ZIYARAR MASALLACIN ANNABI MAI AL-FARMA TARE DA FADAKARWA DA KUMA NUSARWA GAMAI ZIYARAR
wagga madda an tarjamata zuwa
nau o, i
kafofi
Full Description
- ZIYARAR MASALLACIN ANNABI MAI AL-FARMA TARE DA FADAKARWA DA KUMA NUSARWA GAMAI ZIYARAR
- GABATARWA
- Wuraren da aka yarda da Ziyararsu:
- Fadakarwa da kuma nusarwa ga mai niyyar ziyartar Masallacin Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-
ZIYARAR MASALLACIN ANNABI MAI AL-FARMA TARE DA FADAKARWA DA KUMA NUSARWA GAMAI ZIYARAR
Wallafar
Dr. Abdullahi Bn Naji Al-mikhlafi
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai
Gabatarwar
Godiya ga Allah wanda ya sanya Ziyarar Masallacin Annabinsa -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- daga cikin Manyan Ayyukan Ibada, kuma ya sanya Salati ga Annabi a cikinsa karin Darajoji, Kuma Sati da Aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad Mafi tsarkin Halittu, Kuma haka ga Alayansa da Sahabbansa da duk wadanda suka bisu da kyautaye har zuwa Ranar Mutuwa
Bayan haka
Yana farantamun in gabatar da wannan littafi (ZIYARAR MASALLACIN ANNABI MAI AL-FARMA TARE DA FADAKARWA DA KUMA NUSARWA GAMAI ZIYARAR) na babban Malamami Dr. Abdullahi Naji Al-Mikhlafi, wanda ya zo cikin saukin bayaninsa, kuma ya game komai cikin abunda ya kunsa, kuma ya kwaso mafi muhimmancin bangarori wadan da suka wajaba akan Mai ziyara ya kula da su a cikin Ziyararsa.
sai ya bayyana Ziyarar Shari'a da ingantacciyar Hanya don yi Sallama ga Annabi SAW, da Abokansa biyu -Allah ya yarda da su- da kuma wuraren da shari'a ta yarda a ziyarce su a Birnin Madina wajen Masallacin Annabi MargirmaKari kan wasu fadakarwoyi da kuma Nusarwa wadan da Mai ziyara yake bukatarsu, wadan da sukai daidai ingantacciyar Akida kan Turbar Manyan Magabata na Kwarai, wadan da aka gina su kan koyarwar Al-qurani da Sunnar Annabi; kuma saboda Muhimmancin wan nan littafi da abun da ya kunsa, don haka nake Wasiyyya da a buga shi da kuma yada shi, ina rokon Allah Madaukakin sarki Mai iko da ya anfanar da shi duk wanda ya karanta shiKuma ina farin cikin gabatar da godiyata mai kamshi da cikakken yabo ga Hukamar Mai Hidima ga Haraman nan guda biyu, Sarki Salman Bn Abdul'aziz Ali Su'ud- Allah ya dada Kare shi- da Yarima mai jiran gadonsa Mai Alfarma Sarki Muhammad Bn Salman Ali Su'ud -Allah ya dada tsare shi- kan abun da suke jibantar nauyin kulawa da ta wuce kan gaba ga wadan nan Haramai guda biyu masu Alfarma , da kuma gabatar da dukkan gudunmawa, da kuma gyara dukkan Hanyoyi, da kuma saukakaka dukkan abubuwa masu Wahala ga masu ziyararsuHaka godiya dai ta Musamman ga Baban Shugaba mai kula da Harkokin Masallacin Haramin Makka da kuma Masallacin Annabi, Maigirma Shiekh Dr. Abdulrahman Bn Abdul-aziz Al-sudais, kan abinda kan Kokarin sa Mai Al-barka wajen yin hidima ga Haraman nan guda biyu da kuma bada gudunmawa wacce bata yankewa ga Cibiyar da take kula da Umarni da kyakkyawan aiki da hani ga barin Mummuna, wacce take karkashin Babbar Cibiyar Kulawa da Masallacin Annabi
To Allah ya saka musu da kyakkyawan Sakamako, kuma Allah ya datar damu da su don Hidima ga Musulunci da Musulmai, Kuma tsira da Aminci ga Annabinmu Muhammadu da Alayansa da Sahabbansa baki daya
Aliyu Bn Salih Al-Muhaisini
Daraktan Cibiyar Umarni da kyakkyawan aiki da Hani da Mummuna wadda take karkashin Gamammiyar Cibiyar dake kula da al-amuran Masallacin Annabi
GABATARWA
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai
Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai kuma tsira da Aminci su tabbaat ga Shugabanmu Annabi Muhammad da Alayansa da Sahabbansa masu hasken dama
Bayan haka: yakai Dan uwana mai ziyara: Amincin Allah a gareka da rahamarsa da Alabarkatunsa, kuma Lale Maraba da kai a cikin Birnin Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-
Dan Uwana Mai Ziyara: ka godewa Allah Madaukakin Sarki kan cewa ya baka Lafiya kuma ya wadataka kuma ya datar da kai da iya halartar garin Manzonsa -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, to saboda Kasancewar Allah Maitsarki ya datar da kai da hakan don wasu da yawa Allah bai basu damar halartar ba duk da suna kwadayin hakan da kaunarsu da hakanTo idan ka isa Birnin Madina mai Haske, to ya wajaba ka sifantu da kuma ladabtuwa da ladaban Shari'a wadan da Annabin Shiriya ya kwadaitar da mu akan su -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- to cewa su ababan bukata ne ga Musulmi a kowane guri ya samu kansa amma fa sun fi karfafa a Birnin Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-Kuma ka godewa Allah Madaukakin Sarki wanda ya datar da kai da Ziyarar Masallacin Manzon Allah wanda yana daya daga cikin Masallatai guda Uku Mafifita da fadinsa -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi: "Ba'a nikar gari don tafiya sai zuwa wajen Masallatai guda Uku; Masallacin Harami da Masallacina wannan da Masallacin Baital Mukaddas" Bukhari da Muslim ne -Allah ya yarda da su- suka rawaito shi
kayi yabo ga Allah -wanda ya girma kuma ya daukaka- cewa ya datar da kai ziyarar Masallacin Annabi da Ziyarar Kabarin Annabinmu Muhammad -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- to abun da yake wajibi akanka ka tafi kan Turba daidaitacciya wacce ya Sunnantawa Al-Ummarsa kuma ya Shar'anta Musu waccan ziyarar kuma ya Kuma Magabata na Kwarai suka kasance a kanta -Allah yayi musu rahama
Dan Uwana Mai Ziyara Maigirma: idan kai niyyar halartar Masallacin Annabi Mai Al-farma to sai Kayi wanka sannan kayi Al-wala kuma ka sanya Turare kuma ka nisanci zuwa Masallaci da wari Mara dadi, kuma idan ka isa Masallacin sai ka shiga da kafarka ta dama yayin shiga, kuma ka ce lokacin shigarka:Da sunan Allah kuma tsira da Aminci su tabbata ga Manzon Allah, Ya Ubangiji kayi mun gafarar Zunubaina kuma ka bude mun kofofin rahamarka, ina neman tsari da Allah Mai girma da kuma fuskarsa Mai girma da ikonsa dadadde daga Shaidan abun nisantawa daga Rahama
Sannan sai ka fuskanci wajen Raudha mai girma kayi Sallah Raka'a biyu don gaisuwar Masallaci -in hakan ya yiwu- kuma idan ya kasance akwai cinkoso a can to kayi Sallah a kowane guri a cikin Masallacin maigirma, kuma ka nisanci kawo cikoso ga Musulmai da cutar da su, saboda haka bai halarta ba, kuma kai kazo ne Masallacin Annabi don samun Lada ba don daukan Al-haki ba
Sannnan sai ka nufi Kabarin Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- cikin Ladabi da Nutsuwa da kuma bi a sannu to idan ya Kasance akwai cinkoso to ka kiyaye wajen kawo cunkoso ga Mutane koda kuwa zaka dan koma da baya zuwa lokacin da babu cunkoso sosai, kuma ka kiyaye dai cewa hakan kar ya kasance bayan Sallolin Farilla kai tsaye saboda wancan lokacin cinkoso yana yawaita galibi, kuma ka kiyayi daga Murya saboda Allah ya hana bayinsa Muminai hakan inda yake cewa:Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba.Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma.Al-hujurat: 3Ibn Kasir Allah yayi masa rahama ya ce a cikinTafsirinsa"An hana daga Murya a wajen Kabarinsa -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- Kamar yadda aka hana a lokacin rayuwarsa SAW domin shi abun girmammawa ne yana raye haka ma yana cikin Kabarinsa, SAW kuma har abadan"Kuma Umar Bn Khattab -Allah ya yarda da shi- yaji Muryar wasu Mutane guda biyu a cikin Masallacin Annabi SAW suna daga Muryarsu sai ya ce: Ku Su waye? kuma daga ina kuka zo? sai suka ce: Mu mutanen Da'if ne sai ya ce: da ace ku 'yan gari ne da jikinku ya gaya muku, kuna daga Murya a Masallacin Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-Imam Al-bukhari -Allah ya yarda da shi:To idan ka isa gaban Kabarin Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- sai ka tsaya cikin Hankali da Nutsuwa kayi masa Sallama da fadinka:Amincin Allah a gareka Ya Manzon Allah da Rahamar Allah da AlbarkatunsaAmincin Allah a gareka Ya Annabin AllahAmincin Allah a gareka Ya zababben Halittun AllahAmincin Allah a gareka Ya Shugaban Manzanni kuma Jagoran Masu jin tsoron AllahNa shaida cewa kai tabbas ka isar da Sako, kuma ka bada Amana, kuma kayi Nasiha ga Al-umma kuma yayi Jahadi a tafarkin Allah Matukar kokarinsa, Allah ya saka maka da mafi Alkairin abun da ka Sakawa Annabi kan Al-ummarsa"Allahumma Salli Ala Muhammad, Wa'ala Aali Muhammad, kama Sallaita Ala Ibrahim, Wa ala Aali Ibrahim, Innaka Hamidun Majid. Allahumma Barik Ala Muhammad, Wa'ala Aaali Muhammad, Kama Barakta Ala Ibrahim, Wa'ala Aali Ibrahim, Innaka Hamidun Majid",
kuma kana da damar yin Sallama ba irin wannan sigar ba da wata sigar da Shari'a ta yarda da ita
Sannan sai ka matsa Kadan wajen Damanka kayi Sallama ga Halifan Manon Allah SAW Abubakar -Allah ya yarda da shi kana mai cewa:Amincin Allah a gareka Ya Abubakar Al-siddiq da Rahamar Allah da al-barkatunsa, Amincin Allah a gareka ya Halifan Manzon ALlah SAW kuma abokinsa a cikin Kogo su biyu, Allah yai Maka Sakamakon kan abunda kayiwa Musuluci da Musulmai mafi Alkairin sakamako, ko kuma abunda yayi kama da haka na sigogiSannan Ka Matsa kadan kuma wajen damarka kadan sai kayi Sallama ga Shugaban Muminai Umar Al-faruq -Allah ya yarda da shi- kana mai cewa:Amincin Allah a gareka Ya Umar Faruq da Rahamar Allah da al-barkatunsa, Amincin Allah a gareka ya Halifa na biyun Halifofi shiryayyu Allah yai Maka Sakamakon kan abunda kayiwa Musuluci da Musulmai zafi Alkairin sakamako, ko kuma abunda yayi kama da haka na sigogiDa wannan ne kuma Ziyararka ta Masallacin Annabi da Kabarinsa, -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- ta cika da abokansa guda biyu -Allah ya yarda da su-Kuma idan kai niyyar rokon Allah, ya kai Dan uwana Mai ziyara to ka fuskanci Al-kibla a ko ina kake a cikin Masallacin Annabi Mai girma kuma a kowane lokaci kake so dare ne ko rana, kuma ka zabi wurin da babu cinkoso saboda hakan shi ne mafi samun Nutsuwa gareka kuma yafi taro maka Hankalinka kuma shi ne mafi yawan Nutsuwa ga ZuiciyarkaKuma Ka roki Allah Madaukakin Sarki gareka da 'yan uwanka Musulmai Al-kairan Duniya da LahiraDan uwa mai ziyara Maigirma ka nisanci yin Ta'addanci a cikin Addu'a kuma hakan yana da Salo salo Masu yawa daga cikin su: Ka roki Wanin Allah ka nemi wata bukata a wajensa ko ka nemi agajinsa, saboda hakan ya kore Umarnin Allah da manzonsa SAW, wannan ma shi ne Shirka da Allah; Saboda Allah ya hanaka Addu'ar waninsa Allah Madaukakin Sarki ya ce:Kar ku kira Allah tare da wani,Surat Al-Jinn 18kuma Allah Madaukaki ya ceKuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Makusanci ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu.Bakara: 186kuma Allah Madaukaki ya ceKuma wãne ne mafi ɓata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda da bã zai karɓa masa ba, bar Rãnar Kyama, alhãli sũ (waɗanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiransu?Al-ahkaf: 5Kuma a cikin Hadisin Bn Abbas -Allah ya yarda da su- fadinsa -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-"Idan aka roka to ka roki Allah, kuma idan aka nemi taimako to ka nemi taimakon AllahImam tIRMIZI -Allah ya yarda da shi ya rawaito shi
A'a ka ce: Ya Ubangiji ka sanya Annabinka ya cece ni, Ya Ubangiji kada ka haramta mun ceton Annabinka SAW,Kuma kayi Tawassuli ga Allah SWT da Soyayyarka ga Manzonsa SAW da kuma biyayyarka gare shi haka da baki dayan Ayyukanka kyawawa.
Kuma kasani ya kai Dan'uwa na Mai ziyara cewa wannan Ziyarar ita ce koyarwarwar Magabata na kwarai -Allah Madaukakin Sarki yayi Musu Rahama
Wuraren da aka yarda da Ziyararsu:
A cikin garin Madina wajen Masallacin Annabi Mai Daraja
1-Al-Baki'a: ita ce Makabartar Mutanen Madina wacce aka Bizne mafi yawa daga cikin Sahabbai da Tabi'ai da kuma Magabata na Kwarai Allah ya yarda da su saboda Manzon Allah ya kasance yana Ziyartar Ma'abota Baki'a kuma yana yi musu sallama da kuma Addu'a a gare su
To idan ka tafi Zuwa Makabartar Baki'a sai kayi Sallama a gare su kuma ka ce kamar yadda Annabinmu yake cewa: -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-Amincin Allah a garelku ya ku Mazaunan wannan gida na Muminai da Musulmai, Muma in Allah ya so muna nan zuwa, ina rokon Allah sauki mu da kuImam Muslim ne ya rawaito shi -Allah ya ya yi masa RahamaKuma kayi Addu'a ga Mutanen Bakia' ka nema musu gafara wannan ita ce Ziyarar da Shari'a ta yarda da itaKuma ya kai Dan uwana kiyayi taka Kabari ko ka zauna a kansa saboda yazo daga Manzon Allah SAW yayi hani kan hakan da fadinsa:"Kada kuyi salla zuwa Kabari kuma kada ku zauna akansu"Imam Muslim ne -Allah ya yi masa Rahama ya rawaito shi
Ka kiyayi shafar Kabari, ko sunbantarsa ko kuma diban wani abu daga cikin Kasarsa ko rokon na cikin su saboda ba zasu iya cutar da kai ba ko anfanarwa
2-Shahidan yakin Uhudu: shi ne yakin da ya faru a tsakanin Musulmai da Mushirikai, wanda yai sanadiyyar Shadar Sahabbai Saba'in -Allah ya yarda da su- kuma Annabi ya Kasance yana ziyartar Shahidan Uhudu yana musu sallama kuma yana musu Addu'a kuma ka sani cewa wadan nan Shahidan an kashe su ne wajen kare Addini kuma yana daga cikin hakkinsu akan mu muyi musu Addu'a kuma mu nema musu gafara baki dayansu, to idan kaje ziyararsu kayi musu Sallama kamar yadda kai Sallama ga Mutanen Baki'a da wasun su na Mamata
3- Masallacin Kuba kuma Shari'a ta yarda da ziyararsa, kuma hakika Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- yan zuwansa duk Sati akan abin hawa ko kuma a kafa sai yayi Salla a cikinsa kuma duk wanda ya je shi kuma yayi Sallah a cikinsa to yana da ladan Umra, Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- ya ce:"Duk wanda ya yi tsarki daga gidansa sannan ya taho Masallaci Kubaa sai yayi salla a cikinsa to yana da ladan Umra"Imam Ibn Majah-Allah ya yarda da shiya rawaito
To kada kayi wa kanka asarar wannan Al-khairi ya kai Dan uwana
Fadakarwa da kuma nusarwa ga mai niyyar ziyartar Masallacin Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-
Dan Uwana Maigirma Mai Ziyara
Ka kiyaye wajen yin Zikirorin da suka zo wajen shigarka ko futarka daga Masallacin Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- ko kuma kowane Masallacin daban
"Kada ka Kuskura ka sunkuya wajen yin Sallama ga Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-ka dai tsaya cikin Sannu sannu da ladabi da Nutsuwa
Kada ka shafi Bangwaye ko shigaye ko kofofion Masallacin Annabi ko Munbarin ko Haraba ko tagogi da suke kewaye da Dakin Manzon Allah don neman Al-barka, saboda hakan bai halatta ba
Imam Al-nawawi -Allah yayi masa rahama ya ce: a cikin littafin "Al-Majmou'a" (8/257) game da shafar Kabari da Hannu: "Kuma duk wanda ya darsu a Ransa cewa shafa da Hannu da Makamantansu yafi kawo Al-barka to yana daga cikin Jahilcinsa da gafalarsa cewa Al-barka tana cikin dacewa ne da bin Shari'a kuma ta yaya zai nemi falala cikin sabawa daidai" Nan Maganar ta kare
Ka sani ya kai dan Uwana Mai ziyara cewa Ziyara batada wani lokaci kididdigagge: Mai tsawo ne ko gajere ko kuma da wasu salloli kididdigaggu, Masu yawa ne ko Kadan kuma yana daga cikin Kusa kurai da suke faruwa ga wadanda suke ziyartar Masallacin Annabi cewa su dole sai sunyi wasu salloli kididdigaggu kodai Salloli Arba'in ko mai kama da haka kuma wani yana matsantawa kansa yana dorawa wadanda suke tare da shi, kuma wan nan kuskure ne; saboda bai tabbata daga Annabi ba -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- iyakance wasu Salloli wadanda Mai ziyara zai Sallace su a Masallacinsa, saboda haka ka Sallaci abunda ya Sawwaka na Salloli Masu yawa ne ko kadan ne
Kuma Hadisin da yake kayyade Sallah Arba'in a Masallacinsa kuma wanda ya zo a cikin Musnad din Iman Ahmad daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-"Duk wanda yayi Salla Araba'in a masallacina, ko salla daya bata shige shi ba za'a rubuta masa kubuta daga Wuta da kuma tsira daga Azaba, da kubuta daga Munafunci"To wannan Hadisin yana da RauniKuma wani Hadisin wanda Tirmizi ya rawaito shi daga Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- cewa shi ya ce:"Duk wanda yayi Salla Kwana Arba'in saboda Allah a cikin Jama'a yana riskar kabbarar farko za'a rubuta masa kubuta daga abu biyu: Kubuta daga Wuta, kubuta daga Munafunci"To wannan Hadisin ya inganta daga Manzon ALlah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-
Saboda Haka ina maka Nasiha kai Dan uwana Mai ziyara cewa ka Mori wannan Kubuta kuma wannan duk daya ne kayi aiki da wannan Hadisin a nan ko a garinku
Asali dai cewa Mai Addua zai fuskanci Al-kibla ne lokacin Addua, kuma wasu Mutane suna tsayawa a bangarororin Masallaci Annabi, suna masu daga Hannayensu suna rokon Allah , suna masu fuskantar Kabarin Annabi, kuma wannan aiki ba'a sanshi ba a wajen magabatan kwarai ko kuma jagororinta da Malamanta Masu Daraja, ku kiyayi wadan nan Ayyuka kuma ya tsaya iya inda Sahabban Annabi suka tsaya, da wadanda suka biyo su da Magabata Muminai na Kwarai, saboda Addu'a Alkiblarta Ka'aba
Bai halatta rubuta wasiku da a cikinsu akwai rokon Annabi SAW da sanya su a kan tagogin Dakinsa ko Raudha ko kuma a cikin kowane bangare na Masallacin Annabi saboda hakan abun ki kuma bai halatta ba, kuma haka kuma daukarsu daga garuwa daban daban da kuma isar da su zuwa Masallacin Annabi
Bai halatta ba yin dawafi a Kabari Mai tsarki, saboda Dawafi Ibada ne bata halatta ba sai a Dakin Allah Maigirma don girmamawa da kuma bin Umarnin Allah Madaukakin Sarki
Ka kiyaye ya kai Dan uwana Mai ziyara wajen karuwa da Ibadu da Ayyuka nagari tsawon Zamanka a Madina Mai Haske kuma ka kiyaye sallolin Farilla a cikin Jam'i a Masallacin Annabi kuma ka yawaita Sallolin Nafila a Raudha -in hakan ya samu- saboda ya zo daga Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- ya ce:
"Tsakanin gidana da Munbari na Dausayi ne daga cikin Dausayin Al-janna"
Bukhari da Muslim ne -Allah ya yayi musu Rahama- Suka Rawaito shi
Kuma kebanceta da wannan sifar banda waninta da wannan Nahiyoyin Masallaci yana nuna Falalarta da kuma fifikonta, ka kiyaye kan Sallar Nafiloli da Anbaton Allah da Karatun Al-qura'ani a cikinta ba tare da turmutsutsu da Mutane ba ko cutar da Masu Sallah, saboda duk wanda yabar wani abu saboda Allah to Allah zai Musanya Masa da Mafi Al-kairi da shi
Amman Sallar Farilla idan yayi ta a Sahun gaba tafi lada saboda fadin Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-"Mafi Alkairin Sahun Maza Na farkonsa, kuma mafi Sharrin su na Karshen su"[Muslim -Allah ya yarda da shi- ya rawaito shi]
Kuma Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce:
"da Mutane sun san abun da ake samu a kiran Salla da Sawun Farko, sannan kuma bai same shi ba har sai sun yi kuri'a a kansa da sun yi kuri'ar"
Bukhari da Muslim ne -Allah ya yarda da su- Suka Rawaito shi
Kuma Ma'anar: "Suyi Kuri'a" zasu jefa kuri'a
Kuma ka sani cewa lallai Salla daya a cikin Masallacin Annabi tafi salla Dubu a wani Masallacin da ba shi ba na sauran Masallatai sai dai Masallacin Harami saboda Sallah daya a cikinsa tafi sallah Dubu a waninsa, Manzon Allah -tsira da amincin Allah a gare shi-"Sallah daya a cikin Masallaci na wannan yafi sallah Dubu a waninsa, sai dai Masallacin Harami da kuma Sallah a Masallacin Harami tafi Sallah Dubu a waninsa"Ibn Maja da Ahmad -Allah ya yarda da su- suka rawaito shi
Kuma kayi kokarin yawaita Karatun Al-Qur'ani da anbaton Allah Madauakin Sarki da gode masa da yabonsa da Sadaka da kuma I'atikafi da Masallacim Annabi in hakan ya sawwaka.
"Idan wani abu ya shigemaka duhu na abubuwan Addininka to sai ka tambayi Malamai daga cikinsu akwai Malaman da suke koyarwa a Masallacin Annabi don aiki da fadin Allah Madaukain Sarki"Ku tambayi Ma'abota Sani in ku kunkasance baku sani ba"Al-anbiyaa: 7
"Ku tambayi Ma'abota Sani in ku kunkasance baku sani ba"
Al-anbiyaa: 7
Ko kuma ka garaya zuwa wayoyin "Cibiyar harkokin fadakar da Masu tambaya" wanda suke da yawa a wajan kofofin Masallacin Annabi a wasu bangarorin sa kuma aka samu da yardar Allah, amsar abun da ya shige maka duhu na Al-amuran iyararka da Umrarka da Hajjinka
Kayi kokarin halartar Karatukan Ilimi da ake yi wanda Manyan Malamai da suke koyarwa a Masallacin Annabi suke yi don karuwa a cikin Addininka kuma ko ka shiga cikin fadinsa -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi-"Duk wanda yaje Masallacina wannan bai je ba sai don Alkairi da zai koyeshi ko zai koyar da shi to shi yanada Matsayin Mai Yaki ne a tafarkin Allah, kuma duk wanda ya je don wanin hakan, to shi yana matsayin Mutumin da yake kallon kayan waninsa"Imamai hududu ska rawaito shi: Ibn Majah da Ahmad da kuma Hakim a cikin Al-mustadrak -Allah yayi musu rahama baki dayansu
"Duk wanda yaje Masallacina wannan bai je ba sai don Alkairi da zai koyeshi ko zai koyar da shi to shi yanada Matsayin Mai Yaki ne a tafarkin Allah, kuma duk wanda ya je don wanin hakan, to shi yana matsayin Mutumin da yake kallon kayan waninsa"
Imamai hududu ska rawaito shi: Ibn Majah da Ahmad da kuma Hakim a cikin Al-mustadrak -Allah yayi musu rahama baki dayansu
Kada ka manta Dan uwana Mai neman Ilimi da Ziyarar Dakin Karatun Masallacin Annabi a babban Dakintamai Yalwa wanda ya ke sama bangaren Yamma na Sabon ginin da Mai yiwa Haramai Hidima Sarki Fahad ya gina -Allah yayi masa rahama- kuma ana hawa ne ta hanyar Matattalar Lantarki Mai lamba (10) saboda zaka samu abun da zai anfanar da kai a cikinta
in kuma ka kasance Mai Sha'awa da kula da litattafan da ba'a buga ba to ka ziyarci Bangare na Musamman a wajen kofar Usman Bn Affan -Allah ya yarda da shi- kuma yana nan a karshen Karin ginin da Saudia tayi na farko a tsakiyar Masallacin Manzon Allah
Kamar yadda kuma cewa akwai Cibiyar samar da abubuwan Sauti da na gani na fadakarwa a kofa mai lamba 17H a kofar shiga ta Umar Bn Khattab -Allah ya yarda da shi- suna aikin nadar Darussa da hudubobi da Sallolin Masallacin Manon Allah ga masu Ziyara kyauta bayan ka kawo Kaset din ka da babu komai a ciki ko kuma CD ko kuma abun bayanai bayanai kuma kamar yadda yake akwai Dakin Karatun Mata a wajen sallar Mata na bangaren Gabas a kofa mai lamba ta 24 da kuma wurin Sallar Mata na bangaren yamma mai lamba 16 da kuma Dakin sauraron sauti na Mata a kofa mai lamba 28
yi gaba kuma ka cika sahun farko sannan mai binsa, kuma kada ka zauna a kofar shiga ko hanyar wucewa ko kuma Matattakala ko kofofon shiga, saboda inkai haka ka toshe Hanyar shiga Masallacin wanda hakan zai tilastawa Mutane yin Salla a wajen Masallaci tare da kuma yalawar wurin a cikin Masallacin.Kayi Kokari kai da 'Yan Uwanka Masu sallah kan ku cika Sahu, kuma ya hadu wani da wani kuma yayi ta jeruwa a bayan ku na sauran Sahun har Sahun ya cika kuma ya jeru, kuma masallacin ya dauke Mutane a cikinsa
Kayi Kokari kai da 'Yan Uwanka Masu sallah kan ku cika Sahu, kuma ya hadu wani da wani kuma yayi ta jeruwa a bayan ku na sauran Sahun har Sahun ya cika kuma ya jeru, kuma masallacin ya dauke Mutane a cikinsa
Kuma idan kayi niyyar yin Sallah a Sahun Farko ko a Raudha to kayi sammakon zuwa Masallacin Annabi, kada kazo a Makare kuma ka rika tsallake Mutane kana taka su kana tsallaka Sallar Mutane kana cunkushe hanaya, saboda hakan akawai cutar da Masu Sallah, kuma cutar Musulmi bai halatta ba
Kuma Annabi yaga wani Ranar Jumu'a yana tattaka wuyan Mutane don ya shiga sahun gaba, kuma Annabi -tsira da amincin Allah a gare shi- ya Kasance yana Huduba akan Mumbari sai ya yanke Hudubar kuma ya ce da shi:"Ka zauna hakika ka cutar, kuma ka zo a Makare"Ibn Maja da Ahmad -Allah ya yarda da su- suka rawaito shi
"Ka zauna hakika ka cutar, kuma ka zo a Makare"
Ibn Maja da Ahmad -Allah ya yarda da su- suka rawaito shi
Ai ka cutar da Mutane da taka musu wuyayen su, kuma ka wahalar, ai ka zo a Makare kuma ya kamata ace kazo da wuri indai kana son shigewa gaba kada ka makara
Kada ka wuce ta gaban Masu Salla, hakika Annabi ya yi hani cikin fadinsa:Mai wuce wa ta gaban masallata da ya san abin da ke kan shi na zunubi, to ya tsaya arba'in shi ne mafi alkhairi da ya wuce ta gaban mai sallahAbu Al-nadhr ya ce: bansani ba ya ce kwana Arba'in ne ko wata ko shekaraImam Albukhari ne ya rawaito -Allah ya yarda da shiImam Ibn Hajar -Allah ya yarda da shi ya ce: a cikin Fathulbari: 1/585Fadin sa da ya tsaya Arba'in yana nufin cewa mai ketarawa da ya san nauyin Alhakin da ya dauka da ketara sallar mai Sallah da ya zabi ya tsaya tsawon lokacin da aka fada don kada ya dau wancan zunubin
Mai wuce wa ta gaban masallata da ya san abin da ke kan shi na zunubi, to ya tsaya arba'in shi ne mafi alkhairi da ya wuce ta gaban mai sallah
Abu Al-nadhr ya ce: bansani ba ya ce kwana Arba'in ne ko wata ko shekara
Imam Albukhari ne ya rawaito -Allah ya yarda da shi
Imam Ibn Hajar -Allah ya yarda da shi ya ce: a cikin Fathulbari: 1/585
Fadin sa da ya tsaya Arba'in yana nufin cewa mai ketarawa da ya san nauyin Alhakin da ya dauka da ketara sallar mai Sallah da ya zabi ya tsaya tsawon lokacin da aka fada don kada ya dau wancan zunubin
Kayi Kokarin yin tsafta da sanya Turare da gusar da Abubawan da ke kawo Warin jiki da Tufafi, saboda Mala'iku suna cutuwa da abunda Mutane suke Cutuwa
Ka kiyaye tsaftar Masallaci da filinsa, kuma kada ka cutar da 'yan Uwanka masu sallah a Masallacin da Tofar da Miyau ko Majina a kan daben Masallacin Manzon Allah ko Bangonsa ko kuma filinsa, kuma ya kamata kaji girman wurin a ranka, kuma ka sani cewa tofar da Miyau a Masallaci Babban laifi ne Kamar yadda Annabi -tsira da amincin Allah a gare shi- ya fada:"Kaki a Masallaci Laifi ne kuma kaffararsa ka burne shi"Bukhari da Muslim ne Allah yayi musu Rahama- Suka Rawaito shi
"Kaki a Masallaci Laifi ne kuma kaffararsa ka burne shi"
Bukhari da Muslim ne Allah yayi musu Rahama- Suka Rawaito shi
Kada ka bar 'Ya'yanka suna wasa da guje guje a Masallaci ko suna ta ihu, saboda hakan ya futa daga ladabi a Masallacin Annabi SAW
Ka nisanci Wuraren Cunkoso ka bi ta wuraren da yake da yalwa a Masallacin kuma ka sani cewa Falalar Sallar a Masallacin ana samunta a kowane wuri kayi Sallar a cikinsa
Dan uwana Mai Ziyara ka dan huta kadan bayan kayi Salloli, kuma kayi Zikirorin da suka zo bayan Sallah, kuma kada ka fara Sallar Nafila daga yin Sallar Farillah kai tsaye, Musamman a wurare da kuma lokutan cunkoso don bada dama ga Masu Uzuri da Masu son futa da wuri da su futa don kada ka gamu da damuwar Masu tsallaka Masu Sallah
Na hore ka da da sannu sannu da rashin gudu da turereniya wajen bude Labulen da ake sakawa don Sallar Mata a Raudha Mai tsarki
Kada ka fitar da Qura'anai daga cikin Masallacin Annabi don Wakafine a ciki
Kada ka jingina da kwabobin saka Quranai, kuma kada ka ajiye Takalmi a gefensu kuma kada ka rika tsallakasu don girmama littafin Allah Madaukakin Sarki
Wajen ajiye Takalma a cikin wuri ne nasa ya kamata ka san wancan wuriKuma hakika anyiwa baki dayan akwatuna lambobi wajen sanya Takalma a ciki ko akai, babu abunda ya rage sai kawai kasan wadan nan lambobi don inka dawo daukansa da sauki da babu wuya
Kuma hakika anyiwa baki dayan akwatuna lambobi wajen sanya Takalma a ciki ko akai, babu abunda ya rage sai kawai kasan wadan nan lambobi don inka dawo daukansa da sauki da babu wuya
Ka sani ya kai Dan uwana Mai ziyara cewa Masallacin Annabi da waninsa daga cikin Masallatai don an tanadesu don Ibada kada kasanya shi wajen Bacci ko Bara ko cigiyar abunda ya bace
Kada ka yi anfani da fanfuna ko abubuwan da aka ajiye zamzam wanda aka tanadi don sha wadanda suke ko ina a cikin Nahiyoyin Masallaci don yin Alwala, kuma kada kayi anfani da shinfudun Masallaci a matsayin matasai ko abun lulluba
Ka kiyayi Shinfida da kwanciya a filin Masallacin Annabi Maigirma
An hana Shan taba a Filayen Masallacin Annabi da kewayensa, kuna ya wajaba ga wanda Allah ya jarrabeshi da da shanta ya kaskantar da kansa ga Allah Madaukakin Sarki a Masallacin Manon Allah SAW kan Allah ya datar da shi da barin ta, kuma ya sani cewa Malamai sunyi fatawar Haramcin saidata da shanta saboda hakan mai shanta yayi sabo, kuma kai Dan uwana kazo ne don karin neman lada, ka kiyayi karin Sabo
Baki dayan kofofin Masallacin Annabi suna da suna kuma an musu lamba, don haka kai dan uwana mai ziyara ya wajaba kasan Suna da Lambar Kofar da ka shigo ta ita don ka futo ta nan yayin futowa daga Masallaci
Idan kaga cinkoso a kofofin to ya kamata ka tsaya a Masallaci kadan har cunkoson ya ragu
Kada ka manta yayin futa ka gabatar da kafarka ta hagu kuma ka ce yayin futa daga Masallacin:"Da sunan Allah, Allah kayi salati da Aminci ga Annabi Muhammad, Ya Allah ka gafarta mun Zunubaina, kuma ka budemun kofofin falalarka"Manyan Limamai suka rawaito shi: Tirmizi Ibn Majah, da kuma Ahmad kuma yana da Madogara a cikin Sahihin Imam Muslim -Allah yayi rahama ga baki daya-
"Da sunan Allah, Allah kayi salati da Aminci ga Annabi Muhammad, Ya Allah ka gafarta mun Zunubaina, kuma ka budemun kofofin falalarka"
Manyan Limamai suka rawaito shi: Tirmizi Ibn Majah, da kuma Ahmad kuma yana da Madogara a cikin Sahihin Imam Muslim -Allah yayi rahama ga baki daya-
Ina maka Nasiha da ka dauki Katin dake dauke da Masaukinka da ka sauka cikinsa,; don yin anfani da ita idan baka gane Masaukinka ba
cikin halin faruwarrashin lafiya a Masallacin Manzon Allah kana bukatar agajin gaggawa, yi saurin sanar da masu kula da Masallacin Annabi ko kuma kowane ka gani yana dauke da Over Over, da kuma masu aiki
Ana bude saman Masallacin Annabi Mai Alfarma don yin Sallar Jumu'a tsawon Shekara da lokuta biyar na Ibada, to idan kaga cunkoso ya kai Dan uwana Mai ziyara a kasan Masallacin Annabi to ka hau Saman Bene zaka samu Wuri yalwatacce a can da yardar Allah
Kuma akwai kekuna ga Masu Lalura da Tsofaffi ana bayar da su ga masu bukata a wajen Masu kula da kofofin shiga Masallacin Annabi a kofa mai lamba 8 a bangaren yamma na Masallacin Annabi don su hau daga Masaukansu ko a Motocinsu zuwa Masallacin Annabi tsawon zamansu
Kada ka shige gaban Liman yayin salla a lokutan cunkoso a filin da ke gaban (Massalacin) don ka kaucewa sabanin Malaman fiqhu
Kayi kokarin anfanuwa da Nusarwar masu kula da Masallacin Annabi wadanda aka saka su don hidimarka da saukake hanyoyin hutunka
Ka yawaita Kankan da kai da Addu'a da jaddada Alkawarinka ga Allah kan tuba na gaskiya, kuma kasani cewa hakikanin Ladabi ga Allah shi ne Sonsa da girmama shi, da kuma tsarkake Ibada gare shi, kuma hakikanin Ladabi ga Manzon Allah shi ne bin Sunnarsa da tafiya kan koyarwarsa da aikin Sahabbansa bayansa kuma cikin yi masa ladabi bayan Wafatinsa -tsira da amincin Allah a gare shi-
A karshe: ina maka Nasiha Dan Uwana Mai Ziyara da ka yawaita Salati ga Annabin mu Muhammad -tsira da amincin Allah a gare shi- saboda ya o daga Amr bn Al-as -Allah ya yarda da shi- cewa shi yaji Manzon Allah -tsira da amincin Allah a gare shi- ya ce:"Duk wanda yayi mun Salati to Allah zai Masa salati goma da wannan Salatin nasa"Muslim ne ya rawaito shi da waninsa
"Duk wanda yayi mun Salati to Allah zai Masa salati goma da wannan Salatin nasa"
Muslim ne ya rawaito shi da waninsa
Kuma ka yawaita Zikiri da aka samo daga Annabi, da kuma Kasakantar da Kai ga Allah kuma ka kama Kafa da shi, saboda kana wurin da ake saka ran amsa Addu'o'i a cikinsa, kuma kada ka Manta da Iyayenka da 'ya'yanka da Iyalanka a cikin Addu'arka haka 'Yan Uwanka Musulamai a ko'ina suke
Tsira da Aminci su tabbata ga Annabi Amincin Allah su tabbata a gare shi da Alayansa da Sahabbansa ka Amince su Amincewa.
ZIYARAR MASALLACIN ANNABI MAI AL-FARMA TARE DA FADAKARWA DA KUMA NUSARWA GAMAI ZIYARAR 1
Gabatarwar................................................................................................................................ 1
GABATARWA................................................................................................................................ 1
Wuraren da aka yarda da Ziyararsu:................................................................................................ 3
Fadakarwa da kuma nusarwa ga mai niyyar ziyartar Masallacin Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- 4