

Dalili kan haka shine saukar da Alkur’ani fiye datsahon shekara ashirin yana kalubalantar mafi fasahar halittu kuma mafi iya zancenta mafi balagarta mafi daukaka wajen iya bayani yana mai cewa:

Su zo da wani zancen kwatankwacinsa in sun kasance masu gaskiya

kace musu su zo da Surori goma in kun kasance Masu gaskiya ne

kace musu su zo da Surori goma kwatankwacinsa wadanda sukekirkirarru

Basu aikata hakan ba duk da tsananin kwadayinsu wajen yin raddi ga Alqur’ani da duk abinda za su iya saboda kasantuwar Harufansa daga jinsin harshen da suke Magana da shi suke rigegeniya kuma suke alfahari da shi sai akayi kira da bayanin mu’ujizarsa gazawarsu da bayyana

Da mutane da Aljanu za su haxu kan su zo da kwatankwacin wannan Alqur’’anin ba zasu zo da shi ba koda kuwa sashinsu yana taimakar sashi

Annabi tsira da Amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Babu wani Annabi daga cikin Annabawa face an bashi daga cikin Ayoyi wadan da mutane za su yi Imani da shi Ni kuma abinda aka bani shi ne wahayi Allah yana yi min wahayi ina fatan na fisu mabiya ranar tashin Alqiyama

Mutane sun wallafa Littattafai kan mu’ujizar Alqur’ani ta fuskar Laffuzan sa da ma’anoninsa da labaran wadan da suka gabata da wadan da zasu zo wadan da gaibu ne duk da haka basu kai maqurar sa ba face kamar yadda Tsuntsu yake tsoma bakin sa cikin kogi

 Dalilin Imani da Ranar Lahira

Mene ne Dalilin Imani da Ranar lahira?

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Lalle ne wadanda bas u qaunar gamuwa da mu ,kuma suka yarda da rayuwar duniya kuma suka nutsu da ita ,da wadan da suke gafalallu ne daga ayoyinmu.Wadan nan matattararsu Jahannama ce saboda abinda suka kasance suna tsuwurwurta

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai abinda ake yi muku alqawari(da zuwansa),haqiqa gaskiya ne kuma lallai sakamako (ga aiyukanku) haqiqa mai afkuwa ne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma lallai ne Sa’ar Tashin Alqiyama mai zuwa ce babu shakka a cikinta

Da wasunsu na daga ayoyi.

 Mene ne Ma'anar Imani da Ranar lahira?

Me ne ne ma’anar Imani da ranar lahira me ne ne kuma zai shiga cikinta ?

Ma’anarta shi ne Imani tabbatacce kan cewa lallai zata zoba makawada kuma aiki kan wajabcin haka Imani da Alamomin tashin Alqiyamav wadan da zasu faru ba makawa.

Da kuma mutuwa da fitinar da zata faru cikin kabari bayan mutuwar da azabarsa da ni’im ominsa da busar qaho da fitar halittu daga kabari da kuma abinda zai faru a filin tashin Alqiyama na daga firgici da rabe raben taron da raba takardu da awo da siradi da kogi da ceto da wasunsu da Aljannah da ni’imominta wanda mafi kololuwar ta shi ne ganin Allah Madaukakin Sarki da kuma Wuta da azabarta mafi tsananinta shi ne hijabi tsakaninsu da Ubangijinsu Madaukakin Sarki.

 Zuwan Tashin Alkiyama yana daga cikin limin gaibu

Shin wani ya san yaushe Alqiyama zata tashi ?

Zuwan tashin Alqiyama yana daga ilimin gaibu wanda Allah Madaukakin Sarki ya boye saninta kamar yadda ya fada :

Lallai Allah a wurinsa kawai sanin Sa’a yake ,kuma yana saukar da girgije ,kuma yana sanin abinda yake cikin mahaifa kuma wani rai bai san abinda yake aikatawa gobe ba ,kuma wani rai bata san a wacce qasazata mutu ba.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Suna tambayarka game da Sa’a,wai yaushe ne zata tabbata ?me ya hadaka da ambatonta? zuwa ga Ubangijinka qarshen al’amarinta yak e.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Suna tambayarka game da Sa’a,wai yaushe ne zata tabbata ?me ya haxaka da ambatonta?zuwa ga Ubangijinka qarshen al’amarinta yak e.

A yayin da Mala’ika Jibril yacewa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi bani labari akan Sa’a sai Yace: ’’Wanda ake tambaya bai fi wanda yake tambayar sani ba ‘’sai ya ambaci alamominta an qara a ruwayar: ’’cikin abubuwa guda biyar da babu wanda ya sansu sai Allah Maxaukakin Sarki’’ sai ya karanta ayoyin da suka gabata.

 Alamomin Sa’a daga Alqur’ani

Me ne ne misalign alamomin Sa’a daga Alqur’ani?

Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:

Shin suna jiran (wani abu )face dai mala’iku su je musu ko kuwa Ubangijinka ya je Aranar da sashen ayoyin Ubangijinka yake zuwa imanin rai wanda bai kasance yayi Imanin ba a gabani ,ko kuwa ya yi tsiwirwirin wani Alheri

Faxin Allah Maxaukakin Sarki:

Kuma idan Magana ta auku a kansu,Muna fitar musu da wata dabba daga qasa ,tana yi musu Magana cewa lallai mutane sun kasance game da ayoyinMu, basu yin imanin yaqini.

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Har sa’ar da aka bude Yajuju da Majuju alhali kuwa suna gaggawadaga kowanne tudun qasa Kuma wa’adin gaskiya ya gabato

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Saboda haka, ka dakata ranar da sama za ta zo da hayaqi bayyananne

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Yak u mutane !Ku bi Ubangijinku da Taqawa Lalle ne girgizar qasa ta tsayuwar Sa’a wata aba ce mai girma

 Alamomin Sa’a daga Hadisi

Me ne ne misalign alamomin Sa’a daga Hadisi?

Misalin hadisin fitowar rana daga yamma da hadisin Dabbada hadisin fitintinu kamar Dujal da Yakuna.

Da hadisin saukowar Annabi Isa ,da fitowar Yajuju da Majujuda hadisin Hayaqi ,da hadisin Iska da zata xauki ran dukkanin Muminai da hadisin Wutar wacce zata bayyana da hadisin Kusufi da sauransu.

 Dalilin Imani da Mutuwa

Me ne ne dalilin Imani da Mutuwa?

Allah ya yi masa Rahama

Kace :Mala’ikan mutuwa ne wanda aka wakkala a gare ku ,shi ne ke karvar rayukanku ,sannan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kowacce rai mai dandanar mutuwa ce ,sa’annan zuwa gare mu ake mayar da ku

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Lallai kai zaka Mutu kuma suma zasu Mutu din

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma bamu sanya dauwama ga wani mutum ba agabaninka Shin to idan ka mutu su madawwama ne?

kuma Allah Madaukaki ya ce

Dukkan wanda ke kanta mai qarewa ne,kuma fuskar Ubangijinka mai girma da Jalala da karamci irtace take wanzuwa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kowanne abu mai halaka ne face fuskarsa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ka dogara ga Mai ran da baya mutuwa

Akan wannan da hadisai waxanda ba zasu qirgu ba ,abin lura anan babu wanda zai jahilce shi babu kuma shakka acikinsa ko wani kaikawo sai dai cewa girman kai ba zai yi aiki kan wajabcin imaninsa da shi babu komai bayansa sai bayin Allah masu Ikhlasi mun kuma yi Imani cewa duk wanda ya mutu ko aka kasha da kowanne irin sababi ya kasance babu abinda zai rage shi da komai saboda hakan

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Kowanne yana gudana zuwa ga ajali ambatacce

kuma Allah Madaukaki ya ce

Idan ajalinsu yazo ba za’a jinkirta musu Sa’a xaya ba kuma ba zasugabace ta ba

 Dalilin fitinar Qabari ko Ni’imominsa daga Alqur’ani

Mene ne dalilin fitinar Qabari ko Ni’imominsa daga Alqur’ani?

Allah ya yi masa Rahama

Kayya!Lallai ne ita kalma ce, shine Mafaxinta ,alhali kuwa bayagaresu akwai wani shamaki har zuwa ranar da za’a tayar da su

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma Azaba Mummuna ta riski Mutanen Fir'auna Wuta ce wacce aka bujuro musu da ita Safe da Maraice kuma a ranar da za'a tashi Alikiyama (za'a ce) ku Mutanen Fir'auna ku shi ga cikin Mafi tsananin Azaba.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Allah yana tabbatar da wadan da sukai Imani da da magana matabbaciya a rayuwar Duniya da kuma a Lahira.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma da zaka ga Azzalumai a cikin Magagin Mutuwa kuma Mala'iku suna mika musu Hannayensu suna ku futo da Kawunanku yau ne zaa saka Muku da Azabar Wulakanci

kuma Allah Madaukaki ya ce

Za Mu yi musu azaba sau biyu ,sa’annan mu mayar dasu zuwa ga azaba mai girma

 Dalilin fitinar Qabari ko Ni’imominsa daga Alqur’ani

Me ne ne dalilin hakan daga Sunnah?

Me nene dalilin haka daga Sunnah

Daga cikinsu akwai hadisin Anas Allah ya qara masa yarda yace lallai Bawa idan aka sanya shi a cikin kabarinsa abokanansa suka juya baya daga gare shi haqiqa yana jin sautin takalmansu sai Mala’iku guda biyu su zo masa sais u zaunar da shi su ce da shi me ka kasance kana cewa kan wannan mutumin Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbbata a gare shi ?Mumini sai yace :na yi Imani ds cewa shi Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne Sai su ce da shi kalli mazauninka a wuta Allah ya canja maka da wani mazaunin a Aljannah sai ya gansu gabakixaya –sai Qatada yace an faxa mana sai a buxa masa kabarinsa .Sai ya koma kan hadisin Anas –yace amma munafiki da kafiri saisu ce masu :Me kuka kasance kuna cewa kan wannan mutumin ?sai yace :ban sani ban a kasance ne kawai ina faxar abinda mutane suka kasance suna faxa sais u ce dashi baka sani ba sais u dake shi da abin duka na qarfe duka ! sai yayi ihu ihun da duk wanda yake zagaye da shi banda mutum da Aljan

Hadisin Abdullahi xan Umar Allah ya qara yarda a gare shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :idan xayanku yam utu za’a gabato masa da mazauninsa safiya da marece wanda ya kasance daga cikin yan Aljannah za’a nuna masa nay an Aljannah wanda ya kasance nay an wuta za’a gnuna masa na yan wuta ace dashi wannan shine mazauninka har zuwa ranar da Allah zai tashe ka ranar tashin Alqiyama

Da Hadisin kabarurruka guda biyu an ce ana yi musu azaba

Da hadisin Abu Ayub Allah ya yarda da shi yace :Mun fita da Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a lokacin rana ta fito sai muka ji wani sauti ,sai Yace :Wata Bayahudiya ce ake azabtar da ita a kabarinta

Da hadisin Asma’ Manzan Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata agare shi ya tashi yana haxuba akan fitinar kabari wacce za’a fitini Bawa da ita sai Musulmai suka fara hayaniya sosai sai Aisha Allah ya qara yarda a gare ta tace :tun daga Nan ban qara ganin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yayi Sallah ba face ya nemi tsari da azabar kabari ,a hadisin kusufi Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya na neman tsari daga azabar kabari duk waxannan hadisan hadisai ne masu inganci sun kai kusan hadisai sittin dagatabbatattun hanyoyi daga jama’a ta Sahabbai

 Dalilin Tashi daga kabari

Me ne ne dalilin Tash idaga kabari ?

Fadin Allah Madaukaki

Yak u mutane !idan kun kasance a cikin shakka a tashin Alqiyama ,to lallai ne mu mun halittku daga turvaya ,sa’annan kuma daga gudan jinni ,sa’annan kuma daga tsoka wadda ake halittawa da wadda ba’a halittawadomin mu bayyana muku kuma muna tabbatar muku da abinda muke so acikin mahaifa zuwa wani loqaci ambatacce

Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:

Wancan ne domin lallai Allah shine gaskiya kuma lallai ne shi yake rayar da matattu kuma lallai shi mai iko ne kan dukkan komai .Sannan kuma Sa’a haqiqa lallai mai zuwa ce kuma haqiqa Allah ne yak e tayar da waxanda suke cikin kabari

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma shine ke fara yin halitta ,sa’annan ya sake ta kuma sakewar tafi sauki a gare shi

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kamar yadda muka fara a farkon halitta muke mayar da ita

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma mutum yana cewa, Shin idan na mutu lallai ne haqiqa da sannu za’a fitar dani ina mai rai

Sannan faxinsa

Shin kuma basu gani ba cewa :lallai Allah ,Wandaya halitta sammai da qasa kuma bai kasa ga halittarsu ba Mai ikonyi ne akan rayar da matattu ?Na’am, lalle Shi ,Mai ikon yi ne akan komai

Har ya zuwa qarshen Surar

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma daga cikin ayoyinsa cewa kana ganin Qasa qeqasasshiya ,to idan mun saukar da ruwa a kanta ,sai ta girgiza kuma ta kumbura .Lallai wannan da ya raya ta ,haqiqa Mai rayar da matattu ne .Lallai Shi Mai ikon yi ne akan kowanne abu.

Har ya zuwa qarshen Surar

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma daga cikin ayoyinsa cewa kana ganin Qasa qeqasasshiya ,to idan mun saukar da ruwa a kanta ,sai ta girgiza kuma ta kumbura .Lallai wannan da ya raya ta ,haqiqa Mai rayar da matattu ne .Lallai Shi Mai ikon yi ne akan kowanne abu.

Da yawa Allah yana Maxaukakin Sarki yana buga misali da yaddayake rayar da Qasa da ruwa sai ta wayi gari ta girgiza ta fitar da korayen tsirrai bayan ta mutu saboda rashin ruwa bayan ta kasance kafin nan matacciya Da wannan ne Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya buga misali a cikin hadisi mai tsaho na Aqil inda yake cewa

Rantsuwa da Ubangijinka babu wani Mutum a bayan kasa da zai Mutu ko a kashe shi sai an tsaga masa Kabari har sai ta tallafo shi ta wajen kansa sai ya Zauna yana cewa: ai maye ya faru ga ke? sabida abinda ya kasance ya saba da shi yana zaton yana zantar da Iyalansa ne sai na ce: ya Manzon Allah yaya za'a hada mu bayan mun rududduge ko kuraye sun cinye mu sai ya ce: ina baka labari ne da Ni'amomin Allah a bayan kasa kuma ita ko da ta rududduge kamar ganyen bishiya sai na ce: ba zai rayu ba? sai Allah ya aiko sama bata dade ba sai kwatatnkwacin kwanaki har ta rufe ta to sai ta zama daya kuma Rantsuwa da Ubangijinka mai iya taro ku ne daga Ruwa kamar yadda yake tare tsirrai a kasa sai ku futo daga Kaburburanku.

 Hukuncin wanda ya qaryata tashi

Mene ne Hukuncin wanda ya qaryata tashi ?

Ya kafircewa Allah da Manzonsa da Littattafan sa

Allah ya yi masa Rahama

Kuma waxanda suka kafirta suka ce: ’’shin idan mun kasance turvaya mu da Ubanninmu shin haqiqa waxanda ake fitarwa ne ?

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma idan ka yi mamaki ,to mamakin kam shine maganarsu ,’’shin idan muka kasance turbaya za mu zama a cikin wata halitta sabuwa ?’’Wadan can ne wadan da suka kafircewa Ubangijinsu ,kuma wadan da akwai ququmai acikin wuyoyinsu ,kuma wadan can ne abokan wuta .Su a cikinta ,masu dawwama ne.

kuma Allah Madaukaki ya ce

‘’Waxanda suka kafirta sun riya cewa ba za’a tayar da su ba .Ka ce :Niina rantsuwa da Ubangijina ,lallai za’a tayar da ku haqiqatan ,sa’an nan kuma lallai ana labari game da abinda kuka aikata Kumawannanga Allah mai sauki ne

Acikin Sahih Muslim ya rawaito kuma cewa Zaidu Dan Arqam Allah ya Kara yarda da shi cewa Annabi tsira da Amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa.

Allah Maxaukakin Sarki yace ‘’Dan Adam ya qaryata ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi bay a zage ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba amma qaryatawar shi gare ni shine ya ce Allah ba zai dawo dani ba kamar yadda ya halicce ni a farko ba wai halittar ta farkon it ace mafi sauqi ba daga dawowar da su ,zagin kuma shine ya ce a kaina faxinsa Allah Madaukakin Sarki yana da da alhalin ni Daya ne wanda ake nufinsa da buqata Ban Haifa ba ,ba’a kuma haifeni ba .Kuma babu daya da ya kasance tamka a gare ni"

 Dalilin busar Qaho

Me ne ne dalilin busar Qaho kuma busa nawa za’a busa cikinsa ?

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Kuma aka busa a cikin qaho ,sai waxanda ke a cikin sammai da qasa suka suma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa ) sa’annan aka hura a cikinsa ,wata hurawa ,sai ga sun tsaitsaye ,suna kallo

A cikin wannan ayar an ambaci busa guda biyu ta farko dan suma ,ta biyu kuma ta tashi

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma ranar da ake busa qaho ,sai wanda ya ke a cikin sammai da waxanda suke a cikin qasa su firgita ,face waxanda Allah ya so

Wanda ya fassara firgita da cikin wannan aya da suma it ace busa ta farko wacce aka ambata a cikin Suratuz Zumar ,hadisin Muslim zai taimaka masa:

Sa’annan sai a busa Qaho babu wanda zai ji sai wanda ya fi kowa ji sai yace na farkon wanda zai ji shine wani mutum sai yace :sai ya suma sai mutaneduka su suma ,sai Allah ya aiko da ko kuma yace:sai Allah ya saukar da ruwan sama kai kace wata inuwa ce ta wani bangare na kaya daga sai Jikunan Mutane su tsuro san nan akuma wata busar sai Mutane su tashi suna kallo"

Hadisi

Wanda ya fassara firgita da ba tare da sum aba to busa ta uku ce wacce ta biyo bayan busa guda biyu abinda ke cikin hadisi mai tsaho kan qaho zai taimaka a ciki an ambaci busa uku: busa ta farko ta firgita sai busar suma sai kuma ta tashi zuwa ga Ubangijin Talikai.

 Siffar taron tashin Alqiyama daga Alqur’ani

Yay a siffar taron tashin Alqiyama take Alqur’ani ?

Akwai ayoyi da yawakan haka daga cikinsu akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki:

Kuma lallai ne haqiqa kun zo mana xai xai kamar yadda Muka halittaku a farkon loqaci

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma muka tara su ba mu bar kowa ba daga gare su

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

A ranar da muka tara masu taqawa zuwa ga Mai rahama suna bakin girma Kuma lallai Muna kora masu laifi zuwa Jahannama da gaggawa

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Kuma kun kasance nau’I uku .Wato mazowa dama .Me ne ne mazowa dama ?Da mazowa hagu .Me ne ne mazowa hagu ?Da waxanda suka tsere .Su wadan da suka tseren nan sun tsere

Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

Aranar nan suna biyar mai kira ,babu karkata a gare shi ,kuma sautuka suka yi kawici ga Mai rahama ,b aka sauraren komai face sautin tafiya.

Shine tafiyar sawaye zuwa wurin taruwa kamar takun Raqumi .Allah Madaukakin Sarki yana cewa :

Kuma wanda Allah ya shiryar to shine shiryayye ,kuma wanda y avatar to ba zaka sami waxansu masoya gare su ba bayan shi Kuma zamu tara su a Ranar qiyama akan fuskokinsu

Da wasun wadan nan daga Ayoyi.

 Siffar taron tashin qiyama daga Sunnah

Yay a siffarsa take daga Sunnah ?

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Za’a tashi mutane akan qungiyoyi guda uku masu kwadayi masu addiniguda biyu kuma akan raqumi ,uku ma akan raquma da hudu ma akan raquma ,sai a tara sauran a wuta ta yi musu loqacin da suka yi Magana ,ta wayi gari da su loqacin da suka wayi gari,ta yi yammaci da su loqacin da suka kai yammaci.

Daga Anas xan Malik Allah ya yarda da shi ya ce: wani mutum ya ce ya Annabin Allah ta yaya za’a tashi kafiri akan fuskarsa sai Yace:

Shin wanda ya tafiyar da shi a duniya kan qafafu biyu a duniya ba mai iko bane ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alqiyama?

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:

Za’a tashe ku ranar tashin Alqiyama mara sa takalma matsiraita kamar yadda aka halittamu farkon halitta zamu koma

Farkon wanda za’a suturta daga ababan halitta ranar tashin Alqiyama shine Annabi Ibrahim ‘’Hadisi sai Aisha Allah ya qara yarda da ita ta ce :Ya Mnzon Allah Maza da Mataduka sashensu yana kallon sashe ?’’Sai Ya ce al’amarin ya fi haka tsanani ballantana wannan ya dame su ‘’

 Siffar wurin tsayawa ranar tashin Alqiyama daga Littafi

Yay a siffar wajen tsayawa take daga LIttafi ?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Kuma kada kayi zaton Allah Mai shagala ne daga abinda Azzalumai suke aikatawa .Abin sani kawai ,Yana jinkrita musu ne zuwa ga wani wuni ,wanda idanuwa su ke fita tsuru tsuru a cikinsa .Suna masu gaggawa,masu xaukaka kawunan su zuwa sama kiftawar ganinsu bata komawa gare su .Kuma zukatansu wofintattu .

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ranar da Ruhi da mala’iku za su tsaya a cikin sahu ,babu mai Magana sai wanda Allah ya yiwa izini ,kuma ya faxi abinda ke daidai

Allah Madaukaki ya ce

Kuma ka tsawatarsu Ranar Alkiyama lokacin da Zukata suka zo iya wuya suna masu hadiye fushi kuma lallai Azzalumai basu da Abokakan Arziki ko wani Mai ceto da ake binsa.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Acikin yini wanda gwargwadonsa ,shekara dubu Hamsin ne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Za mu xauki lokaci saboda ku ,yak u masu nauyin halitta biyu !

Da wasun haka masu yawa:

 Siffar tsayuwar tashin Alqiyama daga Sunnah da siffar hisabi daga Alqur’ani

Yaya siffar tsayuwar tashin Alqiyama daga Sunnah ?

Akan haka da akwai hadisai dayawa daga ciki an karvo daga Ibn Umar Allah ya qara yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta

Sai ya ce :’’Xayansu zai tashi a cikin gumi zuwa kunnensa

Da hadisin Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Mutane za su yi gumi ranar tashin Alqiyama har sai gumi yazo yana gudana a qasatsahon zira’I saba’in sa’annan ya rufe su ya kai har kunnen su

Yaya siffar bijirowa da hisabi daga Alqur’ani ?

Allah Madaukaki ya ce

A ranar nan za’a bijiro da ku (domin hisabi ),babu wani rai ,mai voyewa ,daga cikinku ,wanda zai iya voyewa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma a gitta su ga Ubangijinka suna sahu guda ,(mu ce musu ))lallai ne haqiqa kun zo Mana ,kamar yadda Muka halittaku a farkon lokaci.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma a ranar da Muke Tarawa daga kowacce al’umma,wata qungiya daga waxanda suke qaryata ayoyinMu,sai gas u ana kange su (ga kora) Har idan sun zo (Allah)zai ce ,’’Ashe kun qaryata ayoyinNa,kuma ba ku kewaye su da sani ba? To me ne ne kuka kasance kuna aikatawa?’’

kuma Allah Madaukaki ya ce

A ranar nan mutane za su fito daban-daban domin a nuna musu aiyukansu. to Wanda ya aikata gwargwadon kwayar zarra na alheri zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon kwayar zarra na sharri zai gan shi

kuma Allah Madaukaki ya ce

To rantsuwa da UbangijinKa !Haqiqa ,Muna tambayar su gaba daya game da abin da Suka aikata

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma ku tsayar da su ,lallai su ,waxanda ake yiwa tambaya ne

To ya ya sifar hakan ta ke?

Akwai hadisai masu yawa:

Faxar Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ta gabata

Wanda aka binciki Hisabin sa za’a yi masa Azaba

Aisha Allah ya qara mata yarda ta ce :Shin ba Allah ne ya ce ba :to za’a yi masa hisabi ,hisabi mai sauqi .sai Ya ce :’’wannan shine bijirowar’’

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Za’a zo da kafiri ranar tashin Alqiyama sai a ce dashi shi :shin da za’a ce kana da zinari cikin qasa shin zaka yi koyi dashi ?sai yace na’am ,sai ace dashi an tambayeka abinda yafi wannan sauki –Awata ruwayar kuma haqiqa an tambayeka abinda yafi wannan sauqi cewa kar kayi shirka ga Allah amma sai kaqi kayi shirkar

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

‘’Babu xaya daga cikinku face sai ya yi Magana da Ubangijinsa babu wani tafinta a tsakaninsu sai yayi duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikaata yayi duba zuwa hagu shim aba zai ga komai ba face abinda ya aikata ya yi duba zuwa geffansa ba zai ga komai ba sai wuta tana haxuwa da fuskarsa ku ji tsoron wuta koda kuwa da gutsiren Dabino ne koda kuwa da kalma mai kyau ce ‘’

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

‘’Xaya daga cikinku ,yana nufin mumini zai sunkuyawa Ubangijinsa har sai ya sanya kafaxarsa akansa sai yace da shi ka aikata kaza da kaza sai yace na’am ya kuma cewa ka aikata kaza da kaza sai yace :na’am sai ya miqar dashi sannan yace :na suturtaka a duniya a yau kuma na gafarta maka ita ‘’

Da wasun wadan nan daga Hadisai.

 Siffar watsa takardu dagaLittafi

Yaya siffar watsa takardu daga Littafi ?

Allah Madaukaki ya ce

Kuma kowanne mutum Mun lazimta masa abin rekodinsa a cikin wuyansa kuma mMu fitar masa a ranar tashiin qiyama da littafi wanda zai hadu da shi budadde.Ka karanta Littafinka ,ranka ya isa ya zama mai Hisabi a kanka a yau

kuma Allah Madaukaki ya ce

Idan takardun ayyuka aka watsa su (ga masu su)

Allah Madaukaki ya ce

Kuma aka aza Littafin ayyuka ,sai kaga masu laifi suna jin tsoro daga abinda ke cikinsa ,kuma suna cewa kaiconmu !Me ne ne ga wannan Littafi ,baya barin qarama,kuma baya barin babba ,face ya qididdige ta?kuma suka sami abinda suka aikata halarce kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa.

Allah Madaukaki ya ce

Amma wandaaka bawa littafinsa a damansa ,sai y ace wa (makusantansa )’’ku karva ,ku karanta Littafina’’har zuwa faxinsa :masu ganganci

Acikin ayar suratul Inshiqaq kuma

To ,amma wanda aka bawa Littafinsa a damansa

Kuma ya ce:

Kuma amma wanda aka bawa Littafinsa daga wajen bayansa

Wannan yana nuni kan cewa duk wanda ya karbi Littafinsa da Damansa za’a bashi ta gabansa wanda kuma aka bashi da hannun Hagu za’a bashi ta bayan sa ne muna neman tsari da Allah Maxaukakin Sarki

 Siffar watsa takardu daga Sunnah

Mene ne dalilin hakan daga Sunnah ?

Akwai hadisai masu yawa kan haka daga cikinsu akwai :faxin Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ‘’Mumini zai sunkuya ga Ubangijinsa har sai ya sanya kafaxarsa akan shi sai ya miqar da shi daga sunkuyon nasa yace dashi kasan zunubi kaza? sai yace na sani yace haka ga Ubangijinsa sau biyu na sani ,sai yace na suturta shi a duniya ,a yau kuma na gafarta maka su ,sai a naxe takardar aiyukansa na alheri ,amma sauran ko kuma kafirai sai a kira musu manyan masu shaida su ce

‘’Waxannan ne suka yi qarya ga Ubangijinsu ‘’

Aisha Allah ya qara yarda a gare ta ce n ace da Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi shin masoyi zai ambaci masoyinsa ranar tashin Alqiyama ?sai yace ya Aisha amma a waje uku ,amma a wajen mizani har sai yayi nauyi ko ya yi rauni ,amma wajen watsa takardu ko dai ka karva da Dama ko kuma ka karva Hagu da kuma lokacin da ake fitar da wuya daga wuta.

Ahmad ne ya rawaito hadisin da Abu Dawud da wasun waxannan daga hadisai

 Dalilin Mizani daga Littafi da Siffarsa take

Dalilin Mizani daga Littafi da Siffarsa take

Allah ya yi masa Rahama

Kuma Muna aza ma’aunan adalci ga ranar qiyama ,saboda haka ba’a zaluntar rai da komai .Kuma koda ya kasance nauyin qwaya daga komayyane Mun zo da ita .kuma Mun isa zama Masu hisabi

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma awo a ranar nan gaskiya ne .to ,wanda sikelansa suka yi nauyi ,to waxannan su ne masu cin nasara,kuma wanda sikelansa suka yi sauqi,to waxannan ne waxanda suka yi hasarar rayukansu, suna madawwama a cikin jahannama

Allah Maxaukakin Sarki yace game da kafirai

Ba zamu tsayar musu da awo ba a ranar qiyama

Da wasun waxannan daga ayoyi.

Me ne ne dalilin Siraxi daga Sunnah da Siffarsa ?

Akwai hadisai masu yawa:

Daga ciki akwai hadisin kati wanda cikinsa akwai shahada guda biyu tana da feji saba’in na munanan aiyuka kuma kowacce takarda anyi rubtu a cikin iyakar ganin idonka

Daga ciki akwai faxin Manzon Allahkan Ibn Mas’ud Allah ya yarda dashi:

‘’Kuna mamakin takun qafafu ne to ,a mizani nauyisnsu yafi nauyin wani xayan ‘’

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

‘’Haqiqa za’a zo da wani mutum mai girma mai qiba ranar tashin Alqiyama amma a wajen Allah ba za’a gwada shi ba ma da fiffiken Sauro ‘’sai yace :ku karanta

Ba zamu tsayar musu da awo ba a ranar qiyama

Da wasun waxannan daga Hadisai.

 Dalilin Siraxi daga Littafi

Me ne ne dalili kan Siraxi da Littafi ?

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

Kuma babu kowa daga gare ku sai mai tuzga mata.Ya kasance wajibi ga UbangijinKa hukuntacce Sa’annan kuma Mu tserar da waxanda suka yi aiki da taqawa ,kuma mu bar azzalumai a cikinta gurfane

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ranaar da za ka ga Muminai Maza da Muminai Mata haskensu na tafiya a gaba gare su

 Dalilin Siraxi daga Sunnah da Siffarsa

Me ne ne dalilin Siraxi daga Sunnah da Siffarsa ?

Akwai hadisai masu yawa:

Daga ciki akwai faxin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare cikin hadisin ceto:

Za’a zo da Gada sai a sanya ta tsakanin bayan Jahannama sai muka ya Manzon Allah me ce ce Gada ?sai yace: mai rinjaya ce

Hadisin ya zo a cikin Sahih

Abu Sa’id Allah ya qara yarda da shi yace : na sami labara cewa wannan Gadar tafi gashi siranta kuma tafi takobi kaifi.

 Dalilin kan Haud daga Littafi

Me ne ne dalili kan Haud daga Littafi ?

Allah ya yi masa Rahama

Lallai ne ,Allah ba Ya zaluncin gwargwadon nauyin zarra ,idan ta kasance alheri ce ,zai rivanyata kuma Ya kawodaga gunsa ijara mai girma.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Yau ana sakawa kowane rai a game da abinda ta aikata babu zalunci a yau .Lallai ne Allah mai gaggawar hisabi ne har zuwa faxin Allah :Allah yana yin hukunci ne da gaskiya

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma akayi hukunci a tsakaninsu da gaskiya ,alhalin kuwa sub a za’a zalunce su ba.

 Dalilin Haud daga Sunnah

Me ne ne dalili kan Haud daga Sunnah?

Akwai hadisai masu yawa daga ciki akwai:

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

‘’Farkon abinda za’a fara hukunci a kanshi tsakanin mutane shine Jini ‘’

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

‘’Duk wanda ya san ya zalunci Dan uwansa to, ya biya shi a yau saboda ranar lahira babu Dinari ko Dirhami da zai bawa xan uwansa sai dai a Dauka daga kyawawan aikinsa idan bashi da kyawawan aiyuka sai a xebi munanan aiyukan Dan uwansa sai a zuba masa"

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Za’a fito da mumini daga wuta sai ajiye su tsakanin Aljannah da wuta sais u bawa sashensu labarin wani zalunci da ya kasance a duniya a tsakaninsu har lokacin da za’a tafi da su a tsarkake su sai a yi musu izini da shiga Aljannah

Dukkannin waxannan yana cikin Sahih da wasunsu da yawa

 Dalilin kan Tafki daga Littafi

Me ne ne dalili kan Tafki daga Littafi ?

Allah Madaukakin Sarki yana cewa Manzonsa Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi:

Lallai ne Mu ,Mun yi maka kyautar Alkausara

 Dalilin Tafkin Alkausara daga Sunnah

Me ne ne dalili kan Tafkin Alkausara daga Sunnah?

Akwai hadisai masu yawa akan haka daga ciki akwai faxin Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Ni zan rigaku zuwa Tafkin Alkausara

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

‘’Haqiqa ni rigaku gaba kuma ni mai shaida ne a gare ku Na rantse da Allah ina ganin Tafkin Alkausara ta a yanzu ’’

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Tafkin Alkausara ta tafiyarsa Wata daya ne kuma Ruwansa Fari ne yafi Nono fari kuma Kamshinsa yafi Almiski kofunansa yawan Adadadin Taurarin Sama kuma duk wanda ya sha shi bai kara jin kishi har Abadan"

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

‘’Na je ga wata Qorama tana da qofar Lu’u lu’u rufaffe sai n ace me ne ne wannan ya Jibril?sai yace wannan shi ne Alkausara’’

Da wasun wadan nan daga Hadisai masu yawa akan shi .

 Da wasun waxannan daga hadisai masu yawa akan shi.

Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta? Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta?

AllahMadaukaki ya ce

Ku ji tsoron wuta wadda makamashinta mutane da duwatsu nean yi tattalinta domin kafirai Kuma ka bayar da bushara ga waxanda suka yi Imani ,kuma suka aikata ayyuka na qwarai,cewa lallai ne suna da gidaje a Aljannah Qoramu na gudana daga qarqashinsu

Ya zo a cikin ingantacce daga addu’ar Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a cikin Sallar dare ‘’godiya tabbata gare kaKai gaskiya ne kuma alqawarinka gaskiya ne kuma gamuwa da kai gaskiya ne ,faxarKa gaskiya ce ,Aljannah gaskiya ce ,wuta ma gaskiya ce ,Kuma Annabawa gaskiya ne kuma Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi gaskiya ne kuma ranar tashin Alqiyama gaskiya ce ‘’.Hadisi

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Duk wanda ya shaida cewa babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kadai wanda bashi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne kuma kalmarsa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare shi, kuma Aljanna Gaskiya ce haka wuta ma, to Allah zai shigar da shi Aljanna akan kowane irin aiki ya Mutu.

 Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta? Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta?

Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta? Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta?

Ma’anarsa shine Imani tabbatacce da samuwarsu ba zai gushe ba zai shiga ciki nhar abada sannan duk abinda suka qunsa a daga ni’imomi da Azaba

 Dalili kan samuwr Aljannah da wuta

Me ne ne dalili kan samuwar Aljannah da

Allah Madaukakin Sarki ya bamu labari cewa su an tanada su ne Sai yace akan Aljannah

An tanade ta ne ga masu taqawa

Ya ce akan Wuta

An tanade ta ne ga kafirai

An bamu labari cewa Allah Maxaukakin Sarki ya zaunar da Adam da matarsa Hauwa a Aljannah kafin su ci Bishiya kuma Allah ya bamu labari cewa kafirai za’a ke bijiro da su ga Wuta safe da maraice

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

‘’Na tsinkaye a cikin Aljannah sai nag a mafiya yawan ahalinta talakawa ne ,Na leqa Wuta kuma sai nag a mafiya yawan ahalinta mata ne

Hadisi

Ya gabata akan fitina da Azabar kabari

‘’Idan Dayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazaunin sa

Hadisi

Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce

‘’Ku sanyaya da yin Sallah saboda tsananin zafi yana daga numfashin Jahannama’’

Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce

Wuta ta kai kukanta ga Ubangijinta Maxaukakin Sarki tace ya Ubangiji na sashe na yana cin sashe sai Allah ya bata izinin yin numfashi sau biyu xaya a lokacin sanyi daya kuma a lokacin zafi shine mafi tsananin zafin da zaku ji lokacin zafi da kuma tsananin sanyin da zaku ji lokacin sanyi

Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace zazzabi yana daga numfashin Jahannama ku sanyaya shi da ruwa

Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce

‘’yayin da Allah Madaukakin Sarki ya halicci Ajannah da Wuta sai ya aiki Jibril zuwa ga Aljannah sai ya ce je ka kayi duba zuwa gare ta’’

Hadisi

An bijiro da su ga Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a inda yake zaune ranar da rana tayi kusufi kuma an bijiro masa dasu a daren Isra’I game da haka akwai Hadisai ingantattu da yawa da bazasu kirgu ba.

 Dalili kan samuwr Aljannah da wuta har Abada

Me ne ne dalili kan wanzuwar Aljannah da Wuta har abada ?

Allah Madaukakin Sarki ya ce a cikin Aljannah

Suna Madawwama a cikin ta ,wannan shi ne rabo babba

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma ba zasu zama masu fita daga cikinta ba

Allah Madaukakin Sarki ya ce akanta

Kyauta wacce bata yankewa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ba su yankewa kuma ba’a hana su

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai wannan,haqiqa azurtawarMu ce ,bata yankewa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai masu taqawa suna cikin matsayi amintacce

Zuwa fadin sa:

Ba su Dandanar mutuwa, a cikinsu ,face mutuwar farko

Allah Madaukakin Sarki ya bada labarin tanadarsu da rayuwa madawwamiya ga ahalinta da rashin yankewarta gare su da kuma rashin fitarsu daga cikin ta

Haka kuma Allah yana cewa game da Wuta

Sai dai hanyar Jahannama ,suna masu dawwama a cikinta har abada

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai Allah ya la’ani kafirai kuma Yayi musu tattalin wata Wuta mai kuna basu samun majibinci ,kuma ba zasu samu mataimaki

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wanda ya sabawa Allah da Manzon sa kuma ya qetare iyakokinsa zai shigar dashi Wuta ,yana madawwami a cikinta

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma ba zasu zama masu fita daga Wutar ba

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ba’a saukakar da ita (Azabar )daga gare su alhalin kuwa su a cikinta ,masu kasa Magana ne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ba zai karbi ransu ba ballantana su Mutu kuma bazai Saukake musu Azaba ba

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai shi wanda ya je wa Ubangijinsa yana mai laifi ,to lallai ne yana da Jahannamabaya mutuwa a cikinta kuma baya rayuwa

Da wasun waxannan daga Ayoyi.

Allah Madaukakin Sarki ya bamu labara a cikin waxannan ayoyin da misalansu cewa yan Wuta an halitta Wuta dominsu itama kuma an halittata dominsu zasu dawwama acikinta har abada Allah Ta’ala ya shafe fitarsu daga cikinta da faxinsa : kuma ba zasu zama masu fita daga cikinta bay a kuma shafe yankewarta daga gare su da faxinsa :Ba’a saukakar musu da Azabar ta ,Ya kore shafe karewar zamansu a cikinta da faxinsa :Ba za su mutu ba acikinta ba kuma zasu rayu ba

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Amma yan Wuta wadanda suka kasance sune ahalinta haqiqa sub a zasu mutu ba a cikinta kuma ba zasu rayu ba ‘’Hadisin

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :''Ida’’yan Aljannah suka tafi zuwa Aljannah ,yan Wuta kuma suka tafi zuwa ga Wuta sai a zo da mutuwa a sanyata a tsakanin Aljannah da Wuta sai a yanka ta sai mai kira ya yi kira yace: ‘’yak u yan Aljannah babu mutuwa ,yak u yan Wuta babu mutuwa sai hakan ya qarawa yan Aljannah farinciki kan farincikinsu ,sai kuma ya qarawa yan Wuta bakinciki kan bakincikinsu ‘’a wani lafazin kuma :kowa zai dawwama cikin abinda ya kasance a cikinsa

Acikin wata ruwayar sai Annabi tsira da aminci su qara tabbata a gare shi ya karanta:

Kuma kayi musu gargadi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al’amari alhalin kuwa suna a cikin vata ,kuma bas u yin Imani

Ya zo kuma a cikin Sahih acikin hadisai waxanda bamu ambace su ba

 Dalili kan cewa Muminai za su ga Ubangijinsu tsarki da xaukaka su tabbata gare shi a gidan lahira

Me ne ne dalili kan cewa Muminai zasu ga Ubangijinsu tsarki da Daukaka su tabbata gare shi a gidan lahira?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Wasu fuskokin a ranar nan masu annuri ne Suna Kallon Ubangijin ta

kuma Allah Madaukaki ya ce

Wadanda suka kyautata yi ,suna da abu mai kyau da kuma kari

Allah Madaukakin Sarki yace:

AAha Lallai cewa su ababan Shamaki ne ga barin ganin Ubangijinsu

Idan ya sanya shamaki tsakaninsa da maqiyanSa ba zai sanya tsakaninSa da masoyansa ba

Ya zo a cikin ingantattu guda biyu daga Jarir Bn Abdullah Allahyayarda da shi yace :Mun kasance muna zaune tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi sai yayi duba zuwa ga Wata daren goma sha huxu sai Yace: ‘’Haqiqa zaku ga Ubangijinku gani kamar yadda kuke ganin wannnan idan kun sami dama kuyi Sallah kafin fitowar Rana da kafin faduwarta ku aikata ‘’kamar yadda kuke ganin wannan ‘’yana nufin ai kamar yadda kuke ganin wannan Watan an yi kamanceceniyar gani da gani ba wai kan abinda ake gani da abin ganin ba ,kamar fadinsa a hadisin Allah yayi Magana da Wahayi ‘’Mala’iku sun yi duka da fukafukansu da fadinsa kamar sarqa ce ‘’wannan Kamanceceniya ce ta sauraro da sauraro ba ta abinda ake saurare ba da saurare, Allah ya xaukaka ya kamanta Zatinsa ko ya SiffarSa da wani abu da ya halitta ,Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya tsarkaka ya riqi wani abu a zancenSa ya kamanta Allah alhalin shi yafi kowacce halitta sanin Allah ,a cikin wani hadisin na Suhaiba cikin Muslim ‘’Sai a yaye musu hijabi ba ‘a basu wani abu ba mafi soyuwa a gare su sama da ganin Ubangijinsu Madaukakin Sarki ‘’sai ya karanta wannan ayar:

Wadan da suka kyautata suna da kyautaye da kuma kari

Awannan babin akwai hadisai masu yawa kuma ingantattu baxaxxu mun ambaci wasu a sharhin "Sullamul Wusoul‘’ hadisai arba’in da biyar daga Sahabbai fiye da talatin ,wanda ya mayar da wannan ya kafircewa Qur’ani da abinda Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya zo da shi ,yana daga cikin waxanda Allah Madaukakin Sarki yake fada akansu

A’aha ! Haqiqa ,lallai ne su daga Ubangijinsu ,a ranar nan waxanda ake shamakancewa ne

Muna roqon Allah afuwa da gafara ,ya kuma azurta mu da samun jin xaxin ganin fuskarsa

Ameen

 Dalilin Imani da Ceto Wa ye zai yi ceton ga su wa ceton zai kasance kuma da yaushe Ceton zai kasance?

Me ne ne dalilin imani da Ceto Su wane ne za su yi Ceton ga su wa Ceton zai kasance kuma yaushe Ceton zai kasance

Lallai Allah Maxaukakin Sarki yayi maganar Ceto a wurare da dama a cikin Littafinsa ,Allah ya bamu labari da cewa tana qarqashin mulkinSa shin mamallakinta babu wani da yake da iko da ita sai shi.Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

‘’Kace: ceto gabaxaya ga Allah yake

To amma yaushe zata kasance ?Allah Maxaukakin Sarki ya bamu labari da cewa ba zata kasance ba sai da izininSa kamar yadda Allah yace

Wa ne ne wanda yake iya yin ceto a warinSa ,in bada da Izininsa?

Babu wani maceci face a bayan IzininSa

Kuma da akwai daga cikin Mala’iku da yawa a cikin sammai cetonsu baya wadatar da komai face bayan Allah ya yi izni (da shi )ga wanda yake so ,kuma ya yarda

Kuma wani ceto baya amfani a wurinSa face fag a wanda Ya yi izni gare shi

Amma ga wadanda zata kasance shine kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya bamu labari cewa ba zata kasance ba sai bayan yayi izni Ya kuma bamu labara iznin baya kasantuwa sai ga masoyanSa yardaddunSa ga labarin kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki Ya faxa:

Ba su Magana sai wanda Allah Ya yi masa izni ,kuma ya fadi abinda yake dai dai.

Kuma ya ce:

Ba su mallakar ceto face wanda ya riqi alqawari a wurin mai rahama

Amma ga wanda zata kasance an bamu labari cewa babu wanda za’a ceta sai wanda Ubangiji ya yarda dashi kamar yadda Ya fada

Kuma basu yin ceto face ga wanda Ya yarda

A yinin nan ceto baya yin amfani face wanda Mai rahama Ya yi masa izini kuma Ya yarda dashi da Magana

Kuma Allah Subhanahu wa ta’ala ba Ya yarda sai ga ma’abota tauhidi da Ikhlasi .amma waxanda suke sabanin haka Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa:

Kuma babu wani mai ceto da za’a yiwa Da’a( ga cetonsu)

Allah Madaukakin Sarki yace akanta

Saboda haka ba mu da wadansu maceta.Kuma bamu da aboki,masoyi.

Allah Madaukakin Sarki yace akanta

Saboda haka ceton masu ceto ba zai amfane su ba

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya bamu labari cewa haqiqa an bashi ceto sai ya bamu labari da cewa zai zo zai yi sujuda a qarqashi Al’arshi sai ya godewa Ubabgijinsa da godiyar da shi kadai ne Ya santa ba zai fara da ceto daga farko ba har sai an ce da shi ‘’Daga kanka Ka fada Yana jin ka Ka kuma tambaya za’a baka Ka roqi ceto za’a baKa ceton ‘’Hadisin.Sai aka bada labarin cewa ba zai ceci gabakidayan masu sabo ba daga ma’abota tauhidi a loqaci daya ba sai dai Yace :’’An sanYa min wata iyaka za’a sanya su a Aljannah ‘’sai Ya koma Yayi sujuda kamar haka sai a sanya masa iyaka har zuwa qarshen hadisin.Sai Abu Huraira yace da shi Allah ya qara yarda dashi wane ne mafi farincikin mutane da cetonKa ?Sai Yace : ’’wanda duk yace :La’ilaha illallahu yana mai ikhlasi har cikin zuciyarsa

 Nau’ikan ceto da mafi girmanta

Nawa ne nau’ikan ceto kuma wacce ce mafi girmanta ?

Mafi girmanta Ceto ranar tashin Alqiyama ceto mai girma a filin Alqiyama Allah Maxaukakin Sarki zai zo Ya yi hukunci a tsakanin bayinsa, ceto kawai ya kevanta ne kawi ga Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi itace muqami abin godewa da Allah Maxaukakin Sarki Ya yi masa alqawari kamar yadda Allah Ya faxa:

Akwai tsammanin UbangijinKa ya tashe ka a matsayi godadde

a yayin da mutane suka shiga cikin takura a wurin tsayuwa , kuma tsayuwa ta yi tsayi da yawa, Damuwa ta tsananta, Gumi ya shanye su, sai su nemi ceto kan Allah ya rarrabe tsakanin su , sai su jewa annabi Adamu sa`annan Nuhu sa`annan Ibrahim sa`annan musa sa`annan Isa dan Maryam dukkanin su na cewa: Ta kaina na ke. Har su tuke ga annabin mu Muhammad mai tsira da aminci take sai ya ce: Ni nake da shi kamar yadda ya zo a bayyane cikin sahihai guda biyu (Bukhari da Muslim) da wasun su

Na biyu :wajen buxe qofar Aljannah ,farkon wanda zai fara buxe qofar Aljannah shine Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi farkon waxanda za su fara shiga Aljannah daga al’umatai su ne Al’ummarSa

Na Uku :ceton waxansu mutane an yi musu umarnin shiga Wuta sai ace kar su shige ta

Na huxu :Waxanda suka shiga Wuta daga ma’abota tauhidi su fito daga cikinta sai a fito da su sun koma gawayi sai a tsoma su cikin kogin rayuwa sai jikinsu ya tsiro kamar yadda qwaya take tsirowa cikin mafi kyawun yanayi.

Na biyar: ceto wajen xaukaka darajar waxansu mutane daga yan Aljannah ,amma waxannan ukun basu kevanta ba kawi ga Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi sai ma shine zai fara ta bayanshi kuma sai sauran Annabawan sai Mala’iku da Waliyyai sai mutane suma za su yi ceto ,sai Allah Mxaukakin Sarki da rahamarsa Ya fitar da mutane daga Wuta ba tare da ceto ba Ya shigar dasu Aljannah yawansu ba wanda zai iya irgawa sai Allah

Na shida :ceto wajen sauqaqa azabar waxansu kafirai wannan kaxai ta kevanta ne ga Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ga Baffansa Abi Xalib kamar yadda ya zo a Muslim da wasun sa Wutar Jahannama ba zata gushe ana jefa mat aba tana cewa akwai qari har sai Allah Maxaukakin Sarki Ya sanya QafafunSa ya danne ta sashenta ya haxu da sashe sai tace ya isa ya isa da girman izzarKa sai wasu mutane daga waxanda ba zasu shiga Aljannah bas u shige ta akan wannan akwai nassoshi da ba za su irgu ba wanda ya so ya sansu zai same su a Alqur’ani da Sunnah.

 Tasirin aiki wajen shiga Aljannah da tsira daga Wuta

Shin wani zai shiga Aljannah ko ya tsira daga Wuta saboda aikinsa?

Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Ku kusato ku yi aiki haqiqa ba bu xaya daga cikinku da zai tsira saboda aikinsa sai suka ce ya Ma’aikin Allah har kai ma yace har Ni ma face sai dai Allah Ya lulluve ni da rahama daga gare shi da falalarsa.Acikin wata ruwayar: ’’Ku kusato ina yi muku bushara cewa babu wani da aikinsa zai shigar da shi Aljannah sai suka ce har kai Ya Ma’aikin Allah ?sai Yace har ni sai dai in Allah Ya lullube ni da rahamarsa kuma ku sani mafi soyuwar aiki a wajen Allah shine wanda aka dawwama yinsa komai qanqantarsa.

 Aiyuka na qwarai sababi ne na shiga Aljannah

Me ne ne hadi tsakanin wannan Hadisin da fadin Allah Madaukakin Sarki :’’kuma aka kira su ,da cewa :Waccan Aljannah an gadar da ita gare ku saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa ?

Alhamdulillahi babu cin karo da juna a tsakanin su, domin harafin (B) da yake tabbace cikin ayar harafi ne na sababi; Saboda su ayyuka na kwarai sababi ne na shiga aljanna baza a sami aljanna ba sai da su (ayyuka na kwarai) ta yadda abin da samuwar sa ke da sababi to dole sai an samar da wannan sababin, abin korewa a cikin Hadisin ita ce harafin (B) da take nuna kima, domin da ace bawa zai rayu tsawon duniya gaba dayan ta yana azumi da rana yana kuma tsaiwa da daddare yana nesantar sabo baki daya to da gabaki dayan aikin na shi ba zai fanshi daya bisa dubbai na mafi kan-kantar ni`imar Allah akan shi ba wadda take ta a fili da boye, to ta yaya (ayyukan) nashi za su zama sun kai kimar da za`a shigar da shi aljanna

Ka gafarta mana ,kuma kayi mana ,kuma kaine mafi alherin masu tausayi

 Dalilin Imani da qaddara mai kyau

Dalilin Imani da qaddara a dunkule

Allah ya yi masa Rahama

Kuma umarnin Allah ya kasance abin qaddarawa tabbatacce

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma domin Allah Ya hukunta abinda yake ya kasance abin aikatawa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma umarnin Allah ya kasance abin qaddarawa tabbatacce

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma abinda ya same ku ranar haxuwar jama’a biyu,to da izinin Allah ne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma abinda ya same ku ranar haxuwar jama’a biyu,to da izinin Allah ne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Waxanda idan wata musiba ta same su sai su ce: ’’lallai ne mu ga Allah muke ,kuma lallai ne mu zuwa gare Shi muke komawa ‘’.Waxannan akwai albarka a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama, kuma waxannan sune shiryayyu.

Ya zo a cikin hadisin Jibril ‘’Ka yi Imani da qaddara alherinta da kuma sharrinta ‘’

Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Kuma ka sani duk abinda ya same to dama can bai kasance zai kuvuce maka ba,abinda kuma ya kuvuce maka dama can bai kasance zai same k aba ‘’

Manzon Allah yace: ’’idan wani abu ya same ka kar kace da na aikata kaza da kaza da kaza ne zai faru sai dai kace: haka Allah ya qaddara abinda ya so shi yake aikatawa’’

Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Kowanne abu an qaddara shine har rauni da nuna jin dadi ‘’da wasun haka daga hadisai

 Matakan Imani da qaddara

Nawa ne matakan Imani da qaddara?

Matakan Imani da qaddara guda hudu ne:

Mataki na farko :Yin Imani da cewa ilimin Allah ya game dukkan komai wanda wani ma’aunin Zarra ba zai yi nisa ba daga gare shi acikin sama ko acikin qasa,kuma Allah Madaukakin Sarki Ya san gabakidayan halittarsa tun gabanin Ya halicce su ,Ya kuma san Arziqinsu da ajalinsu ,da maganganunsu,da aiyukansu ,da bakixayan motsinsu da zamansu ,da sirrikansu ,da abin da yake bayyane ,kuma su waye daga cikinsu yan Aljannah kuma su waye yan wuta daga cikinsu .

Mataki na biyu :Imani da rubutu cewa Allah ya rubuta gabakidayan abinda iliminSa ya gabata dama samamme ne ,daga cikin abinda ya kunshi wannan Imani da Allo da Alqalami .

Mataki na uku:Imani da cewa abinda ya so shi yake faruwa wanda ya shiga dukkan komai ,da qudurarsa da ta game dukkan komai ,abubuwa ne guda biyu ababan lazimta ta vangaren abinda ya kasance da wanda zai kasance ,babu lazimta kuma tsakaninsu kan abinda bai kasance ba ko kuma bai zamo daga kasantattu ba ,abinda Allah Maxaukakin Sarki Ya so to, kasantacce ne da qudirarsa babu wani haufi ,kuma abind Allah bai so b aba zai kasance ba saboda rashin sonSa ,ba wai saboda rashin ikon Allah Maxaukakin Sarki akanshi ba ,Allah ya xaukaka ga hakan .

Kuma Allah bai kasance wani abu na iya rinjayarSa ba acikin Sammai da kuma qasa ,lallai shi ne Ya kasance Masani,Mai ikon yi.

Mataki na hudu Imani da cewa Alkah Madaukakin Sarki shine mahaliccin dukkan komai kuma cewa babu wata zarra a sama ko a qasa ko a cikin abinda ke tsakaninsu face ta kasance Alkah ne Mahaliccinta,kuma Mahaliccin motsinta da zamanta Tsarki ya tabbata gare shi babu wani Mahalicci bayan shi babu wani Ubangiji kamarSa

Me ne ne dalili kan mataki na farko wanda shine Imani da ilimi?

AllahMadaukakin Sarki ya ce:

Shi ne Allah ,wanda babu wani abin bautawa face Shi,Masanin fake da bayyane

kuma Allah Madaukaki ya ce

Haqiqa Ya kewaye dukkan komai da sani

kuma Allah Madaukaki ya ce

Masanin gaibi gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare shi a cikin sammai kuma bata nisanta a cikin qasa kuma babu mafi girma face yana a cikin Littafi bayyananne

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma mabudan gaibu suna gurinsa ba wanda ya sansu sai daishi…

kuma Allah Madaukaki ya ce

Allah shi ne mafi sanin inda Yake ajiye manzancinSa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai ne UbangijinKa shine mafi sani ga wanda yake bacewa daga hanyarSa kuma shine mafi sani ga masu shiryuwa.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Shin Allah bai zamo Mafi sani ba ga masu godiya

Shin Allah bai zamo Mafi sani ba daga abinda yake cikin zukatan talikai

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma aloqacin da UbangijinKa Ya ce ga mala’iku ‘’lallai ne ,Ni Mai sanya wani halifa ne a cikin qasa ‘’suka ce :’’ashe zaka sanya a cikinta ,wanda zai yi varna a cikinta ,alhalin mu muna yi maka tasbihi tare da gode maka ,kuma muna tsarkakewa gareka ‘’yace :’’lallai ne Ni Na san abinda baku sani ba

kuma Allah Madaukaki ya ce

Akwai fatar cewa ku qi wani abu ,alhalin shine mafi alheri a gare ku ,kuma akwai fatar cewa ku so wani abu ,kuma shine mafi sharri a gare ku,kuma Allah ne Yake sani ,kuma ku baku sani ba

Ya zo a cikin Sahih wani mutum yace :Ya Manzon Allah shin shin za’a iya sanin yan Aljannah daga yan Wuta ?sai Yace na’am .sai Yace akan me masu aiki suke yin aiki ?sai yace :’’kowa yana aiki ne akan abinda aka halitta shi ko aka hore masa’’

Akanshi aka tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi kan yayan mushirikai sai yace :’’Allah shine Mafi sanin abinda suka kasance suna aikatawa

Yazo a cikin Muslim Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa ‘’Lallai Allah ya halittawa Aljannah ahalinta an haliccesu domin ta tun suna tsatson iyayensu ,kuma an halittawa Wuta ahalinta an halicce sune dominta tun suna tsatson iyayensu"

Akan shi dai Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace:cewa mutum zai yi aiki aiki irin na yan Aljannah abinda ya bayyana ga mutane amma kuma yana daga cikin yan wuta ,wani mutum kuma zai yi aiki aiki irin nay an Wuta daga abinda ya bayyana ga mutane amma kuma yana cikin yan Aljannah

Akan hakan kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :Babu wata rai daga cikinku face Allah Maxaukakin Sarki ya san mazauninta a Aljannah ko a Wuta ‘’sai suka ce:ya Ma’aikin Allah ba sai mun yi aiki ba sai mu dogara,sai yace ‘’ku yi aiki dukkanin komai mai sauqi ne kan abinda aka halitta gare shi ‘’sannan ya karanta:

To,amma wanda ya yi kyauta ,kuma ya yi taqawa,kuma ya gasgata kaima mai kyawu.To,za Mu sauqaqe masahar ya kai ga sauqi.

Da wasun waxannan daga Hadisai.

Me ne ne dalili da mataki na biyu shine Imani da rubutun qaddarori ?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Kuma kowanne abu Mun qididdige shi a cikin babban Littafi Mabayyani.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai wancan yana cikin Littafi

Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa acikin qarar Musa da Fir’auna:

Yace:’’To mene ne halin qarnonin farko? sai Yace :’’saninsu yana a wurin Ubabgijina ,Ubangijina ba Ya vacewa kuma ba Ya mantuwa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wata mace ba ta yin ciki,kuma bata haihuwa ,face da saninSa ,kuma ba za’a rayar da wanda ake rayarwa ba,kuma ba za’a rage tsawon ransa ba face yana a cikin Littafi .Lallai wancan mai sauqi ne ga Allah.

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce: ’’Babu wata rai da take numfashi face Allah Maxaukakin Sarki Ya rubuta wurinta a Wuta ko a Aljannah in ko bah aka ba to an rubuta ita xin yar Wuta ce ko yar Aljannah ‘’Muslim ne ya rawaito,kuma dai kan hakan Suraqa Bn Malik ya ce :ya Manzon Allah Ka bayyana mana addininmu kamar yanzu aka halicce mu, me ne ne aikin yau a kuma kan me Alqalami zai bushe a kan me qaddarori za su gudana ko kuma akan me zamu fuskanto ?sai Ya ce: ’’ku yi aiki gabaki xayan komai mai sauqi ne a wata ruwayar kowanne mai aiki abin sauqaqawa ne ga aikinsa ‘’da wasun haka daga hadisai

 Abinda ke shiga cikin matakin rubuta qaddarori

Nawa ne yake shiga wannan matakin na rubuta qaddarori ?

Abubuwa biyar ne suke shiga wannan matakin kuma dukkaninsu suna komawa ne zuwa ga ilimi :

Qaddarawa ta farko :Rubuta haka tun gabanin halittar sama da qasa da shekara dubu hamsin ,a loqacin da Allah Ya halicci Alqalami ,wannan shine qaddarawa ta farko.

Na biyu :qaddarawa ta shekaru ,loqacin da aka dauki alqawari,

Shin ba Ni ne Ubangijinku ba ?

Na uku :qaddarawar shekaru kuma dai a yayin halittar gudan Jini a cikin mahaifa.

Na hudu: qaddarawa na shekara a Lailatul qadr

Na biyar :qaddarawa ta rana ,shine aiwatar da kowanne daga cikinsu a wurinsa

 Dalilin qaddarawa ta Azal

Dalilin qaddarawa ta Azal

Me ne ne dalilin qaddarawa tun Azal?

Wata masifa ba za ta auku ba a cikin qasa ko a rayukanku face tana a cikin Littafi a gabanin Mu halitta ta

Ya zo kuma a cikin Sahih Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce :Allah Ya rubuta qaddarorin abin halitta tun gabanin ya halicci sammai da qasa da shekara dubu hamsin,Wanda Al’arshin Ya ke kan ruwa Ya ce:

Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’ Haqiqa Abinda Allah Ya fara halittawa shine Alqalami sai Ya ce da shi :Rubuta sai Ya ce Ubangiji me zan rubuta? sai Ya ce :ka rubuta qaddarorin dukkanin komai har zuwa ranar tashin Alqiyama ‘’Hadisin Yana cikin Sunan

Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’Ya Aba Huraira Alqalami ya bushe ga duk wani abin halitta ‘’Hadisin yana cikin Bukhari da wasun shi da yawa.

 Dalilin qaddarawar shekaru ranar alqawari

Me ne ne dalilin qaddarawar shekaru ranar alqawari?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Kuma a loqacin da Ubangijinka Ya karvi (alqawari) daga Diyan Adam daga bayinsa a zuriyarsu ,kuma Ya shaidar da su akan rayukansu (Ya ce):shin ba Ni ne Ubangijinku ba? suka ce: Na’am !Mun yi shaida

Ishaq Dan Rahawaihi ya rawaito cewa wani mutum ya ce :Ya Manzon Allah ‘’shin aiyuka za’a fara su ko kuma hukunci ya rigaye su ?sai Ya ce: ’’haqiqa Allah Maxaukakin Sarki loqacin da ya fitar d zurriyya Adam daga bayansa Ya shaidar da su akan rayukansu sai Ya ce: wadan nan yan Aljannah ne wadannan kuma yan Wuta ne ,yan Aljannah za’a yassare musu alyukan yan Aljannah m,yan Wuta kuma za’a yassare musu aiyukan yan Wuta"

Ya zo a cikin Muwadda cewa Umar Dan Khattabi Allah ya yarda da shi an tambaye shi kawannan ayar

Kuma a loqacin da UbangijinKa Ya karvi (alqawari )daga xiyan Adam ,daga bayinka ,a zurriyarsu kuma Ya shaidar da su akan rayukansu ,(Ya ce ):’’shin ba Ni ne Ubangijinku ba ?’’su k ace :Na’am !Mun yi shaida !’’(ya ce ):kada ku ce a Ranar tashin Alqiyama :lallai ne mu daga wannan gafalallu ne

Sai Umar dan khaddabi ya ce: na ji manzon Allah mai tsira da aminci ana tambayar shi gameda ita (wannan aya) sai manzon Allah mai tsira da Aminci ya ce: “Lallai Allah wanda sunan sa ya yi albarka kuma ya daukaka ya halicci annabi Adamu sai ya shafi bayan sa sai zuri`a suka fito daga gareshi, sai ya ce: Na halicci wadannan saboda wuta, kuma za su rika aiki irin aikin `yan wuta” Hadisin da tsawon sa. Ya zo cikin (littafin) Tirmizi daga Hadisin Abdullahi dan amru Allah ya kara yarda da su (su biyun) ya ce: Manzon Allah mai tsira da aminci ya fito mana a hannun sa akwai littafi guda biyu sai yace: shin kun san wadannan littafai guda biyu na menene? Sai muka ce: a`a yaa Manzon Allah sai dai idan ka bamu labari, sai ya fada gameda na hannun daman sa: wannan littafi ne daga ubangijin halitta baki daya, a cikin sa akwai sunayen `yan aljanna da sinayen iyayen su da kabilun su. Sa`annan ya tattara su har karshen su ba za`a kara wani a cikin su ba, ba za`a kuma rage wani daga cikin su ba har abada. Sa`annan ya fada ga wanda yake hannun hagun sa: “wannan littafi ne daga ubangijin halitta baki daya, a cikin sa akwai

 Dalili kan qaddarawar rayuwa wanda yake tun farkon halittar gudan Jini

Me ne ne dalilin qaddarawar rayuwa tun farkon halittar gudan Jini?

Allah ya yi masa Rahama

Shi ne Ya fi saniga abinda keg are ku a loqacin da Ya qaga halittarku daga qasa ,kuma a loqacin da kuke tayuna a cikin cikin uwayenku.Saboda haka kada ku tsarkake kawunanku,Shi ne Mafi sani ga wanda ya yi taqawa

Ya zo a cikin Sahihul Bukhari da Muslim cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: ’’Cewa dayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa har kwana arba’in yana Maniyyi sannan ya zama gudan jinni misalign haka, sannan ya zama gudan tsoka misalign haka sai a aiko masa da Mala’ika sai ya busa masa rai,sai a umarce shi da kalmomi guda hudu da arziqinsa, da Ajalinsa,da aikinsa,kuma shi Dan Wuta ne ko Dan Aljannah,Na rantse da wanda babu wani Allah bayan shi,haqiqa xayanku zai yi aiki aiki irin na yan Aljannah har sai ya kasance tsakaninshi da tsakaninta sai dai zara’I sai Littafi ya rigaye shi sai ya yi aiki aiki irin nay an Wuta sai ya shige ta,cewa Dayanku zai yi aiki aiki irin nay an Wuta har asi ya kasance tsakaninshi da tsakaninta sai dai zira’I sai Littafi ya rigaye shi sai yayi aiki aiki irin nay an Aljannah sai ya shige ta

Akwai ruwayoyi da yaw aba wannan ba daga Jama’a ta Sahabbai da lafuzza daban – daban amma ma’anar daya ce.

 Dalilin qaddarawa na shekara a kan Lailatul qadri

Me ne ne dalilin qaddarawar shekare kan Lilatul qadri?

Allah Madaukakin Sarki ya ce: A cikinsa (shi daren )ake rarrabe kowane umarni bayyananne.Umarni ne daga wurin Mu Ibn Abbas Allah ya qara yarda da shi ya ce :Ana rubutawa daga Ummul Kitabi a daren Lailatul qadri abinda zai faru a shekara na daga mutuwa da rayuwa da arziqi da ruwa hatta Alhazai za’a ce Wane da Wane za su yi aikin Hajji,haka Alhassan xan Jubair da Muqatilda Abu Abdurrahman As Salmi da wasunsu.

 Dalilin qaddarawar Rana

Me ne ne dalili kan qaddarawar Rana?

Allah Madaukaki ya ce

Akullum Allah na a cikin wani sha’ani

Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gresu ya fada a cikin sahihul hakim: “Lallai yana daga cikin abin da Allah madaukaki ya halitta allo abin kiyayewa (ya halicce shi daga) farin lu`u lu`I, gefunan sa guda biyu daga jan yakutu, alkalamin sa haske ne, rubutun sa ma haske ne ana duba shi a kullum duba dari uku da sittin ko sau dari uku da sittin, a kowane duba daga cikin duban da ake yi masa; ana yin (sabuwar) halitta, ana azurtawa, ana rayarwa ana matarwa, ana daukakawa, ana kaskantarwa, yana aikata abin da ya so. Wannan shi ne fadin Allah madaukaki:

Akullum Allah na a cikin wani sha’ani

Dukkanin wadannan qaddarorin kamar rabo ne na qaddarorin da suka gabata,shine Azal wanda Allah Madaukakin Sarki Ya umarci Alqalami a loqacin da Ya halicce shi da ya yi rubutu a Lauhul Mahfuz,da wannan ne Ibn Umar da Ibn Abbas Allah Ya qara yarda da suka fassara fadin Allah Ta’ala

Lallai Mu,Mun kasance Muna sanya rubutun tamkar abin da kuka kasance kuna aikatawa

Dukkanin wannan tushensa yana daga ilimin Alllah waanda siffarsa ce Maxaukakin Sarki

 Abinda qaddarorin na azaba dana jin dadi suka qunsa

Me ne ne abinda qaddarori suka qunsa na daga azaba da jin daxi?

Xaukacin Littattafai da suka zo daga sama da Sunnar Annabi sun hadu kan cewa qaddara ta rigaya kuma hakan ba zai hana aiki ba kuma baya wajaba dogaro kan hakan,sai dai yana wajabta jajircewa da qoqari da kwadaitarwa kan aiki na gari ,da wannan ne loqacin da Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya bawa Sahabbansa labari cewa qaddara ta rigaya sannan Alqalami ya bushe da ita sai sashensu yace :’’Shin ba zamu dogara akan Littafin mu bar aikin ?sai Ya ce :’’Ku yi aiki komai mai sauqi ne’’sai Ya karanta:

To,amma wanda ya yi kyauta,kuma ya yi taqawa

Allah mai tsarki da daukaka ya kaddara kaddarori ya kuma tanadar da sababan su, kuma shi gwani ne da abin da ya kafa na daga sababai a cikin wannan rayuwar da kuma makoma, Hakika kuma ya saukakewa kowa daga halittar sa ga abin da aka halitta saboda shi a cikin duniya da kuma lahira, shi an yi tanadi gareshi kuma an saukake a gareshi. Idan bawa ya san cewa duk abin da ya ke nema a lahira yana daure ne da sabubban da za su kaishi ga samun wannan masalahar ta shi to zai kasance mafi tsananin dagewa a cikin aikata ta da tsayuwa da ita,mafi girma daga wannan a cikin bin sabubban rayuwar sa da masalahohin sa na duniya. Lallai tabbas ya fahimci wannan dukkan fahimta wanda ya fadi wannan daga cikin sahabbai a lokacin da ya ji hadisan da suke (Magana) kan kaddara, ya ce: Ban kasance mafi tsananin dagewa (akan yin aiyuka na gari ba) kamar yanzu. Annabi mai tsira da aminci ya fada: “ka yi kwadayi bisa abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah kuma kada ka gajiya”. Manzon Aallah mai tsira da aminci ya kuma cewa yayin da aka cemasa: Ya kake ganin magungunan da muke yin magani da su da kuma tawaida da muke yin tofin ta shin tana juyar da kaddarar Allah? Sai ya ce: “Ita ma tana cikin kaddarar Allah” yana nufin cewa Allah madaukaki ya kaddara alheri da sharri da kuma sabubban kowanne daga cikin su

 Dalilin mataki na uku shine Imani da Mashi’ar Allah Ta’ala

Me ne ne dalili kan mataki na uku wato Imani da Mashi’ar Allah Ta’ala ?

Allah Madaukakin Sarki ya ce

kuma ba za ku so ba face sai Allah ya so

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma kada lallai ka ce ga wani abu,lallai ni mai aikatawa ga wancan gobe sai Allah ya so

kuma Allah Madaukaki ya ce

Wanda Allah Ya so Yana vatar da shi ,kuma wanda Ya so zai sanya shi kan hanya madaidaiciya

kuma Allah Madaukaki ya ce

Da Ubangijinka Ya so da dukkannin waxanda ke doron qasa sun yi Imani

Kuma da Allah Ya so da ba za su yaqi juna ba

Kuma da Allah Ya so da Ya ci nasara a kansu

kuma Allah Madaukaki ya ce

Mai aikata abinda Ya so ne

Umarninsavidan Ya yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai,’’Ka kasance ‘’ sai Yana kasancewa

MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi,Mu ce masa,’’Ka kasance ‘’sai yana kasancewa

Domin haka wanda Allah Ya yi nufin Ya shiryar da shi sai Ya buxa qirjinsa domin Musulunci,kuma wanda Ya yi nufin vatar da shi sai Ya sanya qirjinsa mai qunci matsattse

Da wasun haka daga ayoyi waxanda ba za su qididdugu ba

Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’Zuciyoyin bayi suna tsakanin yan yatsu guda biyu daga yan yatsun Mai Rahama kamar zuciya guda xaya Yana juya su yadda Ya so ‘’

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce a cikin baccinsa a wani wadi ‘’Lallai Allah Maxaukakin Sarki Ya na karvar rayukanku a loqacin da Ya so Ya kuma dawo muku da su a loqacin da Ya so’’

Yana cewa :’ku yi ceto za ku sami sakamako Allah Ya na hukunci ne akan harshen Manzonsa da abinda Ya so’’

Ya na kuma cewa ‘’kada ku ce haka Allah Ya so sannan kuma haka wane ya so :sai dai ku ce haka Allah Ya so shi kadai’’

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’Wanda Allah Ya so sai Ya fahimtar da shi a Addini

‘’Ian Allah Ya so wata Al’ummah da rahama sai Ya dauki ran Annabinta gabaninta ,idan kuma Ya so Ya hallakar da itaSai Ya azabtar da ita alhalin Annabinta Yana raye"

Da wasun wadan nan daga hadisai da aka ambaci Mashi’ar Allah da ikonsa wadanda ba za su irgu ba

Amsa ga wanda Ya ce ta ya ya Allah zai so abinda bai yarda da shi ba kuma ba Ya sonsa

Allah Maxaukakin Sarki ya bamu labari cikin Littafinsa ta harshen Manzonsa daga abinda ya sanar damu daga siffofinsa cewa Yana son masu kyautatawa da masu taqawa da masu haquri,Ya kuma yarda da waxanda suka yi Imani suka kuma yi aiki nagari,ba kuma Ya son kafirai ko azzalumai,kuma bai yarda da kafirci ba daga bayinsa,kuma ba Ya son varna.

Tare da cewa duka wannan sun kasance da nufin Allah da ikonSa,lallai cewa da bai so ba hakan ba zata kasance ba,domin duk wani abinda ba Ya so baya kasancewa a cikin mulkinsa,me ne ne amsa ga wanda ya ce Ta ya ya zai so abinda bai yarda dashi ba kuma baya son shi ?

Ka sani cewa Son Allah ya zo a nassoshi da ma’ana biyu :So na kasancewar abu da ikonSa da qudurarSa,shine mashi’arSa,babu wani rabewa tsakaninta da soyayya da yarda,sai dai kafirci da Imani duk suna shigarta,da kuma biyayya da savawa, da yardajje da abin so,da abin qi da kishiyarSa wannan Iradar babu wani da ya fita daga cikinta kamar faxinSa Maxukakin Sarki

Domin haka wanda Allah Ya yi nufin Ya shiryar da shi sai Ya buxa qirjinsa domin Musulunci,kuma wanda Ya yi nufin Batar da shi sai Ya sanya qirjinsa mai qunci matsattse

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa,to ba zaka mallaka masa komai ba,daga Allah.wadannan ne waxanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukatansu ba.

Nufi na addini na shari’a, ya kevanta ne kawai kan abinda Allah Yak e so Ya kuma yarda da shi ,daga cikin abinda ta qunsa akai umarnin Allah da kuma hani ga bayinSa kamar faxin Allah Madaukakin Sarki

Allah Yana nufin sauqi gare ku,kuma baya nufin tsanani gare ku

Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:

Allah Ya yi nufin Ya bayyana muku\,kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suke a gabaninku kuma Ya karvi tubarku.Allah Masani ne Mai Hikima.

Wannan nufin yana haifar da bin shi sai ga wanda nufi na kasantuwa ya rigaye shi.

Irada kauniyya da shar’iyya suna haxuwa acikin hakkin Mumini mai biyayya,sannan Irada kauniyya ita kaxai tana zamowa a hakkin bawa mai savo,Allah Maxaukakin Sarki ya kira bayinsa xaukacinsu zuwa ga abubuwan da Ya yarda dasu da shiryawa dan amsa masa amma wanxanda Ya so daga cikinsu ,kamar yadda Ya ke faxa:

Kuma Allah Yana kira zuwa ga gidan aminci,kuma Yana shiryar da wanda Ya ke so zuwa ga tafarki madaidaici

Allah Maxaukakin Sarki Ya game kira ,amma Ya kevance shiriya ga wanda Ya so :

Lallai ne UbangijinKa shine mafi sani ga wanda yake bacewa daga hanyarSa kuma shine mafi sani ga masu shiryuwa.

 Dalili kan mataki na huxu shine Imani da qaddara itace mataki na halitta

Dalili kan mataki na huxu shine Imani da qaddara itace mataki na halitta

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Allah ne ne Mai halitta dukkan komai,kuma Shi ne wakili akan komai

kuma Allah Madaukaki ya ce

Shin akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da qasa?

kuma Allah Madaukaki ya ce

Wannan shi ne halittar Allah. To ku nuna mini, mene ne wadannan da ba shi ba suka halitta?

kuma Allah Madaukaki ya ce

Allah ne wanda ya halicce ku, sa’an nan ya arzurta ku, sa’an nan ya matar da ku, sa’an nan ya rayar da ku. Ashe daga cikin abubuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga wadannan abubuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma ya daukaka bisa ga abin da suke yi na shika

kuma Allah Madaukaki ya ce

Allah shine wanda Ya halicce ku da abinda kuke aikatawa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Da rai da abinda ya daidaita shi.Sa’annan ya sanar da shi fajircinsa da

kuma Allah Madaukaki ya ce

Wanda Allah Ya shiryar,to shi ne Mai shiryuwa,kuma wanda Y avatar,to waxannan su ne masu hasara

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma amma Allah Ya soyar muku da Imani a gare ku,kuma Ya qawata shi a cikin zukatanku,kuma Ya qyamatar da kafirci da fasiqanci da savo

Yazo a cikin Bukhari halittr aiyukan bayi daga Huzaifa ‘’Lallai Allah Yana sana’anta dukkanin mai sana’a da abin sana’arsa ‘’Annabi tsira da Amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: ’’Ya Allah Ka bawa rai na tsoronta kuma ka tsarkake ta Kai ne Mafi alherin Mai tsarkake ta Kaine masoyinta kuma shugabanta ‘’da wasun waxannan daga Hadisai

Ma’anar faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ‘’Alkhairi dukkaninsa Yana hannunKa sharri kuma baya daga gare Ka

Me ne ne ma’anar faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ‘’Alkhairi dukkanin shi yana hannunKa,sharri kuma baya daga gare Ka ‘’ tare da cewa Allah Maxaukakin Sarki shine mahaliccin komai ?

Ma’anar wannanshine aiyukan Allah Maxaukakin Sarki gabadayan su alkhairi ne kebantacce ta vangaren siffanta su da Shi da jingina su gare shi babu sharri acikinsu ,saboda Allah Madaukakin Sarki Mai hukunci ne mai adalci Yana halitta abubuwa a bigiren da ya dace da su kamar yadda suke sannannu a wajenSA Madaukakin Sarki,duk wani abu da yazo wa bawa na sharri,to yana vangaren jinginawa bawa kan abinda dama an halitta shi gare shi na daga ababan hallakarwa wannan kuwa yana daga abinda hannayensa suka aikata sakamako ne wanda ya dace da aiyukansu,kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki Ya ce:

Kuma abinda ya same kun a wata masifa,to,game da abinda hannayenku suka sana’anta ne,kuma( Allah )Yan a yafewar (wadansu laifuffuka )masu yawa.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma ba Mu zalunce su ba,sai dai sun kasance sune Azzalimai

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lallai ne Allah ba Ya zaluntar mutane da kome,amma mutanen ne ke zaluntar kansu

 Shin bayi suna da mashi’a da qudura akan aiyukansu da aka jingina su a gare su

Shin bayi suna da mashi’a da qadura akan aiyukansu da aks jingina su gare su?

Na’am bayi suna da iko kan aiyukansu,sanan suna mashi’a da dama,a haqiqa aiyukansu an jingina su ne gare su, an yi zaton su zamo masu daukar nauyin, da su za su samu sakamako ko kuma ayi musu uquba,Allah bai dora musu ba sai don Ya san za su iya xauka, wannan duka ya zo musu a Littafi da kuma Sunnah an siffanta su da shi sai duk da haka ba za su iya qaddara komai ba face abinda Allah Ya qaddara mu su, ba za su so wani abu ba face abinda Allah Ya so, ba za su aikata ba face Ya sanya su masu yin aikin kamar yadda ya gabata cikin nassoshin Mashi’a da nufi da halitta,

Kamar yadda ba za su sami kawukansu ba,ba za su sami aiyukansu ba,qudurarsu da mashi’arsu da nufinsu da aiyukansu dukkaninsu masu bin nufinsa ne Allah Maxaukakin Sarki da mashi’arsa da aiyukansa,ba mashi’arsu da nufinsu da qudurarsu da aiyukansu sune ido ga mashi’ar Allah da nufinSa ds qudurarSa da aiyukanSa.Kamar yadda basu kasance shi ba, tsarki ya tabbata ga Allah Maxaukakin Sarki ya tsarkaka daga haka ,aiyukansu an halitta su dominsu, sun dace da su, an jingina su gare su haqiqa, Allah shine Mai aiki na haqiqa, bawa kuma shine mai aikatawa na haqiqa, bawa shine abin shiryarwa, da wannan ne ake jingina dukkanin aiyukan ga wanda ya tsayar da su ,Allah Maxaukakin Sarki Ya ce:

Wanda Allah Ya shiryar,to,shi ne Mai shiryuwa

Jingina shiriya zuwa ga Allah ,an jingina shiryuwar zuwa ga bawa a haqiqa, kamar yadda Mai shiryarwa shi ne idon shiryayye, hakanan kuma shiriya ba itace idon shiryuwa, haka Allah Ya ke batar da da wanda Ya so a haqiqa da wannan bawa sai ya zama batacce haqiqatan,haka Allah Ya ke juya al’amuran bayinSa, wanda Ya jingina aiki da aikatawa zuwa ga bawa ya kafurta,wanda ya jingina zuwa ga Allah ya kafurta, wanda Ya jingina aiki zuwa mahalicci da zuwa ga abin halitta gabaxayansu a haqiqa wannan shine mumini.

 Me ne ne amsar wanda ya ce shin ba ya yuwuwa cikin qudurar Allah Ya sanya dukkanin bayinsa su zamo muminai masu biyayyya kuma shiryayyu

Me ne ne amsar wanda ya ce shin ba ya yuwuwa cikin qudurar Allah Ya sanya dukkanin bayinsa su zamo muminai masu biyayyya kuma shiryayyu

Eh haqiqa Allah mai iko ne akan haka kamar yadda Ya ce:

Da Ubangijinka Ya so da dukkannin waxanda ke doron qasa sun yi Imani

kuma Allah Madaukaki ya ce

Sai dai hakan da ya aikata musu shine ya qunshi hikimarSa ya kuma wajabta Rububiyyarsa da

Uluhiyyarsa da SunayenSa da SiffofinSa ,to faxar mai Magana :saboda me zai zamo a cikin bayinSa akwai mai biyayya da mai savo ?kamar faxin mai cewa ne me ya sa bai zamo cikin sunayenSa ba mai Cutarwa ,Mai amfanarwa,Mai kyauta,Mai hanawa,Mai qasqantarwa,Mai xaukakawa,Mai ni’imtarwa,Mai kamawa da wasun haka ?da wannan sai mu ce aiyukanSa Maxaukakin Sarki sun qunshi sunayenSa ,kuma ragowar ne na sunayenSa ,har ma kan UluhiyyarSa da RububiyyarSa:

Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al’arshi daga abinda suke siffantawa.Ba’a tambayarSaga abinda Yake aikatawa ,alhalinalhalin kuwa suna tambayar su.

 Matsayin Imani da qaddara a cikin addini

 Yankin Imani

Me ne ne matsayin Imani da qaddara a Addini?

Imani da qaddara tsari ne na Tauhidi,kamar yadda da sababan da suke sadarwa zuwa ga alherinsa ta kuma nesatar daga sharrinsa sune tsari na shari’a,babu wanda zai bi tsarin addini kuma sai wanda ya yi Imani da qaddara ya kuma bi shari’a,kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce kan Imani da qaddara sa’annan Ya ce da waxanda suka ce da shi shin ba zamu dogara ba akan Littafinmu ba mu bar aiki,Sai ya ce :’’ku yi aiki kowa an sauqaqe masa abinda aka halittashi dominsa ‘’

Wanda ya kore qaddara yana riya korewar ga shari’a, haqiqa Allah Maxaukakin Sarki Ya aiyukansa da qudurarsa,Ya sanya bawaya zamo mai tsayawa ne kan aiyukansa shine mahaliccinsu, ya tabbata cewa Allah Maxaukakin Sarki shi ne mahalicci ya kuma tabbatar cewa dukkanin halittu Allah ne ya halicce suWanda ya tabbata mai buqatuwa ne dashi kan shari’a,mai yaqarsa ne da shi,ya korewa bawa qudurarsa da zavinsa wanda Allah ya bashi ya kuma dora masa gwargwado sai ya riya Allah Ya dora bayinsa abinda ba zasu iya xauka ba kamar dora makanta wannan ya nasabta Allah da zalunci,shugaban shi shine shaidan Allah Ya la’ance ni a loqacin da Ya ke cewa:

Ya ce ‘’To ina rantsuwa da halakarwar da ka yi mini ,lallai ne,ina zaune musu tafarkinKa madaidaici

Amma mumini na gaskiya ,zai yi Imani da qaddara alkhairinta da kuma sharrinta,kuma Allah shine mahaliccin dukkanin waxannan,suna miqa wuya ga shari’a umarninta da haninta suna hukunta kawunnansu gare shi a fili da boye ,kuma cewa shiriya da vata a hannun Allah suke Yana shiryar da wanda Ya so da falalarSa,Yana kuma vatar da wanda Ya so da adalcinsa ,Shine mafi sanin wararen falalarSa da adalcinSa

Lallai ne Ubangijinka Shi ne Mafi saniga wanda ya ke vacewa daga hanyar Sa kuma Shine Mafi sani ga masu shiryuwa

A cikin haka akwai hikima matuqa da hujja kwakkwara,kuma cewa sakamako da uquba matakai ne na shari’a a aikatawa da kuma bari ba kan qaddara ba,suna xaukaka kawunan da qaddara a yayin masifu ;idan kuma suka tsinci kawunansu cikin mai kyau sai su gane gaskiya ,Allah Yana cewa akansu suna cewa

Godiya ta tabbata ga Allah da ya shiryar da mu ga wannan ,ba mu kasance muna iya shiryuwa ba ,ba domin Allah Ya shiryar da mu ba

Kan abinda suka ce,fajiri kuma ya ce:

An ba ni shi ne a kan wani ilimi wanda yake gare ni ne kawai

Idan suka aikata mummuna sai su ce kamar yadda iyaye guda biyu suka ce:

Ubangijinmu mun zalunci kawunanmu ,idan har baka yafe man aba ka yi mana rahama za mu zamo daga cikin tavavvu

Ba su fada ba kamar fadin shaidan jefaffe:

Ubangiji ina rantsuwa da hallakawar da kayi min

Idan wata musiba ta same su:

Lallai Mu daga Allah Muke kuma zuwa gare shi zamu koma

Ba za su ce kamar yadda waxanda suka kafirce suka ce ba:

Suka wa yan uwansu idan,sun yi tafiya a cikin qasa ko kuwa suka kasance a wurin yaqi :Da sun kasance a wurinmu da bas u mutu ba ‘’(Wannan kuwa )domin Allah Ya sanya waccan maganar ta zama nadama a cikin zukatansu. Allah shine Yake rayarwa kuma shine Yake mataewa.Kuma Allah ga abinda kuke aikatawa,Mai gani ne.

Nawa ne rabe – raben Imani?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Bai zama Addini ba domin kun juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma,kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi Imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da Littattafan sama da Annabawa,kuma ya bayar da dukiya,akan yana sonta ga mai zumunta da marayu da matalauta da dan hanya da masu roqo,kuma a cikin fansar wuya,kuma ya tsayar da sallah,kuma ya bayar da zakka,da masu cika alqawari idan sun qulla alqawarin da masu haquri cikin tsanani da cuta da loqacin yaqi.Wadannan sune suka yi gaskiya ,kuma wadannan sune masu taqawa.

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’imani sittin ne da kadan ‘’a wata ruwayar ‘’yanki saba’in ne da kadan na qololuwarta shine fadin La’ilaha illallah na qarshenta shine kawar da abinda zai cutar daga kan hanya,kunya wani yanki ce na imani’’

 Fassarar malamai kan rabe—raben Imani

Da me malamai suka fassara rabe –raben Imani?

Qoqari sun kuma fa’idantu ,sai ba sharaxi ba ne saninta a cikin Imani,sai dai Imani yana isa da ita a dunqule,kuma ya zamo bata fita daga Alqur’ani da kuma Sunnah ,ya wajaba akan bawa ya yi aiki da umarninta ya kuma guji haninta,ya kuma gaasgata labaranta,rabe –raben Imani ya cika,waxanda suka qididdige su sun tabbatar da gaskiyarsu cewa duka suna daga cikin Imani,sai dai yankewa wanda shine manufar Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi kan wannan yana buqatar tsayawa

 Rufewa kan abinda malamai suka qididdige daga rabe – raben Imani

Ka abaci rufewar abinda suka qididige?

Hafiz ya taqaita abinda Ibn Hibban ya rawaito a cikin’’Al Fath’’yane cewa :Waxannan rabe –raben sun haxa ne daga aiyukan zuciya da na harshe da na jiki,

Amma aiyukan zuciya :sune iitiqadi da niyyoyi su xabi’u ne guda ashirin da huxu ,Imani da Allah ya shiga ciki,Imani da ZatinSa da siffofinSa,da tauhidinSa ,cewa babu wani abu kwatankwacinSa shi Mai ji ne kuma Mai gani ne da I’itiqadin rashin samuwar wani bayanshi,da Imani da Mala’ikuda LittatafanSada ManzanninSa da qaddara alkhairinta da kuma sharrinta ,da Imani da ranar lahira ,mas’alal kabari ma zata shiga ciki da tashi bayan mutuwa ,da hisabi da mizani ,da siraxi da Aljannah da Wuta ,da soyayyar Allah ,da soyayya da qiyayya saboda Allah,da soyayyar Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi da qudurcewa wajen girmama shi ,sannan salatin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya shiga ,da bin Sunnar shi ,da Ikhlasi ,barin riya ya shiga ciki ,da munafurci ,da tuba,da tsoro ,da fata ,da godiya,da cika alqawari,da haquri,da yarda da qaddara ,da tawakkali,da rahama,da qanqan da kai,ya shiga cikinsa girmama babba,da rahama ga qarami,da barin girman kai da mamaki ,da barin hassada ,da barin kyashi,da barin fushi

Aiyukan harshe :ya qunshi Dabi’u guda bakwai :yin lfazi da tauhidi,da tilawar Alqur’ani,da neman ilimi da koyar da shi ,da Addu’a ,da zikiri,Istigfari zai shiga

Ya gabata gare ka cewa Imani shi ne magana da kuma aiki ,faxin zuciya da kuma harshe ,da kuma aikin zuciya da kuma harshe da gavovi,shine gasgatawa ,fadin harshe kuma ,shine zane da Kalmar musulunci,aikin zuciya kuma shine niyya da ikhlasi ,aikin gabbai kuma shine ,miqa wuya da dukkanin biyayya ,idan gabakixayan wadan nan abubuwa hudun suka gushe fadin zuciya da aikinta fadin harshe da aikinshi da aikin gavvai Imani ya gushe baki daya,idan gasgatawar zuciya ya gushe sauran ba za su yi amfani ba ,domin cewa gasgatawar zuciya wani abu ne daga sallamawarta ta kuma kasance mai amfani wannan kamar wanda ya qaryata sunayen Allah ne da siffofinSa ko da kowanne abu da Allah ya aiko da shi ya saukar da LittattafanSa da shi ,idan aikin zuciya ya gushe tare da I’itiqadi na gaskiya.

 Dalilin kyautatawa daga Littafi da Sunnah

 Kyautatawa cikin ibada

Me ne ne dalilin kyautatawa daga Littafi da Sunnah?

Akwai dalilai ma su yawa daga ciki akwai fadin Allah Madaukakin Sarki:

Ku kyautata lallai Allah yana son masu kyautatawa

Lallai Allah Yana tare da wadanda suka yi taqawa da wadan da su ke su masu kyautatawa ne.

Kuma wanda ya mika fuskarsa zuwa ga Allah, alhali kuma yana mai kyautatawa to lalle ya yi riko ga igiya amintacciya

Wadanda suka kyautata suna da Kyautaye da kuma Kari

Shin kyautatawa na da wani sakamako ?(A’aha )face kyautatawa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce :’’haqiqa Allah Ya rubuta kyautatawa akan dukkan komai ‘’a wata kuma fadar yana cewa :Ni’ima ta tabbata ga bawa ace yam utu yana mai kyautata Ibadar Allah

Me ne ne kyautatawa a cikin ibada?

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya fassara shi a cikin hadisin Jibril a loqacin da ya ke cewa ‘’ba ni labari akan kyautatawa ?sai ya ce :Ka bautawa Allah kamar kana ganinSa ,idan kai ka kasance baka ganinSa ,to ,shi Yana ganinka ‘’Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya bayyana cewa kyautatawa sau biyu ta hanyoyi daban –daban ,na qololuwar su:shi ne bautawa Allah kamar kana ganinSa,wannan shine abin dubawar ,shine bawa zai bautawa Allah gwargwadon yadda yake ganin Allah a zuciyarsa ,shi ne zuciya ta zamo tana haskaka da Imani

Na biyu: shi ne muraqaba ,shi ne bawa ya yi aiki yana mai halarto da ganin Allah tare da kusatuwa zuwa gare shi ,idan bawa ya halarto wannan a cikin aikinsa yayi aiki akan shi yana mai Ikhlasi ga Allah ;saboda halarto da Shi hakan cikin aiyukansa zai hana shi juyawa zuwa ga wanin Allah da nufarsada wani aiki

Ma’abota waxannan maqaman suna wucewa gwargwadon tasirin hangensu

 Abubuwan da suke kishiyar Imani

Me ne ne kishiyar Imani?

Kishiyar Imani shine kafirci,asli yana da rabe – rabe kamar yadda Imani shima a asali ya da su .An sani a abinda ya gabata cewa aslin Imani shine gasgatawa tare da miqa wuya da Da’a ,shi kuma kafirci shine musawa da taurin kai abin lazimtawa ga girman kaida savawa, Da’a gabadayanta yanki ce na Imani ,an ambace ta a cikin nassoshi masu yawa tana daga cikin Imani kamar yadda ya gabata ,shi kuma savawa gakixayansa yanki ne na kafirci ambaci haka a nassoshi da dama da kafirci kamar yadda zai zo,idan ka san wannan zaka san cewa kafirci gida biyu ne ,kafirci babba yana fita daga Imani gaba daya ,shi ne kafirci da yin I’’itiqadi mai kore faxin zuciya da aiki da shi ko da daya daga cikinsu ,shi kuma qaramin kafirci shine yak e kore cikar Imani bay a korewa a sake ,shi ne kafirci na aiki shi baya warware fadin zuciya ko aikinsa baya lazimta haka

 Yadda za’a kore qudurtaccen kafirci da Imani gaba daya

Bayyana min yadda za’a kore qudurtaccen kafirci da Imani gabaxaya ka kuma rarrabe abinda nah axe shi wajen gusar da shi?

Ya gabata gare ka cewa Imani shi ne magana da kuma aiki ,faxin zuciya da kuma harshe ,da kuma aikin zuciya da kuma harshe da gavbobi,shine gasgatawa ,fadin harshe kuma ,shine zane da Kalmar musulunci,aikin zuciya kuma shi ne niyya da ikhlasi ,aikin gvvai kuma shine ,miqa wuya da dukkanin biyayya ,idan gabakidayan waxannan abubuwa hudun suka gushe faxin zuciya da aikinta fadin harshe da aikinshi da aikin gavvai Imani ya gushe baki daya,idan gasgatawar zuciya ya gushe sauran ba za su yi amfani ba ,domin cewa gasgatawar zuciya wani abu ne daga sallamawarta ta kuma kasance mai amfani wannan kamar wanda ya qaryata sunayen Allah ne da siffofinSa ko da kowanne abu da Allah ya aiko da shi ya saukar da LittattafanSa da shi ,idan aikin zuciya ya gushe tare da I’itiqadi na gaskiya.

Ahlus Sunnah sun haxu kan cewa gushewar Imani gaba daya baya amfanar gasgatawa tare da tsarkakewar aikin zuciya shine sonsa da kuma miqa wuya ,kamar yadda suke qudurce gaskiyar Manzon Allah suna masu girmama shi a fili da Boye suna cewa shi ba Maqaryaci ba ne sai mu ba zamu bi shi ba ,ba kuma zamu yi Imani da shi ba

 Nawa ne kasha – kashen babban kafirciwanda ya ke fitarwa daga addini?

 Me ne ne kafirci na jahilci da qaryatawa?

Nawa ne kasha – kashen babban kafirciwanda ya ke fitarwa daga addini?

Mun sani daga abinda da ya gabata cewa ya kasu gida huxu :kafirci na jahilci da qaryatawa ,kafirci na musantawa,kafirci na taurin kai da girman kai ,da kuma kafirci na munafurci.

Me ne ne kafirci na jahilci da qaryatawa?

Shine abinda ya kasance a zahiri da kuma badini kamar kafiran quraishawa da wadan da suka gabace su daga al’ummatan da suka gabata

Allah Maxaukakin Sarki Yan a cewa akan su:

Wadan da suka qaryata,game da Littafin,kuma da abinda Muka aika Manzanninmu da shi.To za su sani.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma ka kau da kai daga Jahilai

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma a ranar da Muke Tarawa daga kowacce al’umma,wata qungiya daga waxanda suke qaryata ayoyinMu,sai gas u ana kange su (ga kora) Har idan sun zo (Allah)zai ce ,’’Ashe kun qaryata ayoyinNa,kuma ba ku kewaye su da sani ba? To me ne ne kuka kasance kuna aikatawa?’’

kuma Allah Madaukaki ya ce

A’a,sun qaryata game da abin da ba su kewaye da saninsa ba,kuma fassararsa ba ta riga ta je mu su ba

 Kafirci na musantawa

Me ne ne kafircin Musantawa?

Shine wanda ake boye gaskiya da rashin miqa wuya gare shi a zahiri tare da sanin hakan ,saninsa yana boye ,kamar kafircin Fir’auna da mutanensa ga Musa,da kuma kafircin yahudawa ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Kuma suka yi musunsu,alhali zukatansu sun nutsu da su domin zalunci da girman kai

Kuma suka yi musunsu,alhali zukatansu sun nutsu da su domin zalunci da girman kai

Allah Ta’ala Ya ce akan yahudawa:

To a loqacin da abin da suka sani ya je musu,sai suka kafirta shi

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma lallai ne wani vangare daga gare su,haqiqa,suna boyewar gaskiya alhali kuwa suna sane.

 Me ne ne kafircin taurin kai da kuma girman kai?

 Kafircin munafurci

Me ne ne kafircin taurin kai da kuma girman kai?

Shine rashi miqa wuya ga gaskiya da guje masa,kamar kafircin Iblis loqacin da Allah Maxaukakin Sarki yak e cewa:

Face Iblis ya qi,kuma ya yi girman kai,kuma ya kasance daga cikin kafirai

Bai dace daga gare shi ba musa umarnin Allah ko yi masa inkari ,sai dai ma ya juya baya gare shi ya kuma soke shi cikn hikimar umarnin shi da adalcinSa, ya ce:

Shin zan yi sujuda ne ga wanda Ka halitta daga Tavo ?

Kuma ya ce:

Ya ce: ’’ban kasance ina yin sujuda bag a mutum wanda Ka halicce shi daga busasshen yunbuun laka wadda ta canja’’

Kuma ya ce:

Ya ce: Ni ne mafificidaga gare shi,Ka halittani daga Wuta alhalikuwa Ka halitta shi daga laka

Me ne ne kafircin munafirci?

Shine abinda ya kasance da rashin gasgatawar zuciya da sanin shi rtare da miqa wuya a zahiri dan riya ga mutane,kamar kafircin Ibn Salul da jama’arsa

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Kuma akwai daga cikin mutane wanda yake cewa :’’Mun yi Imani da Allah kuma da yinin Lahira ‘’ alhali k sub a Muminai ba ne .Suna yaudarar Allah da waxanda suka yi Imani ,alhali bas u yaudarar kowa face,kansu kuma basu sakankancewa.Acikin zukatansu akwai wata cuta,sai Allah Ya qara musu wata cutar,kuma suna da azaba mai raxaxi saboda abinda suka kasance suna yin a qarya –har zuwa ‘’Lallai Allah akan dukan koai Mai iko ne"

 kafirci wanda baya fitarwa dag Addini

Me nene kafirci wanda baya fitarwa dag Addini ?

Shi ne kowane irin Sabo da Shari'a ta kirashi da sunan Kafirci tare da wanzuwar Sunan Imani ga Mai yinsa, Kamar fadin Annabi tsira da Aminci su tabbata a gareshi "kada ku koma bayana Kafirai wasu daga cikinku suna kashe wasu" da kuma fadinsa "Zagin Musulmi Fasikanci ne kuma yakarsa Kafircin" sai ya kira yakar Musulmi tsakanin junansu da cewa shi Kafirci ne kuma ya kira wanda yake yin hakan da Kafiri, tare da fadin Allah Madaukakin Sarki

kuma idan jama’a biyu ta muminai suka yi yaki, to kuyi sulhu a tsakaninsu- zuwa fadinsa- kadai muminai ‘yan’uwa ne to kuyi sulhu a tsakanin ‘yan’uwanku guda biyu

Sai Allah madaukakin sarki ya tabbatar musu da Imani da kuma ‘yan’uwantakar Imani kuma bai kore musu wani abu daga hakan ba

Kuma Ubangiji madaukaki ya fada acikin Ayar kisasi:

To wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga dan’uwansa to abi da Alheri, da biya zuwa gare shi da kyautatawa

Sai Allah madaukaki ya tabbatar masa da ‘yan’uwartakar Musulunci bai kore ta daga gare shi ba

Haka kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:“Mazinaci baya zina alokacin da yake zinar alhalin yana mumini, kuma baya sata alokacin da yake satar yana mumini, kuma baya shan giya yayin da yake shanta yana mumini, kuma tuba abin bujurowa ne daga baya” yayi kari a cikin wata riwayar” kuma bazai yi kisa ba a lokacin yana mumini- acikin wata riwayar kuma-kuma ba zai kwaci wani abu mai Daraja ba da zai sa Mutane su rika daga kansu sama sabida ganinsa, Hadisin yana nan cikin Buhari da Muslim

Hadi da Hadisin Abi zarrin kuma, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace: babu wani bawa da zai ce Laa’ilaaha illallahu sannan ya mutu akan haka sai ya shiga Aljanna” sai nace kuma koda yayi zina kuma yayi sata? Sai yace: koda yayi zina kuma yayi sata” ya fada sau uku sannan yace ana hudun ”Ko da kuwa Abu Zarr baya so"

To wannan yana nuni da cewa ba’a kore gaba ki dayan imani ga Mazinaci da Barawo da Mashayin giya da wanda yayi kisa matukar yana mai dayanta Allah, domin cewa shi da yana nufin hakan ba zai bada labari ba da cewa duk wanda ya mutu abisa La’ilaha illallahu zai shiga Aljanna,kuma idan ya aikata wadancan laifuka to bazai shiga Aljannaba sai dai rai Mumina,

Yana nufi da hakan tawayar imani da kuma kore cikarsa, kuma kadai Bawa yana kafirta ne da wadan can laifuka tare da halartawarsa ita mai lazimta karyata Alkur’ani da Manzo acikin haramtata barima yana kafirta da kudirce halaccinta, kuma koda bai aikatata ba Allah shi ne mafi sani.

 Yiwa Gumaka sujjada da wulakanta Alkur’ani da zagin Manzo da kuma wasa da Addini

Idan akace da mu shin yin sujjada ga Gumaka da kuma wulakanta Alkur’ani da zagin Manzo da wasa da Addini da makamantan wadannan wannan dukkaninsa yana daga kafirci na aiki cikin abinda yake bayyana, to saboda me ya kasance mai fitarwa daga addini kuma bayan kun san kafirci karami da aiki?

Kasani cewa wannan hudun da wanda yake shakalinta ba itace take daga cikin kafirci na aikiba sai dai ta fuskar kasantuwarta mai afkuwa da aikin gabobi cikin abinda yake bayyanuwa ga mutane, kuma sai dai cewa ita bata afkuwa sai tare da tafiyar Aikin zuciya na daga Niyyarsa da tsarkakewarsa da Soyaryarsa da kuma jawuwarsa ba wani abu da yake wanzuwa tare da ita daga wannan, to ita duk da ta kasance ta aiki a zahiri to cewa ita ba makawa mai lazimta kafircice na kuduri, kuma wannan baza ta afku ba sai daga Munafiki mai fita daga Addini ko mai kin gaskiya kuma shin abinda ya dauki munafukai a yakin tabuka abisa fadar Kalmar kafirci kuma sun kafirta bayan musuluntarsu kuma sun yi himma da abinda basu samu ba sai dai wancan tare da fadin su yayin da aka tambaye su “ kawai mun kasance muna hira kuma muna wasanni.

Ubangiji madaukakin sarki yace: kace shin da Allah da ayoyinsa da manzonsa kuka kasance kuna izgili? Kada ku kawo wani uzuri, hakika kun kafirta a bayan imaninku,kuma mu bamu san kafirci karami na aiki kawai ba sai dai na aiki tsantsa wanda bai lazimci I’itikadi ba kuma bai warware fadin zuci ko aikinsa.

 Kashe kashen zalunci da fasikanci da kuma munafunci

Zuwa kaso nawa zalunci da fasikanci da munafunci suka kasu?

Kowannen su ya kasu gida biyu Babba shi ne Kafirci da kuma Karami shi ne kasa da haka

 Misalin zalunci babba da karami

Mene ne Misalin zalunci babba da karami?

Misalign zalunci babba shine abinda Allah madaukaki ya ambata cikin fadinsa: hakika shirka wani zalunci ne maigirma. Da kuma fadinsa madaukakin sarki: lalle ne shi wanda ya yi shirka da Allah to lalle ne Allah ya haramta masa Aljanna. Kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai.kuma misalin zaluncin da yake koma bayan wancan sh ne wanda Allah ya ambata da fadinsa cikin suratu-aldalak: kuma ku ji tsoran Allah Ubangijinku kada ku fitar dasu daga gidajensu kuma kada su fita sai dai in suna zuwa da wata Alfasha mabayyaniya. Kuma wadan can iyakokin Allah ne.kuma duk wanda ya ketare iyakokin Allah to lallai ya zalunci kansa. Da fadin sa madaukakin sarki: kuma kada ku rike su a kan cutarwa domin ku yi zalunci, kuma wanda ya aikata wancan, to hakika ya zalunci kansa.

 Misalin zalunci babba da karami

Mene ne Misalin zalunci babba da karami?

Misalin fasikanci babba shi ne wanda Allah madaukakin sarki ya ambata cikin fadinsa lalle Munafukai su ne Fasikai. Da fadinsa madaukakin sarki sai dai Iblis ya kasance daga Aljanu sai ya yi fasikanci ga barin umurnin Ubangiji. Da kuma fadinsa: kuma muka tserar dashi daga Alkaryar nan da take aikata munanan aiyuka. Lalle su sun kasance mutanen mugun aiki,fasikai. Kuma misalin fasikanci koma bayan wancan shi ne fadinsa madaukakin sarki ga masu kazafi: kuma kada ku karbi wata shaida a gurinsu har abada, wadancan su ne fasikai. Da kuma fadinsa madaukakin sarki: ya ku wadanda suka yi imani idan fasiki ya zo muku da wani labari to ku nemi bayani, domin kada ku cuci wasu mutane a cikin zalunci , saboda haka ku wayi gari a kana bin da kuka aikata kuna masu nadama. An rawaito cewa ita ta sauka a kan Walidu dan Ukbata

 Misalin kowanne daga Babban Munafunci da kuma Karami

Mene ne Misalin zalunci babba da karami?

Misalin munafunci babba shi ne wanda ambatonsa ya gabata a cikin ayoyin farko na suratu-albakra da kuma fadinsa madaukaki: lalle ne Munafukai suna yaudarewa da Allah, alhali kuwa shi ne mai yaudarar su zuwa fadinsa lalle ne Munafukai suna cikin magangara mafi kaskanci daga wuta. Da fadinsa madaukaki: idan Munafukai suka je maka suka ce, muna shaidar lalle kai hakika Manzon Allah ne kuma Allah yana sane da lalle kai Manzonsa ne kuma Allah yana shaida lalle Munafukai hakika makaryata ne. da kuma wadan su wadan can daga ayoyi, kuma misalin munafunci wanda yake koma bayan wancan shi ne wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada a cikin fadinsa: Alamar Munafiki uku ce, idan ya yi zance sai ya yi karya, idan kuma ya yi alkawari sai ya saba, idan kuma aka amince masa sai ya yi ha’inci. Da kuma hadisin “abu hudu wanda suka kasance a cikinsa ya kasance Munafiki

 Hukuncin tsafi da Matsafi

Menene hukuncin tsafi da Matsafi?

Tsafi samuwarsa da tasirinsa tabbatacce ne amma tare da dacewa da kadaru na kasancewa, kamar yadda madaukaki ya fada: suna neman Ilmin abin da suke Rarrabewa tsakanin mutum da Matarsa das hi daga gare su. Kuma sub a su zama masu cutar da kowa da shi ba, face da Iznin Allah. Kuma tasirinsa tabbatacce ne cikin Hadisai ingantattu.

Amma kuma Matsafi duk da kasancewar tsafin nasa daga abinda yake samu ne daga Shaidanu kamar yadda ayar Bakara ta yi nassi a kansa to shi Kafiri ne saboda fadinsa madaukaki: kuma ba su sanar da kowa ba face sun ce: mu fitina kawai ne, saboda haka kada ka kafirta zuwa fadinsa- kuma suna neman ilmin abinda yake cutar dasu,kuma ba ya amfaninsu. Kuma lalle ne hakika sun sani tabbas wanda ya saye shi ba shi da wani rabo a cikin Lahira.

 Haddin Matsafi

Menene haddin Matsafi?

Tirmizi ya rawaito daga Jundubi y ace: Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: haddin Matsafi dukansa da takobi. Kuma ya inganta wakafinsa

Ya ce kuma aiki a kansa yake a wajan sashin ma’abota ilimi daga sahabban Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma shi ne fadin Maliku dan Anas

Kuma Shafi’i Allah madaukaki ya jikansa ya ce: kadai ana kasha Matsafi idan ya kasance yana aiki da tsafin nasa abinda yakai matsayin kafirci, amma idan ya yi aiki koma bayan kafirci to baya ganin kisa a kansa, kuma ya hakika ya tabbata kasha kasha Matsafi daga Umar da dansa Abdullah da ‘yarsa Hafsah da Usman dan Affan da Jundubi dan Abdullah da Jundubi dan Ka’abu da kais bin Sa’ad da Umar dan Abdul’aziz da Ahmad da Abi Hanifa da wadansunsu Allah ya ji kansu.

 Ta’arifin Al-nushrah da Hukuncinta Rukiyya da aka shara’anta

Menene Al-nushra kuma menene Hukuncinta?

Al-nushrah it ace warware tsafi ga wanda akaiwa tsafin to idan hakan ya kasance da tsafi ne kwatankwacinsa to ita daga aikin Shaidan ne, kuma idan ta kasance da rukiyya ce da kuma matsarai wanda aka shar’anta to babu laifi da hakan.

Mecece rukiyyar da aka shara’anta?

Ita ce wacce ta kasance daga Kur’ani da sunna tsarkakakkiya kuma ta kasance da harshen larabci, kuma kowanne daga mai rukiyyar da wanda akewa rukiyyar suka kudirta cewar tasirinta baya kasancewa said a izinin Allah mabuwayi kuma madaukaki domin cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi hakika Jibrilu ya yi masa rukiyya, kuma shi da kansa ya yiwa da yawa daga cikin sahabbai kuma ya tabbatar musu da aikata ta barima kuma ya umarce su da ita kuma ya halatta musu karbar lada a kanta, dukkan wancan yana cikin Bukhari da Muslim da wadansunsu.

 Rukiyyar da aka hana

Mecece rukiyyar da aka shara’anta?

Ita ce wacce bata kasance ta Alkur’ani da sunna ba kuma bata kasance da larabci ba bari dai ita daga aikin Shaidan da kuma neman yi masa hidima, da kuma kusanci zuwa gare shi da abinda yake so kamar yadda da yawa daga makaryata da ‘yan rufa ido

 Hukuncin rataye rataye na daga layu da tsirkiya da Guru da Kashi da Maikama da su

Menen Hukuncin rataye rataye na daga layu da tsirkiya da Guru da Kashi da Maikama da su?

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: wanda ya rataya wani abu to an jingina shi a gareshi

Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin sashin tafiye tafiyansa ya aiki wani jakada a bisa cewa kada ya bar wata laya ko rataye a wuyan wani rakumi face ya tsinke ta

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: lalle rukiyya da layu da maganin soyayya shirka ne

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: duk wanda ya rataya laya kada Allah ya kare shi kuma duk wanda ya rataya dodon kodi to kada Allah ya kare shi A cikin wata riwayar kuma “wanda ya ya rataya laya to hakika ya yi shirka

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada ga wanda ya ga a hannunsa akwai kewaye na daga tagulla, sai y ace masa menene wannan? Sai y ace maganin raunin tsufa ne.sai y ace masa jefar da ita domin ita ba za ta kara maka komai ba face rauni,domin cewa da ka mutu tana jikinka dab a za ka rabauta ba har abada

Kuma Huzaifa Allah ya yarda da shi ya yanke zare daga hannun wani mutum sannan ya karanta fadinsa madaukaki:

Kuma da yawa mafi yawansu basa imani da Allah face suna masu shirka

Kuma Sa’idu dan Jubair Allah ya jikansa y ace wanda ya yanke wata laya daga wani mutum ya kasance kamar wanda ya ‘yanta wuyaye,

Kuma wannan yana da hukuncin Hadisi marfu’i.

Menene hukuncin abin ratayawar idan ya kasance daga Alkur’ani ne?

An rawaito halaccinsa ga sashin magabata kuma mafi yawansu sun tafi abisa hana shi kamar Abdullah bun Akim da Abdullah bin Amru da Abdullah bin Mas’ud da sahabbansa tsira da amincin Allah su tabbata a gare su kuma shi ne ya fi saboda gamewar hanin ga ratayawar, kuma saboda rashin wani abu na daga hadisi marfu’I da zai kebance wancan kuma saboda kiyaye Kur’ani daga wulakanta shit a inda za’a iya daukarsa galibi ba tare da tsarki ba, kuma hakan yana iya bayuwa izuwa rataya waninsa,kuma saboda toshe kafa abisa I’itikadin abinda aka hana da kuma karkatawar zuciya zuwa ga wanin Allah musamman a cikin wannan zamani.

 Hukuncin Bokaye

Menene hukuncin Bokaye?

Bokaye suna daga Dagutai kuma sune masoyan shaidanun da suke yi musu wahayi kamar yadda Allah madaukaki y ace:

Kuma lalle ne shaidanu hakika suna yin ishara zuwa ga masoyansu

Zuwa karshen ayar

Kuma suna sassauka a kansu suna jefa musu kalmomin da suka jiyo sannan sai su hada tare da ita karya dari kamar yadda madaukaki y ace:

Shin in gaya muku a kan wanda shaidanu kan sauka? Sukan sauka a kan dukan makaryaci, mai zunubi. Suna jefa ji alhali mafi yawansu makaryata ne.

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi y ace: a cikin hadisin wahayi sai mai satar ji ya ji ta da kuma wani mai satar jin haka dai sashinsa yana birbishin sashi to sai ya jefawa wanda yake kasansa sannan shima ya jefawa wani da yake kasansa har sai ya jefata abisa harshen Matsafi ko Bokan to wani lokacin sai tauraro ya riske shi kafin ya jefata wani lokacin kuma zai sami jefatan amma zai hada ta da karya dari. Hadisin yana cikin Bukhari da cikarsa

Kuma yana daga wancan zane da kasa wanda suke kiransa da bugun kasa, kuma da ta hanyoyin yi da tsakuwa da makamantansu.

 Hukuncin wanda ya gasgata Boka.

Hukuncin wanda ya gasgata Boka.

AllahMaukakin Sarki ya ce

Ka ce: wanda suke sammai da kassai basu san gaibu ba sai Allah

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma mabudan gaibu suna gurinsa ba wanda ya sansu sai dai shi kakaranta har zuwa karshen Ayar

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ko kuma suna da ilimin gaibu ne, da suke rubutawa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Shin akwai ilimin gaibu a wurinsa, saboda haka yana ganin gaibin a cikin sa?

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma Allah ne ya sani kuma ku ba ku sani ba

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi y ace: dukkan wanda ya je wajan dan duba ko Boka ya kuma gasgata shi da abinda ya fada to hakika ya kafirta da abinda aka saukarwa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: wanda ya je wajan dan dubakuma ya tambaye shi ga wani abu sannan kuma ya gasgata shi ba za’a karbi sallar kwana arba’in daga gareshi ba

 Hukuncin Ilimin taurari

Menene Hukuncin Ilimin Taurari?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Kuma shi ne wanda ya sanya muku taurari don ku shiryu da su a cikin duffan tsandauri da ruwa.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma lalle mun kawata saman Duniya da fitilu , kuma muka sanya su abin jifa ga shaidanu

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma taurari Horarru ne da umarninSa

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi y ace: dukkan wanda ya dosani wani yanki na taurari to hakika ya dosani wani yanki na daga tsafi ya kara abinda ya kara

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace: kadai abinda na ke tsoro abisa al’umata si ne gasgatawa da taurari da kuma karyatawa da kaddara da zaluncin shugabanni

Kuma dan Abbas Allah ya yarda da su ya fada ga mutanen da suke rubuta Abajada kuma suke duba a cikin taurari” ba na ganin ga wanda yak e aikata wancan yana da wani rabo a wajan ubangiji”

Kuma Katada Allah ya jikansa y ace: Allah ya halicci wannan taurarin saboda abu uku: don ado ga sama da kuma jifa ga Shaidanu da kuma alamomi da ake samun shiriya dasu, to wanda ya yi fassara ba wannan ba to hakika ya kuskurewa rabonsa kuma ya tozartar da nasibinsa kuma ya kallafawa kansa abinda bas hi da ilimi das hi.

 Hukuncin Rokon Ruwa da taurari

 Hukuncin shu’umanci da abinda yake tafiyar da ita

Mene ne Hukuncin Rokon Ruwa da taurari?

Allah Madaukakin Sarki ya ce: Kuma kuna sanya Arzikinku lalle ku kuna karyatawa. Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:abubuwa Hudu a cikin al’umata yana daga al’amuran jahiliyya kuma baza su barsu ba: alfahari da iyaye, da sukar dangi, da kuma neman shayarwar ruwa ga taurari, da kuma kukan kera

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace Allah madaukaki y ace: a cikin bayina an wayi gari akwai wanda ya yi imani da ni da kuma wanda ya kafirta, amma wanda y ace an yi mana ruwa da falalar Allah, to wannan shi ne ya yi imani da ni ya kafirta da taurari, amma wanda kuma wanda y ace ammana ruwa saboda tauraro kaza da kaza to wannanya kafirta da ni kuma ya yi imani da taurari

 Hukuncin shu’umci da abinda yake tafiyar da ita

Allah ya yi masa Rahama

Ku saurara! Kadai shu’umcinsu yana ga Allah

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Babu adwa(harbin cututtuka ta kashin kansu) babu shu’umci babu camfi da mujiya, ba camfa watan safar

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Shu’umci shirk ace shu’umci shika ce

Ibn Mas'ud ya ce:

Kuma babu wani daga cikinmu face (wato wani abu da wannan ya darsu a cikin zuciyarsa) amma Allah yana tafir dashi da dogaro ga Allah

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Shu’umci kawai shi ne abinda ya sa ka ka aikata wani abu ko ya hana ka, kuma an karbo daga Ahmad daga hadisin Abdullah bin Amru : wanda shu’umci ya komar das hi ga barin bukatarsa to hakika ya yi shirka. Sai suka ce to menene yake kankare hakan? sai Ya ce: ku ce ya Allah babu wani alheri sai dai alherinka, babu shu’umci sai abinda ka halitta, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai kai

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Mafi gasgatuwarta kyakkyawan fata kuma kada ta komar da musulmi, to idan daya ya ga abinda yake ki to y ace: ya Allah ba wanda yake zuwa da kyakkyawa sai kai kuma ba wanda zai ije mummuna sai kai, kuma babu wayo babu karfi sai sai daga kai

 Hukuncin kambun baka

Menene hukuncin kambun baka?

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Kambun baka gaskiya ne kuma Annabi ya ga wata Baiwa a fusarta ta Dashe sai yace kuyi mata Magani Kambun Baka ya kamata

Aisha- Allah ya yarda da ita -

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarce ni ko Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi umarni a nemi magani daga kambun baka

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Babu rukiyya sai dai daga kambun baka ko zazzabi

Kuma dukkaninta tana cikin Bukhari kuma a cikinta akwai hadisai masu yawa banda wadanda muka ambata,

Kuma bata da tasiri face da izinin Allah kuma hakika an fassara da ita fadinsa mai girma da daukaka kuma lalle ne wadanda suka kafirta suna yin kamar su kayar da kai saboda kallonsu, a lokzcin da suke jin karatun Alkur’ani, daga masu yawa na daga magabata na kwarai Allah ya yarda da su.

 Kashe kashen sabo

zuwa kaso nawa sabo ya kasu?

Ya kasu zuwa kananu it ace munana, da kuma manya suna masu halakarwa.

 Abubuwan da ake kankare munana da su

Da menene ake kankare munanan ?

Allah ya yi masa Rahama

Idan kuka nisanci manya manyan abinda aka haneku da shi to zamu kankare muku munanan aiyukanku kuma mu shigar daku mashiga ta karamci

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lalle kyawawan aiki suna tafi da munanan

Sai ubangiji madaukakin sarki ya bamu labari cewa munanan ana kankareta da nisantar manyan da kuma yin aiki mai kyau

Haka nan kuma ya zo a cikin hadisi

Ka bibbiyi mummuna da kyakkyawa ta shafe ta.

Haka kuma ya zo a cikin hadisi ingantacce cewa kyautata alwala a bisa lokutan ki,da cirar taku izuwa masallaci da kuma sallolin biyar biyar da juma’a zuwa juma’a, da ramadana zuwa ramadana da tsaya shi da tsayuwar daren lailatul kadri da azimin ranar ashura da wadansunsu na daga da’o’I lalle ita mai kankare munana ne kurakurai

Da yawan wadancan hadisan akwai kayyadewa a cikinsu da nisantar manyan kuma akansa ne ake daukar sakakken daga gareta sai ya zama nisantar manyan sharadi ne na kankarewar kananun da kyawawa da kuma koma bayan ta.

 Ta’arifin manyan

Menene manyan

A cikin tabbatar da hakikaninta akwai maganganun sahabbai da tabi’ai da wadansunsu, aka ce it ace dukkan zunubi da aka bishi da tsinuwa ko wuta ko kowace irin ukuba,kuma aka ce: it ace kowane laifi wanda ake jin aikata shi da rashin kin mai aikata shi da addini da kuma rashin damuwa da shi da kuma karancin tsoransa da Allah, kuma aka ce wani ba wannan ba, kuma hakika ya tabbata a cikin hadisai ingantattu ambaton da yawa daga cikin zunubai da kaba’ira bisa banbancin darajojinsu yana daga cikinsu kafirci mafi girma kamar shirka da Allah da tsafi, kuma yana daga cikinsu babba daga cikin manyan sabo da alfasha, kuma shi ne koma bayan wadancan, kamar kasha rai wanda Allah ya hana a kasha sai da gaskiya, da kuma juyawa a fagen fama, da cin riba da cin dukiyar maraya da fadin karya, yana daga cikinsu yiwa katangaggu rafkanannu muminai mata kazafi da shan giya da sabawa iyaye da wadansun wadannan

Ibnu Abbas ya ce Allah ya yarda da shi: "Su ne zuwa Saba'in kuma mafi kusanci da Bakwai"

Da wadannne Abubuwan da ake kankare Manyan Zunubai da da kanana da su

 Abubuwan da ake kankare Manyan Zunubai da da kanana da su

Da wadannne Abubuwan da ake kankare Manyan Zunubai da da kanana da su

Ana kankare su baki daya da tuba na gaskiya

Allah ya yi masa Rahama

Ya ku wadanda suka yi imani ku k0ma zuwa ga Allah komawa ta gaskiya. Mai yiwa ubangijinku ya kankare muku miyagun aiyukanku kuma ya shigar da ku a gidan Aljanna, koramu na gudana daga karkashinta

Kuma mai yiwuwa daga Allah tabbas ce

kuma Allah Madaukaki ya ce

Sai dai wanda ya tuba kuma yayi imani kuma ya yi aiki aiki na gari to wadannan sune wadanda Allah yake canza munanansu da kyakkyawa….

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wadanda suke idan suka aikata aifasha ko suka zalunci kansu sai su tuna allah, saboda su nemi gafarar zunubansu ga Allah,kuma wanene yake gafarar zunubai face Allah?kuma ba su doge a kan abinda suka aikata ba,alhali kuwa suna sane. Wadannan sakamakonsu gafara ce daga Ubangijinsu da kuma gidajen Aljanna wanda koramu ke gudana a karkashinsu

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Tuba tana kankare abinda yake kafinta

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Allah yafi farin ciki da tuban bawansa daga mutumin da ya sauka a wani masauki yana da matsera,kuma a tare dashi akwai abin hawansa akanta akwai abincinsa da abin shansa sai ya sanya kansa ya yi bacci sosai, sai ya farka abin hawansa ya gudu har saida zafi da kishirwa suka yi tsanani a gare shi, ko sanda Allah ya so sai ya ce: bari na koma gurina sai ya koma ya kara yin bacci sosai sannan ya daga kansa kawai sai yaga abar hawansa a wajansa

 Tuba na gaskiya

Menene tuba na gaskiya?

Shi ne tuba na gaskiya wanda ya hadar da abubuwa guda uku: ciruwa daga sabo, da kuma nadama abisa yinsa da yin niyya abisa ba za’a kuma komawa sabon ba har abada, kuma idan ya kasance a cikinsa akwai wani abin zalunta na wani musulmi sai ya warwareta daga gare shi in hakan ya yiwu domin cewa shi da sannu za’a neme shi da ita ranar alkiyama idan bai warwareta daga gare shi ba a yau, kuma za’a yi masa kisasi daga gare shi babu makawa, domin shi yana daga zaluncin da Allah baya barin komai daga gare shi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:

Wanda ya kasance a gurinsa akwai wani abin zalunci na dan uwansa to ya yi kokari ya warware shi daga gare shi a yau tun kafin lokacin da babu dinare babu dirhami,in ya kasance yana da kyawawan aiki sai a dauka daga kyawawansa in kuwa babu sai a dauko daga munanan aikin dan uwan nasa sai jefa masa a kansa

 Abinda ake yanke tuba dashi a cikin hakkin kowane Mutum

Yaushe ne ake yanke tuba a cikin hakkin kowane daya daga daidaikun mutane?

Allah Madaukakin Sarki ya ce:

Abin da yake tuba kawai ga Allah, it ace ga wadanda suke aikata mugun aikida jahilci sa’annan su tuba nan kusa.to wadannan Allah yana karbar tubansu, kuma Allah ya kasance masani ne, Mai hikima.

Sahabban manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun hadu a kan cewa dukkan abinda aka sabawa Allah da shi to wannan jahilci ne dai dai ne ya kasance da ganganci ne ko waninsa, kuma dukkan abinda ya kasance kafin mutuwa to wannan kusa ne

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace: lalle Allah yana karbar tuban Bawa matukar bai kai gargara ba wannan ya tabbata a cikin hadisai masu yawa,

Amma idan ya ga Mala’ika kuma rai ya zo kirji kuma ya isa makogaro kuma numfashi ya zo gangara to babu karbar tuba a wannan lokacin kuma babu kubuta

Kuma wancan shi ne fadinsa mai girma da daukaka a karshen wannan Ayar

Kuma tuba bata kasance ba ga wadanda suka aikata munanan aiki har said a mutuwa ta zowa dayansu sai ya ce: lalle ni na tuba a yanzu

Zuwa karshen ayar

 Lokacin yankewar tuba daga rayuwar Duniya

Yaushe ne lokacin yankewar tuba daga rayuwar Duniya

AllahMadaukakin Sarki ya ce:

A ranar da sashin Ayoyin Ubangijinka suke zuwa, Imanin rai wanda bai kasance ya yi imanin ba a gabani, ko kuwa ya yi tsiwirwirin wani Alheri, ba ya Amfaninsa

Kuma acikin sahihul Bukhari Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: lahaira ba zata tashi ba har sai rana ta fito daga mafadartato idan ta fito mutane suka ganta sai suyi imani baki dayansu kuma a wannan lokaci rai imaninta ba zai amfanar da ita ba

Sannan ya karanta Ayar,kuma hakika ya zo a cikin ma’anarta hadisai masu yawa daga jama’a na daga sahabbai daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cikin iyaye mata da makamantansu

Safwan dan Assal y ace: na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: lalle Allah ya bude wata kofa a yamma fadinta tafiyar shekara arba’in ne saboda tuba ba za’a rufeta ba har sai rana ta fito daga gareta.

Tirmizi ne ya rawaito shi da nasaa’I da dan majah a cikin wani hadisi mai tsayi.

 Hukuncin wanda ya mutu daga cikin masu dayanta Allah yana mai zarcewa a bisa manyan sabo

Maye Hukuncin wanda ya mutu daga cikin masu dayanta Allah yana mai zarcewa abisa manyan sabo

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

Kuma muna sanya ma’aunan adalci ga ranar kiyama, saboda haka ba a zaluntar raid a kome. Kuma koda ya kasance nauyin kwaya daga komayya ne mun zo da ita.kuma mun isa zama masu Hisabi

kuma Allah Madaukaki ya ce

a wadannne Abubuwan da ake kankare Manyan Zunubai da da kanana da su

kuma Allah Madaukaki ya ce

A ranar da kowane rai yake samun abin day a aikata daga alheri, a halarce,da kuma abin da ya aikata daga alheri

kuma Allah Madaukaki ya ce

A ranar da kowane rai yake samun abin day a aikata daga alheri, a halarce,da kuma abin da ya aikata daga alheri

Kuma ya ce:

Kuma kuji tsoron wata Rana wacce kuke komawa zuwa ga Allah sannan a sakawa kowace Rai da abinda ta aikata kuma ba za'a Zalunce su ba

kuma Allah Madaukaki ya ce

A ranar nan mutane za su fito daban-daban domin a nuna musu aiyukansu. to Wanda ya aikata gwargwadon kwayar zarra na alheri zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon kwayar zarra na sharri zai gan shi

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Wanda aka binciki hisabinsa za’a yi masa Azaba

Sai A’isha Allah ya yarda da ita ta ce da shi shin ba Allah ne yake cewa: to da sannu za’a yi musu hisabi hisabi mai sauki? Sai ya ce haka ne,kadai wannan bujirowa ne kuma sai dai cewa duk wanda aka bincike hisabinsa za’a yi masa azaba

Kuma hakika mun gabatar da nassoshi game da tashi da halayen matsaya da ma’auni da bude littattafai da bujirowa da hisabi da siradi da ceto da kuma makamantansu abin da ake sani das hi fifikon darajojin mutane, da kuma bayyanar halayensu a cikin lahira ta gwargwadon fifikonsu a gidan duniya cikin biyayyarsu ga Ubangijinsu, da kuma kishiyarta na daga mai tserewa da mai tsakaitawa da kuma mai zaluntar kansa;

Idan kasan wannan to kasani lalle abin da ayoyin kur’ani da sunnonin annabta suka tabbatar kuma magabata na kwarai da na farko daga sahabbai da wadanda suka bisu da kyautatawa daga shugabannin tafsiri da hadisi da sunna suka tafi a kai cewa: masu sabo daga ma’abota tauhidi dabaka uku ne:

Ta farko: jama’ar da kyawawansu suka rinjayi munanansu to wadannan za su shiga Aljanna kuma wuta ba za ta shafe su ba har abada.

Ta biyu: jama’ar da kyawawansu da munanansu suka yi dai-dai munanansu ta takaita da su ga shiga Aljanna kuma kyawawansu ta tsallakar da su ga shiga wuta, wadannan su ne ma’abota bango wadanda Allah ya ambata cewa su ne wadanda ake tsayar da su tsakanin Aljanna da wuta iya lokacin da Allah ya nufi a tsayar da su sannan a yi musu izinin shiga Aljanna kamar yadda Allah ya fada bayan ya bada labara da shigar yan Aljanna Aljanna da kuma shigar yan Wuta Wutarkuma za’a kira su daga cikinta

Ya ce:

Kuma a tsakaninsu akwai wani shamaki, kuma a kan A’araf akwai wasu maza suna sanin kowa da alamarsu: kuma suka kirayi abokan Aljanna cewa: “Aminci ya tabbata a kanku: “bas u shigeta ba, alhali kuwa su, suna tsammani. Kuma idan aka juyar da gannansu wajen abokan wuta, su ce: “ ya Ubangijinmu! Kada ka sanya mu tare da mutane azzalumai

Zuwa fadin sa:

Ku shiga Aljanna, babu tsoro a kanku, kuma ba ku zama kuna bakin ciki ba.

Jama’a ta Uku : jama’a ne da suka hadu da Alllah suna masu dogewa abisa kaba’irar sabo da Alfasha amma a tare da su akwai asalin tauhidi da imani to sai munanansu suka rinjayi kyawawansu  To wadannan su ne wadanda za su shiga Wuta na gwargwadon zunubansu to daga cikinsu akwai wanda zata kamashi zuwa guiwoyinsa,

Kuma akwai wanda zata kamashi zuwa rabin kaurinsa da wanda zata kamashi zuwa guiwoyinsa har cewa daga cikinsu akwai wanda Allah bai haramta wuta daga gare shi ba sai dai kawai bigiran sujjada, wannan jama’ar su ne wadanda Allah madaukaki yake bada ceto a cikinsu ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma waninsa a bayansa daga Annabawa da waliyai da mala’iku da wadanda Allah ya so day a girmamashi, sai Allah ya yi musu wata iyaka sai su fitar dasu sannan ya kara yi musu wata iyakar sai su fitar dasu

sannan hakanan sai su fitar da wanda ya kasance a zuciyarsa akwai gwargwadon nauyin zinare na daga alheri, sannan wanda ya kasance a zuciyarsa akwai gwargwadon rabin nauyin dinare na daga alheri sannan wanda ya kasance a zuciyarsa akwai nauyin kwayar komaiya na daga alheri, zuwa su fitar daga cikinta wanda ya kasance a zuciyarsa akwai misalin nauyin kwayar zarra na daga alheri izuwa mafi koma baya daga misalin kwayar zarra izuwa masu ceton su ce Ubangijinmu bamu bar wani alheri a cikinta ba kuma ba daya wanda zai dawwama a wuta cikin wadanda suka mutu abisa tauhidi, kuma koda yayi kowane aiki, sai dai cewa duk wanda ya kasance mafi girman imani daga cikinsu kuma mafi saukin zunubi zai kasance mafi saukin azaba a cikin wuta kuma mafi karancin zama a cikinta kuma mafi saurin fita daga gareta, kuma duk wanda ya kasance mafi girman zunubi kuma mafi raunin imani zai kasance da kishiyar hakan.

Kuma hadisai a cikin wannan babi ba zasu kididdigu ba saboda yawansu kuma izuwa haka ne Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi nuni da fadinsa

Wanda y ace : la’ilaha illallahu zata amfane shi wata rana daga zamani abinda zai same shi zai same shi kafin haka

Wannan wani mukami ne wanda fahimtu suka bace a cikinsa kuma diga digai suka zame a cikinsa, kuma suka yi sabani a cikinsa sabani mai yawa to sai Allah ya shiryi wadanda suka yi imani ga abin da suka yi sabani a cikinsa na daga gaskiya da izininsa kuma Allah yanaa shiryar da wanda ya so zuwa ga hanya madaidaiciya

 Shin haddi kaffara ne ga wanda akayi wa?

?Shin haddi kaffara ne ga wanda akayi wa

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce a gefensa akwai wasu jama’a daga sahabbansa:ku yi min mubaya’a abisa baza ku tara Allah da wani abu ba kuma ba za ku yi sata ba kuma ba za ku yi zina ba kuma ba za ku kashe ‘ya’yanku ba kuma ba za ku zo da wata karya da kuke kirkirawa a tsakanin hannuwanku da kafafunku kuma ba za ku saba da wani abu da aka sani na shari’a ba to wanda ya cika daga gareku to ladansa yana wajan Allah, kuma wanda ya yi wani abu daga wancan sannan Allah ya suturta shi to shi yana ga Allah in ya so ya yi masa afuwa,in kuma ya sosai ya yi masa ukuba yana nufin ban da shirka Ubadat ya ce: sai muka yi masa mubaya’a abisa haka.

 Hadawa tsakanin hadisan azabar Allah ga masu yin zunubi da kuma afuwarsa a gare su

Yaya za’a hadatsakanin fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cikin wannan hadisin to shi izuwa Allah yake in ya so ya yi afuwa a gare shi, in kuma ya soya yi masa ukuba da kuma tsakanin abinda ya gabata daga cewa wanda munanansa suka rinjayi kyawawansa zai shiga wuta?

Ba mai korewa a tsakaninsu domin cewa wanda Allah ya so da ya yi masa afuwa sai ya yi masa hisabi sassauka wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara da bijurowa kuma ya fada a cikin siffanta shi dayan ku zai dinga kusantar Ubangijinsa mai girma da daukaka har sai ya saukar masa da kariyarsa, to sai ya ce: ka aikata kaza da kaza sai ya ce: haka ne sai ya kara cewa ka aikata kaza da kaza sai y ace : haka ne sai ya tabbatar masa sannan y ace: lalle na suturta ka a cikin duniya, kuma ni na gafarta maka ita a yau amma kuma wadanda za su shiga wuta da zunubinsu to su ne wadanda ake bincika hisabinsu kuma hakika tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace: wanda aka yiwa binciken hisabi to za’a yi masa azaba

 Hanya madaidaiciya wanda Allah madaukaki ya umarce mu da binta kuma ya hane mu ga bin watanta

Wacce ce hanya madaidaiciya wanda Allah madaukaki ya umarce mu da binta kuma ya hane mu ga bin watanta

Shi ne Addinin musulunci wanda ya aiko manzanninsa da shi, kuma ya saukar da littattafansa da shi kuma ba zai karbi waninsa ga daya ba kuma ba wanda zai tsira sai wanda ya bishi, kuma duk wanda ya bi waninsa hanyoyi za su karkasu a kansa, kuma hanyoyi za su rarrabu da shi

Allah Madaukakin Sarki ya ce

Kuma lalle wannan ne tafarkina, madaidaici sai ku bi shi kuma kada ku bi wasu hanyoyi, su rarrabu da ku daga barin hanyata

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zana wani zane sannan y a ce: wannan itace hanyar Allah madaidaiciya kuma ya kara zana wani zanen a damansa da hagunsa, sannan ya ce: wannan hanyoyin babu wata hanya daga gareta face akwai Shaidan yana kira zuwa zuwa gare shi sannan ya karanta “kuma lalle wannan ne tafarki na, madaidaici sai ku bi shi kuma kada ku bi wasu hanyoyi,su rarrabu daku daga barin hanyata

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Allah ya buga misalin hanya madaidaiciya kuma abisa geffan hanyar akwai bangwaye guda biyu acikinsu akwai wasu kofofi budaddu, kuma abisa kofofin akwai labulaye sakakku kuma abisa kofar hanya akwai wani mai kira yana cewa: yak u mutane ku shiga wannan hanyar madaidaiciya baki dayanku, kuma kada ku rarrabu da kuma wani mai kiran yana kira ta birbishin hanyar, to idan mutum ya nufi zai bude wani abu daga wadannan kofofin sai y ace kaitonka kada ka bud eta domin cewa kai idan ka budeta zaka shigeta,

To hanyar ita ce musulunci bangwayen biyu su ne dokokin Allah kuma kofofin budaddu su ne abubuwan da Allah ya haramta, kuma wancan mai kiran a kan hanyar shi ne littafin Allah, wanda yake kira a birbishin hanyar shi ne wani mai wa’azin Allah a cikin zuciyar kowane Musulmi.

 Abin da zai zo da shi wajan bin hanya madaidaiciya da kuma kubuta daga karkacewa ga barinta

Da menene zai bi hanya madaidaiciya da kuma kubuta daga karkacewa ga baranta

Wancan ba ya samuwa sai ta hanyar riko da Alkur’ani da sunna, tafiyarwa irin tafiyarwarsu da kuma tsayawa nanga iyakokinsu, da kuma haka ne ake samun tsiraituwar tauhidin Allah da kuma tsiraituwar bi ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Kuma wadanda suka bi Allah da manzo to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni’ima a gare su daga Annabawa da Siddikai da Shahidai da managartan bayi kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya.

Kuma wadan nan da aka yi ni’ima a gare su da aka ambata anan a rarrabe su ne wadanda aka raba hanyar izuwa gare su acikin surar fatiha da fadinsa madaukaki

Ka shiryar damu hanya madaidaiciya hanyar wadanda ka yi ni’ima a gare su,ba wadanda aka yi wa fushi ba, kuma ba batattu ba

Kuma babu wata ni’ima ga bawa mafi girma wacce takai ta a shiryar das hi izuwa hanya madaidaicya, da kuma nisanta shi daga hanyoyi masu batarwa, hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bar al’umarsa akan hakan kamar yanda ya fada tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: na barku akan hanya mai haske darenta kamar ranarta ne babu mai karkata ga buranta a baya na sai halakakke.

 Bidi’o’i fararru

Menene kishiyar sunna?

Kishiyarsu su ne bidi’o’i fararru kuma ita ce shari’ar da ba Allah ne ya yi izini da ita ba kuma ita ce wacce Annabi tsira da amincin Allah yake nufi da ita da fadinsa “wanda ya farar da wani abu a cikin addininmu wannan, wanda babu daga gare shi to shi abin juyarwa ne “da kuma fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi “ina horanku da sunnata da sunnar halifofina shiryayyu ababan shiyarwa a bayana, ku yi ruko da ita, kuma ku yi cizo akanta da fika, kuma ina muku hani da fararrun al’amura, domin cewa kowa ne fararran abu bata ne sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi nuni izuwa afkuwarta da fadinsa “da sannu al’umata za ta karkasu izuwa kaso saba’in da uku dukkansu suna cikin wuta face guda daya kuma ya ayyana tada fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi su ne wadanda suka kasance akan misalign abin da nake kai da sahabbaina” kuma hakika Allah madaukaki ya barrantar da shi daga ma’abota bidi’a da fadinsa “lalle wadanda suka rarraba addininsu kuma suka kasance jama’a jama’a ba ka tare da su a cikin wani abu kadai al’amarinsu yana ga Allah…

 Kashe kashen bidi’a ta izna da shigarta ga Addini

Izuwa kaso nawa bidi’a ta kasu ta izna da shigarta ga Addini?

Ta kasu zuwa kaso biyu: bidi’a mai kafirtarwa da kuma bidi’a komawacce bata kai waccan ba

 Bidi’o’I masu kafirtarwa

Mecece bidi’a mai kafirtarwa?

Ita tana da yawa amma yadda take, wanda ya yi inkarin wani al’amari wanda aka hadu akansa kuma yake da tawaturi a shari’a kuma larura ne a san shi a addini; domin cewa hakan karyatawa ne ga Alkur’ani da kuma abin da Allah ya aiko manzanninsa da shi kamar bidi’ar jahamiyyai a cikin inkarin siffofin Allah mai girma da daukaka, da kuma fadi da halittar kur’ani ko halittar kowace siffa daga siffofin Allah madaukaki da kuma inkarin cewa Allah ya riki Ibrahim badadayi kuma ya yi Magana da Musa Magana sosai da wadansun wadannan.

Da kamar bidi’ar ‘yan kadariyya cikin inkarin ilimin Allah madaukaki da aiyukansa da hukuncinsa da ikonsa, da kamar bidi’ar ‘yan tajsimi wadanda suke kamanta Allah madaukaki da halittarsa da wadansu wadannan na daga son zuciya, sai dai kuma wadannan akwai daga cikinsu wanda aka san cewa ainihin manufarsa shi ne rushe Addini, da san ya wa ahalinsa shakku a cikinsa to wannan abin yankeawa ne ga kafircinsa bari ma dai shi manisaci ne ga Addini kuma yana daga manyan makiyansa, kuma wadansu ababan rudarwa ne to wadannan kadai ana hukunci da kafircinsu bayan an tsayar musu da dalili a kansu da lazimta musu ita.

 Bidi’a wacce bata kafirtarwa

Wacce bidi’a ce bata kafirtarwa

Ita ce wacce bata kasance kamar waccan ba ta daga abinda bai lazimta daga gare shi ba karyatawa da Alkur’ani bada kuma karyata abin da Allah ya aiko manzanninsa da shi ba kamar ‘yan marwaniyya wacce sahabbai masu falala suka yi inkarinta,kuma ba su tabbatar da su akanta ba kuma ba su kafirta su da wani abu daga gareta ba,kuma ba su cire hannu ba wajan yi mu su mubaya’a saboda ita ba, kamar jinkirtawarsu ga sashin wasu sallolin izuwa karshen lokutanta, da kuma gabatarwarsu huduba kafin sallar idi da zama a cikin ita dai wannan hudubar a cikin juma’a da watanta, da kuma zaginsu ga sashin sahabbai akan minbarai da makamancin wancan daga abin da babu gare su na i’atikadi na shari’a bari dai kawai sai dai wani nau’I na tawili, da sha’awa sha’awe na rai, da manufofi na Duniya.

 Kasha kashen bidi’a ta fuskar abin da take fadawa a cikinsa

Nawane kashe kashen bidi’a ta fuskar abin da take fadawa a cikinsa

Ta kasu zuwa bidi’o’i na cikin ibadu da bidi’o’i na cikin mu’amaloli.

Kashe kashen bidi’o’i na ibadu

Izuwa kaso nawa bidi’o’i suka kasu a cikin ibadu?

Zuwa kaso biyu:

Na farko: yin bauta da abin da Allah bai izini a bauta masa da shi ba yanke kamar bautar da jahilan sufaye suke yi da alolin wasa na rawa da tafi da rera waka, da nau’ikan kayan kida da makamantansu na daga abubuwan da suke a cikinsu akwai koyi da aikin wadanda

Allah madaukaki ya fada a kansu “ kuma sallarsu a wurin ‘Dakin ba ta kasance ba face fito da tafi.

Na biyu: yin ibada da abin da asalinsa abin shara’antawa ne sai dai kuma an sanya shi ba’a muhallinsa ba kamar bude kai a misali, shi a lokacin da ake cikin ihrami ibada ce, to idan wanda ba muharrami ba ya aikata shi a cikin Azimi ko a cikin Salla ko a waninsu da niyyar yin ibada ya kasance bidi’a haramtacciya.

Haka nan da kuma aikata sauran ibadu ababan shara’antawa a inda ba’a shara’nta ayi su acikinsa ba, kamar sallolin nafila a cikin lokutan hani da kuma azimtar ranar shakku, da azimtar idi biyu da makamantan wadannan.

Halayen bidi’a tare da ibadar da ta afku a cikinta

Nawa ne halayen bidi’a tare da ibadar da ta afku a cikinta?

Tana da halaye biyu

Ta farko: ta bata ta baki dayanta Kamar wanda ya kara a cikin sallar asubahi raka’a ta uku ko a cikin magariba ya kara ta hudu cikin wacce take hudu ya kara ta biyar da gangan, haka nan cewa idan ya rage misalign hakan.

Hali na biyu: cewa bidi’ar ta baci ita kadai, kamar inda take batatta kuma aikin da ta afku a cikinsa ya kubuta kamar wanda ya kara a cikin alwala abisa wanki uku to lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai c eta baci ba bari dai ya ce wanda ya kara a kan haka to hakika ya munana kuma ketara haddi kuma ya yi zalunci

 Bidi’o’I a cikin mu’amaloli

Mecece bidi’a a cikin mu’amaloli?

Ita ce sharadanta abin dab a ya cikin littafin Allah kuma bay a cikin sunnar manzansa kamar shardanta walicci ga wanda ba shi ya ‘yanta ba kamar yadda yake a cikin kissar Barira lokacin da ahalinta suka sharadanta walicci, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsaya sai ya godewa Allah ya yi yabo a gare shi sannan ya ce: bayan haka meye ruwan wasu mazaje da zasu dinda sharadanta wani sharadiwanda ba ya cikin littafin Allah, to dukkan wani sharadi da ba ya cikin littafin Allah to shi batacce ne, ko da ya kai sharadi dari kuma hukuncin Allah shi ne mafi gaskiya kuma sharadin Allah shi ne mafi inganci, meye ruwan wasu mutane daga cikinku wanda dayansu yake cewa: na ‘yantaka kai wane kuma waliccinka yana wajena kadai walicci ga wanda ya ‘yanta ne. haka nan da kowane sharadin da aka halatta haram ko aka haramta halal.

 Abinda ya wajabta a lazimce shi a cikin sahabban Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ahalin gidansa?

Menene ya wajabta a lazimce shi a cikin sahabban Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ahalin gidansa?

Abin da yake wajibi a kanmu a gare su amintar da zuciyoyinmu da harsunanmu a gare su da kuma yada falalolinsu da kamewa ga barin kura kuransu da kuma abin day a afku a tsakaninsu, da daukaka sha’aninsu kamar yadda madaukaki ya daukaka da ambatonsu a cikin Attaura da Injila da Kur’ani

Kuma hadisai ingantattu cikin littattafai shahararru na daga manyan da ma wadansunsu sun tabbatar da falalolinsu,

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

Muhammad Manzan Allah ne. kuma wadannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganin su suna masu ruku’u masu sujjada, suna neman falala daga Allah, da yardarsa. Alamarsu tana a cikin fuskokinsu, daga kufan sujjada. Wannan shi ne sifarsu, a cikin Attaura. Kuma siffarsu a cikin Injila, it ace kamar tsiron shuka wanda ya fitar da reshensa, sa’an nan ya karfafa shi, ya yi kauri, sa’an nan ya daidaita a kan kafafunsa,yana bayar da sha’awa ga masu shukar, domin(Allah) ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah ya yi wa’adi ga wadanda suka yi imani, kuma suka aikata aiyukan kwarai, daga cikinsu, da gafara da sakamako mai girma.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma wadanda suka yi imani kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihadi, a cikin hanyar Allah, kuma da wadanda suka bayar da masauki, kuma suka yi taimako, wadannan su ne muminai da gaskiya, suna da gafara da wani arziki na karamci.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Kuma masu tserewa na farko daga Muhajirai da Ansar da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda daga gare su su kuma sun yarda daga gare shi, kuma ya yi masu tattalin gidajen Aljanna: koramu suna gudana a karkashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma.

kuma Allah Madaukaki ya ce

Lalle ne hakika Allah ya karbi tubar Annabi da Muhajirai da Ansaru wadanda suka bi shi a cikin sa’ar tsanani…

zuwa Karshen Ayar

kuma Allah Madaukaki ya ce

Ga matalauta masu hijira wadanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah da kuma yarda, kuma suna taimakon Allah da Manzansa, wadannan su ne masu gaskiya. Da wadanda suka zaunar da gidajensu (ga Musulmi) kuma (suka zabi) imani, a gabanin zuwansu, suna son wanda yayi hijira zuwa gare su, kuma ba su tunanin wata bukata a cikin kirazansu daga abin da aka bai wa muhajirai, kuma suna fifita wadansu akan kawunansu, kuma ko da suna da wata larura…

Zuwa karshen ayar

Mun sani kuma mun kudirce da cewa Allah madaukaki ya yi duba ga ma’abota Badar, sai y ace: ku aikata abin da kuka so saboda hakika na gafarta muku kuma sun kasance dari uku da goma sha uku zuwa sha tara, kuma da cewa shi ba zai shigar da daya daga cikin wadanda suka yi mubaya’a a karkashin bishiyar nan kadai dai Allah ya yarda da su kuma suma sun yarda da shi, kuma sun kasance su dubu daya da dari hudu ko kuma aka ce da dari biyar

Allah Madaukaki ya ce

Lalle ne Allah ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubaya’a a karkashin bishiyar nan domin ya san abin da ke cikin zuciyarsu

Kuma muna masu shaidawa da cewa su su ne suka fi falala a karnonin wannan al’ummar kuma lalle wanda ya ciyar da da misalin dutsen Uhudu na zinare daga wadanda suke bayansu ba zai kai mudu daya na dayansu ba, kuma ba zai kai rabinsa ba, tare da kudircewa da su ba wadanda basa sabo ne ba, kadai dai za su iya yin kuskure, kuma sai dai cewa su mujtahidai ne ga wanda ya yi daidai daga cikinsu zai sami lada biyu ga wanda kuma ya yi kuskure yana da lada guda daya na ijtihadinsa, kuma kuskurensa abin gafartawa ne, kuma suna da falaloli da managartan aiyuka da rigaye wanda zai tafiyar da mummunan abin da ya afku daga gare su in ya farun, shin najasa kankanuwa tana canja kogi idan ta fada a cikinsa? Allah ya yarda da su kuma sun yardar da shi.

Haka kuma Magana a cikin Matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Ahalin gidansa wadanda Allah ya tafiyar da kazanta ga barinsu kuma ya tsarkake su tsarkakewa, kuma mu barrantu ga duk wanda ya sanya a cikin kirjinsa ko harshensa wani abu mummuna a bisa sahabban Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da Ahalin gidansa ko a bisa daya daga cikinsu, kuma mu shaidar da Allah madaukaki a bisa sonsu da jibintarsu, da kariya a gare su gwargwadon ikonmu saboda kiyayewa ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi cikin wasiyyarsa ya yin da yake cewa: “ kada ku dinga zagin sahabbaina ina yi muku magiya a cikin sahabbaina, kuma ya ce: lalle na bari a cikinku nauyaya guda biyu, na farkonsu littafin Allah to ku karbi littafin Allah kuma ku yi ruko das hi sannan ya ce: da kuma Ahalin gida na ina tunasar da ku Allah a cikin Ahalin gida na. hadisin yana cikin Bukhari da Muslim da wadansunsu.

 Mafifitan Sahabbai a Jumlace?

Su wanene mafifitan sahabbai a jumlace?

Mafifitansu su ne marigaya na farko daga Muhajirai da Ansarawa sannan ma’abota Badar,sannan ma’abota Uhudu, sannan masu bai’atu ridwan, sai wadanda suke bayansu sannan kuma wadanda suka ciyar kafin cin nasara kuma ya yi yaki, wadancan ne mafifita girman daraja bisa ga wadanda suka ciyar daga baya kuma suka yi yaki. Kuma dukkansu Allah ya yi musu tanadin sakamako kyakkyawa

 mafifitan sahabbai a Bayyane?

Su wanene mafifitan sahabbai a Bayyane?

Abdullahi Dan Umar - Allah ya yarda da su

Mun kasance a lokacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba ma hada Abubakar da daya, sannan Umar, sannan Usman,sannan mu bar sauran sahabban Annabi babu fifitawa a tsakaninsu

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Abubakar a cikin kogon nan menene zatonka da mutum biyu wanda Allah ne na ukunsu

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Da zan riki wani badadayi daga al’umata da na riki Abubakar badadayi sai dai kuma dan’uwa na ne kuma sahabina.

Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi

Lalle ne Allah ya aiko ni izuwa gare ku sai kuka ce na yi karya sai Abubakar ya ce: ka yi gaskiya kuma ya yi min muwasati da kansa da dukiyarsa to shin ba za ku bar min Abokina ba? ya fadi haka sau biyu

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Ji ya dan Haddabi na rantse da wanda raina yake hannunsa Shaidan ba zai ganka ka bi wata hanya ba face ya bi wata hanyar da ba hanyarka ba

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Lalle ne hakika ya kasance a cikin wadanda suka zo kafin ku masu zantarwa, to in akwai a ciki al’umata to cewa Umar ne

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce a cikin Maganar Kura da Saniya domin cewa ni na yi imani da shi da Abubakar da kuma Umar da basu ba sannan: ya yin da Usman ya tafi izuwa Makka lokacin bai’ati ridwan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi isara da hannunsa na dama wannan shi ne hannun Usman sai ya buga ta a hannunsa sai ya ce: wannan ce ta Usman

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Dukkan wanda ya tone rijiyar Rumat to yana da Aljanna to sai Usman ya tone ta

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Dukkan wanda ya kintsa rundunar al’usra to yana da Aljanna to sai Usman ya kintsa ta

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Ku saurara bana ji kunya daga wanda Mala’iku suke jin kunya daga gare shi

Kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada ga Aliyu Allah ya yarda da shi: kai daga gare ni ne kuma ni daga gare ka ne. kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bada labara a kansa cewa shi yana san Allah da Manzansa kuma Allah da Manzansa suna sansa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Wanda na kasance majibincinsa to Aliyu ma majibincinsa ne

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Shin ba zaka yarda ka zamo min kamar yadda Annabi Haruna yak e ga Musa ba sai dai babu wani Annabi bayan ni

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Goma suna Ajanna Annabi yana Aljanna, Abubakar ma yana Aljanna, Umar ma yana Aljanna, Usman ma yana Aljanna, Aliyu ma yana Aljanna, Dalha ma yana Aljanna, Zubair dan Auwam ma yana Aljanna, Sa’ad dan Malik ma yana Aljanna, Abdurrahman dan Auf ma yana Aljanna, Sa’id dan Zaid ya ce: da kuma na so da na jiyar da kai na goman yana nufin kansa Allah ya yarda da su baki daya

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Mafi jin kan al’umata ga al’umata Abubakar mafi tsananinta a cikin addini Umar mafi gaskiyarta kunya Usman, mafi saninta ga halal da haram Mu’az dan Jabal, mafi karatunta ga littafin Allah Ubayyu, mafi saninta ga rabon gado Zaid dan Sabit, kuma kowace al’umma tana da amintacce to aminin wannan al’umma shi ne Abu Ubaida dan Aljarrah

Kuma tsira da amincin Allah ya ce: a cikin Hasan da Husain cewa su ne shugabannin samarin Aljanna, kuma sune abin kanshinsa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace

Ya Ubangiji lalle ne ni ina sonsu to ka so su kuma y ace a cikin Hasan lalle wannan shugaba ne kuma da sannu Allah zai yi sulhu da shi a tsakanin jama’a biyu manya na musulmai to haka al’amarin ya kasance kamar yadda ya fada

Kuma ya fada ga mahaifiyarsu cewa ita ce shugabar matan Aljanna

Kuma hakika ya tabbata ga da yawa daga sahabbai falaloli a bisa gamewa da kuma a daidaiku da yawan da ba za’a iya iyakancewa ba

Kuma ba ya lazimta daga tabbatar da wata falala ga dayansu cikin wani abu da ya kasance ya fi falala daga sauran daga kowace fuska ba face halifofin nan hudu,

Amma ukun saboda hadisin Dan Umar wanda ya gabata, amma kuma Aliyu saboda ijma’in ma’abota sunna cewa shi ya kasance a bayansu mafificin wadanda suke fuskar kasa.

 Tsawon Halifanci bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

Nawa ne muddar halifanci bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi?

Abu dawuda ya rawaito da waninsa daga Sa’id dan Jamhan daga Safinah ya ce manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace: halifancin annabta shekara talatin ce, sannan Allah ya bada mulki ga wanda ya so to wancan ya kasance muddar halifancin Abubakar da Umar da Usman da Ali Allah ya yarda da su, Abubakar ya yi shekara biyu da wata uku, Umar kuma shekara goma da wata shida, Usman kuma shekara goma sha biyu, Aliyyu kuma shekara hudu da wata tara,kuma shekara talatin ta cika da mubaya’ar Hasan dan Aliyyu wata shida kuma farkon sarakunan musulunci.

Mu’awiyya Allah ya yarda da shi shi ne mafi alherinsu kuma mafificinsu sannan mulki matsananci ya kasance a bayansa har izuwa Umar dan Abdul Aziz ya zo Allah ya yarda das hi ahlul sunna sun kidanya shi halifa na biyar saboda tafiyarwarsa irinta halifofi shiryaryu ce.

 Dalili a bisa halifancin halifofi shiryayyu guda hudu a jumlace

Menene dalilin halifancin wadannan halifofi hudu a jumlace?

Dalilai a kan haka suna da yawan da ba za su lissafu ba to suna daga cikinsu: takaice muddarta a shekara talatin sai ta kasance muddar shugabancinsu.

Kuma yana daga cikinta abin day a gabata na daga fifita su a bisa waninsu da kuma fificinsu a bisa jerin halifancinsu,Kuma yana daga cikinta abin da Abu dawuda ya rawaito da waninsa daga Samurata dan Jundub cewa wani Mutum ya ce ya Manzan Allah lalle ne ni na ga kamar wata guga ta sakko daga sama sai Abubakar ya zo ya riketa da jibin goshi sai ya sha sha mai rauni, sannan Umar ya zo ya riketa da jibin goshi sai ya sha har ya koshi, sannan Usman ya zo sai ya riketa da jibin goshi, sai ya sha har ya koshi sannan Aliyyu ya zo sai ya riketa da jibin goshi, sai ta shinfidu sai ya yayyafa a kansa wani abu daga gar eta, kuma yana daga cikinta wanda shi ne ma mafi karfinta ijma’in wadanda ake dogara da ijma’insu abisa halifancin wadannan hudun,kuma ba wanda yake suka da halifancin daya daga cikinsu face batacce dan bidi’a.

Dalili a bisa halifancin halifofi shiryayyu su hudu a jumlace

Dalili a bisa halifancin Abubakar da Umar Allah ya yarda da su a jumlace

Dalili a bisa halifancin Abubakar da gabatar da shi akan kowa

Mene ne? Dalili a bisa halifancin Halifofi Uku a Jumlace

Dalilai abisa haka suna da yawa daga cikinsu abin da ya gabata a baya, kuma yana daga ciki hadisin Abubakar Allah ya yarda da shi cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada wata rana wanene daga cikinku ya yi mafarki? Sai wani mutum ya ce ni naga wani ma’auni ya sauka daga sama sai aka auna ka da Abubakar sai ka rinjayi Abubakar, sai aka auna Umar da Abubakar sai Abubakar ya yi rinjaye, sai aka auna Umar da Usman sai Umar ya yi rinjaye sannan aka dauke ma’aunin sai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce wani Mutum salihi ya yi mafarki a daren nan cewa Abubakar an rataya ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma an rataya Umar ga Abubakar kuma an rataya Usman ga Umar. Kuma duk hadisan nan biyu suna cikin littattafan sunan.

Dalili a bisa halifancin Abubakar da Umar a jumlace

Menene dalili a bisa halifancin Abubakar da Umar Allah ya yarda da su a jumlace?

Menene dalili abisa halifancin Abubakar da gabatuwarsa a cikinta?

Dalilai akan haka ba za su kirgu ba yana daga cikinsu abin da ya gabata, yana daga cikinta abin da yake cikin sahihul Bukhari da Muslim cewa wata mata ta zo wa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya yi mata umarni da ta koma sai t ace ya kake gani idan na zo ban same ka ba? –kamar ka ce ita tana nuni da mutuwa ne- sai mai tsira da amincin Allah ya ce: in ba ki same ni ba to ki je wa Abubakar kuma yana daga ciki abin da yake cikin sahihu Muslim daga A’isha Allah ya yarda da ita t ace Manzon Allah y ace da ni ki kira min mahaifinki dad an uwanki har na rubuta wani rubutu domin cewa ni ina jin tsoran kar wani mai burin ya yi buri, mai fada ya ce ni ne mafi cancanta kuma Allah ya ki da muminai sai dai Abubakar kuma haka nan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada a cikin gabatar da shi a cikin salla a lokacin rashin lafiyar mutuwarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma baki dayan sahabban Manzan Allah na daga Muhajirai da Ansaru da wadanda suke bayansu suka hadu abisa yi masa mubaya’a.

 Dalili abisa gabatar Umar a cikin halifanci bayan Abubakar

Menene dalili abisa gabatar Umar a cikin halifanci bayan Abubakar?

Dalilansa suna da yawa yana daga cikinsu abin day a gabata, kuma yana daga cikita fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi lalle cewa ni ban sani ba menene gwargwadon zamana a cikinku to ku yi koyi da wadanda suke baya na sai ya yi nuni izuwa Abubakar da Umar Allah ya yarda da su.

Kuma yana daga ciki hadisin fitina wacce take tashi kamar tashin kumfar kogi.

Huzaifa ya fada Allah ya yarda da shi ga Umar cewa tsakaninka da tsakaninta akwai wata kofa rufaffiya sai y ace shin bud eta za’a yi ko karyata? Sai ya ce: bari dai karya ta za’a yi sai Umar ya ce to b za’a kulleta ba. To kofar ta kasance Umar ne kuma karya shi kashe shi ba’a daukaka takobi a bayansa ba tsakanin Al’umma, kuma hakika al’umma ta hadu abisa gabatar da shi a cikin halifanci bayan Abubakar Allah ya yarda da su.

 Dalili abisa gabatar da Usman a bayan Abubakar da Umar a cikin halifanci

Menene dalili abisa gabatar da Usman a bayansu a cikin halifanci?

Dalilai abisa haka suna da yawa abin da ya gabata yana daga ciki, kuma suna daga cikinsu hadisin Ka’abu dan Ujrat ya ce Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ambaci wata fitina sai ya tabbatar da ita, sai wani Mutum yana mai rufe da kansa ya wuce sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace wannan a wancan lokacin yana kan shiriya sai na tashi sai Usman ya ruko min dantse na, sannan na fuskanci Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai nace wannan ya ce wannan. Ibnu Majah ne ya rawaito shi,

Kuma Tirmaizi ya rawaito shi daga Murrat dan Ka’ab kuma y ace hadisi ne mai kyau ingantacce

Kuma daga A’isha Allah ya yarda da ita ta ce: Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ya Usman idan Allah ya jibinta maka wannan lamari a wata rana sai Munafukai suka nufeka da ka cire rigarka wacce Allah ya sanya maka to kada ka cire shi yana fadar haka har sau uku,Ibn Majah ne ya rawaito shi da isnadi ingantacce kuma Tirmizi ya kyautata sh da Ibni Hibban cikin sahihinsa

Kuma ahlul shura sun hadu a bisa mubaya’arsa sannan kuma da sauran sahabbai, kuma farkon wanda ya fara yi masa mubaya’a Aliyyu ne Allah ya yarda das hi bayan Abdurrahman dan Auf sannan mutane baki daya bayansa.

 Dalili a bisa halifancin Aliyyu kuma shi ne mafi dacewarsa da gaskiya bayan Abubakar da Umar da Usman

Menene dalili a bisa halifancin Aliyyu da kuma dacewarsa da gaskiya a bayansu?

Dalilan wancan suna da yawa yana daga cikinsu abin da ya gabata kuma yana daga ciki fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Allah ya jikan Ammar jama’a ‘yan ta’adda za su kashe shi yana kiransu zuwa Aljanna, su kuma suna kiransa izuwa Wuta. kuma shi ya kasance yana tare da Aliyyu Allah ya yarda da shi sai ahalin Sham suka kasha shi, kuma shi yana kiransu izuwa sunna da jama’a, da kuma da’a ga shugaba na gaskiya Aliyyu dan Abi Dalib Allah ya yarda da shi, kuma hadisin yana cikin Bukhari.

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:

Wasu masu fita za su fita ta yadda a lokacin za’a sami wani bangare na mutane wanda sune mafi dacewa da gaskiyar bangare biyun za su yake su, to sai khawarijawa suka fita kuma sai Aliyyu Allah ya yarda da shi ya yake su lokacin yakin Nahrawan.Kuma shi ne mafi dacewa da gaskiya da ijma’in Ahlussunnah gaba daya Allah madaukaki ya jikansu.

 Abin da yake wajibi a yiwa shugabanni

Menene abin da yake wajibi a yiwa Shugabanni?

Abin da yake wajibi a yi musu shi ne yi musu nasiha ga shugabancinsu a bisa gaskiya, da yi musu da’a a cikinsa da umarninsu da shi da kuma tunasar da su cikin tausasawa, da yin salla a bayansu da jihadi tare da su, da bada sadakoki izuwa gare su da hakuri da su koda sun zalunci, da barin futa da takobi a kansu mutukar basu bayyana kafirci a sarari ba, kuma kada a rudu da yi musu yabo na karya a kansu, kuma a yi musa addu’a da gyara da dacewa.

 Dalili a bisa wajabcin da’a ga ma’abota al’amari

Me ne ne dalili akan haka?

Dalilai a bisa haka suna da yawa yana daga ciki fadinsa madaukaki “ ya ku wadanda suka yi imani ku yi da’a ga Allah kuma ku yi da’a ga Manzon da kuma da ma’abota al’amari daga cikinku

Fadin Annabi tsira da Aminci su tabbata a gare shi

Ku ji kuma ku yi da’a kuma koda an shugabantar muku da Bawa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Wanda ya ga wani abu day ake ki daga shugabansa, to ya yi hakuri a kansa domin cewa shi wanda ya rabu da jama’a koda tsawan shibiri ne kuma ya mutu face ya mutu mutuwa ta jahiliyya

Ubada Dan Al-samit Allah ya yarda dashi ya ce:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kira mu sai muka yi masa mubaya’a to yana daga cikin abin da ya rika a gurinmu mubaya’a a kan ji da kuma bi a cikin manishadinmu da kuma abin da muke ki, da matsinmu da yalwarmu da kuma zabi daga a kanmu, kuma kada mu yi jayayyar al’amari ga ahalinsa face in kun ga kafirci a bayyane a gurinku akwai dalili daga Allah a cikinsa

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Idan an sugabantar muku da Bawa mai yankakken hanci baki zai ja ku da littafin Allah to ku ji daga gare shi kuma ku yi da’a

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Yana kan mutum musulmi ji da kuma da’a a cikin abin da yake so ko yake ki sai dai in an umarce shi da sabo, to idan an umarce shi da sabo to babu ji kuma babu da’a, kuma ya ce kadai ana da’a ne a cikin abin da shari ta san da shi

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Kuma koda ya daki bayanka kuma ya karbi dukiyarka to ka ji kuma ka yi da’a

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Wanda da duk yake nufin rarraba kan wannan Al'ummar kuma shi yana cikinta to ko sare masa wuya da Takobi kuma ko waye shi.

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

Wanda ya cire hannu daga da’a ga Allah ranar Alkiyama ba shi da hujja, kuma wanda ya mutu kuma babu mubaya’a a cikin wuyansa ya mutu mutuwar jahiliyya

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce

“ Da sannu wasu shugabanni za su kasance kuna gane halayensu da aiyukansu kuma kuna kin wasunsu wanda ya ki ya barrantu wanda kuma ya musa ya kubuta kuma sai dai wanda ya yarda kuma yabi Suka ce ba ma yake su ba? Ya ce a’a matukar suna salla” da wadansu wadannan na daga hadisai kuma wannan dukkansa yana cikin sahihin Bukhari.

 A kan wa ya wajaba umarni da kyakkyawa da hani ga abin ki kuma menene darajojinsa?

A kan wa ya wajaba umarni da kyakkyawa da hani ga abin ki kuma menene darajojinsa?

Fadin Allah maigirma da Daukaka:

Kuma wata jama’a daga cikinku , su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umarni da alheri,kuma suna hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan su ne masu cin nasara

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ” wanda ya ga wani abin ki to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to ya canza shi da harshensa, idan ba zai iya ba to da zuciyarsa, kuma wancan shi ne mafi raunin imani “ Muslim ne ya rawaito shi

A cikin wannan babi a kwai ayoyin kur’ani da hadisan Annabi wadanda ba za su lissafu ba kuma dukkanita suna nuni da wajabcin umarni da kyakkyawa, da kuma hani ga abin ki a bisa duk wanda ya gan shi ba zai fadi ga barinsa ba sai dai in an sami waninsa ya yi shi kowanne da rabonsa, kuma duk lokacin da Bawa ya kasance mafi iko a bisa hakan kuma shi ne mafi sani ya kasance a kansa mafi zama wajibi, kuma ya fi lazimta a kansa kuma ba zai tsira ba ya yin saukar azaba ga ma’abota sabon sai dai masu hani ga buranta, kuma hakika mun kadaitawa wannan mas’ala da wata risala a kanta cikakkiya kuma isasshiya ga masu neman gaskiya godiya da baiwa na ga Allah.

 Hukuncin karamomin waliyai

Menene hukuncin karamomin Waliyai?

Karamomin waliyai gaskiya ne kuma shi ne bayyanar al’amari mai keta al’ada a bisa hannunsu wanda babu kallafawa a kansu a cikinsa kuma bai kasance ta hanyar tahaddi ba bari dai kadai Allah yana sanya shi a bisa hannunsu,kuma koda ba su san da shi ba kamar kissa ma’abota kogo, da kuma ma’abota fan dutse, da Juraiju malamin Yahudu kuma dukkansu Mu’ujizozi ne na Annabawansu, kuma saboda wannan ya kasance a cikin wannan al’umma a kwai mafi yawa da girma saboda girman mu’ujizozin Annabinta,da kuma karamarsa a wajan Allah mai girma da daukaka, kamar yadda ya afku ga Abubakar a lokacin ridda da misalin kiran da Umar ya yi wa Sariyat alhali shi yana kan minbari, kuma kiran ya isar masa shi yana Sham, da kuma misalin wasikar da ya aikewa ruwan Nilu na Misra sai ya gudana, da kuma misalin dokin Al-ala’u dan Al-habrami yayin da ya kutsa da ita cikin kogi lokacin yakin Rum, da misalin misalign sallar da Abu Muslimul khaulani ya yi a cikin wuta wacce Al’aswadul ansi ya hura masa ita da wadansun wadannan na daga abin day a afku ga da yawa daga cikinsu a zamanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da bayansa daga cikin zamanin sahabbai da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa da wadanda suke bayansu izuwa yanzu, kuma izuwa lokacin tashin kiyama,

Kuma dukkansu a hakika mu’ujizozi ne ga Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi domin cewa su sun sami wannan ne saboda binsa, to idan aka samu wani abu daga wannan ya afku ga wanda ba mai bin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba to wannan fitina ce da kuma rufa ido ba karama ba, kuma ba shi daga cikin waliyyan Allah bari dai kawai yana daga waliyyan Shaidan, muna neman kariya daga Allah.

 Waliyyan Allah

Su wanene waliyyan Allah?

Su ne dukkan wanda ya yi imani da Allah kuma yake jin tsoransa kuma yake bin Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi

AllahMadaukakin Sarki ya ce:

To lalle ne masoyan Allah babu tsoro a kansu, kuma ba za su kasance suna yin bakin ciki ba, sannan ya bayyana su sai ya ce: wadanda suka yi imani kuma suka kasance suna yin takawa

kuma Allah Madaukaki ya ce

Allah shi ne masoyin wadanda suka yi imani, yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske, kuma wadanda suka kafirta, masoyansu Dagutu ne, suna fitar da su daga haske zuwa ga duffai…

kuma Allah Madaukaki ya ce

Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da Manzansa, da wadanda suka yi imani, wadanda suke suna tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka kuma suna ruku’i. kuma wanda ya jibinci Allah da Manzansa da wadanda suka yi imani, to kungiyar Allah su ne masu rinjaye

Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:

Lalle cewa ahalin gidan wane su ba masoya na ba ne kadai masoya na su ne masu tsoran Allah

Alhasan Allah ya qara yarda da shi ya ce:

Wasu mutane sun yi da’awar son Allah to Allah ya jarrabe su da wannan ayar “ kace in kun kasance kuna son Allah to ku bi ni sai Allah ya so ku…

Shafi’I Allah ya qara yarda da shi ya ce:

Idan kuka ga mutum yana tafiya a kan ruwa ko kuma yana tashi a cikin sama, to kada ku gasgata shi kuma kada ku rudu das hi har sai kun san binsa ga Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

 Jama’ar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake nufi da cewa ita ce a kan gaskiya

Wacece jama’ar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake nufi da fadinsa: wata jama’a ba za ta gushe daga al’umata a kan gaskiya ba wanda ya saba musu ba zai cutar da su ba, har sai al’amarin Allah mai tsarki da daukaka ya zo.

Wannan jama’a ita ce rabon da zai tsira daga cikin rabuwa saba’in da uku kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya togace ta daga wadancan rabe rabe da fadinsa: dukkanninta suna cikin Wuta face guda daya kuma ita ce jama’ar,Kuma a cikin wata riwayar y ace: su ne wadanda suka kasance a bisa abin da nake kai a yau da sahabbaina,Muna rokon Allah madaukaki ya sanya mu a cikinsu, kuma kada ya zamar da zuciyoyinmu bayan ya shiryar damu, kuma ya bamu rahama daga wajansa lalle cewa shi ne mai yawan kyautaTsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin rinjaye, daga barin abin da suke siffantawa, kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai

Kuma a cikin wata riwayar y ace: su ne wadanda suka kasance a bisa abin da nake kai a yau da sahabbaina,

Muna rokon Allah madaukaki ya sanya mu a cikinsu, kuma kada ya zamar da zuciyoyinmu bayan ya shiryar damu, kuma ya bamu rahama daga wajansa lalle cewa shi ne mai yawan kyauta

Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka Ubangijin rinjaye, daga barin abin da suke siffantawa, kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai